Showing 15001 words to 18000 words out of 65710 words
Chapter 6 - ZATO NE (1 TO End) BOOK COMPLETE By Maman Islam.pdf
da gudu, ganin yadda tazage iya k'arfinta tana falla gudu abin saida ya
bashi dariya, aransa yace yarinyar nan tafara koyan rashin kunya wajen su Hauwa'u zanyi
maganinkine, kayan ya kwashe ya mayar bedroom d'inshi kafin ya shige bath room.
Da yamma suka shirya Amma ta aike su gidan wata aminiyar ta inna shatu, Fatima tace "Amma
kibamu aron mukullin motarki muje da kanmu dan Allah"
Amma tace "jimin 'ya da k'arfin Hali ke da kike bak'uwa agarin kuma ki tambaya kiji ko Meema
da tasan gari bana bari tafita ita kad'ai"
Nacin da takafane yasa Amma ta bata mukullin tareda gargad'arta akan ta kula tayi tuk'i cikin
nutsuwa.
Ai da gudu Fatima,tayi bangaren Mammy tana kwala kiran meema meema wace ta gama
shirinta itama tafito tana taku d'ai d'ai dakagansu kaga 'yan mata masu aji gaji da gayu sannan
sam kud'in iyayensu baisaka su girman kai ba.
Abakin falon suka gabza karo dukansu saida suka kai k'asa meema ta dallamata harara tace "ji
dalla zata fasamin kai ke komai bazakiyishi da nutsuwa" ta fad'a tana shafa inda sukayi gwaran.
Itama hararanta tayi tace "ai garin murnan infad'a miki Amma tabada mukullinne mukayi
gwaren"
Meema zaro ido tace "haba da gaske?"
D'ago mata mukullan tayi batareda tace mata komiba, wani tsalle meema tayi ta dira gaban
Fatima suka tafa, suna murnan samun damar fita sukad'ai batare da driver ko wani daga cikin
yayyennasuba.
Da sauri meena taja hannun Fatima,tace "kinga zo mutafi kafin mammy taganmu tunda dama
Amma ta fad'a mata zata aikemu, dan muddun taga key d'innan wallahi k'wacewa zatayi tasa
driver ya kaimu.
Ai da gudu suka fita suka shige rantsatsiyar motar Amma ta miliyoyin kud'ad'e Fatima ta figa da
gudu, dan da meema tave tabata tuk'in cewa tayi tabari adawowa sai ta kawosu gidan.
Sanda mai gadi ya bud'e musu get suka fita suna shan kwana motar Abdul majid yana danno
tasa hancin motar dake glass d'in mai duhune babu damar ganin na ciki saida naciki yaga
nawaje.
Shima baisan su waye acikiba a tunaninsa Amma ce zataje unguwa shiyasa ya wuce ciki
abinsa.
Yayin da meema da Fatima suka kalli juna suka tafa suka kwashe da dariya Fatima tace "
hummmm yaya kenan ai inkasan wata baka san wataba.
Hankali kwance sukaje gidan inna shatu bayan sun gaisa suka fad'a mata sak'on Amma tasa
mai aikinta takawo musu ruwa da lemo suka d'an tab'a hira.
Sannan sukayi mata sallama, tace "kubari driver ya maidaku sukace ai da akwai mota a
hannunsu nan ta basu turare da hijabai irin na saudiyyannan.
Bayan sun bar gidan inna Shatu kai tsaye gidan watak'awar meema sukaje Maryam Aminu.
Sanda suka shiga maman Maryam,suka,samu afalon ita da yayan Maryam d'in mai
suna,Muktar.
Maman ce ta amsa sallamar da sukayi suka sami waje suka zaune mama tanayiwa Meema
tsiyar wai batason zumunci.
Meema tace "wallahi ba haka bane mama tunda yaya Abdul ya dawo kowa yashiga taitayinsa
agidan ya kasa ya tsare ya hana kowa sakat"
Yaya muktar yayan Maryam wanda sai yanzu yayi magana tun zuwansu yace "ai gwara haka
kawai asaki yara sakaka babu kwab'a babu harara ni ya burgeni wallahi"
Yak'are maganarsa idanunsa na kan Fatima wace tun shihowarsu yakafeta da idanu kamar
wani maye suk inda ta juya saitaji idanunsa na yawo ajikinta shiyasa taji duk zaman ya
gundireta.
Meema tace "wai' ina mutuniyarne mama banji duriyaryaba?"
Mama tace "nan mak'otanmufa na turata takaima mara lafiya abinci kinga taje tayi zamanta"
Mama tana rufe baki Maryam ta shigo falon da sallamarta, gaba d'aya suka amsa, tabisu da
kallo dukansu idanunta yafara sauka kan meema ta daka wani uban,tsalle cikin ihun murna ta
ruk'unk'umeta tana fad'in
"K'awata dama kina,suniyar gaba d'aya kin b'uya abinki dama gashi ba wani damunki zumunci
yayiba mune,sarkin naci muka gaji muka daina"
Murmushi meema tayi tace "ai kema kin sani basai namiki k'arin bayaniba"
Maryam tace "wai kina nufin yaya Abdul majid bai fara aiki da gemanyn ba?"
Tace "Daddy ne ya hanashi wai bai yarda yayi nisa dashiba, aikinma dan ya nuna yanasone
Amma daddy yafison ya zauna tareda shi a companynsa"
Maryam tace" Allah ya taimaka tashi muje d'akina in nuna miki wani abu, da sauri Fayima ta
rigasu mik'ewa dan dama gaba d'aya atakure take saboda mayataccen kallon da Muktar yake
binta daahi.
Abdul majid kuwa yana shiga gidan da motarsa ya hango sa'idu drivern Amma aransa yace yau
kenan Amma an tuna baya da kanta taja,motar kenan.
Direct b'angaren Amma ya nufa dan yasan bazai rasa wani d'an abin tab'awa ba tunda bata
rabo da kayan motsa baki.
Ga mamakin sa Amma na zaune saman doguwar kujera da kwqnon shan fura tana shan
kayanta, da baki asake ya k'arasa shiga cikin falon ywna kwllon Amma yace.
"Amma waye naga yafita a motarki yanzu shigowana Amma ta d'an dubeshi tace tace "ban
saniba uba na ka wani shigomin babu sallama zakayi min tambayar rainin hankali"
"Yi hak'uri Amma nayi tunanin nayine, ya fad'a tareda komawa yayi sallamar ya shigo Amma ta
amsa tareda mik'a masa kwanon furar datake sha, ya amsa yana kallonta, tunma kafin yakuma
yi mata wata tambayar tace "Fatima ne da meema na aikesu gidan Shatu"
Wani irin kallo Abdul maji ya dingabin Amma dashi wacce tunda tayi masa bayanin ta d'auke
kansa daga gareshi, yace "yanzu Amma fisabilillahi wannan mahaukatan yaran kikabawa mota
suka fita dashi?"
Wani banzan kallo Amma ta watsa masa kafin tace "ina katin shaidar da ka amso musu ?"
Ta fad'a tana mik'a masa hannu alamun yabata, ransa ne yab'a ya mik'e yana fad'in "gaskiya ni
ba a kyautamin ba da za aba yara tuk'i yqran da kansu yake rawa suje suja mana wata fitinar"
Amma tace "aniyarka ta bika mai bak'in baki babu abinda zai faru sai alkhairi kuma babu abinda
zai samu jikokina kuma babu ruwanka da harkansu ehe"
Shidai kam a zuciye ya juya ya fita falon Amma tayi tsaki tace "aikin banza mutum ka d'auki
zafin rai da rana tsaka ya d'orawa kansa" ta maida hankalinta kan akwatin tv tana ta mita.
Shiko Abdul majid kai tsaye gidan inna Shatu yaje, nan gwaggo shatu ta tabbatar masa da ai
sun tafi, kenan yawonsu suka tafi, lallaima yarannan zan koya musu hankali haka yai ta zagaye
har yagaji ya koma gida.
Yana zaune wajen mai gadi yana jiran yaga ita inda zai b'ullo har aka kira sallar magrib babu
alamarsu sukaje masallaci suka dawo.
Suko su Fatima basu tashi sanin lokaci yajaba saida sukaji kiran sallar magrib, take kuma ido
ya raina fata suka mik'e a gigice suna salati da salallami.
Da k'yar Maryam tasamu sukayi sallah sannan suka kamo hanyar gida.
Abakin get suka tadda Abdul majid yana waya bak'aramin faduwa gabansu yai da ganinsaba
adake Fatima ta danna hon mai gadi ya bud'e yanai musu sannu da zuwa suka shige cikin sauri
Fatima ta tsaida motar ta fito a guje tayi b'angaren Amma tunma kafin ya shigo dan rasan dole
ransa zai b'aci tunda ya kafa musu dokar fita da mota su kad'ai.
Amma na saman abin sallah da carbi,a hannunta tana ja.
Dakai ta amsa sannun da suke mata sunsan intana lazumi bazata yi musu maganaba dan haka
suka,ajiye mata sak'on. Harda wanda innan tabasu da kayan kwalliyar da maman maryam ta
basu duk nan suka bar mata, sukayi bangarensu jin ana,kiran sallar isha.
Tana murd'a kofar falon suka four eyes dashi take dabara ta fad'o mata kawai sai ta d'an
durk'ushe abakin k'ofar tayi sak.
Shi kuma ganin haka ya buga mata wata uwar tsawa yace "bazaki k'arasoba 'yan banzan yara
marasa kunya ku kun raina mutane ko?"
.
Itako duk da cewa ba k'aramin girgizata tsawar da yamata tayiba amma hakan baisa tayi ko
gezauba ammafa zuciyarta wani irin bugu take na tsoro haka kawai mutum ya koyi masifa k'arfi
da yaji.
Shi kuwa ganin haka ya mik'e a fusace yayi kanta tunkafin ya k'araso jikinta ya kama wani irin
rawa da ta tuna inya damk'eta bazai mata da sauk'iba yasa yana zuwa wajen ta ta fad'i tana
wata irin jijjiga.
Ganin haka yasashi k'arasowa wajen da gudu tareda kwalla mata kira da k'arfi Fatimaaaaaaaa
K'aransane yasa Ummi dake d'akinta idar da sallar ta kenan ta fito da sauri ganin Fatima ajikin
sa asank'ame yayinda shi kuma yake ta maimaita kalmar innalillahi raji un .
Take gaban ummi yayi mummunan fad'uwa musamman da ta tuna mafarkin datayi jiya ga kuma
Abdul ga Fatima ita innalillahi wainna ilahi raji un ta firta da k'arfin gaske wanda yasa Abdul
d'agowa da k'arfi yana kallon yadda jikin ummin yake wani irin rawa.
Fatima kuwa jin muryan umminta cikin wani hali saura k'iris ta bud'e idonta sanin me hakan zai
haifarne yasa tafasa bud'ewar amma take awajen takama wata irin jijjiga.
Muje zuwa wllh daurewa kawai nayi nayi muku wannan saboda girman alk'awari
Taku maman islam
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
ZATO NE
NA
HASSNA ABDUL AZIZ YAKASAI
WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
DAGA MARUBUCIYAR
ABINDA YAKE RAINA
WAYYO RAYUWATA
Page 9
................a rud'e Abdul yake jijjiga Fatima yana tofa mata addi'a, da sauri Ummi ta k'araso tana
jijjiga 'yar tata wacce zuwa lokacin ta daina jijjigar tayi lub' ajikin Abdul.
Dubansa Ummi tayi tace "Abdul d'auketa kakai min ita d'akina" tattare hannun rigarsa yayi ya
sunkuce ta yai d'akin Ummi da ita,
Saman gadon ya kwantar da ita ta d'an bud'e idonta taga yadda yai wani wujiga wujiga dashi
gaba d'ayansa a rud'e yake shi tsoronsa d'aya kar wani abu yasami Fatiman.
Juyawa yayi da niyyan fita Fatima ta bud'e idonta tarwai tana kallonsa tana sakin wani
kyakyawan murmushi, aranta tace maganin bak'in ran da ka koyo kenan mutum ya wani koyi
wulak'anci.
Alamu yaji ajikinsa ana kallonsa ya juyo da nufin ganin ko itace ta farko, yana juyowa Fatima ta
saki wani irin mummuna ihu wanda yai daidai da shigowar Ummi atare suka nufi Fatiman da
gudu, ihu take tana fad'in "na shiga uku ummi zasu kasheni rayuwana suke nema ummi karki
bari yatab'ani ummi hannunsa na macijine ki taimakamin ummi dan Allah" wani irin gigitaccen
ihu tasaki lokacin da Abdul ya k'araso asukwane yakai hannunsa jikinta.
Take ta sandare awajen sai kuma numfashinta yad'auke amugun firgice ummi da Abdul suka
kalli juna jikin Ummi na wata irin rawa tace "innalillahi,wainna ilaihi raji un ni Ummusalam na
shiga uku karda abinda naganine yake shirin faruwa kallonta Abdul majid yake jikinsa yana
tsuma zuciyarsa na wani irin razanannen bugu ya dubi ummi yace "menene yake shirin faruwa,
me kika gani, kiyi fad'amin dan Allah ummi"
Ya fad'a jikinsa na rawa kallonsa kawai Ummi take idanunta yana zubda wasu irin zafafan
hawaye yayin da itama jikinta yake wata irin rawa bugun zuciyarta kuwa har ya zarta kima.
"Abdul majid matuk'ar kusancinka da Fatima yacigaba da faruwa to babu shakka zasu kashe
Fatima sun tabbatar min da haka wanda da farko na d'auka cik8n baccine suke fad'amin hakan
amma sai na fahimci ido rufe suke fad'amin hakan, ma'ana koda babaccinake ba matuk'ar zan
rufe idanuna to zan dinga jin maganganunsu kuma acikin muryoyin yabbas kamar akwai wadda
na sani saidai bansan a inaba kuma yaushe? kuma da wane lokaci? nida ba mazauniyar
k'asarba wannan shine abinda ya shigemin duhu Abdul majid me akayi musu suke mana
wannan rashin mutuncin da zaluncin?"
Ta k'arasa maganarta tareda fashewa da wani irin matsanancin kuka, Abbi dake tsaye abakin
k'ofar yagama sauraran komai ya k'araso cik8n nutsuwarsa da kalama da kwarjini irin na
malaman addini, batareda ya kalli kod'aya daga cikinsuba ya k'arasa kusa da Fatima ya d'agota
ya dafa goshinta ya tofa mata sannan yasa ummi da har lokacin bata daina kukaba kuma jikinta
bai bar rawaba.
Yace "kawomin ruwa a kofi" batareda tace komaiba ta juya takawo masa ruwan ta koma gefe
tana kallonsa yana tofa addu a aciki sannan ya soma guntsar ruwan abakinsa yana fesa mata
saida yayi haka har sau uku, sannan ya tsiyaya hannunsa yana shafa mata a fuska shima sau
uku.
Wata irin ajiyar zuciya ta saukebsannan naga tayi mik'a gamida salati sai kuma ta runtse
idanunta da mugun k'arfi a hankali naga bakinta yana motsawa, sai kuma naga taware idonta
tarwai akan Abdul majid, da sauri Abbi yace "kul karki kuskura kinji ko dama irin rayuwar da
kukeyi a gidan kenan aka gagara gayamin? Dama a gidana za ayi irin wannan shed'ancin Ummu Ammar kirufemin?"
Ita dai ummi har lokacin bata daina kukan da takeba kuka sosai takeyi ya d'an dubeta kad'an
yace "ki d'an fita zanyi magana dasu kuma ki daina kukannan haka dan yanzu kika farashi
domin ina,shirin,aurar da 'yarki ga d'ana Abdul majid"
Wata irin juyowa ummi tayi ta k'ure Abbi da ido takasa ko k'ibtawa yayin da hankalinta yayi
mugun tashi zuciyarta ya tsinke gabanta yake wata irin fad'uwa, rawa leb'enta yana wata irin
rawa, saidai takasa cewa komai sai uban tsuma da jikinta yakeyi tafita daga d'akin da gudu.
Shiko Abdul majid wata irin zabura yayi kafin yace "Abbi banasonta dan Allah Abbi karkace
zaka had'amu aure da Fatima kallon k'anwa nake mata Abbi bantab'a jin sonta arainaba"
Wani murmushi Abbi yasaki kafin ya dafa kafad'arsa yace "malam Abdul kenan ba shawartarka
nakeba kuma ba yardarka nake nemaba kawai dai amatsayina na wanda ya isa na yanke
wannan hukuncin"
"Abbi akwai maganar Yusra fa kuma har sun gama magana da Abban ta da daddy"
Abbi yace "kai mijin mace hud'une dan haka bayan yusra zaka iya k'aro biyu duk zan had'a na
d'aura muku aure jeka zan gana da amaryar taka" yafad'a cikin sigar zolaya.
Fatima ya kalla cik8n kwantar da murya yace "ke nasan bazaki k'i abinda nazo dashiba ko
Fatimana?"
Ya fad'a cikin sigar tambaya.
Cikin wata irin kad'uwa Fatima tace"wallahi Abbi bana sonsa na tsaneshi Abbi banji araina zan
iya sonsaba bayan son 'yan uwan taka san Allah Abbi kamin rai Abbi karkayi wannan had'in"
Zama Abbi yayi gefen gadon sannan ya d'an dafa kanta ya girgiza yace "Fatima kece zan
aurawa Abdul majid ba waniba kumank8sa aranki idan an kashekine kema kinyi shihada kamar
sauran sannan, kuma idan akace kema da kike 'yar uwarsa kin guheshi wa kike tunanin zai
iya?"
"To abinda nakeso kisa aranki Fatima idan kinga baki auri Abdul ba to ki k'addara bakya
numfashi dan haka Fatima daga yau ki fara lissafa nan da kwana talatin zan d'aura aurenki da
d'an uwanki Abdul majid dan haka za'a had'a aurenki dana ita yarinyar dayake magana dan
haka ki fara shiri tun yanzun.
Wata irin zabura Fatima tayi ta mik'e tsaye tace "innalillahi wainna ilaihi raji un Abbi ka kasheni
wallahi Abba idan ka auramin yaya Abdul mutuwa zanyi" sai dai ki mutun Fatima amma aurenki
da Abdul majid babu fashi daga haka ya fice ad'akin.
Afalo yasami ummi tayi wani wujiga wujiga idanun nan nata yayi wani irin ja tsabar tashin
hankalin datake ciki.
Batare da yace komaiba ya kama hannunta yajata d'akinsa har lokacin hawayenta bai bar
zubaba, zaunar da ita saman doguwar kujera, sannan ya zauna a kusa da ita, kwantar da kanta
tayi saman kafad'arsa tace "ya habibi baka sami labarin abinda yake faruwa da Abdul majid
bane?"
Murmushi yayi yace"na sani, nasani ummu salma akwai dalilina nayin wannan had'in kuma
inada manufata kisa aranki ummu Ammar duk wanda kikaga ya mutu lokacinshi ne yayi dan
babu wanda zai tsallake iya kwanakin da ubangiji ya k'addara masa arayuwarsa dan haka k8sa
aranki idan har Fatima ta rasa ranta adalilin auren Abdul majid to ki tabbata lokacinta ne yayi
dan haka kiyiwa 'yarki addu'a Allah ya zab'a mata mafi alkhairi".
Sanin halinsa na kafewa akan magana d'ayane yasa ummi bata k'ara cewa komaiba sai ma
d'aki data tashi ta shige wajen Fatima, Abbi ya girgiza kai kawai yana murmushi.
"Alhaji wai me yafarune naji kuna hayaniya da alhaji marwan?" cikin b'acin alhaji yace "kedai
k'yaleshi kawai hajiya, wai tsinannen mutumin nan dashifa muke jajanta matsalar yaronnan
Abdul, kuma dashi muke gantalin neman magani k'auye k'auye amma shine saboda alhaji
sambo ya zugashi yakemin wannan cin mutuncin"
Ajiyan zuciya mammy tayi tace "to aishikenan alhaji basai a k'yaleshiba tunda dama shi yace
yaji ya gani yanzun kuma yace ya janye kacigaba da yi masa addu'a da neman magani kamar
yadda nima make masa babu dare babu rana da izinin ubangiji asirin koma waye zai tonu"