Showing 72001 words to 75000 words out of 81712 words

Chapter 25 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf

lokacin da ta furta

"Ba ya iya tafiya ne?" Ta faɗa tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki na bayyana cikin muryarta.
Ba tare da kawo komai a ranta ba Maama ta ce

"Wallahi kuwa, kin ga dai ikon Allah." Wani irin bugawa zuciyar Umma ta shiga yi fat!fat!fat! Ba
za ta iya jurewa ba, don haka jiki duk a sanyaye ta ce

"Kenan har tsawon wane lokaci zai ɗauka yana zama kan kujerar nan?" Tana ci gaba da
taimaka masa ɗin dai ta ce

"Har zuwa lokacin da Allah Ya nufa. Su kansu likitocin ba su sani ba, sun dai ba mu tabbacin
idan Allah Ya yarda watarana zai iya miƙewa a kan ƙafarsa. Shi ne ma dalilin da ya sa Abeeyn
Tareeq yake so a yi auren daga zarar an sallame shi, kin ga daga an ɗaura aure sai Jawahir ta
ci gaba da kula da shi."
Wani irin kuka mai ƙarfi Jawahir ta fashe da shi, tana jin yadda ilahirin jikinta ke karkarwa. Kawai
sai ta zube a kan gwuiwoyinta tana ci gaba da raira shi. Maama ta kalle ta cike da tausayi, don
ta san kukan na tausayin halin da Tareeq ya tsinci kansa a ciki ne. Duk da ba ta sake jin wata
magana daga bakin Umma ba, ba ta damu ba, ta shiga tura Tareeq zuwa toilet don ya ɗauro
alwala. Shi dai bai ce komai ba, bai kuma nuna alamar yana tare da su ba, duk da yadda cikin
zuciyarsa yanayin yadda Umma ta yi magana ya shigar da shi wani yanayi na kokwanto da
kuma fargaba. Komawa Umma ta yi kawai ta zauna a kan gado idanunta a kan Jawahir. Shiru
ba tare da ta ce komai ba, take ci gaba da kallon ta. Ta kasa furta komai, ta kasa ko da
ƙwaƙwƙwaran motsi ne. Ita ta haifi Jawahir, ta kuma fi kowa sanin halinta. Wannan kukan da
take, daga ita Jawahir ɗin, sai kuma ita suka san na mene ne.

Suna yin Sallahr Maghrib suka bar asibitin, bayan sun yi sallama da Maama a gaggauce. Shi
dai Tareeq bin su kawai ya yi da kallo, don ba ƙaramin mamaki yanayin yadda suka fita daga
asibitin ya ba shi ba. Ita kuwa Maama ba ta kawo komai a ranta ba, ta ci gaba da harkokinta.


... "Toh shi ke nan, amma kin san abin da za a yi?" Maami da ke riƙe da waya kare a kunnenta
ta faɗa bayan ta nemi waje ta zauna. Daga can ɓangaren aka ce

"A'ah."

"Kin san halin 'yar taki, ba za ta taɓa yarda da auren haɗi ba. Saboda haka ki turo yaron ya zo
da niyyar ya zo gaishe ni, daga nan zan san yadda za a yi su haɗu. Bayan ya tafi sai na sanar
da ita ya nemi da a ba shi numberta. Kin fahimci fa'idar yin hakan?" Jinjina kai matar ta yi kamar
Maamin na gabanta kafin ta ce
"Ehh, na gane. Hakan kuma ya yi matuƙa, Allah Ya haɗa mana kansu."

"Ameen." Maami ta amsa da hakan. Daga haka ba su ƙara wasu mintuna masu yawa ba, suka
yi sallama. Murmushi Maama ta saki tana kallon Maman Abdoul da ke zaune kujerar da ke kusa
da tata.

"Barkan ki da wannan lokacin Madam."

"Barka dai Hajiyata.. Wai Sultanah ake nema wa abokin haɗi?" Ta haɗe gaisuwar da tambayar
ta yi su lokaci guda. Jinjina kai Maami ta yi kafin ta ce

"Ita fa. Amma ki yi a hankali kar ta ji. Kin san halin Sultanah."

"Na sani kam. Amma me zai hana tun da ga na gida a tafi wani wajen? Wallahi da mun haɗa ta
da Abdoul. Ina son yarinyar wallahi, ko don nutsuwarta." Girgiza kai Maama ta shiga yi kana ta
ce bayan ta yi murmushin yaƙe

"A'ah ke kam, wani irin haɗi kuma tsakanin Abdoul da Sultanah?"

"Wallahi kuwa ƙawata, na ɗauka kamar sai ya fi koh?" Sake girgiza kai Maami ta yi ta ce

"Toh ai kin ga mun riga mun gama magana da Hajiya Ati, da ba mu yi magana ba sai a yi yadda
kika faɗa ɗin." Ɗan jujjuya kanta Maman Abdoul ta yi sannan ta ce

"Toh hakan ma ya yi. Allah Ya tabbatar da alkhairi." Sai a lokacin sannan Maami ta saki
murmushi tana faɗin

"Ameen, ƙawata."


... Gyara zamansa Abeey ya yi, kafin ya ɗan sauke ajiyar zuciya. Dukka hankalin 'yan ɗakin sai
ya dawo gare shi. Sai da ya gabatar da addu'a sannan ya soma faɗin

"Wato dalilin haɗa wannan taro da na yi ba komai ba ne, face don na sanar da ku ɗaurin auren
Tareeq da za a gabatar da shi ranar juma'ar nan mai zuwa idan Allah Ya yarda. Ba kuma shi da
kowa ba face 'yar'uwarsa Jawahir. Muna fatan Allah Ya tabbatar da alkhairi, Ya kuma kaɗe
dukkanin abin ƙi. Idan wani na da magana zai iya yi."
"Toh, Allah Ya amsa addu'o'in nan, sannan kuma Ya yi muku albarka gaba ɗaya. Ni kam me ya
kamata na ce? Bayan godiya ga Allah. Tun da ga shi jikokina biyu suna ƙoƙarin auren junansu.
Allah Ubangiji Ya sanya albarka." Dada ji ta faɗa, har cikin muryarta farin cikin da take jin ta ciki
na bayyana.
"Ameen." Maama ta faɗa tana murmushi.

Wani banzan kallo Umma take watsa wa Jawahir daga inda take zaune. Duk da sanin halin 'yar
tata, amma ko babu komai ta san za ta ji kunyar buɗe baki ta yi magana, musamman saboda
kwarjinin Abeey. Amma ya za su yi? Ya zame musu dole su magantu. Ita dai Jawahir ta rasa ta
inda za ta fara. Shin me za ta furta kai tsaye ba tare da wani kwane-kwane ba, wanda ko ba ta
yi bayani ba za a fahimci abin da take nufi? Tabbas ta san tana son Tareeq, ba kuma don komai
ba sai don kyawunsa, kyawun surar da Allah Ya ba shi. Tafiyarsa, komai nasa su ne suke burge
ta, ko kuma ta ce su ne take so. Toh yanzu kuma ga shi babu ƙafa, yana zaune ne a kan kujera,
ya zama gurgu, mara ƙafa. Kenan me za a kira shi? 'Musaki?' Ta ji zuciyarta ta yi saurin ba ta
amsa. Ta runtse idanunta tana jin yadda zuciyarta ke ci gaba da bugawa. Ke nan duk yadda ta
tsarawa rayuwarta hakan ba zai yiwu ba? Wato suna nufin ta auri Tareeq a yadda yake a
yanzun, ke nan me za ta je yi gidan auren? 'Bauta' Ta sake jiyo hakan a cikin kwanyarta. Tuni
har ta fara hasaso kanta a cikin gidan Tareeq. Duk da kayan alatun da ke gidan, ta san muddin
ta shiga gidan nan tata ta ƙare. Sai dai ta lalace a banza a wofi wajen kula da nakashashshshen
mijin da ake ƙoƙarin liƙa mata. Ita ba ta san da gaske ba shi take so ba, ƙirar jikinsa take so ba
sai yanzu. Yadda kuma ta ji zuciyarta ta yi na'am da hukuncin da suka yanke ita da Ummanta
ya ƙara tabbatar mata da hakan. Don haka cikin ƙarfin hali, ta tattaro jarumta ta afawa kanta. Ta
haɗiye tsoron da take ji, kafin ta runtse idanunta na tsawon wasu sakanni, kana ta buɗe. A
hankali ta buɗe bakinta da ƙyar ta soma faɗin

"Abeey don Allah ka yi haƙuri, amma ba zan iya auren Yah Tareeq a halin yanzu ba." Gaba
ɗaya mutanen ɗakin kallon ta suke yi cikin matuƙar tashin hankali, idan ka cire Umma. Cikin
matuƙar mamaki Maama ke ci gaba da kallon ta, tana jin abin kamar wani wasan yara. Cikin
ƙarfin hali ta furta
"Jawahir, kin san me kike faɗa kuwa?" Ta faɗa jikinta a matuƙar sanyaye, wanda ya ja har

muryarta ma a sanyayen take. Shiru Jawahir ta yi, ta kasa ɗaga ido ta kalli Maaman. Sam
Maama ba ta yi tunanin za ta sake jin wata magana daga bakin Jawahir ba, duk kuwa da ita ta
tambaye ta. Amma sai ta ji ta ce

"Eh Maama. A yi haƙuri don Allah."
Wani irin kallo Sultanah da Hidaya suke bin Jawahir da shi. Gaba ɗayansu sun kasa furta
komai. Ganin abin suke kamar almara, ko kuma shirin film. Anya kuwa Jawahir ɗin ce? Jawahir
dai Jawahir masoyiyar Yah Tareeq? Cike da ƙarfin hali, da kuma ƙaryata abin da kunnuwanta
suka jiye mata Dada ji ta ce bayan ta sauke duka idanunta a kan Umma.
"Maimunatu, kin ji abin da yarinyarki take faɗa kuwa?"

Ɗaga idanunta Umma ta yi ta kalli Dada ji. Karo na farko da ta fara kallon Dada ji ɗin ba a
matsayin mahaifiyarta ba, bayan tsawon shekaru masu yawa. Ba za ta iya bari a ce tana ji tana
gani, duk yadda ta ci buri da 'yarta a ce ta ƙare a auren nakashashshshe, musaki, mara ƙafa ba.
Wanda ko likitoci ba su da tabbacin zai warke ko kuwa nan gaba kaɗan za a yanke ƙafar ne
idan ta daina aiki. Daga lokacin kenan sunan ɗiyarta zai tashi daga Jawahir ya koma 'Matar
Gurgu' Abin da ba za ta iya jurewa ba ke nan. Tabbas ta matuƙar so haɗin Tareeq da Jawahir,
ko don yadda Jawahir ɗin ke son shi. Ita kuma tana matuƙar ƙaunar abin da ɗiyarta ke so, shi
ya sa ta yi ta fafutuka wajen ganin auren nan ya yiwu. Amma fa a lokacin ba ta taɓa tunanin
Tareeq ɗin zai tashi daga cikakke kuma lafiyayyen mutum zuwa nakashashshshe ba. Don haka
ba za ta iya jure ganin 'yarta ta ƙare rayuwarta wajen kula da miji ba, a banza a wofi ta lalace.
Kullum babu hutu, sai dai kula da nakashashshshen miji. Ina za ta iya zuba ido ta din ga kallon
shalelen 'yarta cikin wannan hali? Hakan ne ya sanya ta ɗan jan wani numfashi, tana ji ya zama
dole ta buɗe baki ita ma ta magantu ko da hakan na nufin rugujewar zumuncinsu.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 29

"Ki yi haƙuri Dada ji, ban san me zan yi mata ba." Shi ne abin da ta faɗa, ba tare da ta bari sun
haɗa ido da ita ba. Kallon ta kawai Dada ji take yi cike da tsananin mamakin da ya hana ta furta
komai. Ji take kamar ba gaske ba ne, waɗannan maganganun ba daga bakin Maimunatun suke
fitowa ba.
"Jawahir har cikin zuciyarki kike faɗar wannan maganar?" Abeey ya faɗa bayan ya kalli Jawahir
ɗin. Kasa haɗa ido ta yi da shi, kawai ta ci gaba da kallon wani wajen kana ta buɗe baki da
niyyar soma magana, Abeey ya katse ta da faɗin

"Ɗaga idanunki ki kalle ni sannan ki tabbatar mini da abin da kika faɗa." Kamar ba za ta ɗaga
idanun nata ba, haka dai ta daure ta kalli Abeeyn a ɗan tsorace. Ba ta buƙatar ƙarin bayani, don
ta san abin da yake buƙatar ta ce, don haka ta buɗe baki ta ce

"Eh Abeey a yi haƙu..." Ɗaga mata hannun da Abeey ya yi, shi ne ya sanya ta katse maganar
da ta fara, ta yi saurin yin ƙasa da kanta. Tun da ta fara magana ya ɗaga lumsassun idanunsa
ya kafe ta da su, ba ya buƙatar wani ƙarin bayani daga Jawahir. Domin kuwa, duk wani bayani
da yake so ya sani ya fuskance shi daga cikin muryarta. Ya san Jawahir tana son shi, bai kuma
taɓa tunanin tana son shi don ƙirar jikinsa ba, duk da yadda ya kamata ya fahimta, ko don
yadda maganganunta da yawa ba sa wuce a kan kyawunsa ne da sauran su. Amma bai taɓa
barin hakan ya yi tasiri a zuciyarsa ba. Sai ga shi yanzun ƙiri-ƙiri ta bayyana ba za ta iya
aurensa ba, ba kuma don komai ba sai don nakasar da ya samu a ƙafarsa. A hankali ya lumshe
idanunsa yana jinginar da kansa kan kujerar da yake kai ba tare da ya ce komai ba. Dubansa
Abeey ya maida kan Umma ya ce

"Maimunatu kin amince da abin da yarinyar nan take faɗa?" Ya ƙare maganar har lokacin yana
kallon ta. Shiru ta yi na tsawon sakanni kamar mai tunani, kafin ta gyara zama ta ce

"Toh ya zan yi da ita Yaya? Ita ta ce tana so tun farko, yanzu kuma ta ce ba ta so saboda wani
dalili. Sai nake ganin kamar babu abin damuwa, tun da dai ra'ayi ne. A yi haƙuri kamar yadda ta
faɗa ɗin." Tun da ta fara magana Abeey ke kallon ta har ta ƙarasa. Ya yi matuƙar mamaki,
maganar Umma da ita kanta Jawahir ɗin sun ba shi mamaki. Ya kuma jefa shi cikin shakkun
halayya da ɗabi'un mutane da ka iya sauyawa cikin ƙanƙanin lokaci. Bai taɓa tunanin haka daga
Umman Jawahir ba. Bai taɓa tunanin akwai ranar da za ta zo, don Tareeq ya samu nakasa a
ƙafarsa ta bi bayan ɗiyarta na ƙin aurensa ba. Ta ɓangaren Dada ji kuwa shiru ta yi tana kallon
Maimunatun. Lallai duk inda aka ce ɗa ba naka ba ne, wani lokacin sai hakan ya bayyana. Tun
da ta ɗauki Maimunatu take riƙe da ita tsakani da Allah ba tare da ta taɓa nuna mata wani
bambanci tsakaninta da Alhassan ba. Duk wanda ma bai sani ba, ba zai taɓa cewa Umman ba
'yar Dada ji ce ba. Don kuwa tun da take ba ta taɓa buɗe baki ta ce ba 'yarta ba ce. Kullum
burin ta ma kar wani ya gane ba ita ta haife ta ba. Duk wata kulawa da ya kamata uwa ta ba wa
ɗiyarta ta ba wa Umma. Babu abin da ta rage ta da shi wanda uwa za ta yi wa ɗanta. Sai ga shi
lokaci ɗaya ta guji jininta, don kawai Allah Ya jarabce shi da ciwo. Ciwon da suke fata da
addu'ar Allah Ya yaye masa, Ya sa ya warke. Amma ita da ɗiyarta sun juya masa baya, sun
nuna ba su yarda da ƙaddara ba, sun fito fili sun nuna dalilin da ya sa suke son Tareeq, ba tare
da tunanin yadda hakan zai janyo tangarɗa wa zumuncinsu ba.

"Za ku iya tafiya. Allah Ya saka da alkhairi." Abeey ya faɗa yana jin yadda zuciyarsa ke zafi. Ya
fi jin zafin ƙanwar tasa a kan ɗiyarta, domin bai taɓa zaton haka daga gare ta ba. Ba su ce
komai ba dukkansu suka miƙe, ba tare da sun kalli kowa ba, suka fice daga ɗakin. Daidai
lokacin da suka fito daga ɗakin, ita ma Maami ta fito daga nata sashen. Ta kalle su saboda
yadda ta gan su kamar a birkice. Ba wani mutunci suke yi da Umman ba, amma yau ɗin sai ta ji
ina ma a ce suna yi, ko don ta ji abin da ya faru, saboda yadda yanayin Umman ya nuna kamar

ba lafiya ba. Kamar ba ita ba, ta ce bayan ta ɗan rage tazarar da ke tsakanin su

"Lafiya me ya faru?" Ta faɗa tana ƙare musu kallo, kallon da a idanunsu ya fi kama da na rainin
hankali ko wulaƙanci. Wani banzan tsaki Umma ta sauke tana jan hannun Jawahir, kamar ba za
ta ce komai ba, don kwata-kwata ba ta yin Maamin, amma sai ta ce

"Ban sani ba. Idan gulmar kike so, me ya hana ki zuwa taron da Yaya ya shirya? Ba fa na son
iya-shege." Umma ta ƙare maganar tana jefa mata wani banzan kallo. Daga haka ba ta jira ta ce
komai ba, ta ja hannun Jawahir suka wuce suka bar ta a wajen. Bin su ta yi da wani
wulaƙantaccen kallo, tana ji yau ɗin gaba ɗaya ta gama muzanta. Me ya sa ma ta yi mata
magana bayan dama tun can ba shiri suke yi ba? Ta ja tsaki tamkar za ta tsinka harshenta.
Baƙin ciki ya bi ya cika mata zuciya. Kawai sai ta juya ta koma sashenta ranta a mugun ɓace.

A ɗaya ɓangaren kuwa tun bayan da suka fita shiru ne ya biyo baya na tsawon mintuna masu
yawa. Babu wanda ke da niyyar cewa komai, saboda yadda dukkanninsu kowa da abin da yake
saƙawa. Sosai zuciyarsa ke masa wani irin zafi. Wanda rabon da ya ji shi tun bayan rabuwarsa
da Diyana. Me ya sa ba shi da sa'a ne shi kam? Sun yi soyayya da Diyana kamar babu gobe,
sai dai ashe gaba ɗaya tana son shi ne don dukiyarsa, dukiyar da ta yi ƙoƙarin mallake ta tun
kafin ta kai ga shigowa gidansa. Ba domin ikon Allah ba da tuni wani zancen ake ba wannan ba.
Bai so Jawahir ba, amma kuma ya amince da aurenta, ita kuma ga abin da ya faru. Kenan shi
ƙaddararsa a kan soyayya take? Ko kuwa ya kira ta a kan mace ne? Macen ma wadda sai yana
dab da aurenta?

"Hidaya." Da kaushashshiyar muryarsa ya ambaci sunan, bayan ya buɗe idanunsa da suka rine
daga fari fat, zuwa ja. Shi kaɗai ya san irin zafin da yake ji a ƙirjinsa. Ba ya tunanin zai iya ci
gaba da zama cikin ɗakin, gwara ya samu ya keɓance kansa ko ya ji sukunin abin da yake ji.

"Na'am Yah Tareeq." Ta faɗa a matuƙar sanyaye tana kallon ɗan'uwan nata cike da tausayawa.
Tun kafin ya yi magana ta fahimci abin da yake nufi, don haka ta miƙe, kai tsaye ta ƙarasa
bayansa ta shiga tura shi. Daidai suna dab da gifta Maama ta yi ƙarfin halin faɗin

"Ba na son tunani Tareeq. Ka samu ka yi bacci, za mu yi magana zuwa safiya. In Sha Allah
hakan ne mafi alkairi, kar ka saka wa kanka damuwa. Hakan ma taimakonmu Allah Ya yi, ta
hanyar nuna mana masoyanmu na gaske da kuma waɗanda ba na gaske ba." Shiru ya yi yana
saurarar abin da Maaman take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login