Showing 6001 words to 9000 words out of 65710 words
Chapter 3 - ZATO NE (1 TO End) BOOK COMPLETE By Maman Islam.pdf
k'rin ga wata iska irin maijar k'asar nana take sukayi
saurin zuge glasan motar Fatima ta gangara gefen hanya dan yadda garin yayi duhu babu
damar tafiya dole su tsaya garin ya washe dan ita ba damuwarta bane tafi acikin ruwa.
Jingina tayi ajikin kujeran tana maida numfashi k'ura mata ido yayi yana kallonta, sosai yakejin
Fatima ajininsa.
Ruwane ya tsuge da gudun gaske ta rik'a kallon yadda ruwan yake gudu ta gilas yayinda shi
kuma ya gyara zamansa yana kallonta tareda d'ora duka hannayensa akan fuskarsa.
Juyowa tayi tanayi masa magana bayan ruwan ya lafa, amma baisan tanayiba sai da taja dogon
hancinsa, sannan yayi firgi git kamar wanda yatashi abacci
D'an had'e rai tayi tace "wallahi yaya ka koyi wani irin kallon k'urillah wanda a da sam ba halinka
bane"
Murmushi yayi ya d'an jata jikinsa ya mannawa goshinta kiss batare da yace komai ba ya gyara
zamansa yana kallon hanya.
Jan motar tayi cikin sauri tana fad'in "bana son muyi dare badanma ruwannan ba aida tuni mun
kusa" gyara belt d'inta tayi tafigi motar, shikam kallonta yake yana mamakin yadda take gudu da
motar ko tsoro bataji.
Sai da sukayi tafiya mai d'an nisa suna ta ratsa gonaki ruwan yadad'a tsugewa dan dole ta rage
gudun, amma bata dakataba saboda yanzun garin a washe yake babu duhun.
Haka sukaci gabada tafiya har yanayin ya d'an sauya domin ruwan da akayi yasa garin yad'anyi
duhu kad'an, awannan yanayinne Fatima taga wasu abubuwa sunfara giftawa ta gabanta da
mugun gudu, shit saitaga abu ya wuce da gudu sai ta ganshi d'an mik'il.
Haka abubuwan suka cigaba da giftawa a idonta ta kalli Abdul majid da nufinyi masa magana
taga shi idanunsama a rufe suke ya d'ora tafukansa asaman fuskarsa.
juyowan da zatayi domin cigaba da tuk'inta ganin Abdul majid yana bacci sukayi ido hud'u da
wani k'atoton zaki mai girman gaske wanda ko alabari bata tab'a ganin irinsaba ya taho da wani
irin mahaukacin gudu.
Jitai wani irin abu ya tsarga mata tundaga tsakiyar kanta har zuwa tafin k'afarta yayinda wani
irin tsoro ya lullub'e ta take ta runtse idonta tana addu'a tana bud'e idon tasaki firgitaccen k'aran
dayasa Abdul majid bud'e idonsa da sauri dan ganin tasaki sitiyarin motar yafara juyawa dasu.
Da wani irin zafin nama ya haye kan cinyarta batareda yasan yayi hakanba yasamu ya tsai da
motar da k'yar yana maida numfashin tsoro.
Muje zuwa
Taku maman islam
[8/10, 9:28 PM] MAMAN ISLAM: *مسب الله نمحرلا ميحرلا *
*☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️*
FCWA
*Home of qualities and trusted writers of the nation*
https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?ty
pe=3&source=45&refid=17
_________________________
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
DAGA MARUBUCIYAR
.ABINDA YAKE RAINA
WAYYO RAYUWATA
Page 6
......................kallon yadda ta ta kure kanta yake bayan ya koma wajen zamansa.
Wani irin rawa jikinta ya kamayi, har lokacin kuma idanunta suna kulle katamau,
Dafa kafad'arta yayi wanda yasa ta zabura dasauri ta bud'e a idon azaton ta zakinne ya k'arasa
inda take, ilai kuwa tana kallon gefenta taga zakin atsaye kyam yana kallonta da wani irin jan
ido.
Wani irin gigitaccen ihu tasaka tareda furta duk addu 'ar dayazo bakinta tunda taje arayuwarta
bata tab'a ganin kalar wannan zakinba me wasu irin idanu masu abin tsoro, har wuta ta hango
yanaci acikin idanun nasa.
Duk jikinta babu inda baya rawa saboda ba k'aramin firgita tayiba tunda take bata tab'a ganin
zaki yana tafiya da k'afa biyu kamar mutum ba sai yau.
Jawo ta Abdul majid yayi a tsorace ganin yadda take had'a uban gumi ga jikinta da har ya d'auki
zafin zazzab'i tsabar firgicin da ta shiga.
Kwantar da kanta tayi akan k'irjinsa har lokacin jikinta bai bar rawaba a hankali ya kai bakinsa
kunnenta yace "haba Fatima nifa banga zakin da kike ta magana akaiba duk kinbi kin rud'a
kanki nima kin rud'ani ki mutsu mana kiyi addu'a babu abinda zai sameki in sha Allah".
A tsorace ta kuma bud'e idonta still yananan kuma idanunsa akanta ko k'ibtawa bayayi, wannan
karon bata rufe idontaba kuma batayi ihunba.
Duk da bugawar da zuciyarta yakeyi har ya zarta k'a'ida fuskar Abdul majid ta kamo tajuyo
dashi ta inda zakin yake tsaye cikin rawar murya tace "ka ganshifa kallon tuhuma yakemin
me,na masa tafad'a tareda fashewa da wani irin kuka.
Kallon inda take nuna masan yayi shi kam baiga abinda take nuna masanba,yace"nifa babu
abinda nagani Fatima wallahi banga komaiba"
"Bakaga komaiba?
Bakagafa komaba kace,
Ta kuma maimaitawa tareda fashewa da wani kukan taba fad'in na shiga uku na lalace" tafad'a
gaba d'aya tagigice fuskarta yayi jajur saboda tsoro da kukan da takeyi.
Ganin haka yace "dawo front seet ki zauna ni najamu kinga magrib ya kawo kai"
Mak'e kafad'a tayi tace "wallahi yaya saida kayi tuk'in nan a haka babu inda zan d'ara daganan
salon na koma gefe yaji dad'in zuro hannu yayi loma d'aya dani"
Kallon yanda ta k'adandane shi yayi sai kuma ya sauke nannuyan ajiyar zuciya dole sai a hakan
yacigaba dajan motar tana jikinsa.
Ikon Allah ne kawai yakaisu bajoga, domin yadda motansu yake zabga uban gudu haka take
ganin zakinna jere dasu dab da dab babu ta inda suka gotashi.
Saida suka sha kwanar gidan gwaggo Hafsatu tanemeshi tarasa kamar walk'iya, wata irin ajiyar
zuciya tasauke tareda lumshe idonta ta bud'esu akan Abdul majid dataji ya dubgure mata kai
yace "matsoraciya kawai dankinganki a gonaki shine duk kika bi kika tsure kike kiran zaki,
banda abinki Fatima zakine zai ganmu yabarmu mu wuce lafiya kuma mema zai kawo zaki
gona?"
Still ajiyan zuciyar ta kuma sauke sannan tace "hum yayana kenan bazaka ganeba wallahi zaki
nagani da idona kuma yanzun da ace zaka kain asbiti babu abinda zai hana aga jinina yayi
mugun hawa"
Dari ya kuma sannan yace "sai ki d'agani ko ai munzo gidan"
Sauka tayi ajikinsa ta fito daga motar shima ya fito suka jera suka shiga gidan.
Gwaggo Hafsatu na bakin famfo tana d'aura alwalan sallan magrib da ake ta kira a kowane
masallaci dan lokacinta ya shiga tagansu.
Take farin ciki ya kamata na ganin d'iyar ka'ninta da kuma d'an yayarta tayi musu sannu da
zuwa yayin da Abdul yayi alwalar ya fice masallaci ita kuma Fatima tayi tabi gwaggo Hafsatu
wadda har ta tayar da tata itama ta kabbara sallah.
Abdul majid bai dawoba sai bayan sallar isha wanda har su sun idar da tasu suna gaisawa,
suna ta hira da gwaggo da Fatima.
Har k'asa Abdul yagaida gwaggo ta amsa cikin sakin Fuska tana tambayarsa mutanen gidan
Yace "lafiyansu k'alau gwaggo duk suna gaida ku"
" muna amsawa "tace daga haka ta mik'e ta fice dan kawo musu abinci.
Binta Abdul yayi da kallo har kullum yana mutuk'ar tausayawa rayuwar gwaggo haihuwar ta
d'aya jal aduniya kuma ta sanadinsa ta rasata.
Wasu kwalla yaji sun kawo idonsa lokacin da ya tuna halinda yake ciki tunda akayi maganar
aurensa da Yusra bashi da kwanciyar hankali har kullum damuwansa shin kasheta zasuyi itama
ko kuma saceta zasuyi kamar yadda suke sauya abubuwan?
Wani karon su sace wani bin kuma akashe.
Bayan sun gama cin abincinne Fatima tace "gwaggo na gaji inajin bacci zanje na kwanta"
Abdul ya dubeta yace "wuri haka rahuwa kawai"
Hararan wasa ta galla masa batareda tace komaiba ta wuce tabarshi anan suna ci gaba da
hiransu da gwaggo.
K'afe d'ayan dare tafarka awani irin zabure tana addu'a addu'abud'e idon dazatayi kawai taga
zakinnan gefanta atsaye ya tsareta da idanunsa da suke ci da wuta.
Wani irin razanannen ihu tasaki take fitsari ya sub'uce mata.
A tare Abdul majid da gwaggo Hafsatu suka shigo d'akin jin ihunta da sauri Abdulbya rik'eta
yana tambayar "lafiya?"
Yayin da gwaggo ta hauyi mata tofi ganin irin zaburan datakeyi ita kuma kuka take tana fad'in
"shikenan kasheni zaiyi yaya ya biyoni nanma.
Sam Abdul ya manta da abinda ya faru a hanya yace "wayevyabiyoki zai kasheki?"
Ya fad'a cikin wani irin tsoro da tashin hankali take jikinsa ya hau rawa yajata jikinsa ya
k'ank'ame yace "ki kwantar da hankalinki Fatima babu abinda zai sameki da yardan ubangiji,
Kuma ko wane tsinann ne ai yazama matsoraci tunda ya kasa tunkarana gaba da gaba yake
bin dunduniyata.
Sosai ya rik'a bala'i yana masifa cikin wani irin mummunan b'acin rai, yayin da gwaggo tayita
kukan tunawa da tilon 'yarta da kuma tausayin galin da d'an yayan nata yake.
Fatima kuwa bata runtsaba aranar da ta kwanta zakinnan zai zungureta yanayi mata kallon
gargad'i.
Dole sai ad'akin suka kwana dukansu Abdul da gwaggon dan ma Allah yasa mijinta mai tafiyae
tafiye ne.
Garin Allah kuwa yana wayewa ko karyawa Fatima bata bari sunyiba tasa kuka tace ita ya mai
da ita gida, lallashin duniya tace itafa batasan zance ba dan dole,sukayi gwaggo sallama suka
kamo hanyar gida.
Plss manage
Daga
Maman islam
[8/11, 7:49 PM] MAMAN ISLAM: *مسب الله نمحرلا ميحرلا *
*☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️*
FCWA
*Home of qualities and trusted writers of the nation*
https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?ty
pe=3&source=45&refid=17
_________________________
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Daga marubuciyar
ABINDA YAKE RAINA
WAYYO RAYUWATA
Page 7
......................kusan abinda yafaru a hanyar zuwan su shine yasake faruwa da k'yar Abdul majid
yakawo kansa gida.
Cikin kwana d'ayannan da sukayi har Fatima tayi wata irin rama tayi wujiga wujiga da ita, abin
tausayi duk ta wani firgice.
Lokacin da suka isa gida ana kiran sallahr azhar Ummi tana kicin ta had'a abincin rana taga
giftawar Fatima da sauri.
Daganin yanayinta babu nutsuwa atattare da ita,da sauri Ummi tak'arasa abinda take tabi 'yar
tata, saidai sanda tashiga d'akinnata har ta tayar da sallah, dan haka itama ta juya dan gabatar
da tata sallar.
Ab'angaren Abdul ma yana shiga b'angarensa wanka yafarayi agaggauce sannan yayi alwala
ya wuce masallaci.
Yana dawowa daga masallaci direct wajen mammy ya wuce , suna dirning area ita da autarta
suna cin abinci.
Mammy tabi d'annata da kallo tana amsa sallamar dayayi memma tayi masa sannu da zuwa
tanafad'in "nidama nasan Fatima bazata iya sati guda abajoga yadai fad'ane kawai.
Kallonta Abdul yayi yana tambayar ta da ido, wai yaushe akayi hakan?
Memma tace sanda kuke shirin tafiya tace min ita tanason ku d'an kwana biyu acan bayan
tafiyar ku kuma naga message d'inta wai zata lallab'aka har kuyi sati"
Murmushi yasaki har saida kyawawan hak'oransa suka bayyana memma tasaki baki tana kallon
yayan nata wani mashahurin kyau yake yi aduk lokacin da zaiyi dariya.
Gaida mammy yayi yana dungure kan meema yace"duk kin d'aukemin hankali da d'an banzan
surutunki ko uwata ban gaisarba.
Dariya memma tayi kafin tace "wai ina Fatimanne yaua naganka kai kad'ai koda gaske ka
barota acan d'in?"
Itama mammy kallonsa take tajiran jin amsar da zaibata, "ban saniba suda kinga k'yaleni yunwa
nakeji mammy zubomin abincin dan Allah"
Mammy tace "bangane baka saniba inakabaromin yarinya?"
Ta masa tambayar tana tura masa flat d'in abincin data zubo masa, saida yayi bismillah yafara
cin abincin dan yunwa yakeji sosai Fatima bata bari sunyi karin kumalloba ta uzzura masa suka
taho.
Duban mammy yayi yace "tana fat d'insu dan ko kari bata bari munyiba tace ita gida zata tafi"
Nan kuma ya kwashe duk abinda yafaru a hanya ya fad'awa mammy, bak'aramin girgiza tayi
dajin wannan abinba tabbas duk ma wanda yake bin baya d'annata baizai denaba ya zama dole
ta fad'ima Abbu dan tasan tabbas zai iya bada taimakon daya kamata.
Abangaren Fatima,kuwa saida tayi sallah sannan tayi wanka,dake sanda ta shigo gidan anriga
da antada sallah.
Bayan ta shirya cikin wasu riga da sket 'ya kanti kalar blue mai duhu sunyiwa jjar fatarta kyau
sosai.
A falo tasami Umminta tana cin Abinci kusa da ummin ta zauna tagaida ita sannan taja abincin
yayinda ummin take tambayarta yanda ta barosu.
Tace "duk suna lafiya ummi tace agaidaku, ummi ta d'an k'ara kallon 'yar tata da kyau ganin
yadda ta zuk'e lokaci d'aya tace
"Ciwo kikayi ne adaren jiya naga kin zuk'e?"
Ajiyar zuciya Fatima tayi kafin ta dubi ummin da idanunta da har sun,ciko da kwalla take abinda
yafaru yafara dawo mata kamar yanzune abin yake faruwa babu 'yar b'oye b'oye tsakainta da
umminta take ta kwashe duk abinda faru ta fad'awa ummin, wanda itama ummin bak'aramin
girgizata abin yayiba karfa kuma wani abu yasami tilon 'yar tata dan tanada kusanci da Abdul
majid?
Ai kusancin su ba aure bane kuma ko Abdul majid yace yanasin Fatima,bazata tab'a amincewa
ba dan,abinda ta lura dashi duk wanda zai mu 'amalance shi koda da soyayyane sunan shi
gawa.
Wannan kenan
Ab'angaren mutuminnan kuwa tsaye yake gaban gunkiyar nan yau idanunta har ya wuce
rannan haka duk wani k'ofa najikinsa babu inda baya kwarar dajini.
D'ago wutar dakeci a idaninta tayi naga ta kalli mutumin wanda duk ranar datayi hakan mutum
ya b'ata mata rai kuma wannan kallon shima azaba ne dan mutum zaiji ajikinsa.
Jinai tana magana yau kuma da muryan jarirai tace "wayace kabita kanason lalatama aiki
bakasan cewa idan ubanta yasan kana bin ta sai ya kawo k'arshenkaba? dan mudai munriga da
munfi k'arfin duk wani mai shiri akanmu"
"Kar ka sake binta lokacin baiyiba idan lokacin yayi dakaina zan d'auko ta domin muna
buk'atarta dan gudanar da wani gagarun shiri amma,ba yanzuba da sauran lokaci
Daga haka ta rufe idanun tana hawayen jini,alamun tagama,bayaninta.
Gani nayi wata irin iska tayi watsi dashi bai fad'i a ko inaba sai bakin falon gidansa, wannan
shine hukuncin duk wanda ya sab'a umarninta
A sume yake tun bayan sa adda wannan aba ta watso shi bashi ya farkoba sai bayan da iskar
asbah ya hurashi.
Da sauri ya tashi yashige d'akinsa duk jikinsa babu inda baya masa ciwo bin matarsa yai da
kallo wadda bata san mai yake faruwa toilet ya shige yayi wanka da ruwa mai mugun zafi wai
ko zaiji dad'in jikin sannan ya d'auro alwala yazo yatashi matarsa sannan shi kuma ya wuce
masdalan [8/11, 8:40 PM] MAMAN ISLAM: *مسب الله نمحرلا ميحرلا *
*☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️*
FCWA
*Home of qualities and trusted writers of the nation*
https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?ty
pe=3&source=45&refid=17
_________________________
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Daga marubuciyar
ABINDA YAKE RAINA
WAYYO RAYUWATA
Page 7
......................kusan abinda yafaru a hanyar zuwan su shine yasake faruwa da k'yar Abdul majid
yakawo kansa gida.
Cikin kwana d'ayannan da sukayi har Fatima tayi wata irin rama tayi wujiga wujiga da ita, abin
tausayi duk ta wani firgice.
Lokacin da suka isa gida ana kiran sallahr azhar Ummi tana kicin ta had'a abincin rana taga
giftawar Fatima da sauri.
Daganin yanayinta babu nutsuwa atattare da ita,da sauri Ummi tak'arasa abinda take tabi 'yar
tata, saidai sanda tashiga d'akinnata har ta tayar da sallah, dan haka itama ta juya dan gabatar
da tata sallar.
Ab'angaren Abdul ma yana shiga b'angarensa wanka yafarayi agaggauce sannan yayi alwala
ya wuce masallaci.
Yana dawowa daga masallaci direct wajen mammy ya wuce , suna dirning area ita da autarta
suna cin abinci.
Mammy tabi d'annata da kallo tana amsa sallamar dayayi memma tayi masa sannu da zuwa
tanafad'in "nidama nasan Fatima bazata iya sati guda abajoga yadai fad'ane kawai.
Kallonta Abdul yayi yana tambayar ta da ido, wai yaushe akayi hakan?
Memma tace sanda kuke shirin tafiya tace min ita tanason ku d'an kwana biyu acan bayan
tafiyar ku kuma naga message d'inta wai zata lallab'aka har kuyi sati"
Murmushi yasaki har saida kyawawan hak'oransa suka bayyana memma tasaki baki tana kallon
yayan nata wani mashahurin kyau yake yi aduk lokacin da zaiyi dariya.
Gaida mammy yayi yana dungure kan meema yace"duk kin d'aukemin hankali da d'an banzan
surutunki ko uwata ban gaisarba.
Dariya memma tayi kafin tace "wai ina Fatimanne yaua naganka kai kad'ai koda gaske ka
barota acan d'in?"
Itama mammy kallonsa take tajiran jin amsar da zaibata, "ban saniba suda kinga k'yaleni yunwa
nakeji mammy zubomin abincin dan Allah"
Mammy tace "bangane baka saniba inakabaromin yarinya?"
Ta masa tambayar