Showing 27001 words to 30000 words out of 65710 words
Chapter 10 - ZATO NE (1 TO End) BOOK COMPLETE By Maman Islam.pdf
Ita kanta haj. Kulu bak'aramin tashi hankalinta yayiba ganin yadda tilon 'yartata ta wani fige
lokaci guda ga kuka tasata gaba tanayi.
Gyara zamanta tayibkafin ta daure tace "Yusra dan Allah idan bazaki fad'amin damuwarkiba to
kitaimakeni kidena wannan kukan jifa yadda zuciyana take bugawa saboda tashin hankalin da
nake ciki adalilin wannan kukannaki"
Kallonta tayi tace "mommy menene sana'ar mahaifina?????
Muje zuwa taku
Maman islam
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
Ina mutukar mika sakon godiya ga masoyana kwarai naga yadda kuka damucdani abisa jina da
kuka yi kwana biyu hakan yasamune sakamakon ziyara da nakaiwa yan uwan garuruwa so
alhamdulillah na dawo lafiya kuma na gode da addu'o'inku ina mugun sonku Love u all my heart
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
DAGA MARUBUCIYAR
ABINDA YAKE RAINA
WAYYO RAYUWATA
Page 17
.......................da mugun gudu suka k'arasa inda Yusra take yasha inda jini yake malala daga
jikinta ba k'aramin tashi hankalinsu yayiba ganin yadda jinin yake gudu.
Da karfi Abdulmajid ya dagota ganin take wata irin jijjiga idanunta suna k'ak'k'afewa ba Fatima
ba hatta shima fashewa yayi da wani mugun kuka mai k'arfin gaske yayinda ya ciccib'ota
akafad'arsa yai waje daita da gudu Fatima ta bishi babu mayafi babu takalmi.
Tun bayan da Yusra tabar gidan suka koma suka zauna jigum yayin da hankalinsu yake
amutuk'ar tashe da k'yar haj. Kulu ta subi alh. Sambo idanunta na zubda hawaye tace "alh.
Kaga irin abinda nake fad'a maka ko?
Shiyasa tunda farko nace maka wannan hanyar abarta kodan tilon 'yarmu amma kak'i yanzun
ga abinda muka binne shekaru talatin yana shirin bayyanuwa tafad'a tareda sakin matsanancin
kuka tace tarihi yana shirin maimata kansa na shiga ukuna ni Kulu".
Sosai take kuka tana dana sanin abubuwa da dama wayyo rayuwa son zuciya baiyi ba wallahi.
Shi kam Alh. Sambo kasa cewa komai yayi domin kwata kwata baya cikin nutsuwarshi
hankalinshi amutuk'ar tashe yake yana sane da zuwan wannan ranar amma bai tab'a tunanin
zata zomasa kwana kusa ba.
Tun tana ganin dishi diahi har ganin nata ya d'auke gaba d'aya take alh. Munzali yakira wasu
k'artin banza suka janye masa ita suka aje wacce yasa aka sakawa irin fuskar hajiya munira sak
awajen tareda dunk'uleta waje guda hannunta saman cikinta alamun tana murk'ususu ta rasu.
Wata irin mahaukaciyar dariya ya kece da ita sannan yasakarwa kansa kirari sannan kuma
naga ya had'e rai tareda fashewa da kuka.
Haka iyayen haj. Munira sukayi jana izarta cikin tsananin bakin cikin rashin kamilar d'iyar tasu
da sukayi yayin da alh. Munzali yake kuka kamar ransa zai fita.
Suko su Abdulmajid koda suka kawo asbiti abinda yai mutuk'ar gigitasu ya d'aga musu hankali
shine ganin yadda gaba d'aya jinin da yab'ata musu jiki da wanda ya yake bin jikin Yusra ya
bace b'at, babu ko alamunsu k'asan motarsa yakai dubansa inda ya b'aci da jinin, Abdulmajid
yakai dubansa take yaga wajen tas babu alamun wani jini take gabansa yai wani irin
mummunan fad'uwa.
Ita ko Fatima dubanta takai kan Yusra dataga kamar tana motsi atake Fatimar ta sandare
awajen sakamaon idanun Yusra da Fatima tagani yana wata irin ci da wuta ga kuma wasu irin
halittu a ciki suna k'yalk'yala mata dariya, take Fatima ta sume ajikin Abdulmajid tsabar gigita da
rud'anin data shiga.
Jin fad'owarta jikinshi yace "Fatima yanzun ba lokacin kuka bane wannan abun addu'a yake
buk'ata tashi kiga mu fara kaita a duba mana lafiyarta tunda nayi imani har ga Allah wannan
cikin mun rasashi kuma nasan tabbas aikin matsafan nanne wallahi Fatima nagaji da wannan
masifar yazama dole nayi fito na fito da wannan azzaluman"
Jin duk maganganun da yake shiru babu amsa yasa hannu yad'agota "innalillahi wainna ilaihi
raji un" yafad'a da k'arfin gaske wanda har saida ya yajawo hankalin wasu mutanen tareda ma
aikatan wajen da gudu suka kawo masa temakon gaggawa aka kwaahe su akayi emmagency
dasu, yayin da Abdulmajid ya kifa kansa saman sitiyarin motar wata irin zazzafan kwalla ya
kece masa.
"Kana sane sarai da matsalar da kaja mana ko abisa wannan hukuncin daka yanke akan
matarka Munira?
To ka shirya wa kanka abinda zaka kare kanka dashi awajen shugaba"
Take hankalin alh. Munzali yayi mugun tashi idanunsa sukayi wani irin ja yace "to yazanyi
Asma'u bani da wani zab'in da yafi wannan domin tariga da tasan komai ammafa ba kasheta
nayiba kawai dai anbuga mata sandar tsafi atsakiyar kaine kin sani sarai zata farfad'o nanda
shekara guda cikin bacewar hankali.
Suna cikin tattaunawar ta bayyana agansu cikin shigar daya d'agawa kowa hankali domin
muddun tayi wannan shigar to babu lafiya,
Take gaban munzali da Asma'u ya yanke ya fad'a suka kalli juna cikin fad'uwar gaba amma
basu iya cewa komaiba.
Sanye take cikin bak'ak'en kaya yayin da k'wayar idanunta ma yasance bak'i k'irin idanun suna
fitar da wani irin hayak'i.
Ga mamakinsu kawai sukaga tafashe da kuka yayin da hawayennata yakasance bak'i kamar
ruwan kwalta tasoma magana cikin tsan tsar bak'in ciki da damuwa.
"Munzali ina mai tabbatar maka ka tafka kuskure mafi muni arayuwarka, wayace ka tab'a
wannan tak'adiriyar matar taka, koda tace maka tasan sirrinka kana tunanin zan bari asirinmu
ya tonune? to ina so kasan cewa duk abinda ya biyo baya kada kayi kuka da kanka amma
badaniba" daga haka tayi wata irin bacewa wadda guguwar da ta taso saida ta watsosu waje.
Wani irin kuka mai k'arfin gaske alh. Munzali ya fashe dashi take haj. Asma'u ta dubeshi
tace"kayi hak'uri kayi shiru kaga a mutane karsu gane abinda yafaru.
Da yake duk abinda yafaru acikin gidansa ne.
Take kuwa mutane suka fara bashi baki cikin tausayawa domin sunyi tunanin yakasa jure rashin
da akayi masane.
Acan asbiti kuwa tuni Fatima ta farfad'o tana ta kuka, amma Yusra ko yatsar ta bai motsaba
fad'an irin tashin hankalin da Abdulmajid yake ciki ma b'ata bakine,
Cikin yini guda kacal yayi wata irin masifaffiyar rama ga kukan Fatima dayake masifar hargitsa
masa tunani, gajiya yayi da koke koken yajata cikin mota ya rungumeta tsam tsam tareda had'e
bakinsu waje guda shikenan ya sami sauk'in kukan.
Muje zuwa
Daga maman islam
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
DAGA MARUBUCIYAR
ABINDA YAKE RAINA
WAYYO RAYUWATA
Page 18
..............................sosai yayi kewar Fatiman ya dinga bi da ita cikin salonsa mai sanyi da saka
nutsuwa.
Bak'aramin tashi hankalinsa yayiba, dole anan cikin motar ya kauda k'ishirwan dayake
damunsa.
Take baccin data dingacin bashinsa ya kwasheta anan, ya dinga kallonta cikin tsantsar so da
k'auna gami kuma da ta sauyawa halin da suke ciki su duka.
"Munxali kanemawa kanka mafita tun kafin dare yayi maka"
Cikin tsantsar tashin hankali yake duban Asma'un kafin yace "to ya kikeso nayi Asma u kina
kallofa ni ina can ina haukata ashe tsirara Munira take kallona, tagama sanin duk wani sirri
nawa bansan wanne abu zan aikata dayafi wannanba"
Cikin matuk'ar damuwa Asma u tace "hakane Munzali koni nasami kaina a irin matsayin daka
tsinci kanka irin hukuncin da zan yanke kenan, sai dai kuma yayinda muka shiga halin k'ak'a
nikayi sai muke mantawa da umarnin shugaba GAZA datace duk wanda zai yi wani abu yafara
shawartata dan haka nema kuka sami wannan matsalar, abinda zai faru kawai yanzu kaje
kasamo mata yara 'yan shekara uku hud'u kaga tana sonsu sosai, kaga idan kai hakan dakanta
zata samar maka da mafita"
Cikin share hawayen dayake tayi tun d'azun yace "kina ganin ganin idan nayi hakan ba wani
damuwa?"
Cikin k'arfafa masa gwaiwa ta tabbatar masa, sun d'an jima tana kwantar masa da hankali kafin
tatafi shi kuma ya koma wajen zaman makokin.
Cikin fad'a shugaba dumb'uru yacewa gaza d"aanme zatayi haka akan me zata bari su rasa
d'aya daga cikin manuan hadiman da suke biya musu kowace irin buk'ata kuma duk
tsananinsa.
Itama gaza cikin tsan tsar bacin rai tace "akan me zai saka Munira cikin doguwar suma yasan
amfanin da numfashinta yake dashi kuwa a cikin tafiyar?
Taci gaba dacewa rayuwarta tamkar nasaran mune haka kuma mutuwarta kamar tona
asirinmune, sanka maza atasheta daga haka ta b'ace.
Cikin tashin hankali dumb'uru yake bin inda gaza ta tsaya da kallo kamar wanda yake neman
wani abu wajen gaba d'aya jikinsa babu inda baya rawa ya shiga had'a sihirin da zai tada Haj.
Munira daga dogon suma amma ba cikin hayyacintaba.
Ta jima tana bacci kafin ta bud'e idanunta fes tasaukesu asaman fuskarshi wanda ya tallafe da
duka hannayensa cikin sanyi ta dinga kallonsa aranta tana tunanin abinda ya hanashi awaitar
da komai yadda ya kamata akanta koda take yarinya mai k'aramin shekaru amma tana da ilimin
da zata gane cewa ba iya haka ake auratayyaba kuma bak'ramin haushi tajiba ganin Yusra da
ciki dole tasan wani abu yafaru amma sai bata nunaba, kuma sautari idan wani abu yataso
masa na shi'awa natuk'ar ad'akinta yake yasan ta yadda zaimawar kansa nutsuwa.
Hura mata iskar bakinsa yayi, tayi saurin dawowa daga duniyar tunanin da tatafi ta watsa masa
dara dara idanunta, ya d'age mata gira tareda fad'in "yane?"
Turo baki tayi tareda kawar da kanta gefe batare data iya cemasa komaiba.
Muje gida muyi wanka "muci abinci sai ki samu ki d'an hutako tunda sunce ta dawo hayyacinta
harma tasami bacci "
Bata sami damar duban inda take ba ta kawar da kanta gefe har ga Allah haushinsa takeji, a
shirme irin nata gani take yamafi son Yusra tunda har yayi nasarar yi mata ciki amma ita baima
tab'a kusantartaba bare tasa ran zai mata cikin, take taji wani irin haushi da b'acin ran abun ya
kamata.
Wata irin mahaukaciyar dariya tasaki mai k'arfin gaske sannan afili tace "Abubakar kayi
ganganci, kuma kayi kuskuren bada tsaronka ga iya Abdulmajid ni kuma da wannan damar
zanyi amfani wajen cimma burina zan had'asu gagarumin fad'a zan saka tsanarka a zuciyar
Fatima Abdulmajid akan abinda bai taka kara ya karyaba.
Abangaren Munzali kuwa da k'yar ya iya samin yara hud'u saboda yanzun idon mutane na
kansu, saboda an riga an farga da yawan sace sacen da ake na mutane andawo da idanu kan
yara.
Lokacin da yakaiwa gaza wannan yaran ba k'aramin farin ciki tayiba domin a lokacin tana kan
wani aikine wanda ake buk'atar jini sosai, dan haka tace maganar Haj. Munira dole suna
buk'atar ta araye saboda cigaban su, dan haka dole za atasheta.
A matuk'ar firgice yake kallon gaza kafin yace"kuma nayiwa danginta k'aryar cewa ta mutufa kar
kuma aganta?"
Tace "kar ka damu za'a tsaface ta ta yadda babu wanda zai ganta ko yaji maganarta amma ita
zataga kowa kuma zataji maganar kowa dan haka zata cigaba da numfashi na sanar da
dumb'uru.
Sosai hankalin Munzali kwanta sai dai kuma yayi maganar boka Duna akan yana son ganin
bayansa wata irin mummunan tsawa gaza ta daka masa tace " kul d'inka domin duna yana da
mutuk'ar amfani ga kowa cikin domin yana da bud'ad'd'en ido naganin kowace irin matsala ce
zata kunno mana kai"
"To maganar 'yatafa yace sai yaga bayantafa kuma son da nake mata ko d'arln dana samu ta
hanyar aure banji inayi masa son da nakewa wannan yarinyar ba"
"Tace wannan kuma,tsakaninku sai kuje ku sulhunta kankau"
Sosai ran Munzali ya b'aci da wannan hukuncin na gaza sai dai babu yadda zaiyi tunda ya
fahimci suna na hannun damarta ne duk abinda yace anyi angama.
Pls manage na dawo gida zaku dinga ganina akan lokaci
By maman islam
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 21
....................cikin tsan tsar bak'in ciki datakaicin abinda tayi masa ya tureta daga jikinsa ya dafe
kansa, yayin da idanunsa sukayi wani irin ja saboda tsabar b'acin rai da kuma halin buk'atuwa.
Hannu yasa da zummar janyeta daga kannk'afafinsa sai lokacin ya lura da cewa ta suma da
k'arfi ya hau jijjigata amma shiru a mutuk'ar firgice ya mik'e ya nufi wajen frij d'insa ya d'auko
ruwa mai mugun sanyi yana zuwa bai tsaya wata wataba ya shek'a matashi a fuska.
Wata irin k'ark'afar ajiyar zuciya tasaki mai k'arfin gaske saboda sanyin ruwan kafin ta soma
bud'e idonta a hankali ta saukesu saman fuskar Abdulmajid.
A tsorace ta somabin jikinsa da kallo ga mamakin ta Abdul d'intane ba wannan mummunan
gwaggon birinba, cikin tashin hankali ta fashe da wani irin gigitaccen kuka ta fad'a jikinsa, yayin
da shima ya k'ank'ameta zuciyarsa tana wani irin bugu saboda tsan tsar b'acin ran dayake taso
masa mak'ogoronsa har wani d'aci d'aci yake masa.
Da k'yar yasamu ya rarrasheta sukaje sukayi wanka gami da d'auro alwalla, har suka fito daga
toilet d'in Abdulmajid yana mamakin abinda yake son faruwa dasu,
Ya fahimci duk ranan daya buk'aci son keb'ewa da Fatima sai wani abu ya faru kamar yau, zai
iya cewa wannan shine kusan karo na uku kenan da irin hakan ta faru dasu yazama dole ya
nema musu mafita.
Kwana sukayi suna sallah dan saida suka gabatar da sallahr asba wanda shi ya wuce masallaci
yayin da ita kuma tayi nata anan saman abin sallan bacci yai awon gabada ita.
Sanda ya shigo tana bacci dan haka ya shiga toilet ya sakarwa kansa ruwa sosai ruwan ya rik'a
ratsashi duk da kasan cewar yanayin sanyi yafara busawa amma hakan bai hanashi sakarwa
kansa ruwan mai d'an karen sanyiba.
Saida yashafe kusan 15 munute ruwan yana ratsa shi kafin yayi wankan ya fito.
Cikin wani fari kar d'in lallausan yadi ya shirya ya fito cik8n sauri ya lek'a d'akin yusra itama
bacci take hankali kwance a hankali yaja mata k'ofar ya fice.
Kai tsaye gidansu ya nufa direct d'akin Amma ya nufa dan yasan yadda yayi sammako to
acenne zai samu iyayennasa wanda yasan duk safiyar duniya anan duka iyayennasu maza da
mata suke karin kumallo.
A hankali ya tura k'ofar glass d'in wanda banda ya had'a da sallama da bazasu ji zuwan saba
domin duk hankalinsu yana kan mahaifiyar tasu datake ta jero musu addu'a kafin su fara cin
abincin wanda hakan zan iya cewa kusan ya zamar musu jiki.
Gaba d'aya su juyo suka zuba masa ido cikin tsantsar mamakin abinda ya kawoshi da sassafe
haka wanda shi kuma idanunsa ya hau rarrabawa inda yaga suk iyayen nasu amma banda
Mummynsa da Umma.
Cikin nutsuwa ya k'arasa ya durk'usa har k'asa yagaida Amma sannan ya gaida iyayen nasa
cikin ladabi sannan ya mik'e ya koma cikin falon ya zauna cikin d'aya daga cikin kujerun falon.
Hannunsa ya zura cikin aljihunsa ya zaro wayarsa ya kama danne danne yayin da Daddynsa
ya tsareshi da idanunsa,
Tabbas akwai abinda yake damun d'annasa saidai yasan ko sama da k'asa zasu had'u abune
me mutuk'ar wahala,ya iya fad'awa iyayyen nasa damuwarsa.
Amma ce da kanta ta had'o masa abincin ta kawo har gabansa ta jera tareda fad'in "bismillah"
Ba tareda yace komai ba ya sauko k'asa yaja kofin data ciko da had'ad'd'en shayi mai uban
kauri yafara kurb'a a hankali yana cigaba da daddanna wayarsa.
Amma tace "to ai sai ka aje wayar ka gama cin abincin ko?"
Kallon ta ya d'an yi sannan yaja flat d'in farfesun kayan cikin wanda Amma tasan yana mutuk'ar
so, amma da k'yar ya iya cin yanka uku saboda halin k'uncin dayake ciki ya ture sauran gefe.
Yayin da amma ta tsareshi da ido, shima kallon yake binta dashi had'i da d'age mata gira
alamun ya dai?
Sannan yace mata "inajin kin fifi kowa sanin bana iya yin kari da sassafe yanzunma nacine dan
karkiji babu dad'i kin had'owa mai gida kari yabarki da kayanki"
Murmushi tayi batareda tace komaiba ta kwashe kayan daidai nan kuma mummynsa ta shigo
falon da sallamar ta itama kallon Abdul d'in take da mamakin abinda ya kawoshi gidan da
sassafe wanda tunda yai aure bai tab'a musu irin wannan sammakonba.
Shi kuwa Abdulmajid ganin har sungama,sun sallami Amma,suna shirin fita yaca "Abbi wajenka
fa