Showing 36001 words to 39000 words out of 81712 words
Chapter 13 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf
Be bi ta kan wayarsa da ke ajje kan gado ba, kai tsaye ya
ƙarasa gaban mirror ya shiga sake kwantar da sumar kansa da ko da ze kwana nawa ba tare
da ya taɓa ta ba ba za ta nuna ba. Sai dai da yake ya riga ya saba, duk lokacin da ya fito daga
wanka ya kan gyara ta yadda take sake zama haɗaɗɗiya, mai matuƙar birgewa. Be jima ba ya
ida shiryawa cikin wata tattausar jallabiya da ta matuƙar ɗaukar kalar fatarsa. Kasancewar ba
zai sake fita daga gidan ba ya sanya shi jan laptop zuwa kan gadonsa, saƙon nan dai ya sake
nemowa ya shiga yana sake karanta abin da ke rubuce da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai kamar wanda ke
koyar yadda ake karatun. Ya yi nisa ba tare da ya ankara ba sai ji ya yi an turo ƙofar ɗakin. Da
sauri ya ɗaga idanunsa ya kalli mai shigowar. Wata ƙatuwar ajiyar zuciya Maama ta sauke
lokacin da ta ga ɗan nata zaune da alama cikin ƙoshin lafiya. Saurin rufe laptop ɗin gabansa ya
yi, yana ajje ta gefe ya soma ƙoƙarin sakko wa daga kan gadon. Ƙarasawa Maama ta yi.
"Tareeq ina ka shiga ne tun ɗazu ina kiran wayarka ba ka ɗagawa? Ka san fa ba na son hakan,
kana tayar mini da hankali wallahi." Maama ta faɗa tana kallan sa bayan ta nemi waje ta zauna.
Sai da ya duba inda ya ajje wayarsa, ya janyo ta ya kunna ta. Tarin missed calls ɗin da ya gani
danƙare a kan wayar tasa ya sanya shi ɗaga kai ya kalli Maama.
"Ki yi haƙuri Maama, na ajje wayar ne ban san kin kira ba."
"Wani abin kake yi ne?" Sai da ya ɗan kalli laptop ɗin kafin ya shafi gefen kansa ya girgiza kai
"A'ah, na ɗan duba wani aiki ne. Ki yi haƙuri Maama." Ya sake faɗa a karo na biyu. Murmushi ta
yi kafin ta gyara zama ta ce
"Shi ke nan, za mu iya yin wata magana?" Jinjina kai ya yi kana ya buɗe bakinsa ya ce a nutse
"Eh." Sai da ta ɗan ja wasu sakanni kafin ta ce
"Ina takardun nan na Diyana?" Shiru ya yi kamar mai tunanin wani abin, kamar ba ze ce komai
ba, sai kuma ya ɗan fesar da iska daga bakinsa kana ya ce
"Na ƙona su gaba ɗaya." Kallan sa Maama ta cigaba da yi, ya yin da ya basar duk da ya san shi
take kalla.
"Toh Allah Ya ƙara kiyayewa. Amm kaa ga gobe idan Allah Ya kai mu Abeeynku zai dawo,
Umman Jawahir kuma tana ta cigaba da yi mini maganar haɗa ka da Jawahir. Tun hankalina bai
kwanta da hakan ba, har kuma ya zo ya kwanta. Tun da ko babu komai dai Jawahir er'uwarka
ce. Don haka nake so na ji daga bakinka, idan dai har ka amince zan sanar wa da Abeeynku
wannan maganar sai a san abin yi. Idan kuma ba ka amince ba shi ma ka sanar da ni, amma
abin da nake so ka tuna shi ne ni mahaifiyarka na amince da haɗin ɗari bisa ɗari, musabbabin
hakan kuma saboda kasancewar Jawahir er'uwarka." Tun da Maama ta soma magana yake
kallan ta har ta ƙarasa. Ya yi mamaki matuƙa da ya kasance Maaman da kanta take yi masa
zancen wata mace bayan abin da ya faru kwata-kwata ba a daɗe ba. Kamar ta san me yake
tunani, sai cewa ta yi
"Kar ka damu Tareeq, na yi hakan ne sanin cewar a kurkusan nan ba lallai ka iya samun
nutsuwar fitar da matar aure ba. Shi ya sa na amince da wannan al'amari. Ka yi tunani sosai
zuwa gobe sai mu yi magana." Maama ta ƙare maganar tana kamo hannunsa ta riƙe har lokacin
tana kallan sa. Ɗan dafe ƙirjinsa da ya yi masa nauyi ya yi, kafin ya janye hannunsa cikin
sakannin da ba su wuce uku ba, ya ɗan lumshe idanunsa kafin ya buɗe a kan Maaman, yana
tunanin abin da ya kamata ya ce mata. Shin ya amsa da cewar ya amince bayan abin da ya
faru tsakaninsa da Diyana? Ko kuwa ya ce be amince ba saboda fidda rai da ya yi a kan mace.
Idan ya buɗe baki ya ce ya amince ya kuma kasance ita kanta Jawahir ɗin halin su ɗaya da
Diyana fa? Tun da ita ma Diyanan duk daɗewar da suka yi bai taɓa sanin halinta na zahiri ba
sai ana dab da ɗaura musu aure.
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 15
Cigaba da kallan sa Maama ta yi tana jira ta ji ko ze ce wani abu. A hankali ya zuro ƙafarsa
daga kan gadon zuwa ƙasa. Ya miƙe a kan ƙafafun nasa kafin ya ce
"Shi kenan Maama, duk abin da kika yanke wa rayuwata daidai ne. Amma tun da kina son ji
daga bakina In Sha Allah zan yi istihara duk yadda ake ciki zan sanar da ke. Babu damuwa za
ki iya sanar da Abeey kafin lokacin." Ya ƙare maganar fuskarsa babu yabo babu fallasa. Cikin
ransa fata yake ka da Maaman ta sake jan maganar da nisa, don kuwa har ta ginshe shi. Ba
don ma Maaman da kanta ke masa maganar nan ba, da ko haɗin kai ba ze bayar ba. Murmushi
ne ya wanzu a kan fuskar Maaman, ta miƙe ita ma kafin ta ce
"In Sha Allah. Allah Ya tabbatar mana da abin da ya fi zama alkhairi."
"Ameen." Ya amsa a saman laɓɓansa yana kai hannunsa guda cikin sumar kansa ya shafa.
Maama ba ta ƙara mintuna masu yawa cikin ɗakin ba, ta fice ta bar shi tsaye cike da saƙe-saƙe.
.. "Yah Tareeq ka yi haƙuri, ban san wane irin kallo za ka mini ba, ban kuma san wane irin
hukunci za ka yi mini ba, idan na sanar da kai cewa na kamu da soyayyar abokinka Abdoul. Ka
yi haƙuri Yaya." Hidaya da ta karanta saƙon da Sultanah ta gama rubutawa ta tura.
"Wallahi Hidaya ina tsoron fushin Yah Tareeq." Sultanah ta faɗa kamar za ta yi kuka.
"Ke ki dena jin tsoro, ina tare da ke fa." Hidaya ta faɗa tana riƙo hannun Sultanah, duk da ita
kanta tana jin tsoron, amma don ta ba wa 'yar'uwarta ƙwarin gwuiwa ya sa ba ta nuna ba. Ganin
alamar blue tick da suka yi ne ya sanya kusan a tare suka gyara zama. Sultanah ta haɗiye wani
yawu da ƙyar tana jin yadda bugun zuciyarta ke ƙaruwa. Ba ta san yadda za ta yi da zuciyarta
ba, ba ta san lokacin da ta faɗa ƙaunar Abdoul ba. Farga kawai ta yi dumu-dumu cikin wata
matsananiyar ƙaunarsa irin mara adadi ɗin nan. Tun tana ganin za ta iya jurewa har ta kasa,
don kuwa yanzu haka ita kaɗai ta san irin zafin da zuciyarta take yi, na rashin isar da saƙon
zuciyarta gare shi, har zuwa wannan lokacin. Ta san halin yayansu, shi ɗin mai damuwa da
damuwarsu ne, sai dai ba ta sani ba, ko a wannan karon ma ze bi bayanta ne bayan ta sanar
da shi tana ƙaunar abokinsa. Ba ta sani ba ko ma hukunci ne ze biyo baya.
"Har yanzu fa be yi reply ba Hidaya." Sultanah ta faɗa ganin da ta yi bayan wajen minti 5 da
ganin saƙon da Tareeq ya yi amma har yanzun be yi reply ba.
"Ze yi ne Sulty, mu ƙara lokaci." Hidaya ta faɗa a sanyaye, saboda yadda ta ji gaba ɗaya ɗan
ƙwarin gwuiwar da ta yi nasarar haɗa shi yana ƙoƙarin zagwanyewa.
A ɓangaren Tareeq kuwa ya karanta saƙon nan ya fi sau uku. Daga ƙarshe dai sai ya sake
dubawa don tabbatarwa da gasken Sultanah ɗin ce ta turo masa saƙon. 'Tabbas ita ce' Ya
tabbatar wa da kansa hakan yana sake kallan saƙon. Shiru ya yi na tsawon lokaci, tabbas abin
ya matuƙar ba shi mamaki, ya kuma ɗaure masa kai. Be taɓa tunanin ƙanwar tasa za ta iya yin
hakan ba, har kuma ta sanar da shi. Sai dai kuma da ya nutsa tunaninsa sai ya ga abin da
Sultanah ta yi kamar shi ne daidai. A matsayinsa na yayanta mai ƙoƙarin samar mata mafita a
kowanne yanayi ne, shi ya kamata ta sanar wa da abin da ke faruwa. Abu na biyu kuma shi ɗin
aminin Abdoul ne, wanda ze iya amfani da kasancewar hakan wajen samar wa 'yar'uwarsa
mafita. Sauka ya yi daga Whatsapp ɗin kai tsaye ya nemo number Abdoul ya kira. Ringing 1_2
ya ɗauka, kafin Tareeq ɗin ya ce komai Abdoul ya ce
"Barka Aboki."
"Yawwah, kana lafiya?" Tareeq ya faɗa hannunsa na kan goshinsa yana ɗan murzawa.
"Alhamdulillahi. Ya ake ciki?" In ji Abdoul.
"Kana gida ne?"
"A'ah, yanzu na ɗan fita ne karɓo saƙo." Sai da Tareeq ya ɗan gyara zaman sa sannan ya ce
"Ohk, gobe za ku shigo ai?" Murmushi Abdoul ya yi kana ya ce
"Eh mana, da wuri ma kuwa In Sha Allah."
"Allah Ya nuna mana, akwai wata muhimmiyar magana da nake so mu yi da kai."
"Ikon Allah! Wacce magana ce wannan?" Abdoul ya faɗa cike da mamaki. Ɗan murmushi ne ya
wanzu a kan laɓɓan Tareeq kafin ya ce
"Kai dai za mu haɗu."
"Malam ka sanar da ni kawai please."
"Sai kuma ka yi ai." Tareeq ya faɗa cikin basarwa.
"Kai fa dama ɗan rainin hankali ne wallahi.." Abdoul ya dakata daga haka, kafin ya yi ƙwafa
kana ya ɗora da faɗin
"Amma ya na iya.. Allah Ya kai mu." Murmushi mai sauti Tareeq ya yi kana ya amsa da
"Ameen." a nutse. Daga haka suka yi sallama.
**
Washe gari sosai gidan ya tashi da karɓar 'yan'uwa na kusa. Waɗanda ke ta shirye-shiryen
dawowar Alhaji Alhassan Dikko. Jawahir da ba su kwana a gidan ba, da sassafe suka diro
gidan don tarbar Abeeyn. Tun safe duk suna sashen Dada ji, Maama, Hidaya, Sultanah,
Jawahir da Mamanta. Maamin Sultanah ce kaɗai tun wayewar garin kwata-kwata ba ta shigo
ba. Duk kuwa da cewa ayyukan da ake gabatarwa sun fi yawa a sashen Dada ji ɗin kamar
yadda aka saba. Duk kuma da cewa ta san duk en gidan suna sashen nata, hakan be sanya ta
zuwa ba. Tana can sashenta tana shirya wa mijinta abubuwa na musamman. Babu kuma
daɗewa ƙawarta, aminiyarta Hajiya Zulaiha ta iso gidan. Mata ga Aminin Abeey, kuma mahaifiya
ga Abdoul Aminin Tareeq. Su biyu suka iso gidan, Abdoul ya wuce sashen Tareeq, ya yin da
Umma ta wuce kai tsaye sashen Maami.
Da sallama ya shiga palourn, idanunsa a kan Tareeq da ya kwantar da kansa a kan kujera
idanunsa a lumshe. Ya ɗora hannunsa ɗaya a kan fuskarsa, wanda hakan ya yi nasarar kare
idonsa guda ɗaya. Sai da Abdoul ya ƙarasa ya zauna a gefen sa ya ce cike da mamaki
"Tareeq." Da sauri Tareeq ya buɗe idanunsa, don kwata-kwata be ji shigowar Abdoul ba.
Idanunsa da suka ɗan janye saboda daɗewar da suka yi a lumshe ya sauke a kan Abdoul. Ya ja
wani nannauyan numfashi da ya fito daga ƙirjinsa a takure kafin ya ce
"Yaushe ka shigo?"
"Bayan ka yi nisa a tunanin." Tareeq ya faɗa yana karantar yanayinsa. Iska kaɗan Tareeq ya
fesar daga bakinsa kafin ya gyara zamansa, ba tare da ya ce komai ba, har lokacin da Tareeq
ya ce
"Anya kuwa lafiya Aboki?" Ya faɗa yana sake karantar yanayinsa. Cikin basarwa Tareeq ya ce
"Lafiya mana, wani abu?" Ya ƙare har lokacin dai cikin basarwa.
"Ko dai har yanzu maganar Diyana ne?" Be san lokacin da tsaki ya suɓuce masa ba.
"Me kake so na ce maka ka yadda na daɗe da cire Diyana a babin rayuwata? Allah ɗaya ne
koh? Toh ina rantse maka da shi, ko kaɗan babu damuwar Diyana a tattare da ni. Ina ga zuwa
yanzu ya kamata ka amince da ni." Numfashi Abdoul ya sauke kana ya ce
"Shi kenan, amma tabbas idan babu wannan akwai wani abu da kake ɓoye mini." Da sauri
Tareeq ya girgiza kai. Ba tare da ya kalli Abdoul ba ya ce
"Kar ka damu kanka, babu wani abu."
"Amm.." Abdoul ya buɗe baki ya fara magana Tareeq ya yi saurin katse shi da faɗin
"Maganarmu.." Girgiza kai Abdoul ya yi, jin yadda ya basar da zancen. A ransa yana saƙa
tabbas ko ma mene ne, idan ta yi tsami ze ji. Idan dai har abin da ya kamata ya sani ne, toh ya
san Tareeq ɗin ze sanar da shi ko ba yanzu ba. Hakan ne ya sanya shi faɗin
"Ina jin ka." Gyara zama Tareeq ya yi, sai dai kafin ya ce komai wayarsa ta soma ƙara. Ya janyo
ta yana kallan mai kiran nasa.
"Yaya wai ka fito muna palourn Dada ji." Hidaya ta faɗa, bayan Tareeq ya amsa wayar.
"Ohk." Ya amsa da hakan, yana mayar da kallan sa kan Abdoul ya ce
"Tashi mu je, Abeey na dab da iso wa." Ya faɗa yana miƙewa. Be jira Abdoul ya ce komai ba ya
shige bedroom ɗinsa. Bayan shuɗewar wasu mintuna ya fito, suka fice daga sashen gaba ɗaya.
... A ɓangaren Daneen kuwa, da mayafin da ke jikinta ta yi amfani wajen nannaɗe fiye da rabin
jikinta. Ta kifa kanta a kan gwuiwarta tana lumshe idanunta. Kewar mahaifiyarta take matuƙa
gaya, kewarta ce ke ratsa duk wata gaɓa ta jikinta. Yanzu ko tana ina?Tana can tana tunanin
suna zaune a ƙauyensu suna jiran ta? Tana can ita ma duk inda take hankalinta yana kansu,
kamar yadda nasu hankalin ke kanta? A nutse ta sake lumshe idanunta tana jin yadda wani
bacci ke ƙoƙarin fizgarta. Haka ta yakice shi, don duk wani hankalinta yana kan Ameer. Ta
kwashe fiye da awa ɗaya tana ta saka ran jin muryar Ameer ya yi mata magana, amma shiru.
Tun tana cigaba da kwanciya har ta gaji ta tashi zaune, ta shiga rarraba manyan idanunta da
suka ɗan faɗa, cikin rashin sanin abin yi. Wasa wasa, har bayan wajen awa uku, babu Ameer
babu alamarsa. Har ba ta san lokacin da ta miƙe a kan ƙafafunta ba, duk da jikinta da babu
ƙwari hakan be dame ta ba, burin ta kawai ta san yadda za ta yi ta je ta nemo inda Ameer ya yi,
ya bar ta a nan tana ta jiransa. Har ta soma takawa don barin wajen, kamar wadda aka tsikara
kuma sai ta dakata. Ta sake kallan inda take tsaye, sai ta mayar da ƙafarta baya. Gaba ɗaya
tunaninta ya tafi kan Ameer, idan kuma har ta bar wajen nan, kai tsaye ba ta san inda za ta nufa
ba. Bayan kuma ya faɗa ya sake jaddada mata da kar ta je ko'ina komai daɗewar da ze yi ta jira
shi. Idan ta bar wajen kuma shi ya dawo be gan ta ba fa? Daga nan me zai faru? Cikin sauri ta
shiga girgiza kanta kamar wadda ke magana da wani. Cikin matuƙar sanyin jiki ta koma da baya
ta zauna inda ta tashi. Tana nan zaune har ta ji an soma kiraye-kirayen Sallahr Azahar, amma
babu Ameer babu dalilinsa. Gaba ɗaya wani tunaninta ya tafi kan inda ya tsaya. Haka zalika
tambayar da ke ta mata yawo a cikin kwanya ita ce 'Ina ya tsaya? Me ya sa har yanzu bai dawo
ba?' Cikin sakannin da ba su wuce biyu ba, ta ji bugun zuciyarta ya ƙaru, nan take jikinta ya
ɗauki rawa, fararen idanunta tuni suka soma sauya kala, cikin sakanni ƙalilan, hawaye suka
taru. Kawai sai ta shiga juye-juye, cikin rashin sanin abin yi, sai ka ce wadda aka cewa idan ta
juya ɗin za ta hango shi. Duk kuma lokacin da ta kalli mutanen da ke kaikawo a wajen, sai ta ga
kamar za ta hango Ameer ɗin a cikinsu, babu kuma abin da take ji, sai ƙarin faɗuwar gaba, da
bugun zuciya.
A yi manage da wannan, In Sha Allah gobe ma za ku samu Update.
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 16
Kamar idanunta za su faɗo, haka take ci gaba da kallon hanyar da ta ga Ameer ya bi. Zuwa can
dai ta miƙe a kan ƙafafunta, ba ta kuma san yadda za ta iya ci gaba da zama a wajen ba, bayan
takamaimai ba ta san inda ɗan'uwanta yake ba. Ga shi kuma har an idar da Sallahr Azahar. Sai
dai miƙewar da ta yi ya yi daidai da lokacin da muryar Ameer ta daki dodon kunnenta.
"Adda." Ai ba ta san lokacin da ta juya da sauri ba. Take idanunta suka sauka a kan Ameer.
Wani murmushi mai haɗe da ƙwalla suka wanzu lokaci guda a kan fuskarta. Idan ta ce tana
farin ciki ma ɓata baki ne, don kuwa fuskarta kawai za ka kalla ka fahimci tsananin farin cikin da
ta tsinci kanta a ciki bayan ganin Ameer.
"Ameer ina ka je?" Ta yi tambayar da ke ta ci gaba da yi mata lugude a ka. Murmushi ne ya
suɓuce masa kafin ya ce
"Aiki na samo Adda, kina zaune zan din ga yin aiki muna samun kuɗi. Mu samu na cin abinci da
komai ma, har kuma mu tara na koma wa ƙauyenmu." Ya ƙare yana murmushin dai. Wani
sabon murmushin ne ya sake ƙwace mata, ta ce
"Da gaske?" Jinjina kai ya yi kafin ya ce
"Ehh, amma dai ki zauna ki fara cin abinci yanzu. Ya jikin naki?" Sai da ta harare shi kafin ta ce
"Bayan duk ka gama tsoratar da