Showing 9001 words to 12000 words out of 65710 words
Chapter 4 - ZATO NE (1 TO End) BOOK COMPLETE By Maman Islam.pdf
tana tura masa flat d'in abincin data zubo masa, saida yayi bismillah yafara
cin abincin dan yunwa yakeji sosai Fatima bata bari sunyi karin kumalloba ta uzzura masa suka
taho.
Duban mammy yayi yace "tana fat d'insu dan ko kari bata bari munyiba tace ita gida zata tafi"
Nan kuma ya kwashe duk abinda yafaru a hanya ya fad'awa mammy, bak'aramin girgiza tayi
dajin wannan abinba tabbas duk ma wanda yake bin baya d'annata baizai denaba ya zama dole
ta fad'ima Abbu dan tasan tabbas zai iya bada taimakon daya kamata.
Abangaren Fatima,kuwa saida tayi sallah sannan tayi wanka,dake sanda ta shigo gidan anriga
da antada sallah.
Bayan ta shirya cikin wasu riga da sket 'ya kanti kalar blue mai duhu sunyiwa jjar fatarta kyau
sosai.
A falo tasami Umminta tana cin Abinci kusa da ummin ta zauna tagaida ita sannan taja abincin
yayinda ummin take tambayarta yanda ta barosu.
Tace "duk suna lafiya ummi tace agaidaku, ummi ta d'an k'ara kallon 'yar tata da kyau ganin
yadda ta zuk'e lokaci d'aya tace
"Ciwo kikayi ne adaren jiya naga kin zuk'e?"
Ajiyar zuciya Fatima tayi kafin ta dubi ummin da idanunta da har sun,ciko da kwalla take abinda
yafaru yafara dawo mata kamar yanzune abin yake faruwa babu 'yar b'oye b'oye tsakainta da
umminta take ta kwashe duk abinda faru ta fad'awa ummin, wanda itama ummin bak'aramin
girgizata abin yayiba karfa kuma wani abu yasami tilon 'yar tata dan tanada kusanci da Abdul
majid?
Ai kusancin su ba aure bane kuma ko Abdul majid yace yanasin Fatima,bazata tab'a amincewa
ba dan,abinda ta lura dashi duk wanda zai mu 'amalance shi koda da soyayyane sunan shi
gawa.
Wannan kenan
Ab'angaren mutuminnan kuwa tsaye yake gaban gunkiyar nan yau idanunta har ya wuce
rannan haka duk wani k'ofa najikinsa babu inda baya kwarar dajini.
D'ago wutar dakeci a idaninta tayi naga ta kalli mutumin wanda duk ranar datayi hakan mutum
ya b'ata mata rai kuma wannan kallon shima azaba ne dan mutum zaiji ajikinsa.
Jinai tana magana yau kuma da muryan jarirai tace "wayace kabita kanason lalatama aiki
bakasan cewa idan ubanta yasan kana bin ta sai ya kawo k'arshenkaba? dan mudai munriga da
munfi k'arfin duk wani mai shiri akanmu"
"Kar ka sake binta lokacin baiyiba idan lokacin yayi dakaina zan d'auko ta domin muna
buk'atarta dan gudanar da wani gagarun shiri amma,ba yanzuba da sauran lokaci
Daga haka ta rufe idanun tana hawayen jini,alamun tagama,bayaninta.
Gani nayi wata irin iska tayi watsi dashi bai fad'i a ko inaba sai bakin falon gidansa, wannan
shine hukuncin duk wanda ya sab'a umarninta
A sume yake tun bayan sa adda wannan aba ta watso shi bashi ya farkoba sai bayan da iskar
asbah ya hurashi.
Da sauri ya tashi yashige d'akinsa duk jikinsa babu inda baya masa ciwo bin matarsa yai da
kallo wadda bata san mai yake faruwa toilet ya shige yayi wanka da ruwa mai mugun zafi wai
ko zaiji dad'in jikin sannan ya d'auro alwala yazo yatashi matarsa sannan shi kuma ya wuce
masallaci.
Abinda zai baka mamaki shi wannan mutumin mutumne mai mutuk'ar sadaka da kyauta sannan
ga taimako gashi babu wani lokacin salla dayake wuceshi
Tun ranar da Fatima tabawa umminta labarin halin data tsinci kanta aciki ta gargad'eta kan
cewa ta fita a hanyar Abdul majid babu ita babu shi idan ba haka ba itama zatabi sahun
matattun 'yan matansa.
Ita Fatima sam ta manta da wannan abin saida ummin ta fad'a sannan ta tuna da yake babu
abinda Abdul majid ya b'oye mata na abinda yake faruwa .
Duk da cewa taji tsoro sosai amma ranta bataji kamar cewa zata iya rabuwa dashiba domin
shid'in d'an uwanta ne kuma jininta
Dan haka rabata dashi cikin sauk'i ba abune mai yiyuwaba, abinda ta nunawa umminnata
kenan kuma hakan baima ummin dad'iba saidai bata k'ara ce mata komaiba gudun kar Fatima
tayi tunanin ko batason alak'arta da d'an uwantane kamar yadda Fatiman tayimata ba haguwar
fahimta.
Wata ranar juma'a Fatima da meema suka shirya zasuje kasuwa siyayyan kayan kwalliya da
wata babbar super market da akeji da ita a fad'in gombe da kewayenta.
Har sun fito saiga Abdul wanda shi tun bayanda ya dawo daga masallaci bai shigo gidanba
yana tareda abokinsa Yasin kallo yabisu dashi kafin yace "ina zakuje haka?"
Fatima tace "kayan kwalliyarmu sun k'are kasan next week zamu fara zamu fara zuwa school"
D'an had'e rai yayi yace "kwalliya zakuje kenan ba karatuba harda wani cewa kayan kwalliyarku
ne ya k'are"
Ya kwaikwayi yadda Fatima tayi magana "to ku koma babu inda zakuje" yafad'a cikin rashin son
wasa fuskarnan a had'e babu shiri suka juya ganin yadda ya had'e gira Fatima harda kwallan
takaici dan tun bayan zuwnsu yaune zatayi fita na biyu dayake gidanma ba wani yawan fita
suke ba inba da kwakwaran daliliba.
Da dare suna falon Amma duka yaran gidan gaba d'aya hayaniyarsu ya hana Amma sakat
maganar duniya idan tayi idan sukayi kamar sunyi shiru sai su kuma kaurewa dan dole tasa
musu ido tana kallonsu wani abin idan sunyi su bata dariya wani kuma tayi tsaki.
Ammar ne k'aninta ya shigo da d'an gudunsa yace anty Fatima yaya Abdul yana kiranki yana
b'angarensa.
Yana gama fad'a mata ya juya da gudu ya fita, itako Fatima cigaba tayi da uzurinta domin har
lokacin takaicin hanasu fitan dayayi bai k'yaletaba.
Sai da Amma ta kuamayi mata magana sannan ta mik'e tana zumb'urar baki, yayinda su
meema suka kwashe da dariya gamida tafawa.
Irindai shak'iyancin nan na 'yan mata, falonsa ta sameshi dagashi sai 'yar farar singlet da tree
queter da robar ruwa hannunshi yanasha.
Tana shiga ya mik'o mata ruwan hannunshi ta karb'a ta nufi frij zata ajiye, a hankali tajiyo
muryarshi tana kallonshi da mamaki, a ranta tace ji mutum saikace nace masa ina jink'ishi da
zai wani bani ruwa.
Kamar yasan abinda yake ranta yace "inbazki shaba bani abina"
Ta kuwa mik'a masa, ganin haka ya had'e rai yace "sha kona b'ata miki rai" kallonsa take da
tsabar mamaki, amma ganin babu alamun wasa atareda shi yasa ta sha ruwan.
Sannan yace tashiga d'akinsa akwai ledoji ta d'ebomasa tashiga, ledodin wajen da sukayi niyar
zuwane ya hanasu manya har guda uku,
Ta kawo gabansa ta ajiye yaja yafara bud'awa sannan ya d'aga kai ya subeta tana tsaye akansa
kamar wata 'yar sanda "zaune mana karki fad'omin aka"
Zama tayi tana wani ciccin magani shi wallahi ma dariya tabashi yadda take wani muzurai
kamar zata saka masa duka.
Kallonta yayi yace "matso kiga kayan da nasiyo ko sunyi muku"
Cikin d'auke kai tace "nifa dama nafasa siyayyar nan kawai kaba meema ko ita tana buk'ata"
Kallonta yayi cikin had'e rai yace "wato kema zaki koyi raini ko ta d'auka i dan kin fita sai ki
zubar.
Nifa nac..........wata tsawa ya buga mata wacce take jikinta yafara rawa da gudu ta d'auki kayan
zata fita batareda ya nuna mata kayan yadda sukeba.
Cikin daka tsawar yace "na fitar miki dana kowane 'yar rainin hankali da gudu ta dawo kawai
tayi tuntub'e da roban ruwan data ajiya saigata ta fad'a masa duk ya rikitata da madifarsa kawai
sai tafashe da kuka
Taku maman islam
[10/6, 6:57 AM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 38
...............lokacin daya shiga har Abbi ya gama shirinsa na tafiya office, ganin d'an uwan nasa
kamar baida nutsuwa yasa ya fasa fitar yaja shi falonsa suka zauna yana dubansa da kulawa
yace.
"Dan uwana lafiya naga kamar kana cikin damuwa?"
Wata irin ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "Abubakar niko na tambayeka mana?"
"Ina jinka Umar Allah dai yasa lafiya dan naga yanayin ka kamar da wani abun da yake
damunka?"
"Akwai"cewar Umar "akwai yaya amma kafinan ina son insan irin marakin daka d'auka akan
lamarin Abdulmajid da kuma abinda yake faruwa?"
Wani irin murmushi Abbi yayi mai ciwo tunowa da yayi da Yusra da abinda yafaru da ita aransa
yace lallai Allah Allah ne idan yai duba da inda yamai da hankalinsa yake neman hujja akan
abin sai kuma abin ya fito ta wani yankin da ban.
Ya d'an dubi d'an uwan nasa yace "Umar abinda ya faru shine ni ina zaton wuta a mak'era sai
kuma na ganta a masak'a abinda nake nufi anan shine wanda nake zargi akan wannan matsala
da ban wanda kuma suke bayyana da ban kaga ikon Allah da kuma k'arfin da addu'a yake
dashi ko? Na sani Rukayya ta fad'a maka abinda haj. Asma'u ta aikata da kuma dalilin mutuwar ta nasan
taga komai, abinda nake so da kai Umar ka kwantar da hankalin ka wannan ba komai bane a
cikin iko da kuma k'udura na ubangiji kaga sai tona aairinsu yake dan haka d'an uwana kayi
hak'uri kaga sarautar buwayi gagara misali.
Acan gidan boka duna kuwa bayan ya d'auke kan haj. Kulu dan yaga nema take ta jik'a masa
aiki shi yasa yaga gwara ya gama mata aikin kafin shi ta tozar ta shi.
"Yaya danAllah ka temaka ka kaini gida kaga bikin Meema sai matsowa yake gashi har yau ban
samu mun tattauna akan komai ba" ta fad'a tana zama ajikin sa d'an janta ya kumayi ya had'e
bakinsu saida ya d'an jima yana kissin d'inta kafin ya dubeta cikin d'an damuwa yace.
"Wai dan Allah Fatima mai yasa bakison zaman lafiya ne?
Na fad'a miki na kuma gaya miki zuwanki gida akwai matsala Abbi yace duk randa na,kaiki
daga ranan kinyi ban kwana da duniya domin yanzu shirin da akayi akanki ta hanyar zuwa
gidankune kawai zaiyi tasiri akanki dan haka nake so dan Allah kiyi hakuri ki rufamin asiri domin
duk ranan da akace babu ke to ki tabbata nima zan biyoki domin kece mahad'ina.
Muje zuwa
Maman islam
[10/6, 8:13 AM] Maman Islam: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*
ZATO NE
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI
STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM
Page 39
........................cikin sanyi jiki Umar yace "wannan wane irin abune? Abubakar wane irin
jagwalgwalo ne haka me Asma'u tanema ta rasa menene yaya baya mana da har zata dinga
jifansa da sharri kala kala?"
"Nima ban saniba Umar amman dai abinda na fi zargi shine son zuciya ne da kuma son abin
duniya wanda ya ke kai mutum ya baro, yanzu duniyar nan ta lalace Umar domin kowa idanun
sa ya rufe so yake ko ta halin yaya sai yayi kud'i kaga wannan burin shi yake haukatamu"
"To wai su waye sauran da suka had'u da ita Asma'un har suke neman kassara rayuwar d'an
uwanmu?"
"Kar ka tsawaita bincike Umar domin hakan bazai haifar da d'a mai idoba sannan kuma ina so
in sanar da kai cewa kabi a hankali kuma kasani da kad'an kad'an yafi maka sanin ko waye
domin sanin hakan lokaci d'aya zai iya zama ajalinka zaka iya tafiya wajen aikinka kuma bance
kaje kayi ta tunani ba"
Cikin damuwa da tashin hankali Umar ya koma b'angaren sa har lokacin Rukaiyya tana inda ya
barta, k'arasawa yayi ya zauna kusa da ita ya kamo hannunta ya rik'a gam kafin yace "Ummu
Ihan ko zaki iya fad'a min sauran mutanen dake tare da haj. Asma'u?"
Girgiza masa kai tayi sannan tace"a a ni babu wanda na tab'a gani tareda ita, abinda na sani
kawai shine duk sanda taso magana da abokan aikin ta to zata d'auko wani k'warya ak'ark'ashin
gadon ta mai d'auke da jan k'yalle da kuma bak'i da wasu tarkace wanda bana gane ko
menene, sannan daga ta bayan madubin ta akwai wani abu wanda da shine take ganin duk
wanda take so kuma taje duk,inda takeso asanda taso batareda ta fice anga fitar nata ba, sai
dai Baffan Ihan ina so kasan cewa da akwai wani shak'ik'in d'an gidan nan da suke k'ulle
k'ullensu tare"
Daga haka ta tashi tabar masa wajen batareda ta jira cewar saba, yana nan zaune kamar
wanda aka dsa kusan mintuna sha biyar wayansa yayi k'ara batareda ya duba yad'aga "Ihsan ta
shirya zasuje rugan yaya Tanimu" daga haka ya datse kiran batareda ya jira cewar saba,
Ruk'ayya ya k'walawa kira tana fitowa ya fad'a mata sak'on ta d'anyi jim cikin shakka yace "nima
daga sama naji dan haka kawai kibisu da addu a"
Tace "wallahi Baffa ina matuk'ar tsoron fita dasu Abdulmajid domin wannan azzaluman kamar
wanda ake sanar dasu duk sanda zasu fita sai sun sa an tafka babban asara"
"Karki damu ki barma Allah komai sai kiga ya duba mana"ajiyan zuciya ta sauke tace "to ai
shike nan bari naje na fad'a mata" yace "yauwa Allah yai muku albarka ya kare minku daga
dukkan sharri"
Amin tace tana ficewa daga d'akin.
"Baby yau zamuje rugan kawu Tanimu maza jeki shirya m" Abdulmajid ya fad'awa Fatima yana
shigewa toilet, da gudu Fatima tayi d'akin ta cikin k'ank'anin lokaci tayi wanka ta shirya cikin riga
da zani na atamfa tayi kyau sosai, sanda ta fito har shima ya gama shirinsa yana zaune cikin
kujera yana faman danne dannen wayarsa.
K'arasowa tayi ta shige jikinsa tareda kwantar da kanta ak'irjinsa tace "baby na shirya" d'an
shafa kanta yayi yace "to zafa mukai sati acan kije ki had'a kayanmu kuma har da Ihsan
zamuje"
Cikin wani irin farin ciki tayi saman da gudu domin tana matuk'ar son rugar kawu Tanimu yana
mata dad'in zama sosai tana shi'awar kiwo sosai ad'an zuwan da suketi kafin su dawo duka duk
zuwa sai Abbi ya kawosu har umminta,
Binta yayi da kallo har sai data gama shigewa sannan ya d'auke idonsa tare da sakin murmushi,
Allah yasani yana matuk'ar son Fatima da komanta mai ban shi'awa.
Bata jima da shigaba Ihsan ta iso gidan itama cikin shirinta dan haka Fatima tana saukowa suka
fito parking space, har ta mik'a hannu da nufin amsar mukullin sai kuma tayi saurin janyewa
tareda komawa gefan Abdulmajid wanda ya bita da kallon mamakin abinda ya hanata amsar
car key d'in,
Ihsan ya mik'awa mukullin tareda fad'in "to ke amshi kijamu" cikin alamun tsoro tace "nifa yaya
hannu na bai gama fad'awa ba" d'an murmushi ya saki kafin ya kira Idi draiver suka
kama,hanya.
"Abu Fatima dan Allah ka maida ni k'asarmu ni wallahi garin nan ya isheni duk a tsorace nake
gashi yanzun kullum na kwanta wasu irin mafarkai nake marasa dad'i"
Kallon ta yayi cikin murmushi kafin yace "ummu Fatima kenan duk kinbi kin sawa kanki damuwa
akan wannan abun babufa abinda zai faru sai ikon Allah"
Cikin damuwa tace "dan Allah Abu Fatima ka maidani garinmu nagaji da nigeria babu dad'"
Sai da ya d'an dara domin maganarta ya bashi dariya kafin yace "to shikenan Ummu Fatima
yanzun ki hak'ura har su Fatima su dawo sai na fara muku shiri har su Naseer ko"
Rungume shi tayi tareda sakar masa kiss sannan tace "na gode mijina.
Su Fatima kuwa ana kiran magrib suna tsayawa ak'ofar gidan kawu Tanimu wanda yake cike da
mutane maza da mata domin kuwa shi d'in babban malamin da duk al 'ummar yankin suke
matuk'ar ji dashi.
Aiwala Abdul yayi yabi su kawu masallaci yayin da su Fatima suma suna shiga alwalan sukayi
suyi nasu sallar tare da sauran jama'ar dake cikin gidan.
Abdulmajid kuwa basu shigo gidanba sai da sukayi sallar isha sannan suka shigo da kawu
Tanimu zuwa lokacin kuwa duk mutanen sun watse wanda sanadin zuwan sune yasa kawun
nasu ya sallame su, banda hakabwasu har kwana suke a gidan .
Bayan sun ci abinci sun huta ne suka shiga har turakar kawu Tanimu domin gaida shi.
Yana zaune saman buzunsa yana lazumi Ihsan wacce bata tab'a zuwaba d'akin take k'arewa
kallo tare da mamakin ganinshi k'al k'al wanda hakan yake nuni da cewa mamallakin d'akin
yana da matukar tsafta.
Gefen sa wata katuwar kanta ce cike da litattafan addini kala kala sannan gefan kantar kuma
turaruka ne irin na wuridi d'innan suma gasunan burjik sai da Ihsan