Showing 51001 words to 54000 words out of 81712 words
Chapter 18 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf
"Toh."
Hidaya ta amsa, kafin ta miƙe tana kallon Daneen ta ce
"Mu je koh?" Babu musu Daneen ta soma ƙoƙarin saukowa daga kan gadon. Da sauri Hidaya ta
riƙo ta saboda ganin yadda ta yi ta koma baya da sauri.
"Sannu." Ta sake furtawa cike da tausayin Daneen ɗin. Kusan a tare duk 'yan ɗakin suka sake
faɗin "Sannu." Ya yin da Abdoul ya ɗora da faɗin
"Bari na je waje Maama, zuwa an jima sai na shigo." Babu musu ta amsa da "Toh." Daga haka
Abdoul ya saka kai ya fice daga ɗakin, Sultanah ta bi shi da kallo tana murmushi.
Hidaya ce ta taimaka wa Daneen sosai wajen yin komai, don har cikin ranta tausayi take ba ta.
Sun kwashe fiye da rabin awa kafin suka dawo ɗakin. Nan ma dai ta taimaka mata ta sake
kwanciya, saboda yadda ta fi jin daɗinta. Don ita kanta ji take kamar ba ita ba. Wajen da aka
mata aikin kuwa babu laifi yana mata ciwo, amma dai ita wannan ɗin bai ɗaɗata da ƙasa sosai
ba, duk kuwa da cewar ba zafi ne normal ba, tana jin zafin har cikin jikinta, amma kuma ba ta
ɗauka hakan da muhimmanci ba. Don gani take duk wani zafi da za ta ji, toh zai biyo bayan
zafin da take ji na ganin ɗan'uwanta cikin halin ciwon da sanadiyyar wasu suka jefa shi. Sai a
lokacin sannan suka gaisa, dukkansu suna yi mata ya jiki.
"Alhamdulillahi." Shi ne abin da take amsawa da shi kawai, don ita dai gaba ɗaya hankalinta
yana kan Ameer.
"Mun gode sosai, Allah Ya saka miki da alkhairi, Allah Ya biya miki buƙatunki na alkhairi, Allah
Ya ba wa ɗan'uwanki lafiya." Dada ji ta faɗa tana jin har cikin ranta abin da yarinyar ta yi musu
yana ɗaya daga cikin alfarmomi masu matuƙar muhimmancin da har abada ba su taɓa
mantawa da shi ba. Ba kuma za su taɓa iya biyanta abin da ta musu ba.
"Ameen, ina so na ga ƙanina." Ta faɗa a narke tana kallon Dada ji. Ajiyar zuciya Dada ji ta
sauke tana kallon Maama ta ce
"Anya kuwa za su bar ta ta fita?" Kallon ta Maama ta yi kana ta ce
"Hakan ba damuwa ba ne, amma kuma ai jikinta za a duba. Ki bari idan kin ɗan ƙara jin
dama-dama ko zuwa gobe ne sai ki je ki gan shi." Maama ta ƙare maganar tana kallon Daneen.
Runtse idanunta Daneen ta yi tana jin yadda take bugun zuciyarta ya ƙaru. Ta yaya ma za ta iya
haƙura ba tare da ta ga ɗan'uwanta ba? Ba ta san lokacin da ta miƙe ba, duk da yadda wajen
ciwonta ya amsa, amma hakan bai dame ta ba. Sai dai ta runtse idanunta na tsawon sakanni
kafin ta buɗe. Ta ce muryarta na karkarwa.
"Don Allah ki bar ni na je na gan shi kin ji? Zan iya tafiya, zan iya komai ma kin gani?" Ta yi
maganar tana soma miƙewa tsaye. Da sauri Hidaya da Sultanah suka miƙe, suka riƙo ta.
"Maama don Allah ki bar ta ta je, tana so ta gan shi ne." Hidaya ta faɗa fuskarta a narke tana
kallon Maama.
"Toh shi kenan, ku je ke da Sultanah ku raka ta. But u should go and ask doctor Adam, za ta iya
fita?" Jinjina kai Hidaya ta yi tana sakin Daneen a hankali ta fice daga ɗakin. Daidai lokacin da
wayar Maama ta yi ƙara. Ta kalli mai kiran kafin ta ɗaga. Sai da suka gaisa kafin daga can
ɓangaren Umman Jawahir ta ce
"Ya mai jikin?"
"Alhamdulillah, jiki da sauƙi." In ji Maama.
"Wallahi na ƙagu mu dawo in ga jikin yarona. Kin ga musamman ma dai Jawahir duk ta bi ta
ɗaga hankalinta. Tun da aka kwantar da shi a asibitin nan ta ɗauki damuwa ta ɗora wa kanta,
yanzu haka ma kin ganta kuka take, don Abbanta ya ce ba gobe za mu taho ba." Murmushi
Maama ta yi, a ranta tana ji idan Allah Ya yarda yaronta ya samu mace mai sonsa tsakani da
Allah kenan.
"Ayyah Allah Sarki Jawahir. Ai babu komai me ye na damuwar? Jikin nasa kuma da sauƙi ai, ki
ƙara rarrashinta."
"Ni ma haka nake faɗa mata. Kin ji koh Jawahir?" Umma ta ƙare maganar tana kallon Jawahir
da ke gefen ta.
"Yawwah." Maama ta faɗa.
"Toh Allah Ya ƙara afuwa. Kuma In Sha Allah muna dawowa nan za mu taho babu ɓata lokaci."
"Allah Ya yarda." Daga haka suka yi sallama. Ba ta daɗe da ajiye wayar ba Hidaya ta dawo cikin
ɗakin. Ita da Sultanah suka taimaka wa Daneen wajen kai ta ɗakin da Ameer yake. A bakin
ƙofar suka bar ta.
"Bari mu jira ki a nan." Hidaya ta ƙare maganar tana sakin murmushi. Ita ma murmushin ta
ƙaƙalo kafin ta jinjina kai. Daidai lokacin da Yohanah ya fito daga cikin ɗakin, yana shirin rufe
ƙofar ya ga Daneen. Sai ya saki murmushi yana faɗin
"Ke ce?" Jinjina kai Daneen ta yi hannunta dafe da gefenta don ta fi jin daɗin tsayuwar.
"Ki ƙara gode wa Allah, saboda da alama an yi aikin nan cikin nasara. Ameer na dab da samun
lafiya." Ba ta san lokacin da wani murmushi ya suɓuce mata ba, sam sai ta kasa amsa wa
Yohanah maganarsa, ban da ƙarasawa ciki da ta yi don ta gane wa idanunta. Shi ma bai damu
da amsar tata ba ya wuce ta gaban su Hidaya da babu wadda ta kalle shi har ya bar wajen.
Cike da sassarfa take ƙarasa wa cikin ɗakin idanunta a kan Ameer da idanunsa ke a lumshe.
"Ameer." Ta faɗa tun kafin ta ida ƙarasawa inda yake. Kamar a mafarki ya ji muryar 'yar'uwarsa,
don bai taɓa tunanin zai sake buɗe idanu ya ga wani ɗan'adam ba, a lokacin da za a masa aiki.
Sai ga shi da alama an gama masa aikin, ga shi kuma zai ƙara ganin 'yar'uwarsa. Abin da dai
bai sani ba kawai shi ne, shin zai sake ganin Inna-wuro?
"Ameer." Daneen ta sake faɗa tana riƙo hannayensa. Wasu irin ƙwalla ne suka sakko daga cikin
idanunsa zuwa kan kuncinsa.
"Addatah." Ya faɗa muryarsa a wani irin cunkushe.
"Na'am Ameer, ka warke koh?" Ta tambaya tana jin wani irin farin ciki na ziyartar ta. Murmushin
yaƙe Ameer ya yi kafin ya ce
"Ba na tunanin har abada zan warke Addaneen. Ina ji a jikina kamar ba zan ƙara ganin Innarmu
ba, duk da yadda nake son ganinta. Na so a ce na ga babanmu kafin na tafi na bar ki Addatah.
Ban san zuwanmu garin nan shi ne silar rugujewar farin cikinmu ba, da ban matsa mun taho ba.
Ban san neman kuɗin koma wa ƙauyenmu zai sake zama wani ɓangare na wargajewar farin
cikinmu ba, da ban nema ba. Na yi nadama matuƙa, na janyo wa kaina. Kalli yadda mutanen
nan suka lalata mini rayuwa, zuciyata kuma rauninta na da yawa shi ya sa ta kasa daurewa.
Adda kin san su ɗin su waye?" Kallon sa kawai take yi tun da ya soma magana har ya dakata, ji
take gaba ɗaya maganganun kamar ba na Ameer ba, kamar ba Ameer ɗinta ƙaninta mai tarin
ƙuruciya da shiririta ba. Sai ta ji maganganun da suke fitowa daga bakinsa tamkar wanda wani
babba yake yin su. 'Shin me yake shirin faruwa?' Ta tambayi kanta tana maida dubanta kan
Ameer.
"Ni na faɗa maka ina buƙatar sanin su waye su Ameer? Wanne irin maganganu ne suke fito wa
daga bakinka Ameer? Ba ka da hankali ashe dama?" Ta faɗa tana jin yadda ilahirin jikinta ke
karkarwa tamkar mazari. Girgiza kai Ameer ya yi, ya yi nasarar kamo hannun Daneen cikin
nasa ya ce
"Ban sani ba ko Allah zai sa ki samu dama ki shigar da su ƙara Addah, ban sani ba ko bayan
raina za ki buƙaci sanin sunan mutanen da suka datse mana farin cikinmu, suka yi mana
katangar ƙarfe da rayuwarmu mai daɗi, suka kuma zamo sanadiyyar rabuwarki da ɗan'uwanki."
Wani mari Daneen ta kai wa Ameer a gigice tana jin yadda jikinta ke ci gaba da ɗaukar rawa.
Tuni idanunta sun soma zubar da hawaye. Jin maganganun Ameer ɗin take har cikin kowacce
gaɓa ta jikinta.
"Ameer ba ka da hankali? Ba ka da hankali ashe dama? Ashe ba ka sona Ameer? Ashe ka
tsane ni Ameer ban sani ba? Wasu irin maganganu kake faɗa haka mara sa daɗin ji? Toh ko dai
so kake zuciyata ta tarwatse?" Ta tambaya cikin kuka tana kallon yadda ya runtse idanunsa.
Duk da yadda ya ji zafin marin, amma hakan bai sa ya ji ya karaya ba. Shi kaɗai ya san me
yake ji yanzu haka a cikin gaba ɗaya jikinsa, wasu abubuwa yake ji waɗanda ko za a kashe shi
ba zai iya kwatanta su ba. Hannunsa ya saka da iya ƙarfin da yake da shi ya janyo Daneen ɗin,
idanunsa a lumshe ya saka bakinsa saitin kunnenta ya soma faɗi a wahalce, sannan kuma a
rarrabe, a kuma hankali.
"Ki yi haƙuri Adda, ko da za ki buƙaci sanin su waye su.." Sai ya dakata a nan yana sake riƙe
hannun Daneen da masifar gaske.
"Ki fara shari'a da yaron gidan Alhaji Dikko, shi ne shugaba kuma ogan duk waɗanda suka yi
amfani da.." Maganar da ta kasa fita kenan, saboda wani yunƙuri da ya yi. Cikin second ɗaya ya
saki hannun Daneen, wanda hakan ya tilasta mata saurin kallon fuskarsa. Numfashinsa ne yake
fita da wani irin sauri, tuni idanunsa suka soma ƙaƙƙafewa, ya yin da ya fara wata irin shaƙuwa.
Wani mahaukacin karkarwa da jikinta ke yi shi ne ya sanya ta runtse idanunta. Ta buɗe su a kan
Ameer da ta ga yana wasu abubuwa waɗanda ba ta taɓa ganin irin su ba. Don haka ta yi saurin
riƙo shi tana faɗin
"Ameer." Ta faɗa da ƙarfin gaske, tana ci gaba da kallon yadda yake kokawa da numfashinsa.
Kwata-kwata tunaninta bai kawo mata ta je ta kira likita ba, don saboda tsananin ruɗewa, kawai
kiran sunansa take. Sai zuwa can da ta ga dai babu sauƙi sai a wajen Allah, hakan ne ya sanya
ta sakinsa, ta sake sauke luhu-luhun jajayen idanunta a tsakiyar kyakykyawar fuskar Ameer
daidai lokacin da ya ja wata ƙatuwar ajiyar zuciya, ta juya don zuwa kiran Likita. Sai dai a
maimakon ɗazu da sautin fitar numfashin Ameer ya cika dodon kunnenta, sai ta ji shiru. Cakk ta
dakata tana buɗe idanunta da har wani rufewa suke don kansu saboda tsabar kukan da suka
sha har suka gaji. Fata take a ce numfashin nasa ne ya daidaita, ya kuma daina duk wasu
abubuwa da ta ga yana yi waɗanda ba ta taɓa gani ba. Sai dai wata daƙiƙiyar faɗuwar gaba da
ta ji ita ce ta sanya ta sake runtse idanunta na tsawon sakanni, kafin ta buɗe a hankali ta juya
idanunta a kan gadon da Ameer ke kai.
*♡☆DANEEN☆♡*
Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)
Mikiya Writers Ass..
Book 1
Pg 21
Ƙura masa kumburarrun idanunta ta yi tana kallon yadda gaba ɗaya ya wani miƙe a kan gadon,
gaba ɗaya sautin nan nasa da take jiyo wa ta daina ji kwata-kwata. Maimakon ta ji farin cikin
fahimtar numfashinsa ya daidaita, sai ta ji wata irin faɗuwar gaba ta ziyarce ta, wadda ta sanya
ta saurin runtse idanunta. A hankali ta shiga taka wa zuwa kan gadon, har lokacin idanunta a
kan Ameer. Hannunta duka biyun ta saka ta riƙo fuskarsa, a sanyaye ta furta
"Ameer." Ta ƙare sunan da ya gama fita da sautin bugawar zuciyarta. Shiru babu amsa. Ba tare
da kawo komai cikin ranta ba ta sake kiran sunansa a karo na biyu, nan ma dai shiru, bai kuma
motsa ba, haka zalika bai kalle ta ba. Cikin ƙanƙanin lokaci jikinta ya ɗauki rawa. Ta sake yin
amfani da duka hannayenta biyu wajen riƙo shi, ta shiga jijjiga shi a haukace tana faɗin
"Ameer ka tashi, Ameer ka tashi mana. Meye haka kake yi Ameer? Ameer.." Ta ƙare maganar
cikin ɗaga murya. Dalili kenan da ya sa Hidaya da Sultanah da ke waje saurin shigo wa cikin
ɗakin. Ko sanin sun wanzu cikin ɗakin ba ta yi ba, a haukace ta ci gaba da faɗin
"Ameer ka tashi mana Ameer ka tashi don girman Allah." Ta faɗa muryarta na wani irin sarƙewa.
A tsorace suke kallon abin da ke faruwa tsakanin Daneen da Ameer, gaba ɗaya tashin hankali
ne ya bayyana a kan fuskarsu. Sultanah ta kalli Hidaya, murya can ƙasa ta ce
"Sisi je ki kira Likita." Sai da Hidaya ta lumshe idanunta tana jin wani irin tausayin Daneen ɗin
na kama ta kafin ta fice daga ɗakin. Babu daɗewa suka shigo tare da Likitan, har kuma zuwa
lokacin Daneen ba ta haƙura ba, ci gaba take da jijjiga Ameer tana kiran ya tashi, ya buɗe
idanunsa. Hidaya ce ta ƙarasa ta riƙo Daneen tana faɗin
"Bari Likita ya duba shi." Hannu Daneen ta saka tana shirin ƙwace jikinta a lokaci ɗaya tana
furta
"Kin gan shi fa ba ya motsi." Ta ƙare tana nuna Ameer ɗin da hannunta ke wani irin karkarwa.
Riƙe ta sosai Hidaya ta yi tana faɗin
"Ehh, ki bari ya duba shi." Ta faɗa cikin rarrashi tana rungumo Daneen ɗin. Tun kafin ta kai ta
jikinta take iya jiyo sautin bugun zuciyarta da yake fita da wani mahaukacin gudu. Gaba
ɗayansu ƙura wa Likitan idanu suka yi, suna kallon lokacin da ya fara gwada Ameer. Daneen ta
kafe shi da jajayen idanunta tana jira ta ji abin da zai faɗa. Zuwa can sai ta ga ya zame abin da
ya saka a kunnensa, ya kuma ja zanin da ke a iya cinyar Ameer ya rufe masa fuska, ya sauke
ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa, kafin ya juyo a sanyaye idanunsa a kan Daneen da ita ma
shi take kalla tamkar idanunta za su faɗo.
"Ameer ba ya tare da mu, Ki yi haƙuri Allah Ya karɓi abinsa." Ya faɗa a sanyaye, don shi kansa
ya matuƙar gigita da mutuwar Ameer ɗin, saboda yadda bayan an gama masa aikin ya gwada
masa komai ya ga normal, kuma suke saka masa ran samun lafiya da yardar Ubangiji cikin
ƙanƙanin lokaci, sai ga shi cikin awannin da ba su da yawa Allah Ya karɓi abinsa. Kwata-kwata
ma ba ta ji abin da ya faɗa ba, saboda yadda hankalinta ya koma kan Ameer da ta ga Likitan ya
lulluɓe.
"Me ya sa za ka rufe shi? Kar ya kasa shaƙar iska." Daneen ta faɗa bayan ta yi nasarar fusge
hannunta daga cikin na Hidaya, ta ƙarasa tana ƙoƙarin buɗe Ameer.
"Ki yi haƙuri Ameer ya koma wajen mahalliccinsa." Likitan ya faɗa don ya ga alama ba ta
fahimce shi ba.
"Ƙarya kake yi Ameer ɗina bai mutu ba, Ameer bai mutu ba, Ameer ba zai taɓa iya tafiya ya bar
ni ba." Ta ƙare cikin ɗaga murya tana kallon Likitan. Kafin ba tare da ta bi ta kansa ba, ta saka
hannu ta yaye lulluɓin da ya yi masa, ya zamana tana iya kallon fuskar Ameer, ta ce tana
bubbuga fuskar tasa.
"Ameer ka tashi ka ƙaryata abin da mutumin nan yake faɗa, ka tashi ka yi mini magana Ameer.
Ameer don Allah kar ka tafi ka bar ni, kar ka yi mini haka Ameer. Ya ya zan yi da rayuwata idan
ya zama babu kai? Mai zan koma na cewa Inna idan ka yi mini haka? Don Allah idan wasa kake
yi ka tashi Ameer. Me ya sa zuciyarka ba ta da juriya ne Ameer, me ya sa ka koyi rashin juriya
bayan a da kai ne me juriyar. Yanzu ni za ka yi wa haka Ameer? Tafiya ka yi ka bar ni a wannan
duniyar Ameer?" Daneen ta faɗa cikin gigitaccen kuka tana girgiza kanta. Idanunta har wani
hazo-hazo take gani saboda tsabar kuka.
"Ka tashi Ameer, ni ce fa nake ce maka ka tashi, wai so kake su sake ce mini ka mutu? Ameer
me ya sa za ka yi mini haka?" Ta ƙare maganar tana kifa kanta a ƙirjin Ameer, ta shiga girgiza
kanta tana fidda wani irin sautin kukan da ke fitowa tun daga can ƙarƙashin zuciyarta. Hannu
Hidaya ta kai ta riƙo Daneen, duk da yadda ta kasa ko gezau ne ta ƙi ɗaga jikin Ameer, hakan
bai hana Hidaya yin iya ƙoƙarinta ba wajen ɗago ta. Sai kuwa ta faɗa jikinta tana fashewa da
sabon kuka, mai tsuma zuciyar mai sauraro. Kuka take irin kukan nan da ke fita haɗe da zafin
da ɗan adam ke ji a cikin zuciyarsa.
"Kin ga ya ƙi kula ni koh? Ya ƙi yi mini magana don in yarda da abin da wancan mutumin ya
faɗa. Me ya sa Ameer zai mutu ya bar ni? Bai san yadda nake ƙaunarsa ba ne?" I zuwa lokacin
Hidaya kasa jurewa ta yi, kawai ita ma sai ta fashe da kukan tana saka hannunta ta dafe kan
Daneen da ke kan kafaɗarta. Wani irin tausayin Daneen ɗin na ci gaba da ratsa ta. Nauyin da ta
ji ne a jikinta ya sanya ta kai hannunta ta goge hawayen kan fuskarta, daidai lokacin da
Sultanah ke faɗin
"Hidaya kamar ta suma fa?" Ta ƙare maganar kamar mai tambaya. Likitan da kansa ya yi kiran
nurses aka zo aka fitar da Daneen ɗin da ta fice a hayyacinta gaba ɗaya daga cikin ɗakin. Duka
suka bi ta da kallo ba tare da kowa ya ce komai ba.
Lokacin da su Maama suka ji labarin rasuwar Ameer ba ƙaramin tashi hankalinsu ya yi ba.
Kusan gaba ɗaya suka