Showing 42001 words to 45000 words out of 65710 words
Chapter 15 - ZATO NE (1 TO End) BOOK COMPLETE By Maman Islam.pdf
3 munute kafin ta zunduma
wani gigitaccen ihu wanda yai sanadin fitowar Yusra a d'aki da mugun gudu.
Ganin abindaa yake faruwa sai data taya Fatima zubda hawaye dama tasan za'ayi haka domin
hannun ya riga yayi tsami,
Duk wani k'ok'arin ta na son k'wacewa a hannunsa abin ya gagara domin sai da aka gama
gyaran tsab kafin yasake ta ta kwanta awajen tana maida numfashin wahala.
"Tsagewar k'ashine tayi gashi kuma wajen yayi tsami shi yasa ya d'an bata wahala" yana shafa
mata magani a wajen sannan yasa bandge ya d'aure hannun tamau
Tare suka fita da mai gyaran ya sallame shi.
Sannan ya dawo tana inda ya barta sai juya kan wahala take tana mai da numfashi, sosai yake
tausaya mata, amma bai bari hakan ya nuna a fuskarsa ba yasa hannu ya cicib'eta yayi d'akinta
da ita.
Allah sarki Fatima sarkin tsabta amma d'akinta ko sharan kirki babu, saman sofa ya kwantar da
ita ya d'an karka d'e mata gadon sannan ya shiga ban d'aki ya had'a ruwa mai d'umi, ya dawo
ya sunkuce ta sai da ya wanketa tas ya dawo da ita ya sauya mata kaya yabata magani tasha
ganin jikinya ya d'auki zafin zazzab'i sannan yaja mata bargo ya rufeta ya d'an k'ara k'arfin acn
yai waje abinsa.
Tunda ta kwanta bini bini ya lek'ota amma sai yatarar tana bacci tajima sosai tana baccin domin
kwana biyunan bata samun bacci saboda hannun.
Tunda ya shige d'akin tana jiyo irin buge bugen dayake da iface ifacen sa mamaki ne sosai ya
kamata na abinda ya sami mijin nata yake abu haka kamar tab'ab'b'e,
Tun tana sa ran zai fito daga d'akin har tagaji taje ta kwanta sai dai takasa samun nutsuwa
domin bata tab'a ganin mijin nata a irin wannan yanayin ba.
Sosai yanayin haj. Asma'u yabawa 'ya'yan ta mamaki domin duk iya binciken likita cewa suke
lafiyan ta k'alau babu wani abu da yake damunta.
Yaune suka gama yanke hukuncin zasu koma gida ayi na garga jiya sai dai kuma yau d'inne
suka ga ta tashi dan gwar gwar ta zauna asaman gadon tana k'arewa d'akin data gama
tabbatar da na asbiti ne kallo.
Sosai gaban ta ya fad'i fatan ta Allah yasa baayi abinda zai tona asirinta ba.
Husna wacce ta d'ago kai tana kallon mahaifiyar tata cikin tsantsar farin ciki da kuma tsabar
mamaki tace "umma?"
Sai kuma ta rungumeta gami da fashewa da kukan farin ciki tace "Allaj na gode maka Allah ka
k'ara mana sutura da rufin asiri daman ubangiji baka d'arawa bawa abinda bazai iya ba sai in
har shi ya d'orawa kansa.
Tare suke jinyar ta shida Yusra sai dai koda wasa baya sakar mata fuska bare takawo masa
wani shirmen itama ko kallon inuwar data d'eboshi batayi sai dai aranta tashabalwashin tana
warkewa zasuyita ta k'are dan dole yayi mata abinda take so ko aji kansu.
Bayan kwana uku mai gyarn ya kuma zuwa ya duba hannun aikin yayi kyau sosai, sati guda
hannun yayi aka kwance d'aurin akaci gaba da shafa mata magani.
"Abubakar wai me yake faruwa ne tun kwanakifa ka soma cemin ka gano masu cin dunduniyar
mu ammavharvyanzun banji kace komai akan maganar ba" wani murmushi Abbi yasaki kafin
yace "ka k'ara hak'uri yaya insha Allahu komai ya kusa zuwa k'arshe da idonka zaka ga abinda
zai matuk'ar baka mamaki dan inbamu yi da gaskeba bama za'a'iya samun matsala"
"To Allah ya kyauta Allah yashiga tsakaninmu da makiyanmu" daga haka sukayi sallama.
Sosai takevsamun sauk'i dan har ta fara gwada d'aukar abu da hannun ta dawo kamar da tana
shiga kicin tayi duk abinda take so, sai dai matakin farko data fara d'auka ta daina girki da su
dukansu kuma tayi mugun janyewa Yusra domin sai ta kwana ta wuni babu wanda yaganta
acikin su shi kuma ganin ta warke yasa ya watsar da al'a muranta ko inda take baya kalla
Taku maman islam
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 33
.....................yau tunda garin ya waye bata fito ad'akin ba haka nan ta tashi da wani irin k'unci
tunda ta idar da sallan asuba take ta faman juye juye asaman gadonta abin karima ta kasa
fitowa ta dafama kanta.
Sau biyu Yusra tana lek'owa tana tambayar ko lafiya sai tace mata lafiyanta k'alau, dan haka
data ga kamar bata son atakura mata sai itama ta shareta.
Sai washe gari ya fito a d'akin wujiga wujiga dashi daganin sa gaba d'ayansa afirgice yake sai
dai ita intama mutum tambaya taga bai fad'a ba bata kuma bin takansa acewar ta idan najin ne
tana zaune zai fad'a.
Bayan yayi wanka ya fito ta kawo masa k'osai da kunu, atake ya d'aga tangamemen cup d'in
kunun ya zuk'eshi tas ya dire cup d'in, da mugun mamaki take binsa da kallo amma bata iya ce
masa komaiba.
Bai ce mataba batace masa ba domin ta lura bayason fad'a mata abinda yake damunsa itama
bata ce me yakevdamunsa bababu huda d'aya data lura shine yakan shiga d'akinsa na saukar
masu neman temako amatsayinsa na malami yajima aciki bai fitoba.
"Duna burinka ya cika nawa ya cika dan haka ka kwantar da hankalinka ni dakaina zan kashe
'yar duna wanda yai sanadin mutuwar tilon 'yarka tak a duniya dan haka duk wani bincike da
kake ka daina shi itama Asma'u na kyaleta abisa ganowa danayi tana da sauran aikin dabata
kammalawa Dumb'uruba wanda ni nasaka yasakata dan haka inaso kasan cewa data gama
zamu gama da ita sai mu gudanar da babban aikin nida kai akan zuriyar Ahmad".
Sosai Duna ya d'anji hankalinsa ya kwanta domin ba k'aramin bashi tsoro had'in kan Munzali da
Dumb'uru ya bashiba, domin shi wani irin shed'anin mutum ne da baisan wani abu waishi
imaniba, zai iya komai akan biyan buk'atar sa.
Yace "angama mai girma Gaza indai wannan abun zai tabbata ni kuma zan temaka miki ki
cimma burinki nazama shugabar matsafan wannan yankin, wanda ta hakane zaki rama abinda
wanda muka kwatoki hannunsu suka miki".
Wani matsiyacin murmushi ta saki tace "shike nan zaka samu yadda kake so dan haka jeka ci
gabada sha'anin gabanka.
Tunda take saukowa daga saman yake kallonta afakaice batare da yabari tagane yana
kallontaba ita sam bata ma kula dashiba saida tazo dab dasu sannan ta kula da su suna had'a
ido da Yusra ta d'an sakar mata murmushi, ta wuce batareda tace komaiba.
Baisan sanda ya buga wani uban tsalle yasha gabanta ba yana kallon cikin idonta wanda fir ita
tak'i yarda ta kalleshi tayi masifar had'e rai ba kuma tace masa komai ba, shima bai ceba sai
hannunta da ya kama ya maida ita d'akinta kafin yace.
"Yanzun ke dan tsabar baki da hankali a haka zaki fita dubafa kiga kayan dayake jikin ki wato
ga d'an iska kina aure bari kiyi shigar da duk ranki yake so ki fita masu aiki suna kallonki ko?"
Jikin nata tabi da kallo, sanye take da fara kar d'in 'yar shet me hannun shimi sai wandan da
yakai mata har kwairinta ita sam bataga aibun shigarta ba domin kayan bawai irin sun kamata
d'innan bane sai dai sun mata cif cif kamar dama an gwada tane.
Kallon sa tayi ranta a matuk'ar had'e kafin tace "wai ina ruwan ka da harka nane ni banshiga
nakaba inba shishi giba ni banga dalilinka nason sai ka shiga nawaba dan Allah ni kasamamin
lafiya haba jabi ka addabeni ka addabi rayuwana ka barni mana nima na shak'i iskar 'yanci"
Ta k'arasa tareda fashewa da kukan dataji ma tana tarashi, shi kam tagumi ya zuba yana
kallonta da mamakin kalamanta sam baiga wani abu daya mata natakura ba saidai bazai
lamunci tafitar masa a hakaba wasu banzaye suyi ta kalle masa ita a haka ina sam bazai
sab'uba bindiga a ruwa.
Batare data hankareba ya fisgota jikinsa ya had'e bakinsu yana mata wani irin salon dayasa
dole tayi lub a jikinsa.
Sosai yayi missing d'inta dan haka bai mata da sanyiba saida ya fanshe duk wani bashi daya
san ya ci, domin Fatima ba irin matan da ake iya dogon fushi dasu bane.
Maman islam ce
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*_____________
_______________________*
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKSAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 34
...................bayan yagama samun dukkan nutsuwar da yake buk'ata atareda ita ne yajata
jikinsa ya k'amk'ameta, wannan halayyasa ne matuk'ar zai sauke wani nauyi sai yayi kamar zai
ballaki tsabar ruk'on da zai miki.
Fahimtar da yayi Fatima tafara bmfushi dashi ne badan ta dainaba yasaka shi ajiye nasa girman
kan agefe ya zage yake baje duk wata fasaha tasa akanta a duk lokacin da yake d'akinta.
Tunda aka
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*_____________
_______________________*
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKSAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 34
...................bayan yagama samun dukkan nutsuwar da yake buk'ata atareda ita ne yajata
jikinsa ya k'amk'ameta, wannan halayyasa ne matuk'ar zai sauke wani nauyi sai yayi kamar zai
ballaki tsabar ruk'on da zai miki.
Fahimtar da yayi Fatima tafara bmfushi dashi ne badan ta dainaba yasaka shi ajiye nasa girman
kan agefe ya zage yake baje duk wata fasaha tasa akanta a duk lokacin da yake d'akinta.
Tunda aka sallamo ta daga asbiti suka kasa gane kanta ta zama wata irin shiru shiru duk fad'a
irin nata yanzun duk abimda yaran zasuyi sai dai tabisu da kallo, sosai abin ya damu yaran nata
domin sunsan cewa uwar tasu bata da hak'uri ko kad'an.
A bangaren Fatima kuwa tunda ta fahimci cewa ta haka Abdulmajid yake son hukuntata sai
tayada makaman yak'inta sai dai tasha alwashin tanaji tana gani bazata bari akansa a wani
salwantar mata da rayuwaba hakane ma yasa ta dage sosai da addu'a dan sosai take jin tsoron
abimda zai iya faruwa nan gaba tunda dai bawai an k'yalesu bane.
"Tunda muka had'e kai da kai nasan dole Gaza zata nemi Duna kuma kasani 7sarai bala in
Duna ya wuce tunanin mu mu duka tunda shi masanin qur'ani ne sannan mahaddaci kaga
yasan komai dan haka nake so ka nemeshi kafin ita kaga ni mun d'an samu matsala kwanakin
baya"
Cikin,damuwa Munzali ya fesar da wani zazzafar iska ya d'an dafe kansa yana kallon Dumb'uru
kafin yace.
"Akwai matsala oga nasan kasan abinda yafaru akan 'yarsa dana bawa qungiya jininta yanzun
haka idanunsa suna kan 'yata Hauwa dan Allah ka san hanyar dazaka b'ullo masa inajin
yarinyar sosai"
Ya k'arasa maganar da matsanancin damuwa afusakarsa, sosai Dumb'uru yayi shiru cikin
dogon nazari shi kansa akwai binciken da yayi akan yarinyar kuma jininta yayi daidai da cikar
burinsa, sannan baiyi zaton inya nemi abinda yake so game da yarinyar za'a sami masalaba
ganin cewa bata hanyar aure yasamu yarinyarba, amma a zahiri sai ya nuna masa zai temaka
masa wanda ba hakanne aransaba shima.
"Ku shirya dukanku zamu je bajoga duba gwaggo Hafsatu bata da lafiya" cewar Abdulmajid da
yafito cikin sauri ya shige d'akinsa.
Da murna,suka tashi kowacce tashiga d'akinta dan shirin, ita Fatima tana murnan yau zata
wataya yayin da Yusra wannan ne karonta na farko dazata je bajogan.
Sanda suka fito tun ya gama shirinsa ya d'an dubesu yace "kowaccen ku ta koma d'akinta ta
d'auko kaya kala d'aya kunsan bazai yiyuwa muje yau mu dawo ayau d'inba"
Sosai suka d'auki hanya tun suna hira har Fatima wacce tasa rigimar ita zata jasu tagaji yace
Yusra ta karb'a itama ta d'ana.
Tunda Yusran ta,karb'i tuk'in Fatima ta koma bayan ta kwant, ta bungire ta kama bacci yayin da
su kuma sukaci gaba da hiran gabansu.
Sosai baccin yayi mata dad'i tana tsaka da baccin taji ana goga mata abu kamar gashin mage
(kyanwa/ mussa) ta d'an bud'e idanunta cikin yanayin bacci me zata gani wata jibgagiyar
magece kwance ajikinta yayin da idanunta suka kasance wani irin fari k'al gwani tsoro Sosai
jikinta yakama rawa, takai dubanta kan Yusra da Abdulmajid da suke ta hiransu suna shek'ar
dariya abinsu saida abinda ya kuma mugun kad'ata zakinnan ne wanda ta tab'a gani awannan
hanyar ta bajoga kuma adaidai wannan wajen dayabisu har gidan gwaggo Hafsatu yauma shine
amma cikin motar su yasaita wuyan Yusra da wata sharb'eb'iyar wuk'a
Suna had'a ido sai taga kamar ma yana mata dariya haba wani irin razanannen ihu Fatima ta
saki wanda yasanadin da motar ta kwace a hannun Yusra tatafi ta daki wani k'aton dutse take
motar takife da su innlillahi wainna ilaihi raji un.
Maman islam ce
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 35
.......................innalillahi wainna ilaihi raji un, shine abinda d'aid'aikun mutanen da sukaga
faruwan abin suke maimaitawa,
Da gudu suka nufi motan da basuyi tsammanin zasu sami wani abu mai rai acikiba, da k'yar
suka iya d'ago motar da ta kife suka juyata.
Innalillahi,wainna ilaihi raji un shine abinda masu k'arfin zuciyar cikinsu ke fad'a masu k'aramin
zuciya kuwa tuni suka fara zubda hawayen tausayi da ganin irin mummunan abinda yafaru da
wad'annan bayin Allahn.
Babu jima jami'an da wasu suka kira suka k'araso suka kwashesu akayi asbiti bajoga da su
domin sunfi kusa da nan.
Ba k'aramin tada hankalin ahalinsu wannan had'arin yayiba sosai suka firgita dajin abinda
yasamu yarannasu babu kamar Abbi wanda yakasa samun nutsuwa tareda tsoron abinda zai
iya faruwa dasu.
Acan gidan Gwaggo Hafsatu kuwa sosai rigima ya b'alle tsakanin malam mijinta da wani bawan
Allah wanda ban gane fuskarsa ba sakamakon yadda fusarsa yayi gaja gaja da ruwan hawaye.
Daga ganinsa kaga wanda yake cikin tsantsar damuwa da tashin hankali kamar ma wanda yake
a firgice.
Tun kafin akaisu asbitin Yusra tace ga garinku nan abin kuma da ya matuk'ar gigita jama'ar
yanka rago suka gani a wuyanta wanda basusan dalilin faruwarsa ba.
Absulmajid wanda da farko bai wani jigataba bayaga 'yar kurkurjewa dayayi amma ganin
abinda yafaru da Yusra take numgashinsa ya d'auke ya sume awajen.
Koda aka samu Yusra ta farfad'o ta farfad'one a wani irin firgice dan da ife ife sakamakon
firgicewar da tayi domin ita kad'aice taga faruwan komai kafin afkuwar had'arin.
Ummi wacce taci kuka har taji babu dad'i ganin yanayin da 'yarta ta farko ba k'aramin damuwa
ya k'ara mataba domin tasan cewa dole akwai abinda ya faru.
"Umma dan Allah ki daina kukannan haka kar wani abun kuma yazo yasameki bafa su mutuba
ance buguwane kuma sun farko" Husna ta fad'a tana share hawayen mahaifiyar ta cikin danne
nata damuwar.
Cikin kuka tace"Husna ke yarinya ce bakisan halinda nake ciki bane baki san masifar dana
wulla kaina aciki bane saboda masifar son abin duniya irin nawa wallahi Husna, na tsani kaina
da duk wani ma mugun hali irin