Showing 42001 words to 45000 words out of 81712 words
Chapter 15 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf
tana bin sa da kallo har ya bar wajen a sanyaye. Sai da
ya ɓace mata da gani sannan ta dena kallon sa, gaba ɗaya wani burinta ya tafi kan yadda za su
yi maza su koma wajen Innarsu. Ba za ta sake barin ɗan'uwanta ya din ga aikin wahala ba.
Tana fata ta yi kuɗi a rayuwarta, Ameer ya ji daɗi. Haka zalika Innarsu ma ta ji daɗi. Gaba
ɗayansu su dena aikin wahala. Zama ta ci gaba da yi a wajen, ta yi shiru tamkar mai tunani. Sai
dai zuwa can idan ta gaji sai ta ɗaga kai ta kalli abin da ke faruwa a gefenta sai kuma ta maida
fuskarta kan cinyarta. A nan ta yi sallah, ko bi ta kan wani abinci ba ta yi ba, ta ci gaba da jiran
Ameer. Zuwa can kuwa sai ga shi ya dawo. Ya wanzar da murmushi a kan fuskarsa da ta sauya
daga da, wadda take koyaushe cikin matuƙar annushuwa, zuwa wata daban. Sai dai duk iya
ƙoƙarinsa yake don kar Addar tasa ta fahimci wani abin. Duk da ya san hakan ma ba mai
yiwuwa ba ne. Sai dai inda Allah Ya taimake shi, yadda damuwar da ke shimfiɗe a kan fuskarsa
ta ta'allaƙa ta da gajiyar aiki kamar yadda ya sanar da ita. Ko minti 2 ba su ƙara ba, suka yi
gaba zuwa wajen da suke zama, suka kuma saba. A nan suka ci abinci sannan suka ci gaba da
zama.
A 'yan kwanakin da suka biyo baya, sosai al'amuran Ameer ke ci gaba da sauyawa, ba shi da
aiki sai tunani da kuma damuwa. Har ta kai yanzu ba ma ya iya ɓoye damuwar a gaban Daneen
ɗin saboda yadda ya gajiya. Duk wani ƙwarin gwuiwarsa ya ƙare. Ji yake kamar ƙwaƙwalwarsa
za ta yi bindiga idan ya cika tunani.
Dare ne, domin kuwa wajen ƙarfe 10pm ne. Daga shi har ita babu wanda ya soma ƙoƙarin
neman wajen kwanciya. Ita ta yi shiru ne kawai tana kallon sa, mamaki take yadda take ganin
shimfiɗaɗɗiyar damuwa a kan fuskarsa amma ya ƙi faɗa mata. Bayan hakan ba halinsa ba ne.
Ta rasa gane abin da ke damun Ameer ɗin, wanda ya sauya shi cikin kwanaki kaɗan haka. Ta
rasa yadda za ta yi, don haka kawai sai ta zuba masa idanu ta ji ko zai sanar da ita damuwarsa.
Sai dai abin da ma ta lura da shi, tamkar hakan ƙara ba shi lasisin yin tunani ne ta yi. Don kuwa
kwantar da kansa ya yi jikin wani gini da ke gefensa ya yi shiru. Daga inda take zaune take ci
gaba da kallon sa, tunani barkatai cikin ƙwaƙwalwarta. Ba tun yanzu ba take hango shi yana
gyara zamansa, daga baya ma sai ya tashi daga inda yake ya sauya waje. A hankali ta miƙe jin
da ta yi gabanta ya ɗan faɗi, kai tsaye ta ƙarasa inda yake.
"Ameer." Ta faɗa bayan ta dafa hannunta a kan kafaɗarsa. Ɗaga jajayen idanunsa ya yi ya kalle
ta hannunsa dafe da cikinsa. Ta bi hannun nasa da kallo ba tare da ta lura da idanunsa ba ta ce
"Me yake damun ka Ameer?" Ta faɗa a ɗan gigice da muryarta da ke rawa. Girgiza kai ya yi
kafin ya ce
"Adda cikina ke ciwo."
"Cikinka kuma?" Ta faɗa tana riƙo hannun nasa. Jinjina kai ya yi yana sake dafe cikinsa. Cikin
matuƙar ruɗewa da rashin sanin abin yi Daneen ta ce
"Me ka ci Ameer? Me ya sami cikin naka?"
"Babu abin da na ci fa." Ya faɗa har lokacin hannunsa a kan cikinsa. Da sauri ta shiga girgiza
kai, daidai lokacin da idanunta suka cika taff da ƙwalla ta soma faɗin
"Me ya sa kake mini haka ne Ameer? Me na maka? Me ya sa kake ta ɓoye mini abubuwa da
dama? Me ya sa ka tsiro da wasu halaye bayan da ba haka kake ba? Idan wani abu ya same
ka me zan faɗa wa Inna? Ba za ka buɗe baki ka yi mini magana ba Ameer?" Ta ƙare maganar
lokacin da wasu kyawawan hawaye suka sauka a kan kuncinta. Abin da ya matuƙar ba wa
Daneen mamaki shi ne yadda Ameer ya fashe da kuka, kuka kuma ba irin na wasa ba, kuka
sosai tamkar wanda ake duka ko ake yi wa wani mummunan abu. Maimakon ta ɗan ji sassauci,
sai kukan nasa ya sake dugunzuma mata hankali, cikin rawar murya ta ce
"Na shiga uku Ameer, faɗa mini abin da ya faru? Cikin ne?" Ta tambaya a ruɗe tana sake riƙo
hannun da ke riƙe da cikinsa.
"Ki yi haƙuri Addatah, ki yi haƙuri kin ji?" Shi ne abin da ya faɗa har lokacin yana kuka tamkar
mace. Cikin ƙanƙanin lokaci jikinta ya ɗauki rawa, muryarta da ta shige ta yi ƙoƙarin janyo ta
wajen faɗin
"Sanar da ni abin da ke faruwa Ameer, na shiga uku." Ta faɗa tana jin yadda wani bala'in tashin
hankali ke ci gaba da rikito mata. Sai da ya sake girgiza kai, idanunsa da suke a lumshe ya
buɗe, ya ɗora su a kan Daneen, ya sauke hannunsa da ke kan cikinsa, duk da yadda yake jin
cikin nasa tamkar ba a jikinsa yake ba, amma ya yi ƙarfin halin kamo hannayenta duka biyun.
Muryarsa har wani sarƙewa take yi lokacin da ya soma faɗin
"Adda ki yi haƙuri, na rasa yadda zan yi, ban san ya zan yi na raba kaina da mutanen nan ba,
ban san tsautsayin da ya haɗa ni da su ba. Ban san abin da ke damun ƙwaƙwalwata ba. Ni dai
kawai na ji ba na son rabuwa da su, ko da zan yi ƙoƙarin hakan ma ba zan iya ba. Adda maza
ne su ba mutum ɗaya ba ba biyu ba, kullum sai sun yi amfani da ni Adda. Ba su taɓa ce mini
kar na sanar wa da kowa ba, amma tamkar an rufe bakina na kasa faɗa miki, na kuma kasa
hana kai kaina inda suke. Na kasa barin ki ki san inda nake zuwa Adda, ina tsoron kar ki hana
ni zuwa kuma in ƙi hanuwa. Don ji nake yanzu haka in da zan wayi gari cikin ƙoshin lafiya toh
zan koma wajen nasu. Kullum cikin kuka nake Adda cikin dare. Na rasa yadda zan yi, na rasa
mene ne mafita. Na rasa abin da ke mini daɗi. Ina jin tamkar ƙwaƙwalwata ba ta jikina, ina ji
tamkar wani noti da ke kaina ya kwance. Adda na rasa abin da ke mini daɗi. Ni da kaina fa nake
kai kaina wajen su, me yake damu na? Anya kuwa ni ɗin ne? Ya zan yi ne ni kam? Na rasa abin
da ke mini daɗi. Na rasa ya zan yi, don Allah Adda ki yi haƙuri ki sanar da ni abin da zan yi, ki yi
haƙuri kar ki ɗauki matakin da ba zan iya jurewa ba. Zuciyata zafi take mini, ina ji ina numfashi
da ƙyar. Ki yafe mini Adda." Ya ƙare maganar yana sake fashewa da wani marayan kuka. A
hankali ta shiga zame hannunta daga cikin na Ameer, idanunta da suka ƙafe ƙaff, babu hawaye
ko ɗigo a kan fuskarsa. Kallon sa kawai take yi tamkar wadda ta soma ganinsa a yau ɗin nan.
Wani irin gudu zuciyarta take, wanda ya mugun wuce ƙa'ida. Don kuwa idan da za ka kalli
ƙirjinta a lokacin, za ka iya ganin yadda zuciyarta ke bugawa a haukace. Kallon sa kawai take
yi, shin da gaske abin da take ji daga bakin Ameer gaskiya ne yake faɗa mata? Ameer Ameer
dai nata shi ne yake faɗin wasu maza suna amfani da shi? Idan dai har ta fahimci abin da yake
nufi kenan wasu sun yi lalata da shi? 'Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un' Ta ambata a fili muryarta
na wani irin karkarwa tamkar yadda jikinta ke wani mahaukacin ɓari tamkar wadda ke shirin
zube wa a ƙasa. Dalili kenan da ya sanya Ameer ya ɗaga idanunsa da suka yi jajur, har sun yi
wani luhu-luhu ya kalle ta, ita ma shi take kalla. Ya girgiza mata kai kafin cikin sanyi ya furta
"Ba laifina ba ne Adda." Maganar da ya yi, ita ce ta ba wa kukan da ya maƙale mata damar
fitowa, ta shiga rera shi kamar za ta shiɗe. Zube wa ta yi a kan ƙafafunta ta shiga rera shi kamar
ranta zai fita. Ita kam wannan wace kalar baƙar rana ce a wajenta? Wace kalar mummunar rana
ce wannan? Wanne kalar bala'i ne wannan ya shigo cikin rayuwarsu ita da ɗan'uwanta? 'Inna
lillahi wa inna ilaihi raji'un' Ta sake maimaitawa, daidai lokacin da Ameer ya ƙaraso inda take
zaune ya zube shi ma a kan ƙafafunsa. A karo na barkatai ya sake furta
"Ki yi haƙuri Addatah, ban san yadda aka yi hakan ta faru ba. Kin fi kowa sanin halin
ɗan'uwanki." Maganarsa da ke fita a wani hahharɗe ta daki dodon kunnenta. Sai a lokacin
sannan ta samu ƙwarin gwuiwar soma magana.
"Me ya sa za ka mana haka Ameer? Me ya sa ba ka bari mun mutu da yunwa da rashin gata
ba, a kan wannan abin. Iyee Ameer? Ba gwara mu mutu ba, da ka jefa kanka cikin wannan
ɗabi'ar. Ameer me ya sa ka yi mana haka? Me ya sa ka canja daga Ameer ɗina da na sani? Me
ya sa haka Ameer?" Ta ƙare hannunta a kan kwalar rigarsa tana ja kamar za ta cire rigar. Tun
daga ƙasan zuciyarta maganar take fitowa, muryarta cikin kuka tamkar ba za ta iya ƙarasa
maganar ba. Yanzu kam kukan Ameer babu sauti, sai hawayen da ke ta tsere a kan kuncinsa.
"Ki kashe ni kawai Adda, ko na dena jin zafin da nake ji a cikin zuciyata. Ki ɗauki wani abun ki
caka mini a ƙahon zuciyata Adda, na san tabbas zan ji sassaucin abin da nake ji a zuciyata. Ni
kaɗai na san me nake ji, ni kaɗai na san irin raɗaɗi da zafin da nake ji Adda. Don Allah ki kashe
ni ko na huta, ke ma ki huta da wannan baƙin cikin da na ja miki, ko hakan ze sa Inna kar ta ji
labarin nan." Ya ƙare a raunane yana jujjuya kansa idanunsa na wani irin lumshewa kamar me
shirin yin bacci.
"Haɗuwata da su kawai zan iya tunawa. Ban san abin da suke yi ba, har na tsawon kwana biyu.
Sun ce mini aikin biredi ne zan din ga yi. Tun daga ranar kamar an sauya ni, shi ne suka soma
amfani da ni, ban san yadda aka yi na kasa ƙin komawa gobe ba. Duk da yadda zan ji a
zuciyata Allah zai kama mu, zai kuma yi mana azaba, hakan ba ya hana ni zuwa wajen su
kullum. Kuma kullum cikin kuka nake Adda, amma ni.. na rasa ma me zan ce." I zuwa lokacin ta
dena kukan kallon sa kawai take tana nazarin maganganunsa. Lokacin da ya kai ƙarshe, sai ta
ji wasu guntayen hawaye sun sauko mata a kan fuskarta. Ta ja ɗan'uwanta ta rungume tana jin
wani sabon kukan na taho mata. Ko babu komai ta san zai samu sassauci a kan abin da yake ji,
ko babu komai ze yi kuka a kan kafaɗar 'yar'uwarsa ya ji tabbas fa yana da wajen da zai iya
ɗora kansa ya yi kuka. Ai kuwa sai ya lumshe idanunsa yana barin hawayen na sauka a kan
fuskarsa tamkar za su ƙare. Sun shafe wajen mintina goma a haka kafin ta ji yana sauke
numfashi da gudun gaske. Ta yi azamar sanya hannu ta ɗago shi tana kallan sa.
"Ameer." Ta faɗa ganin yana ci gaba da lullumshe idanunsa. Fahimtar abin da take nufi ne ya
sanya shi faɗin
"Cikina, da ƙirjina Adda.. Ina ji tamkar za su bar jikina. Wani abu nake ji ya tokare mini
numfashina." Ya faɗa yana ci gaba da kokawa da numfashinsa. Da sauri ta gyara zamanta tana
faɗi cikin rawar murya
"Kar ka damu, za ka samu sauƙi. Kwanta ka yi bacci kaa ji?" Ta faɗa tana taimaka masa, ta
kwantar da kansa a kan cinyarta. Runtse idanunsa ya yi ruff, hannunsa na kan ƙirjinsa da
yanzun ya fi masa ciwo a kan cikinsa. Ji yake tamkar duk wasu abubuwa da ke cikin ƙirjinsa
suna dab da fitowa fili saboda wani irin yanayi da tun da Inna ta haife shi bai taɓa jinsa ba. Shiru
Daneen ta yi tana kallon yadda yake sauke numfashi a wahalce, ta runtse idanunta da hawayen
suka ƙeƙashe, suka ƙafe gaba ɗaya. Haƙiƙa yau ɗin wata rana ce wadda ba za ta taɓa
mantawa da ita ba, yau ɗin wata rana ce da ta kafa musu mummunan tarihi cikin tarihin
rayuwarsu. Abin da suke ji a nesa da su sai ga shi ya faru a kan ƙaninta, rabin jikinta. Su kuwa
waɗannan mutanen su waye su? Waɗanne irin mugaye ne su, da suka rasa wanda za su lalata
sai ƙaramin yaro Ameer? Daga zuwa neman aikin yi don su samar wa kansu abin da za su ci da
wanda za su yi guzurin tafiya ƙauyensu? Don mugupnta da rashin tsoron Allah sun lalata mata
rayuwar ƙani? Ba sau ɗaya ba ma har fiye da a ƙirga? Sun kuma yi amfani da wani abun can
wajen rufe masa baki da jan hankalinsa zuwa wajen, duk da wayo da takatsantsan irin na
Ameer? 'Hasbunallahu wa ni'imal wakeel' Ta faɗa a kan laɓɓanta tana runtse idanunta har
lokacin bugun zuciyarta bai koma daidai ba. Lallai ko ma mene ne har abada sun gama neman
aiki daga ita har ɗan'uwanta, gari na wayewa za su ɗauki hanyar tafiya ƙauyensu da ƙafafunsu,
idan ya so in Allah Ya yi su isa suna a raye, idan kuma bai ƙaddara ba Allah Ya ji ƙan su. Haka
wannan baƙar ranar ta ƙare suna zaune a wajen, ko wajen da take kwana ba ta koma ba, haka
ta ci gaba da zama, kan Ameer na kan cinyarta har zuwa wayewar gari. Sai dai kafin gari ya
gama yin haske jikin Ameer ya yi wani irin mahaukacin zafi, ban da karkarwa babu abin da yake
yi, da ƙyar yake iya buɗe idanunsa saboda zafin ciwo. Zuwa lokacin Daneen ta gama ruɗewa,
tun tana ƙoƙarin danne kukan da ke taho mata har ta kasa. Ta bar shi ya fito saman fuskarta da
ke shimfiɗe da damuwa fall.
"Sannu Ameer." Ta sake faɗa a karo na barkatai. Da kansa ya yi amfani wajen ɗaga mata
alamar ya ji ta. Sai dai jikinsa babu abin da ke sake yi sai ɗaukar uban zafi mara misaltuwa.
"Adda ina ji kamar ana daddatsa mini ƙashi, zuciyata ta yi mini nauyi." Ya faɗa a sanyaye har
lokacin idanunsa a lumshe.
"Sannu Ameer, ko dai mu je asibiti ne?" Ta yi maganar kamar mai tambaya, sai dai kuma a
zahiri ba jiran amsar wani take nema ba. Wannan ne dalilin da ya sanya ta miƙewa cikin
mutuƙar rikicewa ta nemi taimakon wasu don a ɗaukar mata Ameer ɗin ta kai shi asibiti.
Kwata-kwata hankalinta bai kawo mata abin da asibitin za su iya nema ba, ita dai kawai ta ga
Ameer ɗin a asibiti a duba shi a ba shi magani ya warke shi ne burinta, inda kuma hankalinta ya
tafi.
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 18
Da taimakon wasu bayin Allah aka saka mata Ameer cikin napep ɗin da aka tarar mata. Ta yi
saurin faɗa wa ciki tana jin gaba ɗaya jikinta na ci gaba da rawa, tamkar ma ƙafarta ba za ta
ɗauki nauyin jikinta ba. Babu ɓata lokaci drivern ya ja motar suka soma tafiya ba tare da ya jira
jin ta bakinta ba. Saboda ko ba ta masa bayani ba, ya san idan ba asibiti ba babu inda za su
tunkara a yanzu. Don haka ya yi hanyar asibitin da ya san ya fi kusa da inda suke. Yadda
numfashin Ameer ke wani irin rikicewa, yana kai masa cafka cikin ficewar hayyaci, shi ne abin
da ya sake tsorata Daneen. Ta rungumo shi cikin jikinta hawaye na gangaro wa a kan kuncinta,
cikin wata dashashshiyar murya ta furta
"Don Allah Ameer kar ka yi mini haka.." Ta kai ƙarshen maganar tana sake sauke idanunta a
kan fuskarsa da idanunsa ke kusan a rufe, hannunsa ɗaya na sautin zuciyarsa, ya yin da
numfashinsa ke ci gaba da ƙoƙarin barin gangar jikinsa. Abin da ya sanya mai napep ɗin ƙara
gudu kenan, don ƙoƙarin ganin sun isa asibiti a ceci ran wannan bawan Allahn da shi kansa
yake ganin tamkar abubuwan da yake na fitar rai ne. A haka suka ƙarasa cikin asibitin, Ameer
na rungume jikin Daneen, gaba ɗaya ta rasa sukuni, daga zarar ta janyo wannan addu'ar sai ta
ji ta kufce mata, hawaye kuwa har ta gaji da tsaida su, ban da sauka kan kuncinta babu abin da
suke yi. Zuciyarta na ci gaba da bugun da take ji tamkar za ta faso ƙirjinta ne ta fito. Mai napep
ɗin da kansa ya sauka ya ɗaukar mata Ameer da har lokacin ba ya cikin hayyacinsa. Wani irin
numfashi yake yi a wahalce, idan ka gan shi ma ba za ka ɗauka yana da rai ba, saboda yadda
gaba ɗaya jikinsa ya saki. Sai dai idan ka kalli fuskarsa, ko kuma ka ƙura wa ƙirjinsa ido, shi ne
za ka ga yadda yake ɗagawa a wani irin hankali. Bayansa Daneen ta bi da sauri, kamar yadda
shi ma yake saurin. Tana tafe tana goge fuskarta da hannayenta, ba tare da ta san abin da take
furtawa ba take ci gaba da faɗin abin da ya zo mata a rai.
"Ameer kar ka yi mini haka.. Ka tashi ka warke mu koma wajen Innarmu don girman Allah."
Ire-iren maganganun nan take ta furtawa tana bin