Showing 12001 words to 15000 words out of 65710 words
Chapter 5 - ZATO NE (1 TO End) BOOK COMPLETE By Maman Islam.pdf
tayi mamakin yawansu.
K'arasawa sukayi har gabansa suka durk'usa, idanunsa akansu ya aje carbin dayake ja agefen
sa sannan ya dubesu cikin murmushi da farin cikin ganinsu musamman Ihsan wanda yau ne
zuwanta na farko.
Cikin girmamawa suka gaidashi ya amsa cikin sakin fuska tareda tambayar su iyayen,su sukace
duk suna lafiya suna gaida shi, sun d'an tab'a hira ka d'an kafin su nemi makwanci domin duk a
gajiye suke
Maman islam
[10/7, 7:57 AM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 40
....................washe gari tunda suka idar da sallar asuba suka koma suka kwanta domin har
lokacin gajiyar bata gama sakinsuba.
Sai dai kuma hayaniyar da tafara tashi sama sama bai barsu sun kwanta ba domin gidan haka
yake indai akace anyi sallah zakuga mata da maza suna ta tururuwan kama layi.
To yauma hakan ne yakasan ce kafin kace me gidan ya kacame da hayaniyan jama'a hakan
kuma ne yayi sanadin hana su Fatima komawa baccin kamar yanda suka so, sai faman juye
juye sukeyi.
K'a'idar kawu Tanimu baya fara ganin mutane sai k'arfe tara na safe wanda inya fara baya
rufewa sai d'ayan dare sannan kuma idan ya sallami mutane a daidai wannan lokacin yake
nasa uzurin.
Yau kam bai wuce kai tsayeba sai da ya gaisa da 'ya'yan nasa kafin ya wuce d'akin saikar
bak'insa yana fad'in "kai Abdulmajid idan kun gama karin kumallo saika zo tareda su da to ya
amsa sannan ya juya ya fita Ihsan ma ficewa sukayi tare da Hanifa d'iyar kawu Tanimu ce
wacce bata fi sakuwar Ihsan d'in ba,
Suna fita Abdul ya d'an matso kusa da Fatima yajata jikinsa tare da sakin ajiyar zuciya yace
"gaskiya baby jiya kasa bacci nayi"
Zuba masa ido tayi kafin tayi sannan ta tambayeshi da idonta "me yasa?"
Nuna ta yayi yace "kece mana Fatima ada ina iya hak'urin rashinki na kwanaki biyun da kuke
keda marigayiya amma yanzun nasani bazan taba iya rasakiba dan haka gaskiya nidai kisan
yadda zakiyi dani domin bazan iya jurewaba"
Ya fad'a cikin sigar shagwab'a, dariya ta kwashe daahi sannan ta kwanta a jikinsa tana fad'in "to
yanzun ya kakeso ayi?
"Kawai ki tashi mu d'an lalubi wani wajen na d'an rage zafi" ya fad'a yana kallon cikin idanunta,
wanda ta zarosu gaba d'aya tana kallonsa da mamakin sa sannan tace
"Gaskiya badani za'ayi wannan fitsaran ba kai yanzu dan Allah idan nace na amince sai ka
aikata wani abun anan?"
Yace "dan Allah d'an gwada koda wasa ki gani me zai hana yarinya kuma ma da zaki wani ce
fitsara naga ai ba abin kunya nayiba halalina ma amsa" murmushi ta saki sannan tace "bada ni
za ai wannan d'anyen aikinba"
Shima murmushin yayi tareda janta jikinsa yace "amma ai a bari na d'an rage zafi ko dan
wallahi a mugun matse nake"
Kafin ma tayi wani yunk'uri ya had'e bakinsu yana sakar mata wani irin kiss wanda dole yasa ta
mik'a kai batare data shiryawa hakan ba.
Lafiyayyen break first aka kawo musu harda soyayyen naman zabbi kamar ba ruga ba haka
suka zage sukaci suka k'oshi sannan suka he amsa kiran da malam d'in yasa ayi musu.
Wannan karon ba a d'akinsa ya sauke suba a d'akin saukar bak'insa ne shi kansa Abdulmajid
bai taba shiga d'akin ba dan haka sukayi matuk'ar mamakin had'uwar d'akin, wanda falon yaji
wasy irin had'ad'd'un kuheru masu d'an karen kyau da burgewa zagaye suke da wani
had'adden glass teble mai sufar kwai sannan ga wasu k'ofofi wanda a k'alla zasu kai guda uku
sai wata k'arama wacce da alama k'ofar toilet ce atak'aice dai zasu iya wajen da d'an
madaidaicin gidan da akayiwa kofar shago daga ta waje da cikin gidan malam d'in.
Cikin nutsuwa suka k'arasa gaban malam d'in sabuwar gaisuwa suka sake masa sannan ya
nunawa Ihsan kwanukan daya gama kari yace taje dasu ciki, a hankali ta taahi ta tattare kayan
tayi cikin da su sannan shi kuma ya maida hankalin shi kansu yace.
"Yauwa Abdulmajid duk da kasan cewar Abubakar yamin bayanin,abinda yake,faruwa daku
zanso k'arin bayani dan kunsan masu karin magana sunce wak'a abakin mai ita yafi dad'i"
batare da wani b'ata lokaci ba Abdulmajid yafad'a masa iya abinda ya sani sannan Fatima ma ta
bashi labarin duk irin abinda take gani tareda mugayen mafarkan da idan tayisu suke zama
gaske.
Sosai ya fahimci bayaninsu sannan yaja k'asa take gaban Abdulmajid ya b'aci dan bai tab'a
sanin kawu Tanimu yana duba ba kuma ya sani duba ba abune mai kyau ba, amma sai baice
komai ba.
Shikuwa kawu Tanima zane yafara yi akan k'asar yana gogewa sai da ya shafe kusan mintuna
sha hud'u kafin ya nuna ma fatima wani glass fari kar mai masifar santsi yace ta mik'o masa
yana karb'a ya d'orashi saman k'asar rufe ido yayi yana magana a zuciyarsa wanda su basa jin
abinda yake cewa sannan ya bud'e idon ya d'an bugu glass d'in kad'an sai ga shi kuwa ya samu
abinda yake nema,yace su dawo kusa dashi su gani, babu musu kuwa suka lek'a.
Take gaban Fatima yayi wata irin masifaffen tsoro ne ya kama Fatima da sauri ta fad'a jikin
Abdulmajid cikin wata irin kid'ima cikin rawar baki tace "sh...shin wallahi shineee......
Muje zuwa
Maman islam
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: *مسب الله نمحرلا ميحرلا *
*☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️*
FCWA
*Home of qualities and trusted writers of the nation*
https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?ty
pe=3&source=45&refid=17
_________________________
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Daga marubuciyar
ABINDA YAKE RAINA
WAYYO RAYUWATA
Page 7
......................kusan abinda yafaru a hanyar zuwan su shine yasake faruwa da k'yar Abdul majid
yakawo kansa gida.
Cikin kwana d'ayannan da sukayi har Fatima tayi wata irin rama tayi wujiga wujiga da ita, abin
tausayi duk ta wani firgice.
Lokacin da suka isa gida ana kiran sallahr azhar Ummi tana kicin ta had'a abincin rana taga
giftawar Fatima da sauri.
Daganin yanayinta babu nutsuwa atattare da ita,da sauri Ummi tak'arasa abinda take tabi 'yar
tata, saidai sanda tashiga d'akinnata har ta tayar da sallah, dan haka itama ta juya dan gabatar
da tata sallar.
Ab'angaren Abdul ma yana shiga b'angarensa wanka yafarayi agaggauce sannan yayi alwala
ya wuce masallaci.
Yana dawowa daga masallaci direct wajen mammy ya wuce , suna dirning area ita da autarta
suna cin abinci.
Mammy tabi d'annata da kallo tana amsa sallamar dayayi memma tayi masa sannu da zuwa
tanafad'in "nidama nasan Fatima bazata iya sati guda abajoga yadai fad'ane kawai.
Kallonta Abdul yayi yana tambayar ta da ido, wai yaushe akayi hakan?
Memma tace sanda kuke shirin tafiya tace min ita tanason ku d'an kwana biyu acan bayan
tafiyar ku kuma naga message d'inta wai zata lallab'aka har kuyi sati"
Murmushi yasaki har saida kyawawan hak'oransa suka bayyana memma tasaki baki tana kallon
yayan nata wani mashahurin kyau yake yi aduk lokacin da zaiyi dariya.
Gaida mammy yayi yana dungure kan meema yace"duk kin d'aukemin hankali da d'an banzan
surutunki ko uwata ban gaisarba.
Dariya memma tayi kafin tace "wai ina Fatimanne yaua naganka kai kad'ai koda gaske ka
barota acan d'in?"
Itama mammy kallonsa take tajiran jin amsar da zaibata, "ban saniba suda kinga k'yaleni yunwa
nakeji mammy zubomin abincin dan Allah"
Mammy tace "bangane baka saniba inakabaromin yarinya?"
Ta masa tambayar tana tura masa flat d'in abincin data zubo masa, saida yayi bismillah yafara
cin abincin dan yunwa yakeji sosai Fatima bata bari sunyi karin kumalloba ta uzzura masa suka
taho.
Duban mammy yayi yace "tana fat d'insu dan ko kari bata bari munyiba tace ita gida zata tafi"
Nan kuma ya kwashe duk abinda yafaru a hanya ya fad'awa mammy, bak'aramin girgiza tayi
dajin wannan abinba tabbas duk ma wanda yake bin baya d'annata baizai denaba ya zama dole
ta fad'ima Abbu dan tasan tabbas zai iya bada taimakon daya kamata.
Abangaren Fatima,kuwa saida tayi sallah sannan tayi wanka,dake sanda ta shigo gidan anriga
da antada sallah.
Bayan ta shirya cikin wasu riga da sket 'ya kanti kalar blue mai duhu sunyiwa jjar fatarta kyau
sosai.
A falo tasami Umminta tana cin Abinci kusa da ummin ta zauna tagaida ita sannan taja abincin
yayinda ummin take tambayarta yanda ta barosu.
Tace "duk suna lafiya ummi tace agaidaku, ummi ta d'an k'ara kallon 'yar tata da kyau ganin
yadda ta zuk'e lokaci d'aya tace
"Ciwo kikayi ne adaren jiya naga kin zuk'e?"
Ajiyar zuciya Fatima tayi kafin ta dubi ummin da idanunta da har sun,ciko da kwalla take abinda
yafaru yafara dawo mata kamar yanzune abin yake faruwa babu 'yar b'oye b'oye tsakainta da
umminta take ta kwashe duk abinda faru ta fad'awa ummin, wanda itama ummin bak'aramin
girgizata abin yayiba karfa kuma wani abu yasami tilon 'yar tata dan tanada kusanci da Abdul
majid?
Ai kusancin su ba aure bane kuma ko Abdul majid yace yanasin Fatima,bazata tab'a amincewa
ba dan,abinda ta lura dashi duk wanda zai mu 'amalance shi koda da soyayyane sunan shi
gawa.
Wannan kenan
Ab'angaren mutuminnan kuwa tsaye yake gaban gunkiyar nan yau idanunta har ya wuce
rannan haka duk wani k'ofa najikinsa babu inda baya kwarar dajini.
D'ago wutar dakeci a idaninta tayi naga ta kalli mutumin wanda duk ranar datayi hakan mutum
ya b'ata mata rai kuma wannan kallon shima azaba ne dan mutum zaiji ajikinsa.
Jinai tana magana yau kuma da muryan jarirai tace "wayace kabita kanason lalatama aiki
bakasan cewa idan ubanta yasan kana bin ta sai ya kawo k'arshenkaba? dan mudai munriga da
munfi k'arfin duk wani mai shiri akanmu"
"Kar ka sake binta lokacin baiyiba idan lokacin yayi dakaina zan d'auko ta domin muna
buk'atarta dan gudanar da wani gagarun shiri amma,ba yanzuba da sauran lokaci
Daga haka ta rufe idanun tana hawayen jini,alamun tagama,bayaninta.
Gani nayi wata irin iska tayi watsi dashi bai fad'i a ko inaba sai bakin falon gidansa, wannan
shine hukuncin duk wanda ya sab'a umarninta
A sume yake tun bayan sa adda wannan aba ta watso shi bashi ya farkoba sai bayan da iskar
asbah ya hurashi.
Da sauri ya tashi yashige d'akinsa duk jikinsa babu inda baya masa ciwo bin matarsa yai da
kallo wadda bata san mai yake faruwa toilet ya shige yayi wanka da ruwa mai mugun zafi wai
ko zaiji dad'in jikin sannan ya d'auro alwala yazo yatashi matarsa sannan shi kuma ya wuce
masallaci.
Abinda zai baka mamaki shi wannan mutumin mutumne mai mutuk'ar sadaka da kyauta sannan
ga taimako gashi babu wani lokacin salla dayake wuceshi
Tun ranar da Fatima tabawa umminta labarin halin data tsinci kanta aciki ta gargad'eta kan
cewa ta fita a hanyar Abdul majid babu ita babu shi idan ba haka ba itama zatabi sahun
matattun 'yan matansa.
Ita Fatima sam ta manta da wannan abin saida ummin ta fad'a sannan ta tuna da yake babu
abinda Abdul majid ya b'oye mata na abinda yake faruwa .
Duk da cewa taji tsoro sosai amma ranta bataji kamar cewa zata iya rabuwa dashiba domin
shid'in d'an uwanta ne kuma jininta
Dan haka rabata dashi cikin sauk'i ba abune mai yiyuwaba, abinda ta nunawa umminnata
kenan kuma hakan baima ummin dad'iba saidai bata k'ara ce mata komaiba gudun kar Fatima
tayi tunanin ko batason alak'arta da d'an uwantane kamar yadda Fatiman tayimata ba haguwar
fahimta.
Wata ranar juma'a Fatima da meema suka shirya zasuje kasuwa siyayyan kayan kwalliya da
wata babbar super market da akeji da ita a fad'in gombe da kewayenta.
Har sun fito saiga Abdul wanda shi tun bayanda ya dawo daga masallaci bai shigo gidanba
yana tareda abokinsa Yasin kallo yabisu dashi kafin yace "ina zakuje haka?"
Fatima tace "kayan kwalliyarmu sun k'are kasan next week zamu fara zamu fara zuwa school"
D'an had'e rai yayi yace "kwalliya zakuje kenan ba karatuba harda wani cewa kayan kwalliyarku
ne ya k'are"
Ya kwaikwayi yadda Fatima tayi magana "to ku koma babu inda zakuje" yafad'a cikin rashin son
wasa fuskarnan a had'e babu shiri suka juya ganin yadda ya had'e gira Fatima harda kwallan
takaici dan tun bayan zuwnsu yaune zatayi fita na biyu dayake gidanma ba wani yawan fita
suke ba inba da kwakwaran daliliba.
Da dare suna falon Amma duka yaran gidan gaba d'aya hayaniyarsu ya hana Amma sakat
maganar duniya idan tayi idan sukayi kamar sunyi shiru sai su kuma kaurewa dan dole tasa
musu ido tana kallonsu wani abin idan sunyi su bata dariya wani kuma tayi tsaki.
Ammar ne k'aninta ya shigo da d'an gudunsa yace anty Fatima yaya Abdul yana kiranki yana
b'angarensa.
Yana gama fad'a mata ya juya da gudu ya fita, itako Fatima cigaba tayi da uzurinta domin har
lokacin takaicin hanasu fitan dayayi bai k'yaletaba.
Sai da Amma ta kuamayi mata magana sannan ta mik'e tana zumb'urar baki, yayinda su
meema suka kwashe da dariya gamida tafawa.
Irindai shak'iyancin nan na 'yan mata, falonsa ta sameshi dagashi sai 'yar farar singlet da tree
queter da robar ruwa hannunshi yanasha.
Tana shiga ya mik'o mata ruwan hannunshi ta karb'a ta nufi frij zata ajiye, a hankali tajiyo
muryarshi tana kallonshi da mamaki, a ranta tace ji mutum saikace nace masa ina jink'ishi da
zai wani bani ruwa.
Kamar yasan abinda yake ranta yace "inbazki shaba bani abina"
Ta kuwa mik'a masa, ganin haka ya had'e rai yace "sha kona b'ata miki rai" kallonsa take da
tsabar mamaki, amma ganin babu alamun wasa atareda shi yasa ta sha ruwan.
Sannan yace tashiga d'akinsa akwai ledoji ta d'ebomasa tashiga, ledodin wajen da sukayi niyar
zuwane ya hanasu manya har guda uku,
Ta kawo gabansa ta ajiye yaja yafara bud'awa sannan ya d'aga kai ya subeta tana tsaye akansa
kamar wata 'yar sanda "zaune mana karki fad'omin aka"
Zama tayi tana wani ciccin magani shi wallahi ma dariya tabashi yadda take wani muzurai
kamar zata saka masa duka.
Kallonta yayi yace "matso kiga kayan da nasiyo ko sunyi muku"
Cikin d'auke kai tace "nifa dama nafasa siyayyar nan kawai kaba meema ko ita tana buk'ata"
Kallonta yayi cikin had'e rai yace "wato kema zaki koyi raini ko ta d'auka i dan kin fita sai ki
zubar.
Nifa nac..........wata tsawa ya buga mata wacce take jikinta yafara rawa da gudu ta d'auki kayan
zata fita batareda ya nuna mata kayan yadda sukeba.
Cikin daka tsawar yace "na fitar miki dana kowane 'yar rainin hankali da gudu ta dawo kawai
tayi tuntub'e da roban ruwan data ajiya saigata ta fad'a masa duk ya rikitata da madifarsa kawai
sai tafashe da kuka
Taku maman islam
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Masoyana masoya labarin ZATO NE inajin dadin comment dinku ina alfahari daku love u All
love u much
Page 8
......................Zuba mata ido kawai yayi yana kallonta yadda take zubda hawaye babu
k'akkautawa.
Yace "sai ki d'agani karki ballani ko?" da sauri tacsauka ajikinsa tana tura baki
Kansa ya d'an shafo ya zuba mata ido yana sakin wani kyakyawan murmushi, duk wannan
zumbure zumburen baki saiyaga tak'ara masa wani sihirtaccen kyau.
Kayan ya jawo batare da ya kuma bi takantaba, yayin da ita kuma take ta hararansa ta gefen
ido, sarai yaganta sai dai ba bata damar ganewaba yaci gaba da rabaya kayan yabata na kowa
amma nata yafi yawa.
Ta kwashe kayan tayi hanyar waje har takai bakin kofa yace "hi!!
Cak tatsaya batareda ta juyoba yace"daman agarinku haka akeyi idan anbawa mutum abu babu
godiya?"
Kallonsa tayi ta bud'e kofar ta kalli hanya sannan tace "ai ba rok'onka nayiba ga kayanka nan"
Ta ajiye masa ta falla