Showing 39001 words to 42000 words out of 65710 words
Chapter 14 - ZATO NE (1 TO End) BOOK COMPLETE By Maman Islam.pdf
rawa
yake tsabar tashin hankalin da ya kuna rufto masa yanzun.
Da kallo duk suka bishi yayin da Fatima tasaki tsaki Yusra kuwa fuskan Fatiman tana mata wani
irin kallo kafin tace.
"Haba Fatima haba dan Allah meye hakan? Au ashe ko kowa yakasa masa uzuri ke bazakiyi
masaba kintab'a ganin mutumin dayake cutar da har abinda yake mafi soyuwa arayuwarsa?
Fatima tun muna mu biyu dake kije ki bashi hak'uri domin kuwa kin tabka kuskure kinyi laifi sam
bakiyi daidai ba"
Wani irin banzan kallo Fatima ta watsa mata tareda sakin wani dogon tsaki ta kwace fuskanta
tabata waje, sam ita bataga kuskuren magananta ba akan me zai aurosu yabar su kullum cikin
damuwa da fargaba suke nan kullum basu da wani cikakken nutsuwa kullum garin Allah ya
waye da tunanin abinda ranan zata zo musu dashi suke, ina sam bazai sab'uba tagaji kam.
"Ruk'aiyya wannan shine karo na k'arshe da zan k'ara ganinki cikin damuwa na kuma
tambayeki ki raina min hankali wallahi Ruk'aiya duk randa kika k'ureni zan miki abinda baki yi
tunani ba"
Tad'ago idanunta da gaba d'aya suka sauya kala gaba d'ayansu tayo waje dasu sai kuma ta
had'e hannayenta waje guda tace
"Na rok'eka dan Allah ka daina yimin wani tambaya akan duk wani hali da zaka ganni aciki
Abbanau, kowane abu akwai muhallinsa kuma komai da lokacinsa, saboda haka ina so kasan
cewa lokacin kasaninne baiyiba idan lokacin yayi zaka sani"
Cikin tsabar takaici yake dubanta yana mamakin halinta yana lura da itada irin halin damuwan
datake ciki amma kullum ya tambaye ta sai tace tana neman hujja wane irin hujja ne wannan?
Tun ranan da Fatima tayi wannan abun ita dakanta ta fita a harkansu gaba d'aya dan ita a
ganinta da kuma halin k'uruciya irin nata tana ganin ta fad'i abinda yake ranta ne wanda kuma
shine daidai awajenta.
Har ga Allah tagaji datashin hankalin datake fuskanta acikin gidan dabata fi wata biyar acikinsa
ba bazata k'arar da wani jin dad'i na cikakken wata guda acikin wannan gidaba.
Sosai Abdulmajid ya d'auki fushi dasu harda Yusra baiwar Allah datake ta fama da kanta ganin
haka itama ta tattara komai ta aje agefe.
Muje zuwa
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 29
...........tun ranan datayi abinda take ganin shine dai dai awajenta bata k'ara yarda ko d'aya daga
cikin mutanen gidan sun had'uba domin hatta Yusran ma haushinta takeji dan haka ta tattarasu
ta zubasu akwandon shara.
Rabonta da ganin iyayenta tun zuwan da sukayi duba Daddy farkon aurensu kusan wata hud'u
kenan dan haka yau tasha alwashin ko yardansa ko babu zataje taga iyayenta dan haka take
takira Abbi tace ya fad'awa Ummi yau zata zo musu wuni.
Tana kashe kiran yana kiran Abdulmajid, wanda yake zaune a office d'insa bayan yagama
sallamar fatner d'insa hannunsa dafe saman goshinsa har yau bai daina mamakin halin Fatima
na rashin wayo da gab'untaba sosai yake jin b'acin ran abinda ta masa.
Anya Fatima tasan yadda take a rayuwarsa tasan kuwa irin yadda ta kama zuciya da ruhi da
duk wani kafa najikinsa yana matuk'ar jinta a kowane fitar numfashinsa, kai dolene ma abinda
tayin ya tab'a masa zuciya.
Yusra ce ta fad'o masa arai wani irin tausayinta ya kamashi haka kawai batajiba bata ganiba ya
had'eta da mai laifi yana hukuntawa ko halin datake ciki bai dubaba take yaja wayansa da
niyyyan,kiranta sai kuma kiran Abbi ya katse.
Cikin girmamawa yamasa sallama, tareda gaida shi bayan sun gaisane Abbi yace
masa"Abdulmajid me nace maka banace duk runtsi kar ka sake kabar Fatima tazo yanzun ba
har sai na nemi hakan da kaina bayan nagama duk shirin danakeyi ba meyasa zaka biye
matane kasan masifar dayake binku kuwa acikin lamarinfa hummn to maza kaje ka dakatar da
ita kaji na fad'a maka"
Cikin sanyi yace "kayi hak'uri Abbi zanje yanzun na dakatar da ita" suna sallama da Abbin ya
dinga kiranta amma tak'i d'agawa ransa ya kuma b'ata masa rai ya zari mukullin motarsa ya fice
batareda ya rufe office d'inba.
Tun tana wanka take jiyo k'aran wayanta, saidai koda ta fito batabi takan wayan ba saida
tagama shinta tsab ta d'auki makullin motanta da hand bag sannan tazo ta d'auki wayanta
dayake saman gadonta anannema taga me kirannata ta d'an tab'e baki gami da turoshi gaba
kamar yana ganinta.
Ta fito kenan shi kuma zai shiga suka gwabza karo da sauri tajanye tana kallonsa cikin wani irin
tsoro ganin yanayinsa da babu annuri ko kad'an.
Hannunta ya damk'a da mugun k'arfi har sai da tasaki k'ara saboda mugun ruk'on da yamata,
ya jata cikin d'akin ya watsata saman gado ya kafeta da wani irin masifaffen kallo.
Kasa had'a ido tayi dashi duk kuma wani fitina datake ji dashi nemansa tayi tarasa domin
yanayin data ganshi aciki bak'aramin d'amata hankali yayi ba.
Cikin b'acin rai yace "Fatima ki maida hankalinki fa niba wawa bane dazaki mai dani sa'an
wasanki yaushe na fara wasa dake da irin wannan mugun rainin yake neman shiga
tsakanina,dake to wallahi muddun kika sake kika fita zakiga abinda zan miki"
Har yakai bakin k'ofa ya jiyo tana fad'in "wallahi banga wanda ya isa yahani fita yau agidannan
ba tunda ba haifana mutum yayiba"
Azafafe ya koma cikin d'akin da wani irin taku mai mugun k'arfi ganin yanayinsa yasa ta
wuntsula ta shige toilet ta rufo k'ofan kafin ya k'arasa tasaka key.
Wata irin k'wafa yayi sannan yace " tunda babu wanda ya isa me yasa kika gudu mara kunyan
k'aryabki tsaya mana kiga k'arshen mara kunya.
Maman islam be
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ. YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 30
...................tana daga toilet d'in tace "ank'i a bud'e d'in kuma zuwa gidanmu babu fashi dan
banga wanda ya isa ya hanani zuwa wajen iyayenaba ehe"
Bai k'ara bi takantaba ya fita a mutuk'ar fusace a bakin falon sukayi karo da Yusra wacce ta fita
ta aiki draiver gidansu yanzun, ya d'aga rinannun idanunsa ya zuba akan fusakar ta.
Sai dagabansa ya fad'i ganin irin fitinanniyar ramar da tayi ya d'an jata ya had'e ta da jikinsa
yana kallonta cikin tausayawa "ya jikin" yafad'a yana shafar gashin kanta dake kwance a
kirjinsa.
Sai data had'iye wani abu mai d'aci kafin tace "naji sauk'i" ganin yanayin datake ciki bai barshi
ya koma iffice ba nan yazauna tareda ita yana d'an janta da magana har zuwa k'arfe uku dai dai
nan kuma yunwa yasa Fatima saukowa sam bata kula dasuba ta wuce kicin da sauri sam bata
kula dasuba saboda hankalinta baya kansu.
Gas ta kunna ta d'ara 'yar ma daidaiciyar tukunya ta soya mai tasa soyayyar miya da naman
kaza tad'an had'a kayan hadi sai data tabbatar ya d'an tsirata ta tsai da ruwa yana tafasa ta
zuba kayan had'i tareda couscus ta koma gefe tana jiran ya gama ta juye domin ba k'aramin
yunwa take jiba.
Tana gama ta juyo karab idanunsu ya had'u wani irin mugun fad'uwa gabanta yayi sam batayi
tunanin yana gidanba ta yi zaton tun tuni ya koma office shiyasa ta fito kanta tsaye, cikin tsoro
tayi baya bisa tsautsayi ta take tab'aryan data take wajen wanda taga fad'uwanta tana shirin
d'aukewa ta manta, taga taga tayi zata fad'i yayi saurin tarota ita da flat d'in abincin, wanda
dama shi yazo nema dan shima yunwar yakeji sosai.
Sai da ya gama daidaita mata tsaiwar ta sannan ya d'auke flat din abincin batareda yace mata
k'alaba yai waje abinsa batareda ya ko k'ara kallon inda takeba.
Bayansa tabi da harara cikin tsaban takaici batareda yasan tanayiba Allah yasota ta rage wani a
tukunyar wai ko Yusra zata gani taci dama takanyi hakan idan tayi girki kuma Yusran inta gani
tana d'iba taci, anan kicin d'in ta tsaya taci sannan ta wanke kayan da ta b'ata ta gyara wajen
tsab sannan ta dice.
Shi kad'aine yanzun Yusra ta shiga ciki yana zaune saman kafet d'invtsakiyar falon yana cin
abincinsa bai yarda ya kalli inda takeba bare tasa ran yasan da zuwanta.
Itama da gudunta ta haye saman dayanayinsa ba k'aramin tsoro yake bataba duk yabi ya koma
mata wani kalan tsoro.
Yauma kamar kullum zaune take kamar kullum tana faman tunanin,yadda zata sami wayansa
wanda ya d'inma,ta kira iya adadin da bazai k'irguba amma ko tafiya layin bayayi.
Kwatsam taga mutum ya shigo kamar wanda aka wurgo, zumbur ta mik'e tana kallonsa cikin
mamakin ganinsa haka wujiga wujiga kamar wanda yake cikin matsananciyar wahala, baima
kulada itaba ya shige d'akin dayake karb'ar bakinsa idan yana gari, da sauri ta zabura zata bishi
sai dai kafin ta k'arasa ya banko k'ofar da mugun karfi nan ta tsaya tana taradaddin abunda ya
sameshi.
"Abbi nifa gaskiya na takura fisabilallahi awani d'aureni niba akuyaba har ga Allah nagaji
aurennan ya isheni dama kai kamin dole yanzun kuwa Allah ji nake kamar na gudu nabar gidan"
Fatima kenan take korowa mahaifinta wannan bayanin cikin damuwa bayan kiran wayansa
datayi
Wani irin murmushi Abbi yasaki mai ciwo, aransa yace Fatima da ace haka kawai nabarki da
tuni bakya raye aduniyar ke da abokiyar zamanki na riga da nagama kawo badan komai ba
ason zuriyar Alh. Yuseef ta yaduba sai dan dukiyarsa dan haka zanwa tufar hanci.
Amma azahiri sai,cewa yayi "Fatima kiyi hak'uri insha Allahu komai zai wuce kuma nine na hana
Abdulmajid ya kawoki saboda wani abu dana hango zai faru a zuwan naki amma idan kina son
ki mutu zaki iya zuwa"
Sosai Fatima ta tsorata da abinda mahaifinta yace hankalinta yayi mummanan tashi tafashe da
kuka mai sauti tareda aje wayar ta fita da gudu daga d'akin cikin tsan tsar tashin hankali Abbi
dayake jinta ya aje wayar cik8n tausayin halin da suke ciki.
Dake yau,lahadi ne yana zaune ad'akinsa saman gado daga shi sai gajern wanda babu riga da
comouter sa agaba yaba shigar da wasu sakonni, ta bugo kofar da mugun k'arfi wanda ita kanta
batasan tayi hakan ba tsabar rud'anin datake ciki.
Da sauri ya d'ago kansa yana kallon yanayinda tashigo dashi cikin mamakin abinda ymd'aga
mata hankali irin haka.
Muje zuwa maman islam ce
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 31
................,,kallonta yake da mamakin abinda ya d'ago nata hankali haka, sam bata kula da
shiba domin idanta yariga da yagama rufewa.
A hankali yataso yak'araso yackamota jikinsa tuni ya manta da abinda yafaru ganin halinda take
ciki.
K'ok'arin k'wacewa takeyi yayi saurin rungumeta tsamtsam a jikinsa amma hakan bai hanata
fad'in abinda takeson fad'an ba.
"Abdulmajid dan Allah dan Allah ka temakeni dan Allah tak'arasa cikin sakin matsanancin kuka
mai k'arfin gaske,
A rud'e yace "me kikeso Fatima me yake damunki meya tsorataki haka Fatima?"
Ya tambaya yana jijjigata dan ganin kamar bata hayyacinta.
Cikin wani irin matsanancin tashin hankali tace "kaine Abdukmajid kaine bana sonka bana son
aurenka domin babu komai acikinsa sai tsoro da fargaba da tashin hankali
"Ke" ya buga mata tsawan da saida ta girgiza cikin wani irin bak'in ciki da takaicin
maganganunta yaca "bana ciki da iskanci da rainin hankali, har nine Fatima kike kallon tsabar
idona kike fad'ama duk maganar da kikaga dama to Fatima duk abinda kike tunanin zakiyi
saidai kiyi amma kisa ranki kamar yadda nafad'a miki nidake mutu karaba aurena dake auren
zobene ba saki bayaji" daga haka ya tureta da mugun k'arfi yayi band'aki cikin tsautsayi tafad'a
kan hannunta har saida yayi k'ara, tasaki k'aran azaba amma ko kallonta baiyiba bare tasa ran
zai kula yaga abinda yayi mata.
Kuka tafashs dashi tana kallon hannun dayake mata wani mugun zafi ta fashe da kukan
tausayin kanta wani irin k'unci takeji har wani d'aci d'aci takeji mak'ogoronta.
Ta jima awajen tana kuka har yai wanka ya fice yabarta anan cikin wani irin fushin dabata tab'a
sanin yana dashiba sai ranar.
Sai datai kwana uku bata sanyashi a idanuntaba zuwa lokacin kuwa hannun yayi mugun
kumburi har wani k'yalli yake ga wani irin azababben ciwo da yake mata babu yadda Yusra
batayiba akan suje a duba hannun tayi mursisi tak'i yarda aduba hannun wanda tasan cewa
babu tantama karyewa tayi.
Hatta Yusran ma ta daina kulata tun safe take murk'ususu a gadonta ciwo ya isheta kuka kuwa
bata san iya yawan wanda tayiba daga safen zuwa yanzu yunwane ya tasheta wanda duk
abinda ta zuba acikin frij d'inta ya k'are dan haka ta sauko dan samawa kanta abinda zata
zubawa cikinta.
Ta gama saukowa idanunta sukafad'a kansa yana zaune saman kujera me zaman mutum d'aya
da computer sa saman cinyarsa yana faman aiki,
Motsinta ne yasa ya d'an d'ago kansa domin yayi tunanin Yusra ce datace bari taje tayi wanka
bak'aramin fad'uwq gabansa yayiba ganin k'yallin da hannunta yakeyi wanda ta tallafoshi da
d'aya hannun mai lafiyan,
A hankali ya mik'e ya isa kusa da ita yakai hannu da nufin kamo nata sai tayi saurin janyewa
taeda watsa masa wani mugun kallo tareda dosan hanyar kicin tana share hawayen daya
gangaro mata.
Ji yai kamar ya barta amma kuma ganin irin kumburin da hannun yayi sai hankalinta yakasa
kwanciya, ficewa yayi batareda ya kuma bi ta kantaba.
.da kyar tasamu ta iya dafa indomie taci anan kicin d'in ta cinye bata iya wanke kayanba saboda
d'ayan hannun babu lafiya.
Muje zuwa
Taku maman islam
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 32
................ta fito daga kicin d'in kenan shi kuma zai shiga, sukayi karo, da sauri ta janye duk da
cewa sai da ya d'an dunguri hannun kuma taji zafi amma sai ta dake tana k'ok'arin wuce shi yai
bala'in d'aure fuska ya rik'ota.
Take hawayen data ke ta danne wa ya kama zubo mata bai saurari kukantaba yajata har falon
inda mai gyaran daya kira yake har gabansa ya kaita ya zaunar sannan ya tsaya akanta kamar
wani dogari.
A hankali taji yana cewa "gatanan bugewa ne tayi yau kwana uku bansan abun yakai hakaba"
Mai gyaran yakai hannu da nufin kamo hannun nata ta yi saurin jan yewa tana kallon sa da
idanun ta da suke cike tab da hawaye tace "dan Allah malam kayi hak'uri wallahi zafi yake min
sosai kuma dama baya bari nayi bacci dan Allah kar ka fama min.
Cikin tausaya mata mai gyaran yace "kiyi hak'uri kibari a duba miki dole sai kin daure kinga ya
riga da yayi tsami"
Batare da tace komai ba tafara k'ok'arin tashi Abdulmajid yai saurin tsugunawa yasa ta ajikinsa
yana kallon cikin idonta sai dai bai ce mata komai ba domin har lokacin yana jin haushin abinda
tayi masan.
Da ido yayi ma mai gyaran alama, bata yi aune ba taji ya damk'i hannun da mugun k'arfi take
tayi wata irin zabura sai kuma ta shid'e, sao data d'an d'ebi kusan