Showing 21001 words to 24000 words out of 65710 words
Chapter 8 - ZATO NE (1 TO End) BOOK COMPLETE By Maman Islam.pdf
abinda yake fad'aba.
Yajima yana kuka kafin yayi dabarar zuwa ya had'a ruwan wanka ya tsarkake jikinsa sannan
itama yazo ya d'auketa ya sakata a ruwan wata irin ajiyar zuciya ta sauke da k'arfin gaske kafin
ta fara fisge fisge tana surutai.
Menayi muku me mukayi muku kuke binmu dan Allah kuyi hak'uri ku k'yalemu muyi rayuwarmu
me kukeso me kuke nema awajenmu.
Sosai take surutai da k'yar yasamu ya gama mata wankan sai dai babu damar tsarkake mata
jikinta tunda dole sai tayi niyya dan haka ya nad'ota atawul yadawo da ita d'akin yana cigaba da
tofa mata duk addu'ar datazo bakinsa
Plss manage
Taku maman islam
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا رلا ميØ
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
Gaskiya inaji da ku masoya ina mutukar alfaharida ku,
Ammin sadik
Ummu thurab
Adama Aliyu
Bint muhammad
Maman meemat
Tareda sauran wanda ban ambataba ina godiya kwarai Allah yabar kauna bisabilillah
Ummukhaleel alherin Allah ya isar miki aduk inda kike ina gaidake tareda khaleel da khairat
My princess yakike ya rikici gaskiya tsufa yasakaki rikici dayawa princess Aishatu
Allah yabar zumunci
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
DAGA MARUBUCIYAR.
ABINDA YAKE RAINA
WAYYO RAYUWATA
Page 11
..................wata irin ajiyan zuciya ya sauke kafin yace "shikenan Fatima tunda kikace haka
amma fa inaso kisani daga yau baccinki ya k'are baki da wata nutsuwa tunda kika amince da
wannan auren to wallahi babu ke babu ke babu farin ciki.
"Humm yaya kenan ba'ace zan aurekaba ana bina ana firgitani bare yanzun,kuma nafika sanin
wannan kuma nagama yarda ni yanzune ma nafarjin duk duniya babu wanda yakaini k'aguwa
ayi auren dan haka kasa aranka cewa Fatima bata maka so irin na aure amma zata aureka dan
haka karka wani damu zanga tsinannen daya hanaka samun salama arayuwarka"
Daga haka bata k'ara cewa komaiba ya taida idonta kan hanya.
Shiko bansan mai yasaba sai yaji sam baiji dad'in kalmarta ta BANA MAKA SON IRIN NA
AURE.
Wannan kalma yaji d'acinta ba kad'anba kallonta kawai yake yakasa d'auke idanunsa akanta shi
yarinyarma duka mamaki take bashi yanzunefa take shiga shekara 17 amma take iya fad'a
masa wannan maganar agaskiya abin ya masa ciwo.
Har sukaje suka dawo babu wanda ya kuma tankawa d'an uwansa sanda sukayi perking har ta
kama k'ofar zata bud'e yace "bakijiba" fasa bud'ewar tayi ta gyara zamanta yayin da tuni
meema ta wuce abinta.
Dubanta yake da mamakin yadda take ta wani cin magani wani murmushi yayi mai ciwo sannan
yace.
"Wane shirin kukeyi ne kinga abin yana ta matsowa dan haka kiyi maganar abinda kuke da
buk'ata kafin lokaci ya k'ure "
Kallonsa tayi kafin tasaki wani malalacin murmushi tace "yaya kenan wane shirine ga mutumin
da k'afarsa d'aya take alahira d'aya a duniya?
Ai kawai ina ganin kafara lissafin sauran rayuwar data ragewa Fatima aduniya bawai wani
shagaliba, nifa wannan auren zanyi shine kawai dannasan yazama dole ayishi tunda mahaifina
ya furta amma badan hakaba idan ka tona,zuciyata kamar gawayi take saboda tsabar yadda
nake k'in abinnan araina"
Kallonta kawai yake zuciyarsa na masa wani irin suya shine yau Fatima take gasawa magana
irin haka l?
Lallai duniya nakama kenan saboda wata lalura ta sameka shima yana gudunka ina kuma ga
bare wanda bai had'a komai dashiba.
Yana kallo har ta bud'e motar ta fice bai iya k'ara cemata komaiba.
Tana shiga falonsu ummi ta kirata tareda mika mata wani rubutu a d'aure aleda tace "kiyi
bismillah kisha daga tsaye sannan ki wuce kiyi alwala kizo kiyi sallah Abbin ki yace yau k'arfe
uku me miki gyran jiki zatazo"
K'ure ummin tayi da ido saisai zuciyarta na bugawa kafin tace "ummi nifa babu wani shiri da
zanyi auren da babu wata soyayya acikinshi ta ina zaiyi armashi?"
Ummi tace"ai kuwa gyara ya zama dole Fatima kowace amarya ko ta wasan yarace ana
gyarata bare kuma ta d'an mutum dan haka kawai kije kiyi abinda nasakaki"
Jiki a sanyaye ta sha rubutun ta wuce d'akinta.
Umma ce da Anty Ruk'ayya zaune afalon umma Anty Ruk'ayyance ta dubi umma tace" kinga
irin abinda nake fad'a miki ?ko dama saida nace miki may be idan aka had'ashi da yaran
gidannan babu abinda zai faru kik'i yarda kikace ke ba hakaba yanzu gashi za'ahad'ashi da
wannan nunar ranan kuma shiru kakeji babu wani alamu na tashin hankali atareda su yanzu
gashi munaji muna gani wannan dukiyar zaiyi mana nisa"
Umma tace " ke dalla malama ki rufemin wannan k'azamin bakinnaki anan ke k'aramar
yarinyace da bakisan komaiba, ina so ki bud'e idonki sannan ki kasa kunnenki kiga abinda zai
faru idan anyi auren an fad'a miki wanine daban yake bin Abdul majid? to shida kansa yake
shanye jinin duk yarinyar dayake nema,ance miki wannan dukiyar nasu na banzane idan kuma
ba hakaba ai akwai baby meyasa baki bashi itaba ainagama ta girmi Fatima.
Anty Rukayya data gama tsorata tace "a a umma ai bansan haka abin yakeba wallahi nidai
babu ruwana dan Allah mubar maganar iya nan"
Wani muemushin samun nasara umma tayi sannan tace"to dama Rukayya ai wannan ba
maganar yad'awa bace amma kisa ido sosai zakiga abinda nake fad'a miki"
Sosai anty Ruk'ayya ta tsorata jiki na tsuma tafice daga sashin umma, yayin da umman tabita
da wani kallo tana wani shu'umin murmushi.
"Alh na fad'a maka yadda ka lalata maganar nan maza kaje ka gyarata da kanka kabasu hak'uri
sannan ka tabbatar musu da cewa maganar aure tanan kamar yadda aka tsaida ita"
Dubanta alh yayi yace "dan Allah haj kibar maganar nan alh Galinefa yacemin yaron d'an
mafiyane kuma yace shi da kansa yake tsotse jinin,duk matar da ya nema da nufin aurenta"
Wani banzan kallo naga haj. Kulu tanayiwa alh, kafin tace "shi alh, Ghalin indai batare suke
hark'allar da yaronba ta ina yasan wani Abdul majid bare yasan cewa shi d'an mafiyane zaka
tashi kaje kanemi afuwarsa asasanta maganar ko saina yimaka rashin mutunci"
Jiki na rawa alh. Sambo ya mik'e yana fad'in " yadda kikeso haka za'ayi hajiya bari naje na isar
da sak'nki"
"Kuma kwantar dakai zakayi ka nemi afuwarsu karka sake naganka anan batareda ka daidaita
komaiba"
Yace "angama hajiyata"
Daga haka ya fita cikin takaicin yadda haj take masa wanda Allah ya jarabceshi da tsananin
tsoronta.
Agidan Alh. Yusif kuwa da k'yar suka hak'ura da batun dan harda kuka saida alh. Sambo yayi
dan yana tsoron masifar haj. Kulu matuk'ar ya koma mata batareda an sasanta wannan
maganar ba.
Saida Amma da Abbi suka sa baki anan Abbi yake sanar musu da cewa yayi istuhara aurennan
shima dole ayi dan haka kawai su hak'ura kawai a had'a dana Fatima.
Gidan alh. Sambo kuwa yana fita naga wannan mutumin mai zuwa wajen gunki ya ahigo gidan
bak'aramin jijjiga nayi daganinsaba araina nace meye to had'insa da alh. Sambo kodai da gaske
alh. Sambo abokinsa ne ko kuma tare suke k'ulla hark'allar tasu?
Wani irin ciza na gantsarawa yatsana ganin har sun gama maganarsu da haj. Kulu yafito
batareda na saurari maganar da suka tattanaunaba ina can shashancin tunanin abinda ya
kawoshi.
Bayan sati d'aya, sosai Fatima tayi wani irin fitinannen kyau naga tayi saikayi dagaske zaka
ganeta saboda yadda gyaran ya amsheta gaba d'aya ta canja.
Su meema,kuwa shiri suke sosai duk dacewa har lokacin jikin iyayen angon asake saboda
tsoron abinda zaije yazo wannan ne karon farko daza afara aurar da yaran gidan duk da
kasancewar ayanzu Abdul majid yana da shekara talatin da uku cif aduniya.
Ab'angaren Yusra kuwa rankai ba magana sosai take shiri domin ba k'aramin so takewa Abdul
majid ba tana sane sarai dacewa bin na mutum biyune tabar hakan a zuwan saita shiga gidan
zata d'auki mataki kuma tasanarwa Abdul majid cewa yazama dole ta kasance a uwar gida
tunda itace yafara cewa yana so.
Shi kam sanda take wannan batun murmushi kawai yayi dan ya riga yagama yankewa waye
uwar gida waye kuma amarya.
Yauma bai yardaba ya kuma komawa wajen boka duba yace "bikin 'yar abokina sai dad'a
matsiwa yake nace ka dakatar kak'i ko?
Wallahi duna zanyi maganinka ne"
Wata irin dariya naga bokan ya shek'e sannan yace "Ak'ilu kenan ai yanzun wuyana yayi kauri
na wuce tunaninka nayi k'arfin dabaka isa kaja daniba idan kuma kana da ja bismillah, kai
banda kai wawane kayimin sanadin tilon 'yata kayi tunanin zan k'yakeka?
Ina nan shirin ta yadda zanyi maganinka lokaci guda kai kana gudun akashe 'yar abokinka
wanda azahiri ninasan dalilinka akan hakan ka zuga uban 'yar kuma sai akayi dace shid'in
lusarin na mijne, mijin hajiya ko?inanan dawowa kanka" boka yafad'a dawata irinkakkausar
murya ya b'ace ba't yabar alh. Ak'ilu da kuka wiwi da idonsa,
Muje zuwa
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا رلا ميØ
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
WRITTEN
BY
MANA ISLAM
Page 12
.....................yajima sosai awajen cikin tashin hankali sosai yaci kukansa ya godewa Allah
sannan ya mik'e ya nufi gidansa firkai firkai dashi.
Lokacin da yashiga hidan matarsa tana saman kujera hankali kwance tana cin fruet bazaka
tab'a gane yanayin da take ciki na dad' ko rashinsa, ganin yanayin da mai gidan ya shigo
matane hankali atashe ta wani tab'e baki tacigaba da abinda takeyi.
Shi kuwa bai kula ma da ita awajenba ya wuce mugun sauri kamar zai tashi sama ya bud'e
d'akinsa ya maida taciki ya rufe da key jab'ar yayi abakin gado yana kuka wurjanjan kamar wani
k'aramin yaro.
Can kuma kamar wanda aka tsikara naga yayi wani irin tashi tsaye ya nufi gadonsa a haukace
yafara sauke katifar saman gadon sannan ya d'age karagar ya d'age capet saiga wata 'yar kofa
ta bayyana kamar rijiya yana 'bude k'ofar ashe matattakalane aciki, kawai ya shige ciki da
mugun sauri.
Abdul ne zaune a office d'insa babu abinda yake damunsa sai irin maganganun da Fatima ta
gaggasa masa wanda bai tab'a damuwa da al'amarin waniba sai ita kwarai abin yatsaye masa
arai.
Mammy kuwa da kanta ta d'auki wata shak'ik'iyar k'awarta suka had'o lefe na gani abada labari
kayane masu matuk'ar kyau da tsada duka su biyun akwatuna sha biyu akayi musu saidai
kayan Fatima sunfi na Yusra yawa.
Sosai ummi take taya mai gyaran jiki kula da 'yarta gashi ta b'angaren malam ma,ba azaune
yakeba kusan zan iya cewama bashi da lokacin kansa saboda yadda ya maida hankali wajen
son ganin yakamo bakin zaren abun.
Ab'angaren Yusra kuwa kanta ba k'ramin rawa yakeba shiri take sosai na bikin fati kusan kala
hud'u tq shirya wanda Abdul ya tabbatar mata da babu d'aya da zai hallata.
Haka dai biki yacigaba da matsowa duka b'angarorin biyu sunata shirye shirye yayin da d'aya
b'angaren basu da nutsuwa ko ta sisin kwabo domin bazasu manta da Salma ba d'iyar gwaggo
Hafsatu wacce itace mace ta k'arshe da suka kasge shekara biyu daya wuce kisan wulak'anci
sukayi mata kisan gilla domin gunduwa gunduwa sukayi da gab'ob'inta a tsakiyar gadon
mahaifiyarta abinda ya girgiza familynta wanda shi kansa Abdul saida yafi watq agqdon asbiti
domin har ga Allah yana mutuk'ar son Salma saboda itad'in mutum ce mai shiga rai saboda
mutuk'ar hak'urinta da hankalinta.
Ab'angaren su umma da anty Rukaiyya kuwa tun ranan da umma,tace mata Abdul da ubansa
ne suke kashe 'ya'yan mutane dan zalunci yaran da basujiba basu ganiba tayi mugun saka ido
akan takun kowa nagidan duk abinda taga bai mataba take yi mugun sa ido akai.
Meema ce ta ahigo b'angaren ummi cikin kwalliya sosai da alama wani wajen zataje, afalon
k'asa tasami ummi tana sharan falon tace "ummi ina Fatima take?"
Ummi tace " humm 'yar rigimana zakice yanzun muka gama da ita akan shan magani ayi
yarinya bata k'aunar magani kwata kwata"
"Bata da lafiya ne?"
"Tun jiya take fama da ciwon kai jiya da darema saida mukaje asbiti"
Da gudu meema ta haye saman, akwance tasameta asaman gado tana wani irin juyi asaman
gadon kanne yayi mugun matsanta mata.
Da sauri meema tak'arasa kusa da ita ta rik'ota hankali tashe tace "dear me yake damunki
haka?"
Da k'yar Fatima ta d'ago kanta ta dubi meema tace "dear kije Abbi yana d'akinsa dan Allah kice
yabaki wannan man zan shafa kaina cirewa zaiyi wayyo,Allahna"
Ai da gudu meema tayi d'akin Abbi ta karb'o man tazo tad'agota jikinta ta hau shafa mata man
agoshi tanayi tanayi mata tofin addu'o'i ganin yadda take zabura.
Cikin irin yanayin aka shiga shagalin biki wanda kafin lokacin saida akakai Fatima,asbiti kusan
sau uku bareda Abbi yq bari mahaifiyarsa ko 'yan uwansa sun saniba.
Ansha shagali sosai duk da cewa Fatima daurewa kawai take kamar babu abinda yake
damunsu suka gudanar da shirye shiryensu taro yawatse lafiya
Ranan juma'a akakai Fatima yayinda sai ranan asabar akakai Yusra wannan kuma duk tsarin
angone.
Dake tare suka kwana da su meema,koda wasa bataga k'eyar angonba kuma hakan bai
dametaba sosai su meema da su husna 'yan uwanta suka d'ebe mata kewa.
Abdul majid kuwa duk abinda yake faruwa agidan bai saniba saboda baima je gidanba tunda
aka kai amaryar hankalinsa a mutuk'ar tashe yake saboda tsoron abinda zaije ya dawo.
Yaune karo na farko da aka k'addamar da bikin aurensa har amarya ta tare agidansa batareda
wani abu yasametaba duk da cewa itama d'in bawai sun k'yaletaba ne yasani sarai akwai shirin
da koma waye meson ganin ya kassara masa rayuwa.
Sosai abin yake damunsa yarasa ta yadda zai fara abin har yanzu Jamil baizo ba Jamil wani
abokinsa ne wanda tare sukayi karatun gaba da primary sosai Abdul suka shak'u da Jamil
wanda har yakai gidajen biyu suna zumunci adalilin abotarsu.
Cikin yaran da suka mutu akwai k'anwar Jamil Zulaihat wanda itama bak'aramin tashin hankali
daginta suka shiga ba domin Zulaihat salihar mace ce
Kwance take saman gadonta tana kallon saman sillin tunanin yadda zata b'ullowa al'amarin
takeyi idan taga kamar cewa ta samo mafita sai komai ya wargaje tarasa wane bakin zata kama
daga cikin zarurrukan datake kullawa aninne yake neman zarta tunaninta.
Itama Yusra saida nata dangin suka kwana dan haka suma sai lahadi aukabar gidan tareda su
meema gaba d'aya.
Zaune take gefen gadonta zuciyarta na wani irin bugu sai faman murzar hannunta da yasha jan
lalle shar dashi take duk da kasancewar tanajin zafin yadda take murza hannun amna bata
fasaba yayin da zuciyarta yake wani irin bugu jikinta yake karkarwa.
Batasan da me zata faraba batasan abinda zai faruba shin da gaskene bin matan da Abdul
majid yake aure ake ana kashewa ko kuwa wa'adinsune yayii?
Wannan sune tambayoyin data kewa kanta wanda amsarsu ya gagareta
Wannan shine abinda ayanzu ya zauna zuciyar Fatima takasa cireshi takasa samun koda
meema ce suyi shawara akan hakan domin Abbi yace wannan sirrintane tabarshi tsakaninta da
mahaliccinta da sannu Allah zai yaye mata hijabin dake tsakaninsu.
K'amshin turarensa ne yayi mata sallama tayi saurin d'agowa tareda lumshe idanunta saboda
wani irin bugu da zuciyarta yakamayi da mugun gudu tayi saurin maida kanta k'asa tana sauke
b'oyayyar ajiyar zuciya.
Kusa da ita ya zauna yakamo hannunta ya rik'e anasa yana so su had'a ido tak'i bashi damar
hakan ya d'an lek'a fuskarta ba k'aramin fad'uwa gansa yayiba ganin yadda idanunta sukayi
wani irin ja.
Hannu yasa ya kamo fuskarta ya tsura mata ido kusan minti biyu ta lumshe ido ta bud'e
hawayen datake ta k'ok'arin dannewa suka sulalo cikin rashin jin dad'i yace" Allah yasa bagani
nane yab'ata miki raiba har kikemin asarar tsadaddun hawaye"
Jasa kallonsa tayi zuciyarta har lokacin bai daina dukan,tara taraba sosai taji tsoron kusancinta
dashi ayau.
Kafin ta ankare ya had'e bakinsu waje d'aya yana mata light kiss sosai jikinta ya kama wata irin
rawa take hawaye ya zubo mata.
K'aran bud'e kofar ne ya k'waceta daga hannunshi, gaba d'aya suka maida hankalinsu bakin
k'ofar Yusrace tsaye sanye.
Kash kuyi afuwa yauma saida muka koma asbitin yasiní ½í¸Œí ½í¸Œ
[10/7, 5:03 PM] Maman Islam: مسب الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا رلا ميØ
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
ZATO NE