Showing 48001 words to 51000 words out of 65710 words
Chapter 17 - ZATO NE (1 TO End) BOOK COMPLETE By Maman Islam.pdf
azahiri kuma numfashi ya sauke ya kuma
shafar glass d'in sannan ya d'an tab'o Abdul ya nuna masa, wani irin ja dabaya yayi sakamakon
abinda ya gani.
Sosai abin yaso baahi tsoro da mamaki idanfa ba gizo idanunsa ke masaba wani k'aton zakine
mai girman gaske asaman wannan d'an glass d'in har kamar yana masa murmushi tareda mik'o
masa hannu.
Fatima wacce tunda ta rumtse idanunta bata k'ara marmarin bud'ewa ba ya ja jikinsa ya dad'a
rik'eta sosai jikinsa yana wata irin rawa sosai abin ya d'aure masa kai sannan kuma duk abinda
Fatiman take,fad'a masa yayi tunanin mafarkai ne take take cewa tagani amma a yau ya
gasgata.
Dubansu kawu Tanimu yayi kafin yace "wannan shine wanda yake bin Fatima yana firgita ta
yana sone yasamu wata dama akanta ya cimma manufarsa kamar sauran saidai har yau Allah
bai basu nasara akanta ba sakamakon Fatima mutum ce mai tsananin ibada bata wasa akan
addininta".
"To wai kawu duk mai yakawo wannan masifar da tashin hankalin danni a iya sanina banda
wani abokin gaba?"
Kawu Tanimu yace "zan iya kiransa da cewa son zuciya ne kawai da kuma son d'aukar fansa
akan abinda ya tab'a faruwa shekaru arba'in baya lokacin baban ka yana saurayi.
Kallon juna Fatima da Abdulmajid sukayi cikin mamakin maganar dayake fitowa daga bakin
kawu Tanimu, yayin da shi kuma kawu Tanimu ya soma basu,labarin kamar haka
ASALIN ABINDA YA FARU
Kamar yanda nasan kasamu labari mu asalin fulanin wannan gari na gombe ne kuma dukan mu
babu wanda yayi aure a wata k'asa ta daban sai mahaifinki Fatima"
"Amma dukan mu muna mabanbanta waje ne hasalima ni bantaso cikin 'yan uwana ba sakama
kon mahaifiya ta daban kuma ta kasance 'yar wannan rugan kuma baya ga haka ma saida
tajima sosai da rasuwa kafin baffan mu ya kuma auro Amma wannan kena.
Sosai rashin auren Baffa yadamu Innarsu wanda hakan yasa ta nemar masa auren 'yar k'awar
ta wato Rabi Amma.
Amma mutum ce mai matuk'ar mutinci da sanin yakamata wannan ne dalilin dayasa Amma ta
siye zuciyar Baffa domin tana mugun kula dasu shida iyayan sa.
Shekara d'aya ta haifo Yuseef wanda shine d'ansu na farko wato k'anina bayan ta haihu ne
babu yadda batayi ba akan Baffa ya karb'o mata ni, amma Dada kakata tayi mursisi ta hanasu
ni.
Dole suka hak'ura suka mai da hankali wajen kula da d'ansu Yuseef farin yaro kyakyawan
gaske gashi da shiga rai haka Yuseef ya taso cikin soyayyar iyayen sa har zuwa lojacin da Inna
ta kuma haifo RIDWAN daga shi kuma sai hafsatu da Mariya wacce ta rasu tun wajen haihuwar
ta ta farko daga kan mariya kuma sai iyayenki yafada yana nuna Fatima sannan yaci gaba da
cewa kasan cewar iyayenki 'yan biyune wato Abubakar da kuma Umar wanda suka kasance
sune autan Amma"
Duk wannan bayanin sun jima,da saninsa a wajen Amma su yanzun sun k'agune kawai suji
gundarin labarin dan haka suka maida hankali da dukan nutsuwar su ga kawu Tanimun wanda
yaci gaba da cewa
"Duk da kasan cewar Baffa da kuma Inna basuyi karatun boko ba sai na muhammadiya hakan
bai hanasu saka yaransu makarantar bokoba tareda tsaya musu har saida sukayi karatu mai
zurfi duk cikinmu ni kad'ai nake da iya kwalin secondry sai kuma Ridawanu da iya diploma
kawai yayi amma dukansu sunyi karatu mai zurfi wanda ku da kanku kunsan da haka wanda shi
Yuseef dama bangaren kasuwanci ya karanta wanda a yanzun akaf gwambe akeji dashi dake
babu abinda baya tab'awa kama daga kan kayan masarufi zuwa sutura.
Sannan duk 'yan uwansa babu wanda ya bai d'auka aikiba bayan ya hanasu aikin gwamnati ni
kaina yaso na koma naci gabada aiki dasu ni naki saboda nariga da nasaba da zaman ruga"
Cikin k'aguwa da sonjin abinda yafaru Abdulmajid yace "kawu ai duk cikim labarin daka bamu
babu wani abu dayake da nuni akwai matsala wanda yake nuni da cewa akwai wata matsala da
tashsfi halin da muke ciki"
Wani shegen murmushi yasaki wanda har saida gaban Fatima ya yanke ya fad'i saboda ganin
murmushin kamar na muguntane yace.
"Me kake ci na baka na zuba ba ina kaikaba?"
Sannan yaci gabada cewa
"Akwai wata yarinya da sukayi soyayya da Yuseef wacce har maganar aurensu akayi da
Yuseef, sai dai dama itace keson Yuseef bawai shine ke sonta ba tasoshi kamar ranta ta
tasoshi kamar zatai yaya
Sai dai haduwarsa da mahaifiyar ka shine ya canja komai tunda ya had'u da mahaifiyar ka
shikenan ya haukace mata ya rufe idanu,yace shifa Hajara yake so kuma ita zai aura.
Wannan shine yai,sanadin da Hauwa ta kamu da ciwon zuciya ta kwanta jinya har hakan ya
zamo sanadin mutuwar ta wannan shine sanadin faruwar komai sannan shine sanadin da
ruhinta ya had'e da ALJANA GAZA suke tabka ta asarsu son rai"
Sosai hankalin Abdulmajid ya tashi shi sam bashi da wannan labarin bai tab'a sanin akwai
wacce Daddy yaso bayan Mommy ba dan ko da wasa basa makamancin maganar agidan.
Sannan kuma,da alama wannan matar jahila ce tunda bata yarda da k'addara ba kuma banda
abinta ma ai matar mutum kabarinsa Allah yayi ba ta jikinta zasu fitoba ya kamata ace tayi
tawakkali ba wai ta mutu da fansa a,zuciyar taba.
"Kawu to yanzun meye abinyi me suke so muyi wanda zaisa su rabu damu?"
Abdulmajid ya tambaya yana kallon kawun,nasa.
"Ta mutu ne da wutar fansa aranta wannan fansa,ce take d'auka akan 'dan Yuseef sannan idan
kuna,so,komai ya zama daidai dole sai anyi sa daukarwa"
Dukansu suka zuba masa ido cikin rashin fahimta tareda aon k'arin bayani sannan Abdulmajid
yayi k'arfin halin cewa "kamar ya sadaukar wa ban gane ba sadaukarwa wacce iri?"
Sai da ya gama k'are musu kallo ya gama nazartar yanayinsu kafin yace "dole abinda zaka
bada shine zai zama masalaha ga rayuwarka Abdulmajid kuma shine,zai kawo k'arshen,komI
kuma,shine,zaisa ku zaune,lafiya arayuwar ku"
Cikin k'aguwa Abdulmajid yace"kafad'a min ko menene matuk'ar zamu huta da wannan masifar
ni,kuma ko zan rasa duka abinda na mallaka ne zan bada shi"
"Dolene zaka sadaukar da wani abu wanda kake masifar jida shi arayuwar ka kuma,kake
masifar so wanda kuma ba komai bane wannan Abun face matarka FATIMA................
Muje zuwa
Maman,islam
[10/9, 10:47 AM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 42
..............A wani irin zabure Abdulmajid yaja da baya yabi kawu Tanimu da wani irin fitinannen
kallo murya na rawa yace "banfa gane ba kawu ban fahimci koda kalma d'aya nadaga zancen
kaba kana nufin Fatimar tawa zanba mak'iyan Allah la'anannun ubangiji su ahanye min jininta?"
"Ni wane irin mara tunani ne da zan aikata hakan ni wane irin jakine da zan bada Fatina to ni
wane irin dak'ik'in mai kwakwalwan kifine da zanyi sadaukarwa da matata kuma k'anwa ta jinina
wallahi wallahi yau ko ni ko su bank'i muyi fito na fito da duk mai son rabani da rayuwata ba na
shiryawa kowane irin fitina da tashin hankali akan rayuwata.
Gaba d'aya ya gigice ya fita a hankalinsa magana kawai yake batare da yasan me yake cewa
ba, abune wanda mafarkinsa bai tab'a bashi ba, abune wanda bai tab'a zato ko tsammani ba,
abune wanda yake neman rabashi da kwanciyar hankali da nutsuwar sa, abune mai matuk'ar
wuya da barazana da rayuwarsa, wato rabashi da Fatiman sa ita ce rayuwarsa bugun zuciyarsa
taya za ayi lokaci guda wani k'aton jaki yace masa wai ya sadaukar da jininta wa masu sab'on
Allah?
Fashewa yayi da wata shegiyar dariya kamar wanda ya zare yace"kawu kodai kaima kana
cikinsu ne?"
Wata irin k'atotuwar fad'uwar gaba ne ta ruftowa kawu take zuciyarsa ta hau wani irin bugu,
amma dayake shid'in cikakken d'an duniya ne sai kawai ya maze tare da kafe Abdulmajid d'in
da ido yace.
"Wannan wane irin maganar banza ne Abdulmajid?
Wannan wane irin shashanci ne ?
Haba Abdulmajid arasa da wanda za a had'a baki sai dani kai tur Abdulmajid kuzo ku koma gida
kacewa Abubakar nima,kana zargina dan haka bazan iya wannan aikin mai had'arin gaske ba"
"Sannan kuma kafin ku tafin zan fad'a maka cewa wannan ya nuna zakin dake ta haniniya cikin
glass kamar zaici babu yace, shine yazo da wannan abun kuma na fad'a maka banda haka ni
jakin inane da zan amince kawai daga fad'a maka bayanin da akayimin?"
Jikin Abdulmajid ne yayi sanyi dajin kalaman kawu dan haka yace
"Kayi hak'uri kawu ba wai haka nake nufi ba na rud'ene zuciyana ya kasa d'aukan abin dan
Allah kayi hak'uri bazan k'araba kaji"
Ajiyan zuciya kawu yasauke cikin d'an yanayin damuwa yace "wallahi Abdulmajid da wanine ya
fad'amin maganar nan bakai ba da sai inda k'arfina ya k'are wajen neman hakkina"
Bayan ya gama bayaninsa yace su matso Fatima wacce kwata kwata taji zuciyarta bai aminta
da kawun ba kasa motsawa tayi sai Abdulmajid ne yajata suka k'ure glass d'in da ido yayin da
shi kuma kawun yaci gaba da zanensa asaman glass d'in saiga wata fuska ta bayyana cikin
wani irin yanayi da mai wuyar fad'a.
Azabure Abdulmajid yaja da baya yace "kawu wannan kumafa bata mutuba?"
Dubansa kawun yayi yace "kasanta ne?
"Yace matar k'anin baban Yusra ne wacce ta mutu wata bakwai daya wuce
" bata mutuba tana nan da ranta cewar 4domin anhad'ata da wani sihirine zataga kowa amma
babu mai ganinta kuma babu maijin maganar ta, amma ita tana gani kuma,tanajin duk wanda
yai mata magana kuma duk wannan aikin bana kowa bane sai wata aljana wai ita GAZA
sannan kuma duk randa wani yakita ko ya ganta ranan dubun duk wani mai binka,da sharri
yacika babu wanda zai k'ara nasara akanka"
Ajiyan zuciya mai k'arfi ya sauke sannan cikin damuwa ya d'an dubi kawun yace "to shi Baba
Munzalin yasan da wannan abun kuwa?"
"Inafa yasani shidai kawai abinda yasani shine matarsa ta mutu har ma anje an binne ta harma
yayi mata addu a bayan wannan baisan komai ba"
"To kawu ku taimaka mata mana dan Allah kaga fa daga gani azabtar daita suke yi"
.
"Abinda nake ta shirye shirye akai kenan Abdulmajid nafika da muwa da halin datake ciki domin
ta sanadin gano inda takene komai da komai zai zama dai dai zai warware"
"Abu Fatima wai dan Allah mai abinda nake gani yake son nunamin?
Nifa ban yarda da wannan Tanimun ba sam raina bai kwanta dashiba wallahi akwai abinda yake
kullawa jiyafa ra''ayil aini nayi mafarki dashi kamar ido biyu yana cewa" sai kuma taji ta kasa
magana an danne mata harshe da k'arfi dole ta hak'ura"
"Murmushin fargaba Abbi yayi yace "ummu Fatima kibar wannan abin fad'ansa akwai matsala
dan haka kija bakinki ki tsuke ni nasan komai kuma kema zaki sani domin babu abinda yafi
k'arfin buwayi gagara misali idan sunfi k'arfinmu basu k'arfin mai ruwa da iskaba, kuma ki
kwantar da hankalinki lafiya lau Fatimanki zata dawo kuma tura Fatima dakikaga nayi tarko ne
na d'ana wanda yake nufin faruwan abubuwa da dama"
Ga mamaki na yanzun sai tayi magana tace "Abu Fatima murd'emin fa baki akayi"
Yace"eh dan karkiyi magana akayi miki hakan dan haka kija bakinki ki tsuke yafi mana alkhairi"
fashewa tayi da kuka ta tashi tabar,musu wajen.
Acan Fatima kuwa magani kawu Tanimu ya soma,musu kuma abin mamakin na Fatima daban
na Abdulmajid daban sam Fatima aranta bataji kaman ta yarda da kawu Tanimu ba dan haka
koda wasa bata tab'ayin maganin dayake bataba sai dai ta had'a rami ta binne.
Haka sukayi tayi har talsayin kwanaki bakwai wanda sam kawun bai tab'a sanin cewa Fatima
bata amfani da maganinba sai ranan da ya shirya shirinsa na farko wanda zai gwada akan
Fatiman sannan ya kirasu fadar tasa ta k'ofar gida.
Zaune suke dukansu agabansa suna sauraron bayaninsa inda yace "to alhamdulillah, duk wani
k'ok'ari danasan zan iya nayi shi wanda babu yanda banyi ba akan al'amarin amma abun yak'i
dan haka Abdulmajid dole anan zaka bar Fatima kutafi kai da Ihsan domin tafiyar Fatima tare da
ku akwai babban hatsari"
Jin abinda kawun yace yasa Fatiman tayi tsalle ta koma gefen Abdulmajid ta rik'e hannunsa
gam tace "tab wallahi k'afana k'afar mijina babu inda zan yarda ya tafi yabarni, kuma kawu
matsafa kaine kake tsoron su ko tsoron kada suyi maka wani abu amma ni babu tsinannen
danake tsoro duk cikinsu sannan na dogara da Allah shine kad'ai zai iya babu wanda ya isa dan
haka ni nabar masa komai dan haka ina so kasa aranka kawu babu wanda ya isa yamin wani
abu sai yardan mai ruwa da iska wanda daga shi muke gareshi zamu koma kuma da yardan
sane dukkan komai yake wanzuwa ina fatan ka gane ko?
Ta fad'a tareda da finciko hannun Abdulmajid tace yaya kutashi mutafi"
"Inna bari hakan yafaru?"
Suka tsinkayi muryansa yana fad'a atsorace dukansu suka juyo dan tabbatar da abinda
kunnenesu ya jiye musu me,zasu gani
Muje zuwa
Takuce maman islam
[10/11, 10:35 AM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 43
................a tsorace dukan,su,suka juyo dan tabbatar da abinda kunnen su ya jiye musu,
mezasu gani?
Da sauri Fatima ta koma bayan Abdulmajid tareda fashewa da wani irin kuka tace "shikenan
yaya namu ya k'are mutuwa zamuyi, wannan abun shine ana, ZATON WUTA A MAKERA
yanzun daman duk wannan masifar kawu Tanimu ke haifar dashi kai innalillahi wainna ilaihi raji
un shine abimda Fatima tayi maimatawa a fili da kuma k'arfi yayin da ko k'ibta idanunta takasayi
daga kan kawu Tanimun wanda ya rikid'a ya koma wannan k'aton zakin dayake firgitata, zaune
saman wata k'asaitacciyar kujera wadda basu san ta yadda ta wanzu awajen ba.
"Ke" kawun yasakar mata tsawar dayasa sai lokacin Ihsan ta fad'i awajen sumammiya domin ba
k'aramin firgitata abin yayi ba,
"Karki k'aramin wata addu'a anan inba hakaba yanzu insa ayi loma d'aya dake awajennan" cikin
wani irin k'arfin hali,Fatima tace
"Idan Allah ya amince maka kenan ko?
Kadafa ka manta kawi Tanimu komai kanayin sane da sahalewa bisa ga huwace wa na Allahu S
W A dan haka na fad'a yanzun zan k'ara babu abinda ka isa kayimin sai da amincewar wanda
yayi ni kuma yayika, sannan ina so kasan cewa duk wannan abun da kakeyi kanayinsa ne
lokacin da kake da dama duk randa daman ya k'wace maka wallahi sunanka sorry, shidama
ubangiji haka yake buwayi ne shi gagara misali idan yatashi zai baka dama kayi abinda kake so
arayuwa amma duk randa yatashi tonaka wallahi karema saiyafika daraja"
Wani irin zazzafan numshi taja cikin halin damuwa da kid'iman data shiga na abinda idanunta
suke,gane mata a halin yanzu, yayin da tafi Abdulmajid dauriya da k'okarin tsayawa har ta
fuskanci kawun take iya fada masa maganganu.
Shi Abdul tsabar mamaki da halin d'imuwan daya shiga bai barshi ya iya cewa komaiba sai
k'amwa dayayi awajen uakasa koda kwakwaran motsine yainda cikin tsantsar tashin hankali da
matuk'ar tsoro akan yanda taga kawun yana tacanja kaloli tacigaba dacewa
"Kayi abubuwa da dama kawu ka kashe rayikan da bassujiba basu ganiba kayi hukunci akan
wanda bai san asalin wanda yayi maka laifiba sannan kana cigaba da yin yadda kake so,
ZATONKA ALLAH BAZAI KAMAKA BANE?
Ko kuma an tabbatar maka anan duniyan zakaci gabada rayuwa?
An sanar dakai cewa babu mutuwane kuma babu hisabi?
To wallahi kawu kaji tsoron Allah ka tuba abisa sab'onsa da kake, kajima da alhakin rayukan da
kayi ta kashewa na d'aruruwan mutane don nima kaina naga sama da ashirin Allah ne kadai
yasan iya yawansu dan haka nake baka shawara da kaji tsoron Allah"
Tafi kawun ya somayi yana takowa gabansu asuffar dayake batareda ya koma asalin sufarsaba,
duk da irin fad'uwan da gabanta ya tsananta yi hakan bai hanata tacigaba da gaya masa
gaskiyan dayake fitowa daga k'asan zuciyantaba.
"In fad'a miki gaskiua Fatima"ya fad'a