Showing 1 words to 3000 words out of 65710 words

Chapter 1 - ZATO NE (1 TO End) BOOK COMPLETE By Maman Islam.pdf

14 Apr 2025

5213


[8/5, 9:44 PM] MAMAN ISLAM: *مسب الله نمحرلا ميحرلا *

*☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️*

FCWA

*Home of qualities and trusted writers of the nation*



https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?ty
pe=3&source=45&refid=17

_________________________



��ZATO NE��
NA

HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

WRITTEN
BY

MAMAN ISLAM

Daga marubuciyar

ABINDA YAKE,RAINA
WAYYO RAYUWATA

Da sunan Allah mai rahama dajin kai Allah kayi dadin tsira ga shugaba ja gaba annabin rahama
annabi Muhammad S A W tareda dukkan a halinsa da sahabbansa da wanda sukabi bayansa
har izuwa ranar karshe


Sharhi wannan labarin kirkirarren labarine banyishi dan cin zarafin wani ko wataba duk wanda
yaga labarin yayi daidai da rayuwar shi arashi ne


GARGADI

Ban yarda wani ko wata ya juyamin labari ta kowane irin sigaba yin hakan batare da izininaba
babban kuskure ne dan haka a kiyaye


PAGE 1

................wani katafaren gidane k'aton gaske mai dauke da k'aton get ruwan toka, a hankali na
tura get d'in gidan wanda da k'yar na iya bud'eshi.


Wani mahaukacin farfajiya ne mai girman gaske a kalla in za ajera motoci zai d'auki fiye da
ashirin.


Duk da kasan cewar gabana yafad'i da ganin girman gidan, hakan bai hanani bin gidan da
kalloba, filine kamar jeji

Sannan duk da girman gidan haka bai hana an baibayeahi da wasu fararen dutsuna masu
k'yalliba ga fitulu nan kewaye haskene fetal kamar rana.


Kaina tsaye na nufi ainihin k'ofar da zata sadani da cikin gidan, Allah ya temakeni nasami k'ofar
glass d'in abud'e da sauri na lallab'a na shige kamar b'arauniya,

Wata kyakykyawar farar mace na hango wacce akalla zatakai shekaru sittin da bakwai zuwa da
takwas.


Wani farin saurayi na gani wanda bana ganin fuskarsa domin agaban matar yake azaune ya
sunkuyar da kansa k'asa da alama maganar mai muhimmanci ne.

Da sand'a nabi ta gefansu na wuce inuwata yasa matar d'agowa nayi maza na b'uya abayan
d'ima d'iman kujerun da sukayiwafalon k'awanya.


Sosai na soma k'arewa katafaren falon kallo wanda bashi da wani tarkace inbanda rukunin
kujeru wanda ak'alla ya lamushe set hud'u kuma ko wane rukuni akwai wani k'ayataccen centre
table na glass atsakiyansu.


Sai da na ma matsa kusa da matar sannan naji abinda take cewa," ABDUL MAJID gaskiya ban

yarda ka k'ara d'auko wani auren yanzuba har sai komai ya lafa kana ganin fa irin abinda yake
faruwa, bai zan hanaka aure bane amma ina soka da kata tukun har zuwa komai ya lafa kafin
musan abinyi"

Wanda aka kira da Abdul majid ne naga yad'ago kansa, saida na firgita da ganin kyawunsa da
cikar kamalarsa kyakyawane ajin farko fari tas kamar balarabe, manyan idanunsa ya zubawa
matar wanda suka rune sukayi jajur kafin yace

"Amma nifa bani na tsuro da maganar aurennan ba Daddy ne kuma nayi nayi abar maganar
amma yak'i ni kaina banason zargin da mutane suka soma min akan matsalar da bansan daga
ina takeba, had'e hannayensa yayi waje d'aya alamun rok'o yace Amma kisa Daddy ya janye
wannan maganar dan Allah"

Ya k'arasa maganar cikin wata irin murya mai ban tausayi,
Ajiyan zuciya Amma tayi kafin tace "shikenan Abdul zan kira shi alhajin gaskiya ya kamata a
duba lamarin dole akwai abinda yake faruwa tashi kaje Allah yayi maka albarka"

"Amen" ya amsa sannan ya mik'e a hankali cikin takunsa na nutsuwa amma tabishi da kallon
tausayi ya fice ya nufi bangarensa


Yana shiga d'akin ya fad'a saman k'aton gadonsa yayi rigingine yana kallon rufin d'akin fara
tuno abinda yake faruwa dashi


Asalin labarin

Malam Amadu wanda yaran 'yan uwa sukafi kiransa da Baffa. Madu haifaffen garin gombe ne a
yankin bajoga, yakasance kyakyawan balutani, mai cikar kamala da haiba mutum ne mai
mutuk'a kirki da dattako, shi kadaine mahaifinsa ya haifa baffa yusifa wanda bayan haihuwarsa
babu dad'ewa ya rasu sakamakon harbin maciji wanda ya harbeshi agona take ya rasu ko
shurawa baiyiba.


Bayan rasuwar baffa umar babu jimawa itama Inna Hassu mahaifiyarsa ta rasu sakamakon
annobar amaida gudawa.


Sai rik'onsa yadawo hannun innarsa Inna laraba wanda itane taci gaba da rik'on Amadu sosai
take kula dashi tabashi tarbiyya daidai iyawarta.

Shekarar Baffa Amadu ashirin da d'aya kacal Inna laraba ta had'a aurensa da d'iyarta mai suna
Rabi'a .

Shekara daya da auren Allah ya albarkace su da yaro namiji wanda akasawa sunan malam
yusif mahaifin Baffa Amadu

Shekaran yusif biyu aka haifi ramatu, daga ramatu sai Rudwanu, sai Hafsat wadda taci sunan
mahaifiyar Baffa Amadu.

A kuma tak'inne Allah yayiwa inna laraba rasuwa wanda mutuwar bak'aramin girgizasu tayiba
somin Inna laraba makarace d'auki duka.


Bayan rasuwar Inna laraba yara biyu Rabi'a ta k'ara haifa Abubakar da umar daga kansu
haihuwar ya tsaya mata sosai Baffa Amadu wanda yaranshi suma suke kiranshi da haka
yabawa yaransa ilimin addini dana boko, boko kuwa mai zurfi daga mazan har matan duk da
kasancewarsa ak'auye bashida duhun kai ko kad'an.

Kowanne mazan babu wanda baiyi degree da masters ba yayin da matan sukayi N C E yanzu
haka duk sun manyanta dan babu yaro ko daya a gaban Baffa kamar yanda yaransa da
jikokinsa ke kiransa.


Duk ya aurar dasu har suma sun hayayyafa .

Abdul maji d'ane ga Alhaji yusif shahararren d'ankasuwar daya tara dukiyar da baisan
adadinshiba yana da gidajen mai dayaea acikin gombe da hanyoyin k'auyenta.

Yaransa biyu kacal a duniya Abdul majid da Rabi a wadda suke kira meema sosai ka sangarta
meema kasancewarta mace kuma 'yar auta sun bawa yaransu ilimin adduni dana zamani
wanda yanzun haka Abdul majid yake babban likita, wanda mahaifinsa da kansa bai yarda da
aikin gomnati ba dan haka ya bude masa asbiti tasa takansa kuma hakan bai hana Abdul majid
temako ba domin da talaka da mai kud'i duk nasane.


Bayan k'are karatun Abdul majid da murnan bikin bud'e asbitinsa, sai ya bijirowa da mahaifinsa
maganar aurensa da Rashida yarinyar da suka had'u acan Gemany.


Dama abinda alhaji yusif yake bid'a kenan dan haka bayan dogon binciken da akayi akan
tarbiyyar yarinyar manya suka shiga maganar aka tsaida lokacin aure

Ana saura sati biyu biki Rashida sun fita kasuwa siyayya da mamanta aka nemeta sama ko
k'asa aka rasa babu irin neman,da aba'ayiba amma babu ita babu alamunta.


Bakaramin rud'ewa Abdul majid yayiba domin yana mutuk'ar son Rashidat yarinyace nutsatsiya
wanda kud'in iyayenta baisa ta lalata tarbiyantaba haka kuma fita karatu acikin turawa baisa ta
watsar da addinintaba.


Saida suka kai repot har wajen 'yan sanda aka baza hotunata wa gidajen t v da 'yan jaridu
amma babu wani labari k'arshe iyayen Rashidat ne suka dawo bawa Abdul maji hak'uri domin
ba k'aramin mummunan hali ya shigaba.


Bayan komai ya lafane an d'ebi shekaru biyu dak'yar daddynsa da mammy suka sha kansa ya
kuma neman. Wata yarinya Nafisa.


Sosai suka shak'u da Nafisa domin ita irin mutanannan ne masu barkwanci da abin dariya
bak'aramin d'ebe masa kewan Rashidat tayiba ita kuma ana ya saura kwana Uku d'aurin auren
tashiga band'aki wanka umminta tajiyo firgitaccen ihun datayi koda ta shiga sai gawar ta ta tarar
anyi mata yankan rago.

Wannan al'amari saida yai sanadin kwanciyar Abdul majid agadon asbiti wanda yajima sosai
baidawo hankalinsaba

Wasa wasa saida Abdul majid ya nemi aure sau hud'u biyu dai suma b'acewar sukayi ba
angasuba sama ko k'asa annemesu anrasa.



Hakama Daddyansa sau biyu yana nemar masa y'a'yan kannensa d'iyar mama Hafsa agabanta
takama aman jini daganan ta hau shure shure kafin akaita asbiti ma ta cika, itako d'iyar inna
ramatu itama sace ta akayi kamar shauran

Nan fa k'ananan maganganu suka soma tashi wasu suce Abdul majid d'an mafiyane wasi suce
matsafine kud'i yakeyi da yaran mutane maganganuda babu dad'in ji.


To ta k'arshennnan d'iyar baba Ridwanu ce k'anin mahaifinsa itama dai gawar tata aka samu a
d'akinta da kwalaben guba wanda dangi suke zargin ta kashe kanta ne domin dama ta nuna
bata son auren.

Wata biyar kacal da rasuwan Amina Daddynsa ya kuma b'ullo masa da wata fitinar ta d'iyar
abokinsa.


Wata irin ajiyar zuciya Abdul majid ua sauke lokacin da ring d'in wayarsa ya katse masa dogon
tunanin da yatafi.


Saida gabansa ya fad'i lokacin da yaga daddynsa ne yake kiran.

Da sallama ya ya soma kafin yace "barka da hutawa Daddy ya offoce?"

Batare da yabashi amsar tambayanshiba yace "kana ina?"

"Ina d'akina"
"To kazo ina son ganinka"
Amsawa yayi sannan ya mik'e asanyaye ya tafi amsa kiran mahifinnasa


Shin meyake faruwa da Abdul majid? da gaskene shid'in d'an mafiyane ?ko shan jini ko kuma
shid'in matsafine?

Muje zuwa zamuji komai a hankali



Taku har kullum maman Islam
[8/6, 1:51 PM] MAMAN ISLAM: *مسب الله نمحرلا ميحرلا *

*☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️*

FCWA

*Home of qualities and trusted writers of the nation*



https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?ty
pe=3&source=45&refid=17

_________________________

��ZATO NE��
NA
2020
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

WRITTEN
BY

MAMAN ISLAM

DAGA MARUBUCIYAR

ABINDA YAKE RAINA

WAYYO RAYUWATA



Naji dadin yadda naga labarin yasami karbuwa fiyema da tunani ina kaunar ku masoyana aduk
inda kuke nima ina tare daku

Page 2



............da d'an saurin sa ya shige toilet, ruwa ya watso ya fito cikin sauri ya shirya cikin wando
tree quater da 'yar singlet mai fad'in hannu farare k'al


Afalon sa na musamman ya sameshi tareda Mammynsa, yak'arasa a nutse da zube agabansu
yana gaidasu.

Cikin nazarinsa Daddy yake kallonsa kafin ya turo masa abincin dake gabansa yace "d'auka
kaci Abdul magana nakeso muyi dakai"


Duk dayake baya cikin yanayi mai dad'i hakan baisa yayiwa mahaifinsa musu ba dan babu
wannan atsakaninsu.

Tusa abincin kawai yake kamar anmasa dole yayin da Mammy ta k'ureshi da ido tanajin kamar
tafashe masa da kuka, wani irin tausayin d''annata ne yake dawainiya da ita.



"Abdul" Daddy yakirashi yad'ago a hankali ya sauke manyan idanunsa akan Daddyn kafin ya
amsa a hankali "na'am"




"Kasan abinda yasa nace ka auri Yusra 'yar ahaji Lawan?"


Kai ya girgiza masa batareda yace komaiba

Saboda abinda yake faruwa kaga har mutane sun fara camfaka kuma gaskiya bana so
maganar mutane yaci gabada tasiri akanka shiyasa nakeso mubawa yarinyar temako da
kariyan da idanma wani abune yake bibiyanka zai bayyana bada jimawaba insha Allah"


Har lokacin kansa na k'asa bai iya musu da mahaifinsa ba kuma zai fara daga yauba dan haka
yace


"Shikenan Daddu Allah yakawo k'arshen abin kamar yadda kuka ce"


"Shikenan tashi kaje kafara shiri daga yau zamuyi komai ab'oyene hatta 'yan uwana bazasu san
da wannan batunba domin ina da ayar tambaya akan duk wani makusancina Allah yayi maka
albarka"

"Amen" ya amsa acan k'asan mak'oshi ya mik'e kamar wani mara laka yafice yayin da
mahaifiyashi ta bishi da kallo har idanunta ya ciko da hawaye.


Dafata Daddy yayi yace "Amina ke uwace kici gabada yiwa d'anki addu'a komai zai wuce da
yardar Allah".

Kuka tafashe dashi tafad'a jikinsa tace" alhaji ianajin tsoro nakeji alhaji kullum addu'ar mukeyi
munasawa ayi mana amma kullum abin sai gaba yakeyi ina,tsoron,kar yarona yazauce plss
alhaji idan aurenne,matsalar abarshi haka mana".


"A a Amina karkice haka ina wannan juriyan da jajurcewannaki dan Allah karki karyar damu
domin kece kwarin gwaiwarmu"


.tace "shikenan Alhaji Allah yakawo k'arshen abin"
"amen ya amsa.


"Yauwa alhaji naga an bud'e wancan fat d'in anagyarawafa?"

Dubanta yayi yaga yadda ta tsareshi da ido tanajiran amsa murmushi yayi sannan yace "
amarya zan kawo miki wacce zata temaka miki da 'yan aiyukan gida"

Yafad'a yana gimtse dariyar dayataso masa ganin irin kallon data k'ureshi dashi kafin tace


"Kishiya fa alhaji naji kana kirq da girmana,da komai ai wannan ma abin kunya ne, to wallahi
abinda bazai sab'uba kenan bindiga a ruwa karma ka soma ta fad'a cikin fad'a fad'a.


Dariyan dayake ta dannewa ne yakwace masa kafin ya d'an shafi gefen fuskanta yace "o ni Ishu
kishi harda su tsofi?"


Hararan wasa tayi masa kafin tace "alhaji kenan inbanyi kishinka ba to kishin wa kakeso nayi?
Kainefa gatana komaina rayuwata kai karabani da maraicin danake ciki mai da danginka
dangina kabani kulawar da nagaza samu awajan gwaggonnina ka gayamin taya bazanyi kishin
kaba?"

Ganin har idanunta sun canja kala alamun tana son tayi kuka ya rungumeta yace

"Ya isa haka nima wasa nake miki Abunakar ne zai baro can misra zai dawo nan da zama
tareda iyalansa gaba d'aya, saida na bari yagama duk wani shiri nasa sannan na fara aikin
wahen bakiga angamaba fenti akeyi?"


Wani irin farin ciki ne yakawowa zuciyar hajiya Amina farmak'i dajin dawowar su Abubakar dan
duk matan k'annen mijin nata nasu yafi zuwa d'aya da Ummu kursum tana da mutuk'ar kirki ga

ilimi da sanin yakamata ita 'yar k'asar misran ce inda acan ta had'u da Abubakar wanda
karatune yakaishi can bayan ya kammala sukabrik'e shi yayi musu aiki saboda mutum ne
wanda yatara ilimi mai yawan gaske.



Yaransu uku biyu maza daya mace FATIMA itace babbar 'yarsu wacce takasan kyakyawar
gaske sak mahaifiyarta babu ta inda ta baro mahaifiyarta wajen kyau da diri ga nutsuwa tuni
tajima da saukar karatun ta tana hadda yanzun,haka tana,da hadfan izu talatin da d'aya akanat,
sannan a wannan shekaran tagama karatunta na secindry wanda amsar takardunne ma yasa
su jinkirta dawowa nanja.


Sai k'annen ta wanda 'yan biyu ne Abdul samad da Abdul Rashid yarana masu kyau kamar
'ya'yan larabawa fulanin asali kenan su kuma mahaifinsu suka d'auko



Sosai Fatima taji dad'in dawowarsu Nigeria domin jininsu yayi masifar had'uwa daba Meema
k'anwar Abdul majid suna shiri sosai.


Tunda Abdul majid ya koma d'akinsa sai kawai naga yakasa zaune,ya kasa tsaye, sai faman
zarya yakeyi yayin da zuciyarsa yake wani irin bugu mai k'arfin gaske idanunsa suka kad'a
sukayi wani irin ja mai abin tsoro, kuka yake sonyi amma zuciyarsa tak'i bashi had'in kai.


Tashin hankalinsa, damuwarsa, fargabarsa rayuka bakwaine suka sulwanta ta dalilinsa amma
duk Daddy bai duba hakaba yake neman kuma jefashi cikin wani halin nada ban.


Komanshi yanzun yayi baya Abdul majid mutum mai faran faran da jama'a gashi dasan na k'asa
dashi sam baya d'aukan kansa shi wani yana mu'a malantar mutane dai dai yanayinsu.


Dak'yar yasamu bacci ya d'aukeshi wanda bai farkaba sai ana kiran assalatu saboda bai samu
bacci da wuriba yasa d'an tashin daren dayake yi ma yau bai sami damar yiba.


Kasancewar yau d'in ranar juma ace kuma bai cika fita aiki ranan ba yasa baima fitoba kwata
kwata sai Meema ce takai masa abin karinsa d'aki.

Lokacin yana zaune saman sofa yana ta faman danne dannen wayarsa wanda yanzun yazame
masa abokin hira.

Da sallama tashiga d'akin, batareda tajira amsarshiba ta je tajera masa kayan agabansa, har ta
mik'e ya buga mata wani irin tsawa.

Jiki narawa ta koma ta tsuguna agabansa cikin kakkausar murya yace "daman anan kike ajiye
abincin idan kin kawo?"


Cikin rawan jiki dana murya tace a a yaya dama dannag.......

"Dalla mamala kwashe ki maidasu derning ai da sauri ta kwashe kayan jiki na rawa ta nufi
derning d'in dasu, tuni idanunta ya ciko da hawayen tausayin yayannata, duk wannan abinda
yake faruwa dashi yamai dashi wani irin mafad'aci mai zafin rai.

Har ta kai bakin k'ofa yad'ago yana duban yadda k'anwar tasa take ta faman sharar hawaye,
kiranta yayi, ta dawo ta durk'usa agabansa ya mik'o mata hannunsa ta rik'e nasa ta fashe da
wani irin kuka, sosai take tausayin yayannata tareda jimamin halinda yake ciki.


Saida ya rarrashita ya ringa bata hak'urin fad'an da ya hauta dashi ba gaira ba dalili sannan ya
sallameta.


Bayan ya d'an tsakuri abincinne kuma yayi wanka ya shirya cikin kananan kaya blun wanda da
da riga ruwan toka ya gyara sumar kansa mai uban yawa taje uban k'asumbar daya tara.


Ya fito kenan yaga na shigo da kayan d'aki sabbi ana nufar b'angaren dayaga ana gyrawa,
wanda duk a tunaninsa shi akewa gyarn auren da ake shirin k'ak'aba masa, dan Daddy yace
agidan yakeson su zauna da Yusra.


Take yaji wani irin k'unci ya mamaye masa zuciya.

B'angaren Amma ya nufa dan gaishe ta, yana sallama abakin k'ofar yaji an rungumeshi an
cikwaikwaiye shi tareda ihun murna.

Sosai ya ware idonsa akan fuskarta yana mamakin yaushe sukazo dan tashin hankalin dayake
ciki yasa shi mantawa da cewa Abbu da kansa ya fad'a nasa zasu dawo nan da zama,

Kallonta yake da mamaki yace "Fatina?"
Dayake haka yake kirantactun tana yarinya ita kuma tankance yayana tun bata iya fad'aba har
tazo ta iya,.
Itama da mad'aukakin fara'a ta dube shi tace "yayana"

Wani irin rungumeta yayi ajikinsa yanajin wani irin tsoro yana saukar masa wanda baisan
dalilinsa ba sosai ya k'ank'ameta har sai da tasaki k'ara tace "yayana zaka b'allani fa"

Sannan ya sassauta mata rik'on hannunta kama suka shiga falon Amma, nan yaga abin
mamaki Abbu da Ummi zaune gaban Amma sunata hira har da mammy

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login