Showing 54001 words to 57000 words out of 65710 words
Chapter 19 - ZATO NE (1 TO End) BOOK COMPLETE By Maman Islam.pdf
gani take kamar itama,Fatiman zata biyune kamar yadda sauran sukabi janta
yd'anyi jikinsa ya rungume yana d'an bubbuga bayanta shima yanayin sa ya nuna yana cikin
damuwa da tashin hankali bai san me zaice mata ba, ko a wane halin yaran suke shi damuwat
sama kadafa Taniimu yaje ya cutar da yaran tunda ya riga da ya kulle duk wani hanya da zaibi
dan cigaba da gudanar da aiyukansa dole ya mik'e tsaye dan kawo k'arshen kafircin wannan
azzalumin.
Babu inda baya rawa a jikinta saboda mugun zazzab'in daya kamata kimanin kwana biyu da
suka gabata sosai ya zuba mata ido yana kallon ta cikin wani irin masifaffen tausayin ta aransa
kuwa yana raya irin wulak'anci da tozarcin da zaiwa kawu Tanimu duk ranan da Allah ya kub'tar
dasu daga sharrinsa.
Kasa motsawa yayi daga inda yake saboda wani irin abu mai nauyi yake ji tundaga tsakiyar
kansa har zuwa tafin k'afarsa, da k'yar tajawo jikinta tazo ta kwanta akan cinyarsa tana zubar da
hawayen azaba,
Hannu yasa yana ahafar gashin kanta batare da ya iya ce mata komai ba saboda wani abu
daya tokare masa zuciya ji yake kamar ya had'iye zuciyar tsabar bacin ran dake d'awainiya
dashi.
Cikin wata irin murya dake nuna alamun tanajin jiki tace "yaya yanzun haka zamuyi tazama
anan baza mu gwada wata dabarar ba?"
"To ya kike so muyi Fatima kina ganifa k'ofar shafewa take sai in za a shigone zakiga mutum
kawai, taya kike tunanin zamu fita anan kawai muzubawa sarautar Allah ido shine zai iya mana"
Fashewa ta kumayi da kuka tace shikenan nasan tawa ta k'are kai masan babu abinda zaiyi
maka amma ni kam,nasan kashe ni zaiyi kamar sauran shikenan rayuwana ta k'are" nan dai ta
kama sambatun dakaji kasan cewa zafin zazzab'i ne, duk irin yadda yaso rarrashin ta bata iya
tayi shirun ba dan haka bashi da zab'i sai ya had'e bakinsu kawai.
Yau kam ba akawo musu d'an abincin da ake sammu sun ba dan haka abin ya dame shi sosai
saboda da ruwan ne yake samu suyi sallah gashi yau basu samu sunyi sallar ba.
Can wajen k'arfe uku yaji alamun taku abayansu ya d'an juya d'ayane daga cikin wanda suke
kawo musu abinci yau kam yasha mamakin ganinshi da ledodi kusan guda hud'u sai kuma bag
na fiyo wata guda d'a a hankali ya k'araso kusa dashi ya aje ledodin sannan ya mik'a masa
hannu wai su gaisa abin ya d'aure masa kai taya zai yarda da wannan azzaluman mutanen
marasa tsoron Allah masu cin naman mutane?
Shi har ga Allah ko sallaman su bai tab'a amsawa ba domin sai amintaccen mutum ne ake
bawa aminci bawai irinsu ba wanda basu aminta da kansu bama bare kuma wani.
Kamar yasan abinda yake tunani aransa dan haka yace masa,
"Abokina ka d'auka cewa nima ina tareda mutumin nanne domin son cimma wata mafita tawa
amma baya ga haka bani da burin cutar da kowane irin mutum a cikin tafiyar nan, kasaka
aranka cewa duk ranan da birina ya cika tare zamu fita nida ku anan domin d'aukar fansa ne ya
zaunar dani anan"
"Daukar fansa?" Abdulmajid ya tambaya da mamaki shimfid'e a fuskarsa,
"K'warai kuwa abokina" ya tabbatar masa sannan ya d'ora da cewa "kai matan dazaka aura
yake kashewa sai kuma wasu daga cikin dangin ka kad'an ni ahalina ya rabani dasu gaba d'aya
saboda neman da son zuciya da kuma tsantsar zalunci irin nasa"
Sosai Abdulmajid yake kallonsa tareda matuk'ar mamaki duk da kasancewar bai yarda da abin
dayake fad'a masaba amma abin ya matukar d'aure masa kai jin jina masa kai yayi yace
"Taya zan amince da wannan tazo muji tan naka meye dalili ko jujjar ka akan abinda kake
fad'amin yanzun"
Abincin da akabasu na yau yaja kwanon ya bud'e ya tura masa gabansa yallo shar ya ganshi
sannan kuma ya narke alamun ya rub'e kenan, sosai ya zubawa abincin ido sai yaga ai
yanzunma abincin yake dad'a narkewa, sai ya maida hankalinsa ga mutumin yana neman k'arin
bayani da ido.
"Guba ce"yafad' yana kuma bashi hannu su gaisa, wannan karon baikiba shima ya bashi sukayi
musabaha yayin da mutumin yaci gaba da cewa
"Yau anshirya kashe wannan ne yafad'a yana nuna Fatima da har lokacin take kwance saman
cinyarsa tana baccin bashin dataci watavirin mummunar fad'uwar gabane ta ruftowa Abdulmajid
aransa yake nanata kisa Fatimar tasa za akashe masa? lallai kuwa da anyi d'an k'aramin yak'i
agidan Tanimu ya aiyana hakan aransa yayin da wancen gabada cewa "dan a tsari yau aka
shiyar kasheta yayin da kai kuma za a gusar maka da tunanin ka amaida ka gida da gawar ta
kamar dai yadda aka b'atar da hankalin abokiyar tafiyar ku ta manta duk abinda tagani ta kuma
fad'i abinda ya d'orata akai
Ina baran addu arku masoyana kan wani buk'ata mai girma da ya sakoni gaba na gode taku
Maman islam
[11/30, 6:11 AM] Hayat: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 46
.......sosai yake kallon mutumin sannan wani irin tsoron kaidin kawu Tanimu yana shigarsa koda
yake mutumin da ya kashe iyayensa meye ma bazai aikata ba, ai ya tabba imani yajima da yin
k'aura wa zuciyar kawuvTanimu tunda har ya mai da shan jinin mutane ba abakin komai ba
yamai da kisan kai tamkar yankan dabbobi.
Shi kuwa mutumin cigaba yayi da fad'in "kwanannan za ai bikin bawa Gaza jinin al'umma
wanda in irin hakan ya tashi mafi k'aran ta a yanka mata kusan mutum d'ari yara da manya da
kuma tsofi da saffa saffa, to a irin hakane ake kan mai uwa da wabi duk wanda ajalinsa yayi sai
kaga an had'a dashi domin biyan bak'ar buk'tar su, ina mai tabbatar maka matuk'ar akayi bikin
kuna nan to jinin wannan matar taka ya hallata su bawa Gaza dan haka abinda nakeso dakai ga
wannan" yaja ledar take away wanda harda naman kaza acik ya tura musu yace "kuci ku k'oshi
sannan nayi alk'awatin muddin ni aka turo zan fita na siyo muku abinci koda wasa kar ku sake
kuci duk wani abu dazasu kawo muki domin tunda ya fara da haka zai ida nufi"
Sosai jikin Abdulmajid yayi sanyi yazama dolevya k'ara kan addu ar da yakeyi dan ya fahimci
kawun nasa ba k'aramin majununi bane ahi kuwa mutumin d'auar kedar ya jawo ya tura
gabansa sannan yace
"Ga wannan ma dan Allah kayi hak'uri nasan matsayin ka ya wuce nan sai dai bani da zabin da
yafi wannan, garin kwakine da shuga da gyad'a duk ranan da bani aka aiko kawo muku abinci
ba to wannan shine abinda nake so kuci dan gudub afkuwar wani abu a gareku idan oga yaga
baku cin abincin hakan zai fusata shi ya fito daku yace zai d'auki matakin gamawa da ita dan
yanzu duk wani fata da buri nasa yana akanta ne, to ni kuma duk ranan da ya fita daku to a
wannan ranan zan temaka muku ku gudu,dan haka ku kasance cikin shiri kuma ku riga ci kuna
koshi don musamu damar ai watar da shirinmu cikin kuzari wannan ruwan saboda ibadunku na
kawo muku
Sosai Abdulmajid ya gode masa domin ba k'aramin dad'in temakon da yace zai masa yajiba
Yayin da badamasi kamar yadda yace sunansa yacigaba da cewa yana tura musu d'aya kedar
mai take away.
"Ga wannan kuci yanzun"abinci ne mai rai da lafiya sannan ya kuma jan d'aya ledar yace
"Wannan kuma duk lokacin da bani na kawo muku abinci ba kar kuci dan Allah ku daure kuci
wannan na sani kunfi k'arfin wannan amma cin wani abu daga hannun oga kai tsaye akwai
gagarumin matsala.
"Haba abokina kada ka damu, cewar Abdulmajid sannan yaci gabada cewa ai dama bawa babu
inda baya samun kansa kawai dai mu kasance masu godiya ga Allah a duk halin da muka samu
kanmu sai ubangiji ya ni imtamu da abinda bamuyi zato ba dan haka kar ka damu kuma
mungode sosa.
Dariyansu kawai kakeji a d'akin da sukan keb'e da karuwansu idan sunso hutu yau sab'anin
hakane domin k'walewar su suke sosai sukayi mankas ba kowa bane face su alhaji badamasi,
yayinda kawu Tanimu yake tsara abinda zaiyi da su Fatima wanda Gaza tace masa kar yasake
ya bar Abdulmajid d'inma domin shi har yafi Fatima had'ari atareda su.
Tagefe guda kuma ga yadda ahegun yaran suke son tsayar masa da aiki domin yau kwanaki
uku kenan yadda ake kai musu abincin haka ake komawa akwaso basa tab'awa abinda yafi
komai dugunzuma zuciyarsa kenan domin ya fahimci so suke su b'ata masa shiri.
Suna tsaka da holewar su muryanta ya ratso cikin d'akin cikin wani irin mummu nan tsawa tace
"ku wane irin shasha shune kuna nan kuna watsewar ku asirinmu yana shirin tonuwa"
Tsi sukayi cikin wani irin fargaba wanda kusan tunda salon abin ya sauya GAZA takeson
mamaye komai ya kasan ta kusan zame musu tauraruwa mai wutsiya ganinki ba alkhairiba,
shiru suna sauraron yau kuma da ne tazo yayin da jikin kowa yake d'an rawa rawa.
"Kuna nan kuna lalacewa wancen banzan ya d'auko hanyar lalata komai Tanimu zan kashe
shifa wallahi zan gamada rayuwar sa, dan bazai yiyu inaji ina gani wani banza ya rusamin shirin
da nashafe shekaru sama da talatin ina shirya shiba dan haka zan gama dashi kuma,ina so yau
d'innan ka kawomin tsinannun yaran nan da ransu zan zuk'e jinsu, sannan kai Garzali a fitomin
da Munira itama duk taurin kanta yau zan tsotse jininta itama badai tak'amarta tace ban isaba
kuma bazan iya da itaba to yau zanga k'arshenta"ta k'arasa tana huci yayin da sauran duk suka
fice sukabar su suna cigaba da tattauna yadda taron shan jinin su Fatiman zai kasance.
Can b'angaren su kuwa tun ranan da Badamasi yace kar su k'ara cin duk abinda za'a kawo
musu matuk'ar ba shine ya kawo musu ba, basu k'ara sanyashi a idanunsu ba sai yau kimanin
kwanaki shida kenan.
Lokacin daya ahigo talatainin darene wanda da ayaune zasu shanye jininsu sai kuma,suka
sauya wata shawarar acewar Gaza akwai munafiki a cikin yaran,Tanimu kuma,tanasi tasan ko
waye dan dama mutum goma take so masu shegen taurin kai wanda suke nuna,sunfi k'arfin
tsafinta dasune zata zama gagarumar da babu kamar ta a duniya dan haka yanzu tasamu
mutum uku Abdulmajid Fatima haj.Munira, sai kuma wannan b'oyayyen daya bayyana.
Sai dai kuma duk yadda sukaso ganin wanda yake shirin fidda su Fatiman hakan,bai faruba
domin yariga da yagano shirin su ta hanyar shima,nasa shirin dayake dan haka ya had'a musu
gadar zare ta hanyar lalata duk wasu abubuwa da Gaza ta tanada domin ranar yaud'in dan
haka agigice suka rankanya can fadarta inda take gudanar da duk wasu hark'llolinta abinda ya
d'agawa Gaza hankali shine babu Munira babu dalilinta a wajen an fidda ta take ta shige d'akin
data ke shirya duk wani shiri nata cikin tsantsar tashin hankali ta manta da batun su Fatima.
Muje zuwa
Ku kara hakuri dai ankusa cimma matsaya
Maman islam
[11/30, 6:11 AM] Hayat: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
By
MAMAN ISLAM
Page 48
..................ko takan Badamasi bai bi ba ya tsallake shi ya wuce cikin tsantsar tashin hankali
yayin da mutanen da suka kewaye Badamasi suka d'agashi suka gyara shi.
Shi kuwa Tanimu fada ya nufa cikin fitar hayyaci yana zuwa ya tadda gaza cikin tashin hankalin,
da ya ninninka nashi wanda yake ciki take ya k'ame awajen lokacin da take tunkaro shi cikin
wani irin mugun yanayi mai ban tsoro, sannan tayi magana cikin watabirin murya mai masifaffen
amo
"A kashe su duka bana so sukai zuwa azahar suna numfashi" zubewa tanimu yayi a wajen
tareda fashewa da wani shegen kuka wanda ya kuma d'aga hankalin gaza tace
"Lafiya?"
Yace "yaran sun caccakawa Badamasi amintaccen bawana kwalba sun gudu"
Kalalo jajayen idanun ta Gaza tayi cikin wata irin masifaffen fad'uwar gaba tace "ban gane
yarenka ba, ban fahimci mekake nufiba sun gudu fa kace, ina sam da sake wallahi bazai
sab'uba maza abazama a nemosu tun kafin su fice a garinnan dan nasan duk inda suke basuyi
nisaba maza kafin kaima,na dawo kanka jakin banza ka saki baki kana baccin asara har yara
k'anana su naka wayo wallahi kayi asara k'aton banza kawai fita kabanivwaje kuma karka dawo
min nan sai ka kawo minsu inba haka ba zan musanya dakai da kuma,iyalanka ne"
Cikin asalin damuwa da tashin hankali Tanimu ya fice yana kuka shab'e shab'e da hawayen sa
yana ta maimaita ya shiga uku har yaje gidansa sai dai kuma tashin hankalin sa ya nunkune
sakamakon labarin daya samu cewa Badamasi ya gudu.
Washe gari da safe Fatima dakanta ta shiga kicin tayi musu girki mai rai da lafiya sukaci suka
k'oshi, bayan sunyi wanka babu dad'ewa Badamasi ya shigo gidan kamar an wulloshi babu
wata wata yace su taho babu musu kuwa Abdulmajid ya figi hannun Fatima suka nufi tasha
cikin matuk'ar sauri shatar mota ya d'auka musu iya su biyu kawai ya biya yace akaisu har gida.
Kai tsaye gida ya dawo bayan ya tabbatar da cewa motarsu ta d'aga tayi nisa draiban kuwa
gashi da mugun gudu
Shigarsa gida babu dad'ewa saiga kawu Tanimu da tawagarsa lokacin Badamasi yana dressing
ciwon dayaji wa kansa wanda yake masa azabar rad'ad'i.
Akansa kawu Tanimu ya tsaya yana huci yace "kai Badamasi dan ubanka ina ka shiga lokacin
da yarannan suka fice suka gudu"
Sosai gaban Badamasi ya fad'i, sam baiji zuwansu ba dan da gaske ciwon yake masa zafi sosai
cikin sanyi da tsoron kar Tanimu ya gano shirin dayake yace.
"Mai gida shammatana sukayi bansan yadda akayi har suka bud'e k'ofar ba sai saukar makami
naji wanda ban tashi sanin inda kaine yakeba sa hayaniyar mutane ne yatasheni yafad'a" tareda
faahewa da kuka dan ogan nasu ya gasgata shi
"Ba kuka zakayi ba Badamasi tashi kawai zakayi mu bazama tasha tasha munemo su danna
san yanzu daga nan tasha zasu nufa gaza tace indai bamu nemosuba mune masadinsu"
Kai dai kaine madadinsu ni na gama duk wani shirina na ganin na tarwatsa ju daga kai har
azzaluman da kuke wa aikin Badamasi ya fad'a aransa.
Tare suka fita nemansu da tawagar su, saida ya kaisu duk tashoshin dayasan sunfi nisa domin
acewarsa idan suka tashi baza su tsaya akusa ba sun san za a nemesu.
Saida suka gama bulayinsu sannan sikaje asalin tashar da su Fatima suka hau mota inda aka
tabbatar musu da cewa zuwa lokacin sunjima da tashi ai kuwa Badamasi yasha ruwan zagi da
rashin mutunci dan acewar sa duk shine yaja musu badan haka ba da tuni su Abdulmajid sun
dawo hannunsu.
Sosai driver ya dinga sharara gudu na fitar hayyaci domin ganin sun isa da wuri yayin da
tsakanin Fatima da Abdulmajid akarasa wanda zai masa magana akan ya rage gudu domin
dukan su babu mai iya magana banda matsanancin gudu babu abinda zuciyarsu yake yayin da
kowannen su yake addu a da fatan kub'uta acikin zuciyarsa.
Sai daya gama k'arewa Badamasi zagi da cin mutunci sannan yace su koma ya bincika yaga
inda suke ya datse hanyar, wani ikon Allah duk k'warewa da iya aikinsa ranar kasa gane komai
yayi wanda kansa yagama d'aukar zafi dan haka ya tarwatsa kayan aikin yayin dayake kuku
wurjan jan.
Wata irin ajiyar zuciya suka sauke lokacin da mai motar yake danna hon a k'ofar gidan suka
rungume juna,cikin tsantsar farin cikin tsallake rijiya da bayan da sukayi.
Sai da mai gadin ya lak'a gidan yaga wad'anda suke ciki yasaki wani irin ihun murna yasaki
wanda sai dayai sanadin fitowar duka mutanen gidan.
Ummi jiki yana rawa ta k'araso da gudu ta rungume Fatima tareda da fashewa da wani irin kuka
yayin da Fatima ta yanke jiki ta fad'i a wajen, duk sukayi kanta a gigice.
Maman islam ce
[11/30, 6:11 AM] Hayat: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA