Showing 24001 words to 27000 words out of 65710 words

Chapter 9 - ZATO NE (1 TO End) BOOK COMPLETE By Maman Islam.pdf

14 Apr 2025

5432

NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
DAGA MARUBUCIYAR
ABINDA YAKE RAINA
WAYYO RAYUWATA



Page 14

Koda ta bud'e idanunta da salati ta bud'e tana sambatu, sosai hankalin Abdulmajid yatashi
ransa inyayi dubu babu wanda bai tashiba bai san lokacin dayasoma zubda hawayen bak'in
cikiba.

Shikam yaga ta kansa sai kace akan danginsa aka fara kud'i duk abin anhana shi samun
nitsuwa da kwanciyar hankali dazaiga waye yake masa wannan masifar da da hannunsa zai
kasheshi.



Fatima tana bud'e ido ta ganshi a zaune kusa da ita tafad'a jikinshi ta k'ank'ameshi tafashe da
wani irin kuka, shiru yayi tareda dad'a janta cikin jikinshi zuciyarshi na masa wani irin rad'd'i shi
kansa dazai samu yayi kukan dayasami saukin wani damuwar.




Mammy ta dubi Daddy tace "alh, yakamata fa mutashi tsaye akan yaronnan kar ciwonsa kuma
yazo yatshi kuma mushiga uku"


Daddy ya dubeta cikin tsantsar damuwa yace "haka Amma tace min wai yazo tunda sassfe
dad'a figewa adare d'aya tak ni narasa yadda zanyi da wannan masifar wallahi hajiya duk
wanda na samu da hannu acikin wannan al'amarin bazan saurara masaba ko waye.




Mammy tace "wallahi algaji yadda ya shigo nima ba k'aramin tsoratani yayiba harfa kuka yayi
anan wajen" tafad'a tana nuna inda yatashin da hannunta.


A firgice daddy ya dubeta yace "kuka dai haj, shi Abdulmajid d'in?"

"Tusawa kake alh, yaronnan yana cikin damuwa sosai ni yanzu sonake duk wanda yake da
hannu acilin wannan tashin hankalin da muke ciki naganshi da idona dakaina zan d'auki mataki
akansa wallahi"



Daddy ya kalketa kawai batareda ya iya maganaba saboda gaba d'aya abin yafara fin k'arfinsa
har cid yasaka ab'oye a dinga bin bayan duk wani takun Abdulmajid da duk wani wanda yake
mu'a malanta amma babu wani labari.

Shin suwaye? me sukayi musu? me suke nema awajensu dazasu gigita rayuwarsu dana
yaronsu haka kawai?



Mik'ewa yai yafita batareda yacewa mammyn komaiba yayn data saki baki tabishi da kallon
mamaki.




"Ak'ilu zaka mutu zaka murufa akan wannan shed'aniyar yarinyar yawan binta dakake yawan
binta da kakevyawan azabar da wannan tsinannen uban nata yake ganamin domin babu wanda
yasani dabk'asar k'afarka yake amfani idan kuwa baka rabuda itaba dakaina zan tsotse jininka
na huta da bala'inka"


A mutuk'ar firgice alh, Ak'ilu yace "kiyi hakk'uri kimin rai bansan wannan kangararren mutunin ya
ganomuba amma na miki alk'awarin sai kinsha jinin Abubakar da 'yarsa"


Wata irin tsawa ta buga masa tace "jinin Abunakar ai gubane bazai tab'a shanyuwa agaremuba
saidai na 'yar tasa Fatima itama kuma bada k'aramin shiriba kabari tasamu ciki sai kafad'amin
da wannan raunin na mai ciki zamu ci galaban saceta muyi yadda muka ga dama da ita dan
haka kabar aikin kawai a hannunaaaaaa"kirib ta maida idanun ta rufe kamar kullum jini na
malala daga idanun kamar hawaye.



Shiko Alh, ak'ilu yabaro wajenne da k'udurin babu shegen da ya isa yasha jinin Abubakar da
'yarsa Fatima inba shiba dan haka ko za amutu wallahi babu wanda zai d'agawa k'afa akan jinin
Fatima da ubanta.






Tundaga wannan ranan babu wani abu daya kuma firgita Fatima domin tundaga lokacin bata
k'ara ganin wani abin tsoroba yayin da basuyi sanua wajen addu'a ba kullum zasu gudanar da
rayuwarsu mai kyau da tsabta sannan suzo su kimtsa kansu kuma sukama na filfili cikin

kwanaki bakwan da yaiwa Fatima har wani k'iba yayi saboda kulawan dayake samu daga
gareta.



Ranan da ya koma d'akin Yusra kuwa yaga iyayi da rawan kai dan ita ko irin d'an jan ajinnan irin
na amare babu ta dinga wani shige masa.


Yasha mamakin daya sameta a cikakkiyar budurwa yanda take rawar kannan saidai kuma
hakan yasanya kimarta mai girma a idonsa.




Haka suka cigaba da zama cikin kwanciyar hankali sai dai abinda yavlura dashi Yusra tana da
yawan k'orafi dakai k'ara abinda bai tab'a samu daga Fatimaba ko da wasa.



Watan su uku Yusra ta samu ciki mai azaban laulayi kullim babu lafiya tana kwance abinda yasa
Fatima ta d'auki dukan kulawarta ta maida kan Yuran duk abinda takeso jiki yana rawa Fatima
zata dafo mata.

Da farko ma da gayya zatace tana son abu idan tavkawo mata saitace bataji bane bashi taceba
kaza tace, haka baiwar Allahn zatayo abinda tace d'in ganin duk abinda tasata bata damuea
yasa ta watsar da komai suke zamansu lafiya.


Sosai hankalin Abdulmajid ya kwanta dan ganin yadda matannasa suka had'e kansu.


Zaune suke afalon k'asa yainda Yusra take zaune saman doguwar kujerar Fatima kuma tana
kai akwance kanta saman cinyar Yusra hira suke tanama Fatiman tsifar kai a haka haj. Kulu tayi
sallama da sauri Fatima ta mik'e tana mata sannu da zuwa, ta shiga kicin takawo mata ruwa da
lemo, tadurk'usa har k'asa ta gaida ita cikin sakin fuska ta amsa mata tareda tambayarta yadda
suke tace suna lafita daga haka ta mik'e ta haye sama tabasu waje su gana




Haj. Kulu wata irin macece mai jarababben son kud'I ita dai indai zata samu kud'I ko boka da
'yan bori bazata biba ganin yadda Abdulmajid yake sakar musu kud'in kamar baisan zafin

nemaba yasa sam bata wani damu da neman wani tenako wa Yusaran ba akan zannasu.




Sannan kuma Fatima bata da mugunta ko kad'an duk abinda Abdulmajid zaiwa Yusra bata da
damuwa tunda itama babu abinda ta nema tarasa hasalima indai maganar kud'ine batasan
adadin nawa take dasu ba domin duk sanda Haj. Kulu tasa Yisra ta rok'I wani abu awajensa to
itama sai yabata kamar yadda yabawa Yusran.



Iyatensuma hankalinsu yabkwanta sosai babu wani damuea ataredasu tunda sunga abin na
Abdulmajid yayi mugun sauk'I amma duk da haka Abbi da Amma basuyo sakacin addu 'a ba
saboda masu iya magana sunce mugu baida kama watak'ila kwanta bau'na sukayi musu.


Haka dai sukaci gabada rayuwa basu da wata matsala har cikin Yusra ya shiga wata na uku
alokacinne kuma al'amarin ya dawo wannan memakon Fatima kan Yusra suka dawo suke
matuk'ar firgitata.



Abin yafara ne wata rana Fatima na kicin tana musu d'an wake kamar yadda Yusran ta buk'ata
ita kuma tana kallin wani shirin film a arewa kawai, aka nuno wata k'atuwar 'yar tsana kaman
jariri atsaye kyam tanata rawa idanunta na zubar da wani irin abu mai kaurin gaske sosai Yusra
ta tsorsta ganintama kamar hannu take mik'o mata sai kawai ta mik'e ta isa gaban tv ta kai
hannu da niyyar shafa allom tvn kawai aka cafki wuyanta da mugun k'arfi take tasaki wani irin
razanannen ihu wanda yai sanadin fitowar Fatima da gudu dagavkicin





Taku maman islam
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*




��ZATO NE��
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM


Page 16

......................sosai gaban haj. Kulu yayi wata irin muguwar fad'uwa ta k'urawa 'yar tata ido ko
k'ibtawa takasayi.


Yayin da Yusran tacigaba dayi mata kallon tuhuma tanaci gaba da tsananta kukanta.



Sosai haj. Kulu 5aji zuciyarta yana bugawa da k'arfin gaske, tunaninta yadda zata dubi y'ar tata
tafad'a mata sana'ar mahaifinta ai wannan ba k'aramin abin kunya bane agaresu 'yarsu tasan
da yadda suka raineta suka girmar daita.


Ana cikin haka Alh. Sambo ya shigo kamar anjefoshi fakam fakam, turus yayi lokacin dayaga
Yusra zaune tana gurzar uban kuka take yaji zuciyarsa ya tsunke.


Me kuma yasameta take kuka haka kodai itama taga abinda yaganine kardai da gaske wannan
shed'aniyar aljanar so take tarabasa da gudan jininsa kwal aduniya.


"Ina bazai yiyuba wallahi"
Yafad'a da mugun k'arfi hankalinsa a mugun tashe, gaba d'aya suka juyo suka kafeshi da ido

wanda maganarsa nema yasa sukasan da zuwansa.



Cikin sauri Yusra ta taso ta rik'eshi tace"dan Allah Abba ka dubeni kadubi rayuwata ka fad'amin
abinda yafaru tsakaninka da wannan halittar datakemin barazana da rayuwata?"


Kallonta yake batareda ya fahimci abinda take cewaba, domin shi yanzu aduniya tunaninsa
yana kan abinda yakeson k'ullawa wannan banzar shed'aniyar da kuma d'an korenta duna
dolene yayi gagarumin shiri akansu.



"Wallahi Alh. Munzali bakaga komaiba indai kace wannan halin zakacigaba dayi kana tunanin
bansan duk abinda kakeyiba ne?
Duk tashin da kake cikin dare da ziyaran wajen tsafinka dakakeyi da kuma yaran mutane
dakake sawa ana satomaka kana amfani dasu wajen neman duniyarka duk akan idona
kakeyinsu kuma da sannu dubunka zata cika Allah baya zalunci kuma baya barin masu zalunci"


A mutuk'ar razane alh. Munzali yake duban haj. Munira kafin yace to wallahi tunda kika sake
kika tonomin sirrina taki ta k'are Munira saidai wata bakeba dan haka yanzun zanje na fad'awa
iyayenki cewa kin mutu a sakamakon ciwon cikin dana ce kina dashi wanda ni na k'irk'ireshi
saboda biyan buk'atar kaina sannan kuma abinda baki saniba Munira nine nayi amfani da
matata uwar yarana wajen neman duniyata kuma dukan yarana mata duk nina sulwantar dasu
ta hanyar tsafi kuma suna bani duk abinda nakeso,



Sannan asalin wanda na fara sadaukarwa sune iyayena da suka haifeni kinga danna sadaukar
da matar data sadaukar da rayuwarta akaina ai bakomai bane,


Yara biyu kawai yanzu suka ragemin d'aya na halak wanda na haifa ta hanyar aure d'ayar kuma
bata hanyar aure na sametaba kuma da matar aure kuma Allah ya jarabceni da tsantsar k'aunar
wannan shegiyar 'yar tawa wanda nakejin dana rasata gwanda na rasa Ammar jinin jikina,


Ina baki wannan amsoshinne na tambayoyin da kika daneni dasu tunda jimawa amatsayin
sallamarki da duniya Muniraaaaaaa"

daga haka taji an kwad'a mata wani abu mai k'arfin gaske akanta take ta yanke jiki ta fad'i
awajen tana kallo alh. Munzali yafashe da kukab munafurci ya kira iyayenta yace musu tayi
mutuwar farat d'aya sakamakon ciwon cikin daya turnuketa daren jiya wannan kenan.




"Abba kaifa nake sauraro ka kafeni da ido da gaskene kai marsafine me shan jinin mutane
dama Abba akan haram ka ginani? Abba me yasa kuka kasa bani ilimin addini? amma na boko
nayi dgree nayi masters me yasa meyasa tafad'a tareda fashewa da matsanancin kuka.


Sosai hankalin iyayennata yakai k'ololuwa wajen tashi duk duniya idan akwai abinda yake d'aga
musu hankali bai wuce damuwar tilon 'yarsu Yusra dan haka aka rasa mai bata ganshashiyar
amsa atsakanin iyayennata duk sai kame kame har zuwa lokacin da Abdulmajid da Fatima
sukazo daukanta.

Kafin lokacin kuwa tayi wani irin wujiga wujiga da ita tayi fayau ta d'ashe saboda damuwar
datake fama da ita.


Ko motama sai faman lallashinta suke domin ta masifar d'aga hankalinta.



Suna zuwa gida tana bud'e d'akin taganta zaune gefen gadon ta d'ora kafarta d'aya akan d'ayar
tana lila da k'arfi Yusra tace innalillahi wainna ilaihi raji un, take taji wani abu yana bin jikinta
koda ta duba jinine wani irin mummunan fad'uwa taji gabanta yayi musamman da ta tuna halin
da Abdul da Fatima zasu shiga akan wannan babban asaran da suka tabka.

D'agon kan da zatayi taganta tana lasan jinin dayakevin k'afarta kafin ta d'ago tace mata "naji
shi'awar d'an tayine sai na tuna ashefa inadake gashi kuma yana da dad'i zan d'aga miki k'afa ki
k'ara samar min da wani babyn na lashe kafin kema na lamusheki"


Daga haka ta busa mata wata iska mai mugun d'umi wanda yai sanadin sumewarta awajen


Yayin da ihun salatin datayi yayi sanadin haurowan su Fatima saman amugun firgice Fatima
tabi jinin dayake malala da kallo yayi take ta fashe da wani irin kuka

Shiko Abdul yana ganin yadda jini yake gudu ajikin Fatima ya tabbatar yayi missing babynsa
take idanunsa suka canja kala sukayi wani irin ja





Muje zuwa
Takuce maman islam
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*




��ZATO NE ��
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
DAGA MARUBUCIYAR
ABINDA YAKE RAINA
WAYYO RAYUWATA


Page

...................k'amewa tayibabakin k'ofar cikin tsansnin tashin hankalin abinda take gani take ta

murza idonta tasake murzawa 'yar tsanace 'yar tsanafa ta cikin tv.



Take jikinta yafara wata irin tsuma takama addu'o'I tana takawa cikin tsan tsar tsoro da tashin
hankali yayin da.


Zuciyarta take tunanin daman ba k'yalesu akayi ba kenan, to me hakan yake nufi kuma dataga
an juyo kan Yusra?


To wai me hakan yake nufi yaxama dole tayi "binciken abinda yake binsu.



Ihun Yusra ne yayi yawa ta k'arasa cikin sand'a ta d'an dafata take ta fad'I kasa sumammiya
takebFatima ta fashe da wani irin kuka.




Sai da tad'an jima a haka kafin tayi dabaran tashi ta haye sama dan d'aukar wanta takira
Abdulmajid.




Wata irin dariya yake b'ab'b'akawa har yana fad'uwa k'asa kafin yace "saini mai burin mulakar
duniya na kusa cika miki burukanki ya shugabata, burukanki sunabda wuyar gaske cikin mutum
ashirin da tara dakika buk'aci nakawo miki kisha jininsu harda matata da wan matata da kuma
yaronta.


Sai kuma yafashe dakuka kafin yace ina son matata, ina matuk'ar sonta tana da kirki tana da
hak'uri bata tab'a b'atamin ba amma akan neman duniya na sadaukar da ita.



Sai kuma ya fashe da kuka mai had'e da dariys kafin yace shege kud,I kunsakani abubuwa da
yawa akanku na rasa abu dayawa zancigaba da rasawa yana cigaba da b'ab'b'aka dariyan
yana birgima ak'asa kawai sai gashi yazama k'aton mage ya d'ane kantaga da gudu

A hankali ta, bud'e idanunta tana bin ruwan dayake shiga cikin jikinta kallo d'an juya idanunta
tayi ta saukesu akan Fatima wacce tayi tagumi da duka hannayenta idanunta yayi jajir da alama
kuka tayi,.


Yanayin d'akin tabi da kallo ko ba'a fad'a mataba tasan asbiti ne, take kuma abinda yafaru ya
rik'a dawo mata kamar amajigi wani irin kuka tafashe da mai k'arfin gaske wanda yai sanadin
da Fatima ta zabura ta mik'e tayo kanta tana fad'in " sannu 'yar uwa kin tashi bari na kira likita"
daga haka ta fita da sauri har tanacin karo da Abdulmajid wanda yake k'ok'arin shiga d'akin
kedan hannunshi suka watse.


Rik'eta yayi a tsorace yace "ke me yafaru?
Wani abunne yasami Yusaran?
Ta farkane?"


Yajero mata tambayoyin ganin yadda ta fito arud'e, ganin yadda yake jera mata tambayoyi da
alama shima baya cikin na tsuwarshi yasa ta d'an shafi fuskarsa tayi murmushin k'arfin hali tace
"karka damu, dama ta tashine zan fad'awa likita" ajiyan zuciya ya sauke kafin yace "na godewa
Allah koma cikin ni bari na kirashi'


Har lokacin bata daina kukan ba jiki asanyaye ta k'araso kusa da ita tace " haba 'yar uwata dan
Allah ki daina kukan hakan ya isa mugidewa Allah dayasa babu abinda yasamu babynmu likita
yace wani abune ya firgitaki amma babu abimda yafaru dake ko babynmu kinga sai mugidewa
Allahko?.


Hannun ta Yusran takamo ta rik'e gam acikin nata tace "'yar tsanafa 'yar uwata 'yar tsana acikin
tv ta zuro hannu tashak'emin wuya kinsan ma abinda tace min?"
Tafad'a tareda zubowar wani hawayen mai yawan gaske.


Girgiza mata kai Fatiman tayi itama nata hawayen na k'ara yawaita tace " a' a


"magana fa tayimin 'yar uwata 'yar tsanafa take cemin itace ajalina wai mahaifina yai silan

mutuwar 'yarta dan haka akaina zata d'auki fansa, abin tamabayar anan dama mahaifina d'an
shan jinine ban saniba?
Dama duk wannan daular arzikin kud'in haram ne?
dama akan haram muke ginuwa bansaniba 'Yar uwata?
Da sauri Fatima ta toshe mata baki tana girgiza mata kai alamun tadaina fad'ar hakan,



Janye hannun Fatima tayi yayin da wasu zafafan hawayen suka kuma fito mata tace "barni nayi
magana 'yar uwata harka da matsafannan yana da matuk'ar wahala tunda tace saita kasheni
inkinga ta barni to ki tabbata kwanana bai kareba" tafad'a dawata irin murya mai ban tausayi
sannan tacigaba da fad'in.



Na tabbata mommyna tasan sana 'ar mahaifina domin kuwa ita d'in muguwar 'yar bin bokaye da
'yan tsubuce nasan ko awannan yawin dole wani zai fad'a mata sana'ar mijinta, na shiga uku na
Fatima iyayena basu kyautawa rayuwataba da suka kasance masu son kansu tafad'a tareda
fashewa da wani irin kuka.


Dai dai lokacin Abdul suka shigo da likita ya k'araso da sauri ya rik'o hannunta cikin damuwa
yana kallon yadda take gabzar uban kuka kafin yasamu da k'yar yace.



"Dan Allah kidaina kukannan haka kinga k'anwarkima tana kuka"



Hannun nasa ta rik'e gam gam tace "dan Allah ka kaini gidanmu ina son ganin mommyna"


Kallonta yayi sosai da tausayinta a fuskarshi kwance yace "zan kaiki amma sai kin daina
wannan kukan.





Kusan awa guda kenan tunda ya kawota gidan takasa cewa mommynnat komai sai uban kukan

datakeyi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login