Showing 3001 words to 6000 words out of 65710 words

Chapter 2 - ZATO NE (1 TO End) BOOK COMPLETE By Maman Islam.pdf

14 Apr 2025

5224

da Umma matar kawu
Ridwanu da anty Ruk'aiyya matar Abba Usman yasha mamakin ganinsu.

Yasan sarai kan iyayensu a had'e yake basuda yawan fad'a ko gulmace gulmace irin na
faccaloli sam bazaka tabajin kansuba.


A hankali ya k'arasa kusa da Amma yasami waje ya zauna yayin da Fatima ta zaune kusa
dashi har kafad'ansu yana gugar juna.

Gaida su yayi suka amsa da kulawa Ummi ta dubi Mammy tace "yarona yayi ciwone naga ya
rame dayawa haka?"




Ajiyan zuciya Mammy ta sauke tace






Taku maman islam
[8/7, 8:29 PM] MAMAN ISLAM: *مسب الله نمحرلا ميحرلا *

*☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️*

FCWA

*Home of qualities and trusted writers of the nation*

https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?ty
pe=3&source=45&refid=17

_________________________


��ZATO NE��
NA

HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

WRITTEN
BY

MAMAN ISLAM

DAGA MARUBUCIYAR

ABINDA YAKE RAINA

WAYYO RAYUWATA

Page 3




...............bari kedai Ummu wallahi abinne bansan ta inda zan bulloba,
Kallon juna,Umma,da anty Rukaiyya sukayi batare da sun lura da kallon da Abdul majid ya
binsu da shiba wata alama,sukayiwa juna wadda sukad'ai suka san ma'anar hakan.


Mik'ewa yayi tareda cewa "bari naje d'aki akwai abinda nake son k'arasawa" Amma tace
"anjima kadawo nadama maka furar tanan afirij"
Yace "bani kawai natafi da ita nasaka afrige d'in falona"

Fatima da tamik'e tana shirin binsa Amma ta duba tace "d'auko masa furar nan da Meema
tasaka afrige d'azu.


Da sauri ta d'auko masa tayi waje batare da ta mik'a masa mug d'in ba, yabita da kallo yana
murmushi kafin yace ma iyayennasa sai anjima

A can bakin pat d'insa ya sameta atsaye, ya lakace mata hanci yace "gundura tadawo" kallonshi
tayi tace yaya meye gundura kuma?"

Domin hausa bai ishi bakinta ba, baice mata komai ba yaja hannunta suka shige falon tasaka
furar afrige tadawo ta zauna akusa dashi tace "yayana labarifa zaka bani"


Kallonta ya rinkayi kafin yace "wanne irin labari zan baki.




Abangaren su mammy kuwa bayan sun koma b'angaren mammy dan har lokacin ba'a gama
gyara mata pat d'in taba.

Anan ta kwashe duk abinda yake faruwa da Abdul majid tafad'awa Ummu Kulsum, sosai ta
girgiza dajin wannan mugun labarin, ta dubi Mammy tace.


"Anya mammy ba alajanune suka tab'a yaronnan ba ?"

Mammy tayi wani murmushi mai ciwo tace "babu wasu aljanu domin gurin rukiyya babu inda
bamujeba amma ko gezau "


Ummi tace to gaskiya akwai ayar tambaya dan haka zama bai ganmuba domin idan akace mun
hak'ura anci gabada tafiya a haka akwai babbar matsala fa.

Mammy tace "bana iya bacci Ummu kullum cikin kuka nake da addu'ar sauk'i wa yaronnan
wallahi karkiga yadda nake tausaya nasa Abdul yana da matuk'ar hakuri, zai wuya ya fad'a miki
damuwar sa".


Ummi tace "karki damu mammy nima Abdul d'anane nayi miki alk'awarin sanar da baffi" dake
mahaifinta babban malamin addini ne anan misra.


Mammy tace "shikenan Allah yasa adace"

Ummi tace" tace insha Allahu za'a dace "

Ido ta tsareshi dashi tare da zuba tagumi da duka hannayenta, hura mata iska yayi a idanun, ta
lumshe idon ta kuma bud'esu akansa.

Hannunta ya rik'o shima ya zuba,mata nasa idanun sosai ya had'e idonsa danata take ta had'e
rai gami da kawar da kanta tace "nifa bana sonkallo"tafad'a da sigan shagwab'a.



Shima kwaikwayan muryanta yayi "to nima kidaina kallona"



Had'e rai tayi ta tashi zata fita, ya fusgota tafad'a jikinsa yarik'eta ajikinsa yace


"Ina zakije kuma muna hira k'ok'arin tashi take a jikinsa yak'i bata damar hakan ta hanyar
k'amk'ameta ajikinsa yace "wai meye hakane ki zauna wata magana zan fad'a miki mai dad'i

Jin haka yasa tagyara zamanta tace "yauwa nawan dama inaso muje bajoga kaga sau d'aya na
tab'a zuwa"


Yace "to zamuje amma ba yanzuba sai kin huta kinga yau kuka zo"


Tace "yauwa yayana naji ana tasa lokacin bikinka awajen Ummi meyasa kuma nazo nasamu
babu mata?"


Take yanayinsa ya sauya d'an farin cikin dayasa mu daga gareta yab'ace ba't kalan idonsa ya
sauya yayi jajir



Kuyi hakuri wllh nagaji unguwa naje yau.


Taku maman islam
[8/8, 5:12 PM] MAMAN ISLAM: *مسب الله نمحرلا ميحرلا *

*☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️*

FCWA

*Home of qualities and trusted writers of the nation*



https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?ty
pe=3&source=45&refid=17

_________________________




��ZATO NE��
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI


WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM


DAGA MARUBUCIYAR

ABINDA YAKE RAINA

WAYYO RAYUWATA



Page 4

....................ya kalleta da wani irin yanayi mai wuuar fassara, batareda yace mata komaiba.

Ita kanta saida ta tsorata daganin yanayinsa, take idanunta suka ciko da kwalla, ya dubeta cikin
tashin hankali domin hawayen Fatima fitina ne ga zuciyarsa.

Tallafo fuskanta yayi da duka hannayensa yaja daf dashi har numfashinsu na bugun juna, take
yanayinsu ya sauya wani irin kasala ya rufesu dukansu basu saba da irin yanayinba.


Cikin sanyi murya wacce take d'auke da tsantsar tashin hankali yace "Fatima karkiyi kuka zan

fad'a miki dukkan abinda yake faruwa, duk danasan cewa har yanzu bakiyi hankalin da zaki san
me hakan yake nufiba"


Take ya kwashe dukkan abinda yake faruwa ya fad'a mata wanda kafin yagama har shid'ewa
take sabo da kukan datake gurza.


Wani irin tausayin yayan natane ya rufeta ta d'ora hannayenta saman fuskarta hawayenta yana
cigaba da kwaranya.




Janyota yayi sosai tashiga jikinsa yana dubanta da idaninsa da sukayi wani irin ja, shima kad'an
ya rage yayi kukan yace




"Fatima plss ya isa haka dan Allah ki daina zan iya mutuwa fa kinji yadda nakeji kuwa saboda
wannan kukan da kikeyi?"


Yafad'a tareda kamo hannunta ya d'ora asaitin zuciyarsa.

A firgice ta d'ago rinannun idanunta tana kallonsa, saboda wani irin bugu da zuciyarsa yakeyi
abin har ya zarce k'a'ida, take wasu sabbin hawayamen suka kuma zubo mata.


Hannu tasa itama ta tallafo fuskarshi tana dubansa tace "yayana tabbas kana cikin wani hali
amma kasani ni banyi k'ank'atar da zan kasa gabe halin dakake cikiba yayana, karka manta
kaine d'an uwana wanda nafi shak'uwa dashi kaine mafi soyu acikin 'yan uwana ko Ammar da
Yaseer banajinsu araina kamar yadda nakejinka yaya".

Shiru tayi tareda share hawayen da yak'i tsayaea tun d'azun kafin tacigaba da cewa "yayana ina
tareda kai, duk wani matsalarka nima nawane, dan haka kasa aranka zamu yi maganin wannan
abun da yardan ubangiji, ka daina sawa ranka wannan abun yafi k'arfinka tunda babu abinda
yafi k'arfin ubangiji dan haka mubar masa komai"

Cikin sanyi jiki ya mannawa hannunta da ke cikin nasa wani sassanyan kiss yace "nagode

k'anwatacAllah yayi miki albarka Allah yasa ki gama lafi".



Ranan anan ta wuni wajensa harda Meema da ta nemeta bata samuba tasan tana wajensa
sosai meema tayi mamakin ganin ya d'an saki jiki suna shan hira da Fatima har itama yana sata
aciki.

Kodayake ba abin mamaki bane idan akayi duba da irin shak'uwar dayake tsakaninsu, ita kanta
Meeman saida tabata hak'uri abisa yanda ya rik'ayi mata komai da zafi zafi.


Dake daman Abdul majid mutum ne wanda yake mutuk'a jan nasa ajikinsa.





Talatainin darene misalin k'arfe biyu da kwata naga wani mutum ya tashi daga shimfid'arsa,
saida ya lek'a fuskar matarsa yaga tana bacci hankalinta kwance babu abinda yake damunta.


Cikin d'auke numfashi da sand'a na ya lallab'a yafice daga d'akin a hankali ya maida k'ogar ya
rufe dan kar motsin rufewar ya tasheta.


Cikin gidan nasa naga ya nufi wani lungu mai duhuwa wanda shuke shuken fulawowin wajen ya
k'arawa wajen duhu.



Bayan yayi tafiya mai yawa sosai har yagaji lik'is sannan naga nufi wani k'atoton get mai girman
gaske wanda bud'e shima sai k'arti majiya k'arfi.


Wasu maganganu naji yafara wanda ban fahimci abinda yake cewaba,kafin na ankare kawai
naga get d'in ya bud'e kansa, yana shiga nabi bayansa da gudu sauara k'iris k'ofar ya datse min
k'afa dan yana shiga naga yafara rufe kanshi, shine dalilin dayasa nabisa da gudu.




Wani irin haske nagani tarwai tare da wasu irin kitika kitikan masu wani irin murd'ad'd'an jiki

naga suna ta zarya abakin k'ofar kamar mayuntan zakuna daganinsu k'iris suke jira su dumawa
mutum wawa


Sosai yanayin mutanen zai gurgitaka domin babu alamun rahama a idanunsu bak'i k'irin suke
yayin da idanunsu ya kasance jajur kamar garwashin wuta.





Take jikina yafara rawa amma dan masifa ban fasa bin bayan mutumin danaga wannan
mutanen suna zubewa suna masa sujjada ba innalillahi wainnailaihi raji un.

Wai mutum abokin halitta d'an uwansu sukewa sujjada kai Allah kafisshemu tab'ewa.



Tunbayana tafiya cikin mutane naga yadawo bin hanyar da babu kowai sai uban duhu da lalube
na rik'a bin bayarsa har muka isa wata 'yar siririyar hanya wacce ta mik'e d'od'ar har wata 'yar
k'aramar k'ofa kamar gida mukulli naga yasaka ya bud'e k'ofar ya shiga sannan ya maida k'ofar
ya rufe.

Tundaga tsakar gida na fara ganin gawawwakin mutane abinda ya mutuk'ar firgitani nasaki wani
k'ara ba shiri na toshe bakina nayi wani d'an lungu garin b'uya natake wani abu mai taushin
gaske dake tsabar fitina dazan biyoshi cire takalmana nayi dan kar yaji takun tafiyana yasan ina
binsa, idona na d'ora akan abinda na take me zangani innalillahi wainna ilahiraji un gawar
jaririne wanda da alama ba adad'e da kasheahiba


Kuka na fasheda shi shikenan na kawo kaina inda tawa zai k'are nima.


Tafiya naga mutuimin yaci gaba dayi ya kuma bud'e wata k'ofa mai murfi biyu saiga wani
k'atoton gunki mai siffar mace tsirara yana aman jini yayin da jinin ya malala ki'ina na d'akin




Muje zuwa karku bari abaku labari

Maman islam
[8/9, 3:56 PM] MAMAN ISLAM: *مسب الله نمحرلا ميحرلا *

*☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️*

FCWA

*Home of qualities and trusted writers of the nation*



https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?ty
pe=3&source=45&refid=17

_________________________



��ZATO NE��
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM


DAGA MARUBUCIYAR
ABINDA YAKE RAINA
WAYYO RAYUWATA




Page 5




..................sai yanzu naji mutumin yayi magana da kakkausan murya naji yana cewa, "meyasa
za'amun haka meyasa bafa haka mukayida keba kinyimin alk'awarin duk abinda na nema zan
samu me yasa wannan yake neman gagarana me yasa meyasa????"

Shine abin da naji mutumin yacigaba da maimaitawa, ga mamakina kawai naga wannan
gunkiyar ta bud'e ido al'amarin dayasa naji cikina yayi wani irin murd'a kafin na dawo nutsuwata
kuma saijin muryan nayi kamar da aradu take wani masifaffen futsari ya kubce min sakamakon
jin wannan mugun muryan.


Wani irin murd'awa cikina yaci gabada yi saboda ganin yadda idanun gunkiyar yake balbala da
wuta ci take sosai har tana laso goshin gunkiyar, babu shakka gani da jin wannan mugun abun
saida nasaki gudawa mai k'ara wando wanda badan hargagin wannan mugun halittanan ba
babu abinda zai hana mutumin nan jin k'aran jerin gwanon tusan danake ta b'urkawa saboda
gudawar mai k'arane.



Jinai abin yacigaba da cewa bamu bane bama bibiyan bayanka saboda kanayi mana duk
abinda muka sakaka, kuma muma labari ya ishenu dan haka kaci gaba da bincike mu tuni
namu yayi nisa karka damu bazamu bari acutar mana dakaiba.


Wani irin ajiyar zuciya mutumin yasaki sannan naji yace "nidai banaso asirina ya tonu, nafison
koda asirin zai toni to abari nayi k'arfin da babu wata hukuma da ta isa tajadani".




Jinai mugun halittan yace 'mai lalata maka shiri mafi kusa dakaine idan lokacin kasan kowane
yayi zaka sani"


"Ataimaka abad'amin kozansan hukuncin dazan d'auka akansa domin al'amarin yafara bani
tsoro"


Gunkin yace"kai idan yafi k'arfinka mu kasan baifi k'arfin tsafinmuba, dan duk duniya gunki
d'ayane yafi k'arfin tsafinmu, kuma da sannu zamu had'aka dashi da zarar kagama mana
aikinmu"


Yana gama fad'an haka kirib idanun suka koma yadda suke jinin yaci gabada kwarara, da sauri
naja baya ganin mutumin zai fito.

"Yaya dan Allah kayi sauri kasan gwaggo Hafsatu bata son jinkiri tunjiyafa na bata labarin
munanan tafe ni wallahi na k'agu naga gari tunda mukazofa babu inda nafita ina sank'ame
agida"


Tunda tafara maganan yake bin libs d'inta da kallo yanda take maganar kamar wanda take tsara
abin da salon yanga.


Ido ta hure masa yayi firgigit yana kallonta da ido tayimasa alaman kallonfa?
Sosa k'euansa yayi tareda d'auke kansa batare dayace mata komaiba.



Ganin haka ta kama tsallen shagwab'a tana fad'in "ni wallahi yaya kadena min irin haka sai
magana nake kayi min shiru, saiga hawayen shagwab'a shar shar .



Take ya rud'e ya rik'o hannunta yana fad'in "haba babyna meye haka dan Allah?"

Tace "bakaine ba kak'i kashirya mutafi kasanfa da tafiya daganan zuwa bajoga gashi kuma tuni
azhar ya wuce"


Hannu yasa yana goge mata hawayen tareda fad'in "to ya isa kark8sakani kukan nima maza
jeki k'ara wanke fuskarki ki shafa hoda da jambaki kafin na gama shiyarwa"

Yana gama fad'in haka ya shige toilet yayin da ita kuma ta juya ta fice d'akin kai tsaye bangaren
mammy ta nufa.


Meema ce zaune falon tana ta faman danne dannen wayarta, wani kallo Fatima tayi mata kafin
tace"haba dear wannan wanne irin wulak'ancine kina sane zamu fita amma dubeki dan Allah a
zaune ko shiri bakiyiba?"

Harara Meema ta galla mata kafin tace "wallahi yariyanyar nan baki da kunya ina katsayin
yayarki kikemin fad'a sai kace wata sa'arki?"




Dariya Fatima ta shek'e dashi kafin tace "su yaya manya dukafa wata uku ne tsiranna mu, ai
idan wani yajima sai ya d'auka irin shekara biyunnan kika bani ko uku ni dallah malama jeki
shirya, gayaya can ma yana shitinsa.



Meema tace "nifa babu inda zani bakiga yadda garin yake shan kunuba sanin kankine idan
nafita akayi ruwannan akwai matsala"



Juyawa Fatima tayi ta shige d'akinsu nanan b'angaren tabbas tasan cewa idan Meema ta shiga
ruwa sai ciwonta na limoniya ya motsa dan haka batayi mata gardamaba ta wuce ta hau shirinta


Wani dandatsetden less taka mai mutuk'ar kyau da tsada kalar sky blue ba k'aramin kyau tayiba
ta kafa d'aurin d'ankwali mai kyau da tsari kamar irin k'atuwar 'yar tsanan nan haka takoma
kamanninta da mamatan na balarabiyan asali,ya fito.

Tana fitowa falon dai dai shima ya fito kafeta yayi da idanu babu ko k'ibtatawa yayin da
zuciyarsa take wani irin bugu kamar zata fasa k'irjinsa.



Ita kan meema ido ta kafe ta dashi na kallon,tsabar tsagwaron kyau gaskiya Fatima badai
kyauba Allah ya d'iga baiwarsa anan wajen.



Ganin irin kallon da yaya da k'anwar suke binta dashi yasa ta hau dudduba jikinta ko wani abin
kallonne ajikinta.


Ganin baya ga komai bane yasata tamabayar Abdul majid da ido ko akwai abinda yagani
ajikinta?
Hararan wasa yayi mata sannan yace "gani nayi ko kyau bakiyiba ko k'anwata?"

Ya k'are magananshi da tambayar meema wadda take ta danne dariyanta ganin yadda Fatima
ta had'e rai

Dole tasaki dariyan datake b'oyewa ganin har idanunta yafara cikowa.

A hankali ya k'arasa kusa da ita ya dafa kafad'unta ya d'anjata jikinsa cikin rad'a yace "muddun
kika bari hawayenki ya zubo to babu ke za'ayi tafiyannan.



Kallon Meema,yayi, yayi mata alaman tambaya da ido?



Itama batayi magana ba ta nuna masa sararin samaniya da hannun ta take ya gane me take
nufi dan haka bai k'ara maganaba yaja hannun Fatima suka fice suka nufi d'akin mammy.


Sallama sukayi mata, ta d'an dubeau tace yanzu bazaku bari kuga yadda garin zayi ba
awannan uban hadarin zaku fita?"





Da sauri Fatima tak'arasa gabanta tace "dan Allah dan Allah mammy wallahi tafiya a'irin
wannan weather yafi dad'i"



Mammy tace "to sikenan Allah yadawo daku lafiya, hakama ummi tace musu anan dai Abdul ne
yayi magana ganin Fatima ta damu da tafiyar.


Ganin yadda garin yake dad'a murtukewa yasa Fatima shiga d'akinta tad'ebo kaya kala biyu
tasaka awata 'yar madaidaiciyar jaka.



Dazasu fitama dagewa tayi itace zata jasu, dole Abdul majid ya zauna faront seet ita kuma ta
zauna a mazaunin draiver tayi mata key ta figa da gudu suka fice agidan.

Kasancewar batasan gariba shi ya rik'a nuna mata hanyar yayin da ita kuma take falfala gudu
abinta kasancewar basubi ta babban titiba yasa bata sami matsalan cunkosoba.




Suna tafe suna hira idan yaga zata kauce hanya yayi saurin seta mata jar suka bar cikin gari
suka fara shiga daji daganin yanda take tuk'in cikin k'warewa kasan cewa ta hana dad'e da iya
tuk'inta.



Wani irin hadarine ya dad'a tasowa bak'i

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login