Showing 60001 words to 63000 words out of 65710 words

Chapter 21 - ZATO NE (1 TO End) BOOK COMPLETE By Maman Islam.pdf

14 Apr 2025

5212

AM] Hayat: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p

*_______________________________________*

��ZATO NE��
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

STORY AND WRITTEN
BY

MAMAN ISLAM



Page 52
..................duk suka bishi da kallon mamaki da tsoro domin jikinsa a wani irin kwaile yake
kamar wanda aka kwarawa ruwan zafi jikinsa haka yayi.



Wani irin wahalallen nishi yake tareda sakin wani irin kuka mai ban tausayi yana fad'in "na cuci
kaina na lalata gobena ni tawa ta k'are shikenan tawa ta k'are bani bane banyi da nufiba banyi
da niyyaba ki yafemin matata kiyafe min Hafsatu na cutar dake na gurb'ata yardan da kikayimin
wayyo Allah na shiga uku ba kowa yajamin ba face tsinanne la'ananne Tanimu"



Yadire tareda fashe da wani irin masifaffen kuka wanda kana gani zaka gane Halinda yake ciki
na azaba sosai yake kukan kamar zai had'iyi zuciyansa.




"Tanimu?""
Dukan su suka had'a baki wajen fad'i tareda al'ajabin shed'anci irin na Tanimun basu k'ara shiga
mamaki ba saida Fatima tace "muma shine ya sacemu ya dinga gana mana azaba
k'arshema,guba ya zubo mana wai muci mu mutu yabawa gunkinsu jininmu sannan ya aikowa
da iyayenmu k'ashinmu"

Fashewa daddy yai da kuka saboda takaicin bak'in abubuwan dayake ji yayin da Abbi yace
"babu ko abu guda dayaban mamaki game da halin yaya Tanimu domin najima da sanin cewa
shi mugun makwad'aici ne akan abun duniya babu abinda bazaiyiba shine sila kuma sanadin
faruwar komai amma ku saurari malam Sule shinzaisan komai" Abbi ya fad'a yana nuna mijin
gwaggo Hafsatu.




Agalabaice yasoma cewa "kamar yadda na fad'a tunda farko cewa Tanimu gawurtaccen
matsafine kuma mugu azzalumi bayada aiki sai cutar al'umma duk wanda yasan zai samu wani
cigaba a tattare dashi koda masifa koda bala i sai yajashi cikin qungiyarsu wanda wata bak'a
kuma shed'aniya kuma k'ungurmar kafurar aljana take jagoranta wanda itama da hadimace ga
wani mugun matsafi washi DUMB'URU daga baya bayan tagama sace duk wani surrukan
tsafinsa sai tayi masa tawaye take son had'a qungiya nata na k'ashin kanta, kamar yadda na
fad'a tundaga farko cewa Tanimu ya lalata rayuwan mutane da dama kuma ya gurb'ata
hallayansu ni d'innan ina d'aya daga cikinsu kuma muna da yawa 'yan cikin wannan familyn
atareda shi sannan kuma duk wanda ya mutu shine sila yana aikata munanan aiyukansa ne
dan son zuciyarsa sannan ya tabbatar mana da cewa alh. Yuseef shine shugaban qungiyar
amma baya so asan yana harkar tsafi saboda kar hakan ya tab'a martaba da darajarsa, daga
farko mun yarda da abinda ya fad'a mana musamman idan mukayi duba da irin tarin dukiyar da
ubangiji ya yassare maka, sai daga baya nagane cewa duk abunda yake fad'a k'aryane kuma
yayi hakane dan yad'a manufarsa akanmu da yadda yake amfani damu wajen cimma
manufarsa sai daya maidani qasurgumin bokan da duk yakin sukeji dashi wanda haka ya
mantar dani duk wani hakki da nauyi na ubangijina dake kaina"



Nufasawa yayi yana maida numfashi suna kallo jikinsa ya cigaba da kwaikewa kamar wanda
akewa d'aya irin na k'unan nan ihu yake iya k'arfinsa yana neman taimakonsu amma dukansu
babu wanda zai iya nasa wani abu saboda kwatata babu wajen kamawa ajikinsa duk ya sale,
Abbi ne yayi k'arfin halin fara tofa masa addu'o'i kafin ya daina wannan barbarwar,




Saida yasamu sassau kafin yaci gaba da cewa "wanda yai nasarar fara jefawa acikin
mummunar hark'allar tasa shine MUNZALI k'anin Sambo abokin alh. Yuseef a sanadin haka
suka had'e kai sukayi ta zaluntar sa har suka haifo masa YUSRA wanda shi Munzali yasan
d'iyarsa ce kuma yasan cewa matuk'ar Abdulmajid ya aureta to Tanimu bazai barta da raiba
shine ya ari bakin uban rik'onsa yazo yayi yanda yaga dama dan afasa auren yayin da kuma
yakasance ita haj. Kulu bata da bokan dayake mata gagarumin aikin datake samun nasara

sama dani shine fa nayi yanda nayi har akayi auren ashirina na d'aukar fansar abinda Munzali
yayi min na rabani da tilon 'yata wadda ita kad'ai Allah ya bani a duniya akan idona Munzali yayi
mata yankan rago bisa umarnin Tanimu duk dayasan cewa ina d'a daga hadimansa amma wai
danya cigaba da saka rud'ani azuk'atanku yasa akayiwa 'yata haka shine ni kuma na nace ayi
auren Yusra da Abdul majid na rik'a zuga iyayenta har akayi hakan sannan fa kuma sai abin
yabar hannuna sakamakon GAZA tana son jinin Yusra wanda zatayi wani abu na mussaman
dashi shine itama,tayi mata yankan rago akan idona,kuma akan idon ubanta wanda savoda son
zuciya irin nasa yake neman,fansa akaina shinefa GAZA tasako shi cikin aikinta akan zata
taimakeshi akaina yanzun dai intakaice muku fad'an na kai da kaine sukeyi atsakaninsu domin
mallakar wani kambu na DUMB'URU shugaban mu duka wanda yak'i bata damar hakan yanzu
zancen danake muku suna can suna,fafata yak'i tsakaninsu akan wannan kambun sannan
kuma ta gefe guda ga wata rigimar ta b'ullo wanda Badamasi ya haifar na tabbata GAZA bazata
barshiba"


Kafin yakai k'arahen labarin matan wajen kuka suke sosai babu kamar gwaggo Hafsatu da har
take jin kamar zuciyarta zai fashe dan tsabar takaici da k'yar Abbi yace "kace kuna da yawa
kamar ku da su waye Tanimu ya saye imanin na ku?






Maman islam ce
[11/30, 6:11 AM] Hayat: مسب الله نمحرلا رلا ميح
*__________________________________*


☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*____________________________________*




��ZATO NE��

NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM


Page 50



..............yauma har suka fice babu wanda yasani saida yaje yafara nema mata kwakwar
manjan sannan suka biya gidab cin abinci yaci ya k'oshi tana zaune tana kallonshi ita yanzun
bata iyacin abinci sai kuma abinda suka fara horuwa da cinsa alokacin da suke gidan yarin
kawu Tanimu wanda badamasi ya kai musu wato garin kwaki a lokacin kafin Abdulmajid yasan
cikine da ita har mamakin yadda take zagewa taci ta k'oshi yake bayan zai iya cewa bata tab'a
ganinsa ba sai ranar.






Suna cikin tafiya ta hango mai agwaluma tace ya tsaya ya saya mata nan ma saida suka siya
babban leda aka cika musu, sun d'an yi gaba kad'an taga mai awara tace shi zataci,
intak'aitavmuku kafin sukai gida siyayyar da sukayi ya wuce misali.




Suna zuwa gida ta baje kayanta tayi zaman dirshan takan awaran tafara sannan tace yadafa
tama kwakwar yasa attaruhu da albasa yasaka manja da maggi sannan karyasaka mata kori
yasa tafarnuwa kad'an, murmushi yayi baice komai ba yashiga kicin d'in yafara wanke kwakwar
sannan ya had'a attaruhu da albasan ya jajjaga ya had'a kayan duk datace ya kunna gas ya
d'ora ya koma gefe dan yasan ko ya koma falon cewa zatyi yabar mata abu zai k'one.





Ita ko duk tarkacen da suka siyo babu wanda bataci da yawa ba dan rabonta da abinci,irin haka
tun kafin su tafi gidan yarin Kawu tanimu tana zaune ta jiyo k'amshin kwakwa tace ya kawo

mata haka sannan ya dafa mata indomien yazun taji tana son ci haka dai ranan ya wuni ma
bautan Fatima ko kad'an bata barshi ya hutaba shi kuma bai nuna mata gajiyansa ba






Misalin tara da rabi na dare yashigo d'akinta fitowarta kenan,a wanka tana d'aure da tawul
wanda ta saukeshi a k'uginta batayi tunanin zai shigoba shiyasa bata damu data rufe jikintaba
ihu tasaka lokacin data ga shigowarsa da sauri ta nemi hijab zata saka ya fisge tawul d'in babu
shiri ta rungume,shi tana,masa kukan,shagwab'a tace





"Haba dan Allah yaya meye haka, gaskiya idan zaka shigo ka ding".......bata samu daman
k'arasa abinda zata fad'aba tayi tsi sakamakon manna bakinsa da yayi ak'irjinta yana mata wani
irin abu, jitai kamar zata fadi dan haka ta rik'eshi k'am, shikam tunima ya manta da abinda ya
kawoshi d'akin saboda wata duniya da yafara tafiya hannunsa yasa a hankali,fara shafata
yana,mata wasu irin abubuwa masu wuyar fassarawa tuni,jikinta ya hau rawa takasa tsaiwa
dole ta zame a wajen yabita yana dad'a gigitata da salonsa ranan Fatima da kanta tasan cewa
ba k'aramin missing juna,aukayi ba dan saida ta rik'a rok'on ya k'yaketa haka har saida yaga ta
fara masa kuka kafin ya sarara mata.





Saida suka shafe sati biyi da dawowa kafin Daddy ya had'a meeting ya gayyaci kowa da kowa
nan b'angaren Amma.





Kusan sai da kowa ya rigasu zuwa dan saida suka gama shiriri tansu kafin suka shirya suka zo
kawu Tanimu ne kawai babu awajen wanda da ace yazo kusan duk sanda zasuyi meeting shine
jagoran taron, bayan gaishe gaishe da kuma d'an tab'a hiransu na zumunci sai kuma kai tsaye
daddy ya tashi ya fara jawabi kamar haka.

"Assalamu alaikum ya 'yan uwana barka da wannan lokacin da fatan duk kuna lafiya" du ala
amsa masa da lafiya yace "to Alhamdulillahi kamar yadda kuka sani abubuwa dayawa sun sha
faruwa ga Abdulmajid wanda ya kasance duk matar da zai aura sai dai awayi gari aga babu ita
ta mutu ko yankanta ko an murd'e mata wuya da sauransu kuma mutuwa orin na fija an babu
ciwo babu komai, kamar yadda kuka sani nima na sani wasu dayawa daga al'ummar unguwar
nan suna zargin nike kasge duk wani wandacya rab'i d'ana suna zargi da ZATON tarin dukiyar
da Allahu subahanahu wata ala yabani na jinin mutane ne yayin da acikin gidannan kuma wai
'yan uwana suke ZATON Abdulmajid da kashe duk wacce ya nuna da nufin son aurenta wanda
wannan abun duk ya kasance ZATO NE to amma akace wak'a abakin mai ita yafi dad'i yanzu
dai ga Fatima ga kuma Abdulmajid dan haka sai su dubi girman Allah su fad'a mana ainihin
wanda ua sace su da kuma dalilinsa nayin haka dan haka gareku"





Daddy ya karasa jawabinsa tare da neman waje ya zauna ya lyin da wajen yayi tsit na d'an
lokaci wanda suka rik'awa Abdulmajid wani kallo na daban jikinsu yai sanyi shi kam kawu
Ridwan kasa had'a ido yayi da Abdulmajid domim yafi kowa tada hankalinsa lokacin da
Amma,taso a had'a auren Ihsan da shi tsalle,yai ya dire yace wallahi bazai bawa d'an shan jini
'yarsa ya shanyi mata jiniba yayin da daga gefe marigayiya Asma'u ta dinga zugashi saboda
tsoron hukuci da alk'awarin da aka d'auka akan duk wani wanda ya rab'i Abdulmajid wanda
mutane da dama suke,tunanin domin,dukiyane.






Abdulmajid sai da ya d'ebi kusan second goma kafin ya ce "innalillahi wa inna ilaihi raji un" da
d'an k'arfinsa sannan yace "makashin mu yana tareda damu shine yake aikata komai yake
lalata komai shike aikata duk wani kashe kashe kuma yake zab'ar duk wanda yaso yasaka shi a
k'ungiyar su ta asiri daddy menene had'inka dashi mai kayi masa mai ya tab'a had'aku? domin
yace fansarsa akanka take kuma nine garkuwanka shiyasa yake tab'ani yake sakani cikin duk
wannan halin domin ya girgizaka yasakaka adamuwa ya d'orama kama ciwo wanda zaiyi
tacinka dukiyar dakake tak'ama dashi ya k'are a wajen neman magani kayi mutuwan wulakanci
wai me kamasa ne wacece Hauwa????????

Takuce maman islam
[11/30, 6:11 AM] Hayat: �� ZATO NE��


NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

STORY AND WRITTEN
BY
MAMAN ISLAM

☀️FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIN☀️


Page 54
.......................duk da irin sab'anin da ya rik'a had'a su ba k'aramin duka mutuwar tayi mataba
sosai jikinta yayi sanyi musamman da yau abun da yake ta b'oyewa tsawon lokaci ya fasu
sannan ga kuma mutuwar mijin nata wanda babu tantama tasan cewa Tanimu ne ya kashe shi
innalillahi wa inna ilaihi raji un rabon da gwaggo Hafsatu ta shiga tashin hankali irin wannan tun
mutuwar tilon 'yarta wanda alokacin har ga Allah yayan nata ta zarga kamar yadda sauran
mutane suke fad'a cewa wannan dukiyar nashi Na jini ne, take wanda itama data rasa mafita
kawai tabi bayan magautan d'an uwanta ma hassada masu bak'in ciki da arzik'in da Allah ya
masa.




Wani irin kuka ta kuma kecewa dashi tareda rarrafawa ta shige jikin Amma tana mai cigaba da
sakin shashshek'a yayin da tausayin ta ya hana Amma cewa komai sai shafar kanta da ta hauyi
itama nata hawayen basa tsaiyuwa.

Da farko Kawu Tanimu a iya rugar Tanimu ya rik'a bulayin neman Badamasi sanin kansane
bazai tab'a b'uya a d'aya daga cikin gidajansaba hakan yasa koda wasa baiyi tunanin nemansa
a gidansa ba.



Shima kuma Badamasi tunda yasan cewa dole Tanimu zai gane cewa shine ya temaki su
Abdulmajid kuma yasani Indai har sukayi ido biyu dashi tashi ta k'are rayuwar shi tazo k:arshe
kuma yasan bazai tab'a bawa ransa cewa zai tsaya a rugar Tanimu ba hakan yasa ya koma
gida ya kulle Kansa yana ta addu a tareda rokon Allah ya kawo k'arshen wannan azzalumin
bawan .




Gaza kuwa duk inda ta shin hankali yake to nata ya ninka nan domin aikinnata ma baya tafiya
duk da kasan cewarta jinnu kuma shahararriyar b'arauniyar sirrikan tsafin duk wani matsafi data
sani a wannan karon abin yak'i aiki, tana cikin wannan rud'anin Tanimu yazo mata da bak'in
labarin cewa wai ba aga Badamasi ba take ranta ya b'aci idanunta ya koma wani irin kore shar
kallon datayi masa yasa yafita da sauri batareda yaji daga garetaba, yana fita ta fashe da wani
matsiyacin kuka yana magana da wani irin yare mara dad'in ji take wasu 'yan k'ananun jemagu
suka bayyana tayi musu rad'a a kunne suka b'ace.




Su Abbi kuwa basu fara zuwa neman kawu Tanimu ba saida sukaje gidan da Abdulmajid ya
kwantata musu sun jima suna buga gidan yak'i bud'e musu suka kira Abdulmajid suka fad'a
masa hatta kiran wayarsu yak'i dagawa kuma yana shiga, Abdulmajid yana masa kira d'aya ya
d'aga bayan sun gaisa ya sanar masa cewa Abbi me da Daddynsa zasu taimaka masa ne akan
mugun nufin da Kawu Tanimu yake nemansa da shi, bai yarda ya bud'e musu sai da duhu yayi
yana ganin su yaji sanyi aransa ko ba komai zasu taimaka masa da yak'ar wad'an azzaluman
shed'anun mutanen.



Bayan ya shigar dasu ya kawo musu ruwa da abinci mai kyau dake daman can ya iya girkinsa
sannan kuma dake yana da komai na buk'ata hakan yasa tunda yarufe kansa agidan babu
wanda yasan yana ciki dan ko k'wakwk'waran motsi baya yarda yayi.

Bayan sun gama cin abinci sunyi sallah ne kuma Badamasi ya k'ara shigowa suka gaisa
sannan suka k'ara gaisawa tareda yiwa Badamasi tambaya akan rugar Tanimu kasancewar sa
wanda yafi kowa sanin sirrin rugar ciki da wajen ta.





Sosai ya rik'a tona musu asirin kawu Tanimu tare da kwatanta musu hanyar da zasubi tareda
b'oyayyun abubuwan da kosu makusan tansa bays amincewa dasu akai da wani kafurin d'aki
wanda koda mantuwa ne bai tab'a gigin barinsa a bud'eba sannan bai tab'a bari wani ya shige
shiba koda wasa wannan d'aki daga shi sai Allah ne kawai suka san abinda yake cikin sa,
bayan ya gama musu dukkan bayanai ne Abbi ya dubeshi yace.



"Dole dakai zamuje Badamasi domin kafimu sanin hanya" arazane Badamasi ya subi Abbi
sannan ya hau girgiza kai tareda fad'in



"Kayi hak'uri alhaji na tabbata idan nakai kaina wajen Tanimu sai dai wani baniba kaga kenan
burina na d'aukar fansar ran iyayena ya lalace, dan Allah alhaji karma tilastani zuwa inda
Tanimu yake domin nasan shi nasan waye shi yana da duk wani salo da dabarar mugunta kala
kala sannan cikin ruwan sanyi yake sulwantar da duk wanda ya shiga hannunsa"



Kafad'ar Badamasi Abbi yadafa yana kallon yarda jikinsa yake tsuma har lokacin yace "sanyi
mana abokina kar ka d'aga hankalinka dayawa mana kar wani ciwon ya kamaka abinda nake so
dakai shine kasalokacin cewa duk abinda yasameka daga Allah ne babu maiyi ko hanawa sai
Allah idan kaga har Tanimu yayi nasaran kasheka to dama can lokacin ka ne yayi dan haka ka
k'addara mutuwar ka a hannun Allah yake ba hannun kowaba sai dai ace wani yayi sila amma
rai da rayuwa duk suna hannun mak'agin kowa da komai ne wato Allahus samawati wall arad
dan haka ka daina tsoron komai tafiya zamuyita da kai babu abinda zai faru sai ikon Allah".




Abbi yajima yana rarrashin Badamasi kafin ya amince ya bisu suka tafi har masaukin bak'in
Kawu Tanimu wanda yake tsakiyar daji wanda yake ma mutane rufa ido suke d'auka a k'ofar

gidansa shago yake.







A can gombe kuwa bayan andawo daga kai mashinaulaiman 'yan uwansa suka d'an shishshigo
sukayiwa gwaggo Hafsatu gaisuwa suka d'an zauna na wani lokaci kafin sukayi sallama wa ita
da 'yan uwan ta dan acan garinsu zasuyi nasu zaman karb'ar gaisuwar.





" Baby gaskiya nidai nagaji kawai tunda Abbi sun tafi kamo wannan mugun mutumin mu koma
gidanmu mana dan Allah nidai gaskiya nan gidan an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login