Showing 63001 words to 65710 words out of 65710 words

Chapter 22 - ZATO NE (1 TO End) BOOK COMPLETE By Maman Islam.pdf

14 Apr 2025

5210

takuramu da yawa wai harda wasu masu
tsaro dan kar mu fita" kallon baki da wayo Abdulmajid yayi mata kafin yace "zokiji"





D'an matsawa tayi kusa dashi tana turo baki gaba wai ita a dole an takura su, tana k'arasawa ya
cafke bakin yana aika mata da wani irin hot kuses masu zafin gaske.




Sosai ya shiga rud'ata da salonsa dama yayi missing kwana biyu bai samu ya d'an keb'e da
itaba, ita ko hankalinta ne yayi mugun tashi ganin cewa afalon Amma suke da k'yar tasamu
tajashi b'angaren su na nan dan tasan tunda idanunsa suka rufe indai bai samu muradinsaba
babu zaman lafiya, shikam babu kunya dan a tsananin buk'ace yake da ita yaja hannunta suka
fice daga wajen sukayi shashin su.







Duk wani Abu da zatayi dan ganin ta dai daita komai abin yaci tura ta gano indai tana so komai

ya tafi dai dai dole sai taje da kanta wannan karin ta d'auko abinda ke cikin Fatima dole shine
warwarewar dukkan matsalo linta, gama wannan tunanin ke da wuya ta b'ace dan tasha
alwaahin ko me zai faru wannan karon sai ta shiga gidan ta biya buk'atar ta.





Sunyi nisa sosai sun Lila a duniyar masoya domin ita Kanta tasan cewa tana da buk'atar mijin
nata shiyasa yasamu had'in kanta d'ari bisa d'ari, tafiya tayi nisa sosai yana gabda kaiwa
duniyar masoya tayi ido biyu da wani jib ge gen......


Kuyi min afuwar jina shiru wannan karon mamana ne jikin ya Dan motsa bana zama Sam wllh



Taku maman isi
[11/30, 6:11 AM] Hayat: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p

*_______________________________________*


��ZATO NE��
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM

Page 53
.....................dukvsuka kafeshi da kaifafan idanunsu yayin da zuciyar ko wannen su ya shiga
wani irin bugu suna tsoron kar ya fad'o wani nasu ko makusancin su.



Shi kam lissafi yafara kamar haka.
"Haj. Asma'u matar yaya Rudwan tana da matsayi na musamman acikin qungiyar, sannan ita ba
wanda yajata kwad'ayi da son abin duniyane ya kaita sai, sannan kuma duk wani abuda zai faru
wanda yadanganci cikin gidannan ita ke jan ragamarsa idan kuna musu kuje bayan wadrop
d'inta tanan take gudanar da duk wani abinda takeso kuma tana iya fita batare da wani yaganta
ba dan fitanta yafi tsakiyar dare idan gari yayi shiru sai ta fesawa yaranta wata hoda wanda har
ta dawo bazasu farkaba kuma idan shi yaya Rudwanun yana gari harshi take had'a, da zarar
kuma ta dawo akwai sunadarin dazata k'ara fesawa su farka akan lokaci.




Sai Munzali k'anin alh. Sambo shima,neman duniyarsa ne ya kaishi. yaya Habiba kuma ita,ta
rasu ne akan yajata a cuci d'an uwanta ganin cewa tana da rawar kai sai tak'i shine da ta tashi
haihuwar fari saida ya bari ta hafi d'an ya d'auke shi ya hura mata iska aciki sannan ya murd'e
mata wuya ko shurawa batayi ba, shine likitoci sukace ta rasu bata kai ga haihuwar ba ta rasu,


Bayannan akwai uwar gidan alh. Munzali saudat haihuwar ta goma yaran suna mutuwa in
ka,d'auke d'ansa na fari shima,duk Munzalin ke kaisu wajen tsafi sannan kuma haj. Munira
tanan sun b'oyeta suna ta gana mata azaba akan ta gano cewa mijinta matsafine shine yayi
mata wata allura wacce sai tayi kwanaki bata farkaba ya tabbatarwa da iyayen ta ta rasu
sannan suka koma,daga baya suka hak'o ta sannan ya tsaface haj. Kulu matar abokin yaya
Yuseef ya maidata kamar matar sa duk sanda ya buk'ace ta jiki na rawa zata amince masa, ta
haka ne suka samar da Yusra sannan shine yasace k'wayayan haihuwar d'an uwansa alh.
Sambo ya aiwatar da wani tsafi ta yanda bazai tab'a haihuwaba har abada kuma shi a yanda
aka tabbatar masa idan yayi hakan asirinsa bazai tab'a tonuwa ba sai dai sun manta da cewa
ubangiji yana arawa mutum rana da lokacine duk randa ya tashi tona musu asiri bazasu gane
kansuba kuma sun manta rana dubu na b'arawo rana d'aya tak na mai kaya sannan ramin
k'arya k'urarrene".



Nan dai ya shiga lissafo musu yawan mutanen da suke cikin wannan harkar kuma duk wanda
aka sani sanannu wanda saida mamaki yasa suka rik'a jijjiga kawunan su saboda al'ajabi
sannan yace "ni kuma bance ku yarda dani ba zandai fad'a muku gaskiya ne wanda nake so ku

gane kafin na mutu kamar yadda nace muku NINE BOKA DUNA haka kuma duk wani abu da
zanyi wallahi wallahi wallahi Allah ne shaidana bansan ina,aikatasuba amatsayina na,musulmi
makaranci ma haddaci wanda yai imani da k'addara kharan au sharran nakanyi mamakin wani
abun idan na aikata kuma idan Hafsatu zata shaidrni zataga ina yawan rufe kaina ad'aki to
wallahi bak'in cikin munanan aiyukana ne yake cin zuciyana nayi ta fama domin jinya nakeyi
sosai har ga Allah babu yadda yaya Tanimu baiyi daniba na k'i amincewa saboda bana so na
lalata gobena lokaci guda na tsunci kaina acikin mummunan yanayin da ban san yau shene a
inane taya nake aikatasu ba wallahi duk randa nayi wani abun sai nayi dana sani mara iyaka
kuma sai nayi rashin lafiya sosai shine dalilin da duk lokacin danayi wani mugun aikin matata
zataga na rufe kaina a d'aki ina jinyar zuciyana da kuma gangar jikina da Tanimu yake
azabtarwa acewarsa ta hakane idan bala insa ya isheni zan amince na kasance d'aya daga
cikinsu batare da ya sani wani abun ta hanyar tsafiba, sai dai kuma wani ikon Allah lokaci guda
naji hankalina,ya dawo jikina ta sanadin aikin da yasani nayiwa 'ya'yan wan matata kisan gilla ta
hanyar yankan naman jikimsu gunduwa gunduwa atsakiyar kasuwa wanda yace idan ina
aiwatar da wannan mugun aikin to babu fa wanda zai ganni, ananne hankalina ya dawo jikina
naji wani abu mara dad'i yana sukana abisa aikin da yasani take nayi masa musun wannan
aikin ya d'ebi kwanaki yana bina nak'i amincewa shinefa yayi min alluran guba wai dan kar na
tona masa asiri haka nan suma yanzun ta kwab'e musu dan mafita suke nema sosai sannan
dan Allah ku taimakawa garzali domin shima yana cikin wani hali saboda neman sa suke ido
rufe kuma matuk'ar sukayi ido da ido wannan gubar datake yawo ajikina yana nan yana yawo
da ita dominsa kuma indai suja had'u sai dai wani bashi ba wannan shine gaskiyar abinda na
sani ni yanzun tawa ta k'are domin wannan gubar bata da magani sai in kwana bai k'areba dan
haka nake rok'on dan girman Allah ku yafemin abisa kuskure na badan niba badan na isaba
dan zatin Allah na sani cewa babu ni babu wani rabo domin ban aikta abinda zan adarba
agaban mahalicina duk aiyukana munanane'.





Yak'are tareda jan wani irin zazzafan numfashi wanda ya wuce da rayuwarsa batareda sun
ankare da hakan ba domin jikinsu ya riga da yayi sanyi hankalinsu ya masifar tashi musamman
daddy da mamakin kawu Tanimu yake neman illata rayuwarsa, Abbi ne kawai yayi k'arfin halin
cewa.




"Kar kace haka malam Sulaiman domin Allah mai yawan gafara ne kuma baya hukunta bawa
abisa laifin aka tilastashi yinsa ko kuma ya aikata shi cikin gushewar hankali ko tunani sannan
kuma dakake cewa baka da rabo bakasan gaibu ba sai ubangiji dan haka ka dage da istigifari
tun kafin ka koma ga Allahu subahanahu wata domin shi mai yawan yafiyane ga bayinsa dan

haka mu baka mana komai ba kuma koda kayi mana mun yafe maka duniya da lahira dagani
har 'yan uwana na ari bakinsu naci musu albasa"




'Karan fad'uuwar dayayi ne ya ankarar dasu sukayo kanshi da sauri gaba d'ayansu gwaggo
Hafsatu ne tafara tab'ashi sai kawai tabkoma gefe tareda fashewa da kuka domin tariga ta
tabbatar da cewa rai ya rigada yayi halinsa dama 'yan magana sunce tsakanin mata da miji sai
Allah da duk bayanin da yake cikin zafi take tana sak'a irin matakin da zata d'auka kansa amma
yanzun ganinsa amace yazama gawa sai wani irin imani da tsoron Allah ya shigeta take ta
shiga istigifari tana nema masa gafara wajen Allahus samawati wal ardi.





Sosai mutuwar ta daki 'yan uwanta ga kuma abinda suke shirin yi na binkito inda Tanimu ya
b'oye tare da bin diddigin Badamasi dan cetosa daga sharrin Tanimu dan haka dole suka kasu
kashi biyu rabi suka tsaya suka sallaci malam sulaiman rabi kuma suka had'u da jama an tsoro
suka tafi neman Badamasi da kuma aboki kuma aminin shed'an Tanimu


To masoya labarifa yana ta gangarawa yana tafiya zai k'are zai wuce





Takuce
Maman,isi
[11/30, 6:11 AM] Hayat: ��ZATO NE��
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM


☀️FIRST CLASS WRITTERS ASSOCIATION☀️

Page 55



.............mutsits tsika idanunta ta k'arayi dan tabbatar da abinda idanunta suke gani sai taga ya
sakar mata wani irin shu'umin murmushi mai kama dana mugunta, Abdulmajid ta kalla wanda
yayi nisa a dunyar nishad'i ga wannan mugun abun yafara tunkarota take jikinta ya d'auki wani
irin rawa, dukan sa tafarayi tana "yaya yaya yaya aljana amma ina baisan tanayiba sobad'ad'in
surutai kawai yake mata tak'ark'arewa tayi ta galla masa wani azzalumin cizo take kuwa yai
wani irin zabura ya watsar da ita gefe yana kallonta da mamakin dalilin dayasa tayi masa
hakan, idanunsa ne suka sauka akanta.






Shi ba jemage ya ganiba wata irin halitta ya gani mara kyaun gani, ko ba'a fad'a masa ba yasan
cewa su Abbi suntafi su kuma sun kewayo su gama dasu ta bayan fage kenan.



"Yayaaaaaaaaa" Fatima ta kwalla k'ara ganin yadda abin ya tunkaro ta a gigice, da sauri ya
tarota ganin tana shirin shidewa, cikin azama ya maida mata duguwan rigarta ya d'agata cak ya
goyata abayansa, ya tsaya tunanin ta inda zai fara dan basirar sa ta d'auke bai san me zaiwa
wannan muguwar halittar ba, ita ko Fatima saura kad'an ta sume masa ganin yadda take
tunkarosu tana zaro harshe kuma idanunta akanta gashi tana nuna cikinta yayin da shegen
murmushin bai bar fuskanta ba take taji cikinta yayi wani irin azababben murd'awa take
numfashi ya fara rawa haka jikinta ya d'auki sheking ta ko ina da sauri Abdulmajid ya dubeta
cikin mummunan tashin hankali take ya fara neman tsari da wannan mak'iyiyar Allah da
manzonsa.





Yayin da take tunkaro su tana sakin murmushin k'eta take Abdulmajid ya dage iya k'arfinsa ya
fara fad'in BISMILLAHIL LAZI LAYADURU MA'A ISMIHI SHAI AN FIL ARD WALA FI SAMA I
WA HUWAS SAMI IL ALIM.
Da iya k'arfinsa yake addu ar yana maimaitawa take Gaza ta tsaya cak tana kallonsu da wani
irin yanayi take munafikin murmushin ya bar kan fuskarta sai ma had'de rai datayi tana tunanin
ta yadda zata d'auke hankalinsa daga addu ar da yake yi dan addu o i ya hau jefo mata kala

kala wanda bata isa ta tunkarosu ba, sai a lokacin Fatima ta farajin sassaucin azaban da ya
soma rud'a k'wak'walwan ta ta dubi Gaza cikin k'arfin hali ta saki murmusht tareda d'age mata
gira alamun dai munfi k'arfinki, ni ko nace ji Fatima da k'okari kina ruwa yasin.





Su kuwa su Abbi duk inda hankalinsu yake yayi masifar tashi domin abinda suka gani a wannan
gidan ya wuce tunanin su harda mutum wanda suka aje namansa ya zagwanye ya zama
skeleton gawan jarirai da k'ananan yara kuwa ba a magana duk da kasan cewar su maza wani
abun saida yasaka su hawaye yayin da har masu rai irin wanda aka sace ba akai ga kashe
suba.



Sun jima suna tafi a wannan k'aton gidan kwallin kwal a dajin wanda ak'alla zai kai gidajan wasu
talakawan guda d'ari koma sama da haka tafiyace bata hankali ba kafin su riske k'aton falon da
ya k'awata shi kamar ba za a mutuba k'afar Badamasi ya nuna musu wacce ya basu labarinta
tunkafin su zo yace


"Yanzu dai duk inda za aje a dawo na tabbata yana cikin nan domin tunda yasan cewa
Abdulmajid sun gudu kuma ga bala in da ya sakoshi gaba na Gaza dan nasan bazata tab'a
barinsa ya samu kwanciyar hankali ba to tabbas yana nan yana nemarwa Kansa mafita"




Abbi ne yafara nufar wajen bakinsa d'auke da addu a sannan baba Ridwan shima nasa bakin
d'auke da tasa addu ar suka buga k'afar da mugun k'arfi saiga shi ta bud'e, abinda suka soma
cin karo dashi k'aramin girgizasu yayi ba domin a take daddy ya zube a wajen yana rawan jiki
shi kam dama baba Ridwanu bashi da wahalar kuka take ya fashe da kuka ya ruga zai rungumo
mahaifinsu daya gani a sak'ale yana reto, da mugun azama Badamasi ya Rik'oshi yace "karkaje
Alhaji wallahi tarko ne yaga shigowar mune domin ba anan ya adana gawar mahaifinku ba"


Dukan su suka bishi da kallon rashin fahimta tare da son jin k'arin bayani fahimtar hakanne
yasa yace "tabbas Tanima kafiri ne kuma fajiri mak'iyin addinin Allah uwa da ubansa basu sa an
haihuwa ba na rantse domin duk lokacin da wani zai mutu to akwai sa hannun Tanimu kuma
bayan Jana izar duk wanda ya mutu Tanimu yana komawane ya hak'o gawar dan shi na shi
kalar tsafin da gawa yake amfani, kuma gawar mahaifinku wanda shine ya kashe shi da

hannunsa da kuma gawar mahafiyarsa wadda ita CE farkon gwajin tsafinsa wacce ta mutu tun
yana shekara goma amma lokacin daya zama matsafi saida ya rabota da makwancinta na
gaskiya yazo yake neman duniyarsa da gawarta said kuma ita Hauwa wannan dai wacce yaiwa
su Abdulmajid k'aryar cewa saboda ita yasace su wallahi k'arya ne hatta lokacin auren da akasa
duk da ba haifeni ba ya fad'a min saboda yardan da min yace shine silan komai dan ya amfana
da hakan sai Amma ta bayyana ta lalata masa shiri shine ya shek'e Hauwa sannan kuma ya ya
d'auki alk'awarin hana Amma sakat ta hanyar kaahe duk d'an dazata haifa yayi nasarar hakan
domin yara takwas ya kashewa Amma sai Abdulmajid da Meemah ne kawai suka gagare shi
shinefa yake ta kashe duk wacce Abdulmajid yace yana son aura, sannan kuma fa Kansa yake
shiga har garin yace Alhaji Yusif matsafi ne wannan shine dalilin da yasa kake ganin kamar
mutane na zarginka ba zargi bane tabbatar musu akayi kunga yanzu muyi abinda ya kawomu
dan da yasan da zuwan mu da yanzu muna nan muna k'aramin yak'i"




"Abbi yace baza akai ga haka bama domin bazamu bashi damar hakan ba, take Abbi yafara da
karatun k'ur ani mai girma ayoyin lalata sihiri yafara karantowa take wajen ya d'auki wani irin
kururuwa.





Shi kuwa Abdulmajid saida ya gama gigita Gaza da karatu da addu o i kafin ta ankare ya d'auko
wani ruwa a kwalba da Abbi yabashi ya yarfa mata take tahau wani irin ihun daya firgita su duka
sannan ta hau hajijiya ta b'ace b'at.




Kawu Tanimu da idanunsa suke rufeyaji yaji wani irin zafi yana ratsa shi kamar ana tsatstsaga
masa jikinsa da reza take yai hanzarin bud'de idanun sa take gabansa yai wani irin fad'uwa
ganin Gaza cikin wani irin yanayi ga jikinta yana wani irin kwailila abin ya masifar d'aga masa
hankali dan yasan ba iya Kanta abin zai tsayaba dole ya shafeshi, ilai kuwa cikin b'acin rai tace



"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login