Showing 39001 words to 42000 words out of 81712 words

Chapter 14 - DANEEN BOOK 1 BY ZAHRA YUSUF MHIZ INNOCENT).pdf

ni."

"Wallahi Adda ina can ina tunanin kar ganin na daɗe ki ce za ki je ki nemo ni, in zo kuma ban
gan ki ba in shiga 3." Ya ƙare fuska a marairaice. Har ba ta san lokacin da dariya ta suɓuce
mata ba.

"Mu je mu samu ruwa mu yi sallah tukunna." Ta faɗa. Be musa mata ba, ya amsa da "Toh."


... Tun daga farkon layin idan ka kalla za ka fahimci lallai wani gagarumin al'amari ke faruwa.
Saboda yadda motoci ke ta kai-kawo cikin layin, 'yan sanda na ta zagaye, haka zalika mutane
na ta kai da kawowa. Kowa ka kalli fuskarsa cikin annushuwa yake, wanda hakan ze alamta
maka cewa ko ma mene ne abin da ke faruwa abin farin ciki ne. Tahowar wata ƙatuwar
hamshaƙiyar mota da kallo ɗaya za ka mata ka san kuɗinta ba na wasa ba ne, shi ne abin da ya
sa masu gadin gidan wangale ƙatuwar ƙofar gidan tun kafin motar ta ƙaraso. Tuni kyakykyawan
dattijon mutumin da ke sanye cikin farar shaddar da ta matuƙar yi masa kyau, ta kuma sake

bayyana kwarjininsa da kamalarsa ya gyara zamansa. Tun kafin ya ce komai, drivern ya yi
hanzarin wangale glasses ɗin motar. Wanda hakan ya ba wa mutanen da ke tsaye suna jiran
zuwan Alhajin nasu damar soma ganinsa. Cikin lokaci ƙanƙani fuskarsa ta cika da annuri, ya yi
amfani da hannunsa wajen ɗaga musu hannu fuskarsa na cigaba da nuni da yadda ya yi farin
cikin ganin su. Alhaji Alhassan Dikko kenan, mutum mai matuƙar kima da mutunci a idon
jama'a, mutum mai matuƙar taimako da jiki da dukiyar da Allah Ya ba shi. Mai kirki, mai matuƙar
kula da buƙatun mabuƙata, maƙotansa da kuma mutanen gari. Wanda hakan ya saya masa
soyayyar mutane da dama, ya kuma ƙara masa kimar da tun tale-tale yake da ita. Har sai da
suka dangana da cikin gidan sannan mutane suka haƙura. Daga haka aka rufe gate ɗin bayan
motocin da ke bin bayan ta Alhaji Alhassan su ma sun shige cikin gidan. Shi har ya riga ya
saba, duk lokacin da ya yi tafiya irin wannan haka mutane ke masa duk ranar da ze sauka a
ƙasar. Don kuwa ƙarya ne mutum ya ce be yi kewarsa a en kwanakin da ya yi ba ya ƙasar ba.
Saboda yadda ya kasance mutum mai matuƙar kula da duk wanda ke kusa da shi. Duk da kafin
ya tafi yana ɗora wani a kan abubuwan da yake yi, amma duk abin da ze yi, ba ze kai wanda
yake yi ba. Shi ya sa idan yana nan abubuwa da dama suka kasance na daban, suke kuma
tafiya a tsari.

Ko a cikin gida ma hakan ce ta kasance, mutanen da ke zaune cikin gidan tuni suka fara zuwa
suna kwasar gaisuwa, kamar kodayaushe fuskarsa cike da annuri yake amsa musu. Kai tsaye
sashensa ya wuce kamar yadda ya saba, sashen nasa na nan a gyare tsaff-tsaff kamar yadda
ya tsammata. A gaggauce ya watsa ruwa a jikinsa kana ya sake shiryawa cikin babbar rigar
shadda ita ma fara. Kai tsaye ya wuce sashen Dada ji da gaba ɗaya iyalan nasa ke jiran sa a
can ɗin. Ai kuwa cikin matuƙar farin ciki dukka suka tarbe shi lokacin da ya iso. Kowa ka kalli
fuskarsa ka san tabbas yana cikin farin ciki. Sai da ya shafe wajen mintina goma, sannan
Maami ta iso, ita da Mom Abdoul, ba ta yi tsammanin kai tsaye nan ɗin ze wuto ba. Shi ya sa ta
din ga tsumayin ganin inda ze nufa, sai dai shirun da ta ji ne ya tabbatar mata da tabbas nan ɗin
ya nufo. Wannan ne dalilin da ya sa ta ɗebo 'yan matan ƙafafunta ta taho, duk da ta so tare
suka shigo. Dan da ta san ma ba zai shiga sashenta ba, tun a harabar gidan za ta je ta tarbe shi
don su shiga sashen Dadan a tare. Ko minti 5 ba su yi da zama ba, bayan sun yi wa Abeey
barka da zuwa, Amininsa Alhaji Bashir ya iso gidan, mahaifi ga Abdoul. Sosai farin cikin Abeey
ya daɗu. Bayan kwanaki masu yawa, yau ga shi tare da iyalansa, ga kuma abokinsa ƙwalli ɗaya
takk da yake da shi tun yarinta shi ma. Wannan dalilin ne ya ƙara ƙawata zaman nasu. Nan aka
shiga hirar yaushe gamo. Kafin zuwa can aka nufi ɗakin da ya kasance na cin abinci, nan cikin
sashen Dada ji. Sultanah, Hidaya da Jawahir su ne suka kwaso komai daga kitchen ɗin Dada ji
suka jere shi kan dinning ɗin. Abubuwa ne kala-kala masu aji, waɗanda aka yi abubuwan da
Abeeyn ya fi so a rayuwarsa. Baƙin-ciki kamar ya kashe Maami, da ta tuna abincinta na can
jibge yana jiran Abeeyn. Kenan idan ya zauna ya ci abincin a nan, ita kuma nata ya za ta yi da
shi? Ita fa dama wannan tsohuwar tana matuƙar shige mata hanci da ƙudundune, tana yawan
kawo mata cikas a cikin al'amuranta.
A kusa da Dada ji ya zauna, don babu ƙarya ya yi kewar mahaifiyar tasa. 'Yan matan ba su
zauna ba, sai da suka yi serving na kowa kafin suka ja kujera suka zauna. Duk yadda Sultanah
ke ƙoƙarin ta jure, ba ta din ga satar kallon Abdoul ba, hakan ya gagara, ta kasa daurewa. Don
haka a ɗan fuzge ta din ga satar kallon shi, cike da fatan kar ya kama ta, ko kuma Yah Tareeq

ya gan ta, ya tuna be yi mata faɗa a kan abin da ta yi ba. Don kuwa tun da ta ga ya kalli saƙon
be ce komai ba, ta san tabbas wani abun yake shiryawa, dalilin kenan da ya sa take jin jikinta a
matuƙar sanyaye. Ita dai Jawahir sai sakin murmushi take yi, saboda yadda Ummanta ta sanar
da ita Maama ta tabbatar mata da za ta isar wa da Abeey maganarta ita da Tareeq. Ita kuma
dama ba ta da wani buri illa na mallakar Tareeq ɗin. Ba tun yau ba, kyawunsa ke matuƙar kashe
ta, tana ƙaunarsa ainun, tana matuƙar son kallon kyakkyawar fuskarsa, da kuma irin ƙirar da
Allah Ya ba shi. Sai bayan sun gama cin abincin sannan suka koma palourn Dada ji, nan aka
cigaba da hira sosai. Sai dai idan dai har abin ya shafi Maama, toh ba za ka ji Maami ta ce
komai ba. Don ita hirar ta ta fi kasancewa ne tsakaninta da Hajiya Zulai, da kuma Alhaji Bashir.
Duk abin da take Dada ji na lura da ita, ta yi dai kamar ba ta gani ba ne. Don ita kam har ta gaji
da yi mata magana a kan halayenta. Maamin wata irin mata ce da lokuta da dama ka kan kasa
gane kanta. Ban da haka idan hali mai kyau ne Maama ta fi ta. Amma kuma ita burin ta kawai
kowa ya yi harkarsa, ba ta son wani abu ya haɗa ta da abokiyar zaman nata kwata-kwata. Sai
ka ce masu zaman gaba, wanda ita Dada ji ba za ta ɗauki hakan ba. Duk da hakan ya fi saka
wa su zauna lafiya, amma kuma babu yadda za a yi su zauna babu magana, bayan suna zaune
ne cikin gida ɗaya, ƙarƙashin mutum ɗaya. Kuma hakan ya samo asali ne, tun wani ɗan tashin
hankali da ya faru tsakanin su, Dada ji ɗin da kanta ta shirya al'amarin, ta ce babu ruwan kowa
da kowa. Shi kenan Maami ta riƙe wannan maganar, a cewar ta ai an ce da ita babu ita babu
Maama. Ya yin da ta ɓangaren Maama, duk wani abu da ya shafi Maami babu ruwanta da shi,
amma tabbas idan suka haɗu za ta mata sallama, da sauran su. Girgiza kai Dada ji ta yi. 'Mace
sai ka ce mai zuciyar kafirai, kina abu tamkar ƙaramar yarinya. Toh ai ga mijin naku nan ya
dawo, sai ki ci gaba da gaba da abokiyar zaman naki' Ta raya hakan a ranta.

Kallon Tareeq Abeey ya yi da ya miƙe yana gyara tsayuwarsa hannunsa ɗauke da waya.

"A'ah, Tareeq ina za ka je ne?" Ɗan murmushi ya yi a kan laɓɓansa kafin ya ƙarasa gaban
Abeeyn ya tsuguna a gefen kujerar da yake kai ya ce a nutse

"Abeey, ina buƙatar fita ta gaggawa." Daga haka suka ɗan yi magana ta tsawon mintina biyu a
hankali, wanda babu wanda ze ce ya ji abin da suka faɗa. Kallan Tareeq Abeey ya yi, kana ya
ce

"Ubangiji Allah Ya tsare, zuwa gobe ma samu mu tattauna." Abeey ya faɗa yana ɗan kafe shi da
idanunsa, saboda tabbatar da abin da idanun nasa ke ganar masa a fuskar ɗan nasa.

"Ameen Abeey." Ya faɗa yana miƙewa. Sallama ya yi da duka mutanen ɗakin kafin ya fice. Kai
tsaye sashensa ya wuce, ya ɗauki abin da ze ɗauka ya fice daga gidan. Ba shi ya dawo cikin
gidan ba, sai bayan ƙarfe 12pm. Don haka ruwa kawai ya watsa ya kwanta don yadda idanunsa
ke buƙatar bacci.

... "Idan da zaɓi za ka ba ni, toh tabbas zan nemi soyayyar Hidaya ne, saboda Sultanah
mahaifiyarta duk da kasancewarta aminiyar Ummeey ina shakkar ta wallahi." Abdoul ya ƙare

yana shafa kansa. Dariya Tareeq ya yi jin abin da ya faɗa. Ya ja siririn tsaki kafin ya ce

"Amma dai ka ba ni kunya Abdoul.. Amma dai ba wannan ba, ni nan ni ne amininka, kuma ina
mai ba ka shawara da ka nemi Sultanah saboda ta fi Hidaya sauƙin kai. Abeey dai shi zai aurar
da Sultanah ba Maami ba, idan kuma ba shi ba ni ne. Don haka kar ka ji komai, duk da ma
Maami na da kirki wani lokacin, amma fa idan ka fahimce ta." Jinjina kai Abdoul ya yi irin a
yatsinen nan, cike kuma da rainin hankali ya ce

"Ehh, haka fa." Wani murmushi Tareeq ya saki ba tare da ya ba wa yanayin Abdoul ɗin
muhimmanci ba ya ce

"Uhmm." Gyara zama Abdoul ya yi, bayan ya sauke ajiyar zuciya ya ce

"Ka tabbatar?" Jinjina masa kai Tareeq ya yi ba tare da ya ce komai ba. Don haka Abdoul ya ce

"Shi kenan, zan gwada.. Allah Ya ba ni sa'a." Ya ƙare irin a marairaicen nan. Cike da jin daɗin
yadda burin ƙanwar tasa ke neman cika ya janyo wayarsa cikin basarwa ya ce

"Bari na soma sanar da ita, don ta fi ɗaukar abin da muhimmanci." Da sauri Abdoul ya riƙo
hannunsa yana girgiza kai ya ce

"A'ah kar ka kira ta, kar ya zamana hakan ya koma tirsasawa, gwara ka bar ni da kaina na yi
mata magana, na san duk wani abu da ke ranta za ta fito ta faɗa mini ba tare da wani shakku ko
tsoro ba, tun da ba zan nuna mata ta hanyarka na biyo ba." Sauke ajiyar zuciya Tareeq ya yi,
irin 'Shi kenan toh' ɗin nan, kafin ya ce
"Allah Ubangiji Ya tabbatar da alkhairi. Amma tsaya ka tabbatar ba karɓar tayin nan ka yi
saboda mutuncinmu ba? Za ka so ƙanwata kamar yadda nake fatan ita ma za ta so ka? Ka san
ba na son a wulaƙanta mini er'uwa." Dariya sosai Abdoul ya yi, kana bayan ya dena ya soma
faɗin
"Tareeq manta wane ne kai kake a wajena, ka manta duk wani abu da ya shafe ka dole ne a
wajena na so shi? Toh ka manta da wannan son, ba irin shi zan yi wa Sultanah ba, nata na
daban ne, matuƙar dai ta amince da ƙudurin da zan je mata da shi." Wani irin sanyi ne ya ji yana
ratsa shi, ya lumshe kyawawan idanunsa yana jin har cikin zuciyarsa farin ciki mara misaltuwa.
Wato har abada ba zai daina alfahari da kasancewar Abdoul amininsa ba. Fata yake hakan ya
zama silar farin cikin er'uwarsa na har abada. Yana fatan hakan ya zama dalilin sake ɗorewar
zumuncinsu da su Abdoul na har abada. Yana fatan wannan abu ya zama ɗaya daga cikin abin
da zai zama cikin tarihin gidan Iyalan Dikko na sama-sama.


.. Washe gari ma suna tashi da safe a wajen da suka kwana jiya, Ameer ya yi sallama da
Daneen ya tafi inda ya sami aikin. Ita kuma ta ci gaba da zama a wajen, saboda gurin ya fi

security, kuma babu mutane da yawa, can kuwa maza ne kawai, kafin ka ga mace ma aiki ne.
Shi ya sa ya ce ta zauna, idan ya gama aikin sai ya dawo. Ranar ma be dawo da wuri ba, sai da
ya kai kamar jiya sannan ya dawo da abinci mai rai da lafiya. Kamar jiya ma cikin farin ciki ya
kawo wa 'yar'uwar tasa abincin, ɗan kuɗin da ya samo suka yi amfani da su wajen abubuwan
buƙata, ya yin da Daneen ta ɗauki wani abun ta ajje musu, wanda za ta din ga ɗauka kullum ta
ajiye har su kai adadin wanda suke buƙata su nufi ƙauyensu.

Haka Daneen da Ameer suka ci gaba da kasancewa a wannan wajen. Da safe bayan sun
gama abin da za su yi Ameer zai tafi wajen aiki, ita kuma ta ci gaba da zama a wajen har ya
dawo. Sai dai ga mamakin Daneen, sai ta lura da tun ranar da Ameer ya samu aiki, da kuma
washe gari da yake dawowa cikin matuƙar farin ciki, be sake dawowa kamar haka ba. Tun daga
ranar duk lokacin da ya dawo jikinsa a matuƙar sanyaye yake. Babu wannan nishaɗin, sai tarin
damuwa da kuma tunani.

"Wai Ameer me kake ɓoye mini? Me yake faruwa?" Daneen ta faɗa tana kallansa, cike da sake
nazarinsa. Da sauri ya ɗaga idanunsa ya kalle ta a nutse kafin ya buɗe baki ya ce

"Babu komai Adda.. Wani abun kika gani?" Girgiza kai ta yi cikin ɗan faɗa ta ce

"Shi kenan, amma ka sani daga yau ba za ka sake zuwa wajen aikin nan kai ɗaya ba. Idan ba
haka ba kuma sai dai ka dena zuwa gaba ɗaya. A haƙura da tara kuɗin kawai." Be san lokacin
da ya ɗaga idanunsa ya kalle ta ba, daidai lokacin da ƙirjinsa ya wani mahaukacin bugawa. Sai
ya shiga girgiza kai kamar wani ƙadangare kafin ya ce
"A'ah Adda, kin san gidan biredi babu mata, ba ze yiwu ki ce za ki din ga zuwa ba. Idan ba haka
ba za su kore ni gaba ɗaya."

"Eh, gwara su kore ka, idan dai har za ka ci gaba da dawowa da damuwa." Sauke numfashi
Ameer ya yi, ya lumshe idanunsa masu kama da na Daneen, ya rasa me yake damun
ƙwaƙwalwarsa. Gaba ɗaya kansa a hargitse yake. Idan da zai dena zuwa da sai ya fi kowa farin
ciki. Sai dai kuma yadda yake ji tamkar ana azalzalarsa da zuwa wajen ya ji kwata-kwata ba ze
iya daina zuwa ba. Kai ko da ma Daneen ɗin ce ta ce ya dena zuwa, a yadda yake jin gaba
ɗaya tunaninsa da nutsuwarsa ta tafi can ɗin ba ya tunanin zai iya amincewa da hakan. Sai dai
kuma gefe guda yana ji shi kansa da zai iya hana kansa dena zuwa da ya dena. Wannan dalilin
ne ke sanya shi jinsa tamkar wani zautacce, saboda yadda tunani da ra'ayi biyu ke ta masa
yawo a cikin kwanya, kwanyarsa shi ɗaya. Kuma duka hankalinsa ya kwanta da su.

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 17

Ƙura masa idanu Daneen ta yi, tana so ta ga ko za ta iya karantar abin da yake ɓoye mata, don
tabbas tafarar ɗaya ta fahimci hakan. Sai dai ba ta ce masa komai ba, har zuwa lokacin da ya
dawo daga mara armashin tunaninsa ya sauke idanunsa a kanta. Duk kuma sai ya so ya
duburbuce saboda ganin tana masa wani kallo da ya fi kama da na tuhuma.
"Adda." Ya faɗa a sanyaye. Da sauri ta girgiza kai

"Kar ka kira sunana, kawai ka buɗe baki ka faɗa mini abin da ke faruwa, idan ba haka ba na
faɗa maka ba za ka sake zuwa ba." Ta ƙare maganar da iya gaskiyarta har lokacin tana kallon
sa. A sanyayen dai ya sake faɗin

"Ki yi haƙuri Addatah, shi kenan ki shirya mu din ga tafiya tare ai shi kenan koh?" Sai a lokacin
ta yi murmushi kafin ta ce

"Toh damuwar ta mene ne?"

"Gajiya ce fa kawai." Ya faɗa bayan ya langaɓar da kansa.

"Ai dai mun kusa koma wa wajen Innarmu In Sha Allah." Jinjina kai Ameer ya yi yana murmushi,
sai dai bai ce komai ba.

Kamar yadda ya faɗa kuwa, washe gari tare suka tafi wajen aikin shi da Daneen. Suna tafe
suna hira, tana kallon duk inda suka wuce, saboda ita ba ta taɓa zuwa wajen ba. Don
iyakincinta cikin kasuwa, idan suna buƙatar wani abu ta shiga ta siyo musu, daga nan ta koma
inda suke ta zauna. Sun yi tafiya mai ɗan tsayi kafin Ameer ya kalle ta ya ce
"Ki zauna a nan, kin ga cikin layin nan a nan gidan biredin yake, zan je idan na gama sai na fito
mu tafi." Kallon layin ta yi kamar mai son hango gidan biredin. Sai dai ba ta hango ba, amma ko
babu komai nan ɗin zai fi mata kwanciyar hankali tun da tana kusa da ɗan'uwanta. Don haka ta
gyara tsayuwarta ta ce
"Toh shi kenan Ameer, Allah Ya ba da sa'a, ina jiran ka fa." Ta ƙare a hankali tana kallon sa.

"Toh Adda bari na je." Ya ƙare yana ɗan murmushi, wanda ya yi nasarar lulluɓe tulin damuwar
da ke danƙare a zuciyarsa. Wadda ta hana zuciya da ƙwaƙwalwarsa sukuni.

"Allah Ya tsare." Ta sake maimaitawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login