Showing 36001 words to 39000 words out of 65710 words

Chapter 13 - ZATO NE (1 TO End) BOOK COMPLETE By Maman Islam.pdf

14 Apr 2025

5215

fad'in bari nayi wanka Teema nazo
nabaki labarin danace zan fad'a miki wallahi sai cikin ki ya k'ulle dan dariya.




Da gudu Husna tafito daga d'akinsu tana ihun neman temako Anwar tafara karo dashi tace
"mun shiga uku yaya zokaga umma zata mutu wallahi mutuwa zatayi aman jini takeyi"



"Jini?" yafad'a arazane tareda tureta yai b'angaren nasu da gudu itama ta rufa masa baya tana
matsanancin kuka.



Sanda suka shiga tuni ta sume domin ta riga data gama galabaita da gudu ya sungumota
sukayi waje.

Kuka take ta rusawa tana salallami tareda fad'in "o duniya wai ace makashinka yana tareda kai
ni Rukayya mamaki zai kasheni wallahi"




"Ya kashekin" Alh. Umar yafad'a amutuk'ar fusace sannan ransa a mutuk'ar b'ace, cigaba yayi
da fad'in "wallahi Rukaiyya sabon halinkinnan ya ishenifa 'yan kwanakinnan kullum da kalan
abinda zan gani me yake faruwa?" yafad'a cikin daka mata wata irin mummunan tsawa wanda
tsabar firgici batasan lokacin datace



"Matsafa"



Plss manage
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*




��ZATO NE��
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM

Page 26

.......................a mamakince yake kallon matar tasa data riga gama rud'ewa yace "matsafa
kuma?
A ina kuma meye had'inki dasu?"




Dake bata tareda nutsuwanta sam bata gane me yake cewaba kukanta kawai take casa.


A mutuk'ar hasale ya buga mata wani mugun tsawa yace "dallah malama kija baki kirufemin ki
fad'amin abinda yake faruwa kin wani zauna sai kukan banza kikewa mutane"



Agigice tace "dan Allah kayi hak'uri nima bansan ta ina zan fara fad'a maka wannan
mummunan labarin mai almaraba"




Ganin yadda ta gigice ne yasa ya kama hannunta cikin nutsuwa ya zaunar da ita sannan ya
d'ebi ruwa mai sanyi yabata tasha sannan zauna akusa da ita ya rik'o hannunta yana murzawa
a hankali ya soma magana kuma cikin nutsuwa.




"Rukaiyya ki nutsu ki fad'amin abinda yake damunki suwaye matsafan a ina kika gansu kuma
me had'inki dasu har suke neman haukataki?"




A firgice tad'ago idanunta da suka gama rinewa tsabar kuka ta zuba masa kafin tasaki wani
siririn kuka,zuciyarta na wani irin bugu bata san cewa firgicin data shiga har yakai tona abinda
batason bayyanu warsa yanzuba batasan cewa duk nuk'u nuk'unta da son k'warara hujja akan
abinda takeyi tana neman fasuwaba sai yanzu datake jin wannan tambayoyin awajen mijinnata,

wata dabarane tafad'o mata ta d'an gyara zama tareda goge gutun hawayen ta dubeahi cikin
tsaban damuwa tace




"Abban Salim ina cikin wani hali bana tareda nutsuwata 'yan kwanakinnan abinda nake gani
yana matuk'ar firgitani wallahi Abban Salim matsafane"



"A ina?"
Yayi mata tambayar tace "a mafarkina mana kamar ido biyu haka nake ganinsu wani lokacin"


Wani irin takaicine ya kama Alh. Umar wai duk wannan mummunan d'aga masa hankalin datayi
duk mafarkine tayi, dubanta yai cikin takaici yace




"Sakaci kawai da addu a da ace kuna addu a yayin dazaku kwanta ai da hakan bai faruba jiba
dan Allah yanda abin yake tasiri akanki to da ace kuma yaranki sunanan kike wannan sakarcin
kice musu me?"




Sosai yayi mata fad'a fad'a nasiha nasiha sannan ya jadadda mata ta daina sakacin addu a.





A can asbiti kuwa tunda aka kai haj. Asma'u likitoci suka rufu akanta suke ta aikin ceto ranta
amma wanda yai nasara duk wani gwaje gwaje daya kamata suyi sunyi abinda saka makon
yake basu lafiyanta k'alau, kwanaki uku suka shafe suna abu d'aya amma amsar duk iri d'ayane



'Ya'yanta kuwa ba k'aramin mummunan tashin hankali suka shigaba dan ganin halin da
mahaifiyarsu take ciki.

"Anty Yusra yau ki shirya muje mu dubo umma ance andawo da ita gida"

Tun kafin tace komai Abdumajid da shigowansa kenan yace "babu inda zakije k'afan yawo"




Idanu tazaro tace "saboda me?"
Shima nasa ya zaro mata yace "saboda haka nayi niyya"


D'an b'ata rai tayi tareda matsowa kusa dashi ta rik'o hannunsa tace "haba masoyi haba nawan
wai dan Allah me yasa kake min hakane duk sanda nace maka zan fita saika hana ko gidama fa
sau biyu kacal na tab'a zuwa amma anty Yusra da kanka kake kaita, koda yake dama ni ai tura
makani akayi itako auren so kukayi shiyasa bambancinka mu ma mabayyani ne"



Daga haka ta sakar masa hannu tareda fashewa da kuka tayi hanyar d'akinta da gudu da ido ya
bita har ta banko k'ofar da mugun k'arfi ya sauke ajiyan zuciya kafin ya k'arasa kusa da Yusra
ya dafa kanta yace "baby kuna lafiya?"




A sanyaye tace "lafiya lau" tana shirin tashi ya rik'ota yace "kema tafiyan zakiyi kibarni in ita
yarinya ce aike da hankalinki, in fad'a miki wani abu Yusra?"




D'an dubansa tayi batareda tace masa komaiba yajata jikinsa yace "Yusra duk abinda yake
faruwa dani akwai sa hannun wasu daga cikin mutanen gidanmu, shiyasa kikaga bana son
Fatima ta cika yawan zuwa gidan yanzu har sai komai ya lafa ita kuma take d'aukan hakan da
wani manufa na daban.l"

Da matuk'ar mamaki Yusra take kallon Abdulmajid jikinta yana wata irin rawa ta k'amk'ameshi
tareda fashewa da wani irin kuka rik'eta ya kumayi sosai yana rarrashinta ta d'an jima tana
kukan kafin yasamu tayi shiru.





Ita ko Fatima tunda ta shiga d'aki take ta tisgar kuka tarasa me yasa yake mata haka agabanta
Yusra zata tambayi zuwa gidansu yasata agaban mota yakaita wani lokacin ma har da Fatiman
zasu kaita amma ita data tambayi gida sai yace ba hakaba gaskiya wallahi tagaji da wannan
kisan mummuk'en da yake mata.



Da yake ranan ba ita ke da girkiba ko d'uriyansa bata jiba n
bare tasa ran zai rarrasheta hakan kuwa ba k'aramin k'ona mata rai yayiba.




Washe gari tana tashi ta gyara d'akinta tayi wanka ta shirya cikin wani mini tree quater da wata
'yar best kayan sunyi mugun amsarta badan tanajin mugun yunwaba da babu abinda zai sa ta
sauka k'asan, kasancewar jiya bata samu daman cin abincin dareba yasa ta tashi da
matsanancin yunwa.




Suna dirning suna ka break suka jiyo k'aran takun cokalan takalminta duka suka maida hankali
kanta, suman zaune Abdulmajid yayi domin ba k'aramin tafiya da tunaninsa Fatima tayiba tunda
tazo gidan bata tab'a yi masa irin wannan shigan ba.




Ko kallon inda suke batayiba bare su saka ran zata kulasu ta wuce kicin indomie ta dafa had'e
da soya k'wai guda biyu anan kicin d'in ta tsaya ta cinye ta d'auraye flat d'in juyowan da zatayi
suka gabza karo dashi wanda tunda tafara cin abincin yake tsaye yake kallonta d'agowa tayi ta
zuba masa idanunta na d'an seconds kafin tajanye tareda rab'ashi zata wuce yayi saurin rik'ota.

Iya k'arfinta tasaka da niyan kwacewa sai dai ina k'arfin ba d'ayaba dan haka tsaya kawai
tareda fashewa da kuka tace "ni ka cikani ina da abinyi"




Kallon cikin idanunta yakeyi wanda suke cike taf da hawaye kafin yasanya hannu yana share
mata hawayen tareda fad'in "ni banga abin kuka ba tunda babu abinda nayi miki"




Itama kallonsa tayi tareda mamakin rainin hankali irin nasa yo rainin hankali mana inbanda
rainin hanka duk irin abinda yake mata amma yace baiga abinda yai mataba, lallai ma mutumin
nanan.





"Cikani" ta kuma fad'a cikin zafi "ai kina da k'arfi" yafad'a cikin kallon idanunta sannan kuma ya
d'an jata jikinsa cikin lallashi yace




"Haba babyna wai duk fushinne tun jiya har yanzun baki huceba?"




Wani banzan kallo ta watsa masa batareda tace masa komaiba, yasaki wani k'asaitaccen
murmushi yace "to shirya muje shikenan?"

Maman islam ce
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*





��ZATO NE��
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 27


..........sosai hakan yayi mata dad'i ta haye saman da d'an gudunta, tayi saurim shiryawa
sukabar gidan cikin nishad'i hannunsu sak'ale da juna.




Bai kaita gidanba, yawo sukai tayi gidan abokansa har kusan k'arfe tara lokacin tuni Yusra ta
jima da dawowa, tana zaune afalo tacin indomei ta d'an kallesu ta maida kanta yayin da takejin
wani abu aranta.



A hankali ya k'arasa kusa da ita ya zauna tareda rik'o hannunta yakai abincin data d'ebo
bakinsa tareda lumshe idonunsa akanta yana fuskantar yanayin ta kamar tana cikin damuwa.

"Gaza a daina wahal da Asma'u haka gaza domin ita domin tana da matuk'ar mahimmanci
atareda mu"



Idanunta ta bud'e yagansu wani yellow shar dasu saida gabansa ya fad'i sannan cikin wata irin
murya tace



"Kai dumb'uru karfa ka d'auka tsoronka nakeji nake binka sannan inaso ka rik'a tuna cewa kaifa
mutumne ni kuma aljana ina da sigan da zan iya yin komai na bikane saboda wani buk'ata nawa
kuma na biya dan haka abinda nakeso dakai ka zubamin ido nima burina kamar yanda naka ya
cika ko kashiga bala'i"




A mutuk'ar tsorace Dumb'ur yake kallon Gaza tareda mamakin abinda takeson aikatawa matar
da ya k'watota daga hannun azaluman 'yan uwanta ya maida ita wani abun yau itace take
neman wulak'anta shi ta muzanta shi, shi kam duk randa Gaza ta gujeshi nashi ya k'are.





Gwaggo Hafsa ce zaune ta rafka uban tagumi tana tunanin wannan karon mai gidannata yayi
nisan zango dan bai tab'a dad'ewa hakan ba sai wannan karon.





Zaune duka yaran nata suke cikin tsantsar damuwa sun kafeta da idanu hankalinsu har baya
tareda su ganin halin da mahaifiyarsu take ciki har yau bata samu farfad'owaba, lokaci lokaci
Husna takan share hawayenta.

Sosai Yusra ta canja musu kullum cikin damuwa take sai wata irin rama take wanda sai daya
mutuk'ar d'aga hankalin abokan zamantan, kuma tambayan duniya tace musu lafiyanta k'alau.




Yauma a tsorace tashiga d'akinnata cikin fargaba wanda ya kasance mata kamar jiki ayanzun
sai data gama duk wani abu datake gabatarwa sannan ta haye gadon tayi kwanta da zummar
intaji baccin tayi addu'an amma ina yauma kamar ko yaushe kafin tayi wani yunk'uri baccin ya
kwasheta batareda tayi addu'an ba.



Cikin baccin nata ne taga wannan matar wadda tayi sanadin zubewar gudun jininta, tana
murmushi ta matsota tareda shafar cikinta tana cigaba da wani shu'umin murmushi tace "Yusra
kin burgeni sosai yadda kika kuma cika min burina na kuma samamin muradina yau kuma zanyi
dinner da d'an tayin babyn da kika kuma k'unsa" daga haka ta kuma sa hannu ta bugi cikin
Yusran da d'an k'arfi wanda yayi sanadin da Yusra ta saki wani irin gigitaccen k'ara wanda duk
wani mahaluk'i dayake gidan saida k'aran ya mugun firgitashi domin da iya k'arfinta tayi k'aran.



Rige rigen shiga inda take harda ma'aikatan gidan sosai hankalin Abdulmajid yatashi ganin
yanayin da Yusra take ciki da gudu ya k'arasa yana jijjigata amma ina tariga da ta sume.



A d'imauce ya sungumeta da mugun gudu suka fito yana salati da sauri driver ya bud'e mota
mai gadi ya bud'e get suka tafi da mugun gudu sukayi asbiti.





Sosai hankalin Fatima yatashi ganin irin uban jinin da Yusran take ambaliya harda wani irin
guda guda bakin kirin yayin da likitoci suka rufu akanta dan ceto ranta.



Kuka take kaman zata ranta zai fita hankalinta amugun tashe takasa samun nutsuwa ko kad'an

wani irin tsorone yake bin ko wane huda na jikinta.


Ganin halin datake cikine yasa dole shi ya danne nasa damuwan yajata jikinshi yana rarrashinta
da k'yar uasamu baccin tsoro yayi awon gaba da ita wanda batayi hakan ba saida ta
rungumeshi k'am k'am.




Yusra kuwa sai goshin asbah suka samu suka sha kan matsalan suka yi mata alluran bacci
hankalin hajiyanta kuwa idan yayi dubu to atasheyake.





Muje zuwa maman islam ce
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*



��ZATO NE��
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI


STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM

Page 28


................cikin baccin ne tayi mummunan mafarkin dayasa ta farkawa a mugun firgice take
jikinta ya kama wani irin rawa takama wata irin jijjiga.




Da gudu Abdulmajid da Fatima wanda dama tuntuni suna wajen cikin jimamin abinda ya faru
suka yi rige rigen zuwa har suna bangazar juna batare da sun kula hakan ba.





Wani irin mugun gumine ya rik'a tsatstsafowa ako wane kafan gashi na jikinta, atare suka
ruk'ota suna mata addu'o i kafin tasami nutsuwa ta fashe da wani irin gigitaccen kuka.



Abdul ya rik'o hannayenta duka biyun yana kallon cikin idanunta saidai yakasa ce mata komai
saboda tsaban tausayinta ya saki hannun ya juya da sauri ya fita kiran doctor.




Fatima ta matso ta kamo hannunta tana wani irin kuka takasa cewa komai, rungumota Yusra
tayi jikinta tana son tsaida nata kukan amma abin ya faskara haka suka had'u sunayi gwanin
ban tausayi.





Tare suka dawo da likitan ya dubata tareda yi mata tambayo bata da wata matsala azahiri dan
haka yabasu sallama tareda shawarwarin yadda zata na kulawa da kanta.

Tunda suka dawo gidan yake ta aikin rarrashi sun kasa daina kukan tambayar duniya abinda
yake sata kukan amma ta kasa dan haka ya gabza tagumi yana ta kallonsu yayin da zuciyansa
yake wani irin zafi





"Yusra" ya kirata cikin wani irin yanayi mai wuyan fassaruwa ta d'ago idanuwanta wanda sukayi
wani irin rinewa saboda tsaban kuka ta watsasu akansa batareda ta iya cewa komaiba.






"Kinga k'anwarki itama tun d'azu take ta kuka nayi rarraahin duniya tak'i ta daina, kuma kukanki
ne yasata kuka dan Allah ku taimakeni kar zuciyana ya buga kudaina wannan kukan plss nd
plss kar na had'oye zuciya saboda damuwa, na rok'eki Yusra ki taimaka ki fad'a mana
damuwanki sannan ki daina wannan kukan da bazai amfaneki da komaiba sai k'arin wani
damuwan dmdan Allah"






Ya k'arasa cikin wani irin muryan dayasa Yusra taji wani irin sabon damuwa ya k'ara ya
lullub'eta, abinda yake damunta ba mai k'arewa bane kuma ba mai fad'uwa bane kamar yanda
mijinta da abokiyar zaman ta suke buk'atan ji ta fashe da wani sabon kukan tareda fad'awa
jikinsa tana wani irin shasshek'a, abinda wannan la a nanniyar ta fad'a yana matuk'ar razanata.




"Kai jaririya kina da k'ok'ari kina da himma naji dad'i yanda kika k'ara harbomin sabon baby zan
shana sannan zan ta d'aga miki k'afa kafin amfaninki ya k'are sannan ingigita tunanin ubanki
Munzali mara tsoron Allah sannan abu nagaba ki k'addara idanunki biyu kikejin wannan sharhin
kuma duk wanda kika bawa labari daga ranan bazaki k'ara kwanan duniya ba,zakiyi mutuwa
mafi muni inkuma kina tantama ki gwada ki gani" bayan gama wannan dogon bayaninne ta bugi

cikinta wanda yasa ta kuma missing babynta akaro na biyu.






Wani sabon kukan ta kuma rushewa dashi tareda kamo hannunsa dana Fatima tana fad'in "dan
Allah kuyi hak'uri bazan iya fad'a muku abinda yake damunaba yafi k'arfin na fad'a amma dan
Allah kutayani da addu'a domin ni yanzu addu anma kasashi nakeyi dana soma sai naji kamar
an murd'emin baki nakasa cigaba idan kuma naso yi a zuciyana sai wani abu mai nauyi ya
tokaremin kirjina, abinda nasani kawai shine dole kafin na mutu kusan abinda yake firgitani
abinda yake damuwa na kuwa duk kunsanshi dan haka babu buk'atar ce muku komai akan
hakan.





Sosai Fatima ta fashe da kuka tareda k'ank'ame Yusra a jikinta tana kuma kallon Abdulmajid
tace "wai shin yaya wannan mutanen idan sunfi k'arfinmu sunfi k'arfin Allahne?
Haba yaya so kake acigaba da kashe duk wanda kake tareda shi nidai wallahi bazan yarda inaji
ina gani akasheni akan abinda bansan tushe da makansaba nidai kawai gida zan tafi babu
mamaki ma kasan komai inbanda haka duk abinda akeyinnan ka kasa tab'uka komai mu kenan
kullum cikin tashin hankali da damuwa.




Kwarai maganan Fatima ya mugun dukan zuciyarsa wani irin mamakinta ya kamashi yakafeta
da manyan idanunsa wanda suka k'ank'ance tsabar fitina da tashin hankalin furucin Fatima
gareshi kasa cewa komai yayi ya mik'e a mugun fusace yabar wajen jikinsa har wani rawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login