Showing 27001 words to 30000 words out of 191310 words
Chapter 10 - ABU CIKIN DUHU BY MAKAWA By abooks.com.ng.txt
duk da yanzu nasan nima ina tsabta fiye dacan da nake Ancau din mu.
Na kanyi tunane indon dun kauyancine da kazanta yazu duk na daina wanan a ganina do na canza nayi fes na kara zama shar kamar bani ba.
Ga mai da turare na yan gagu da hjy taban tace in dinga shafawa idan nayi wanka gun kashe gari dana zo.
Komai ina yi shi a taka tsamtsam a gidan ban yarda in ketare iya inda aka ajeni ga aikina dan dama wani lokaci idan zama ya isheni nakan shiga kitchen in taya su mama kande aiki do su basu da hutu kamarni.
Ko yaushe a cikk girki suke dan hutun su kadan ne tundai idan yaran gidan suna gida wancan yace kaza yake so wana yace baya cin kaza yau.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
9️⃣
YAR UWA NOVEL DINA NA KUDINE KIJI TSORON ALLAH KI BAN HAKKINA KAFIN KI KARANTA DON GUJEWA SHIGA HAKKIN WANI, , , ,
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KI TURO KATIN WAYA DARI UKU NE KACAL BA YAWA, , , ,
Ina daki naji muryan hjy tana kwalla min kira daga dakin ta nima na amsa da karfi da Na,am mami.
Fitowana daga wanka ke nan lokacin don haka na dauki riga a gurguje na saka a jikina don zuwa amsa kira hjy din.
Na sameta zaune tana waya saman gadon da yasha gyara a wurina tunda safe nake gyaran dakin mami din don duk wani aiki da zata kai ga bude baki tace inyi kafin ma tace nayi din tunda yanzu nasan aikina a gidan.
Bana jin kiuya ko kasala tunda na saba aikin daya fi wanan a kauye don hakane hjy bata samun matsala dani koda an samu din ma saidai gyaran dan abinda ba,a rasa ba kawai.
Ganin tana waya yasa naja na tsaya daga nesa kadan ina jiran ta gama waya ta bani umurnin abinda zan mata lokacin.
Wasu kaya data fitar ta nuna min da hannu alaman in dauko mata su ban tsaya ba na juya zuwa wurin kayan na fara dauko su ina ajewa a gaban ta.
Sai waya take ta faman yi mai kama da fada da alama dai da danta ne ko wani kanin ta take waya yadda nake jin tana fitar da kalamai gareshi.
Bayan na gama kwaso kayan ne naje gefe na tsaya don bata ban umurnin in tafi ba.
Hango tawul din data fito wanka ta goge jiki nayi gefen gadon ta na juya zuwa wurin na dauke tare da nufar kofan ban daki na shiga na baza shi a dan karfen da ake bazawa.
Unders din da suka taru a duk da na ranan dana daren jiya datai amfani dasu ne kamar rigan nono da buje da handkacin amfanin ta.
Sai na tsaya na wanke tun ina jin muryan mami tana waya har nazo na daina ji da alaman ta dai gama wayan ne a lokacin.
Nafito ta bini da kallo tana fadin wai dama kina cikin dakin nan zeey ?
Ina ciki ina wanke under din da ke ajene tace min kai zee bakya hutu ko yaushe kina cikin aiki ai kiranki nayi kawai don ki miko min kayan nan in gani don jiya aka turo min su daga Dubai.
Daga min su daya bayan daya nagani na duka na fara dauko kayan ina dagawa daya bayan daya tana daga kai idan na nuna mata.
Amma sai naga kamar wanan yafisu tsaruwa zeey tana tambayana ta hanyar dago kanta taji me zan fada.
Mami duk suna da kyau sai dai wanan din zai fi maki kyau gaskiya don kallan jikin ki.
Ido ta kura min kamar tana nazarina kafin tace ashe kin iya zaben abu mai kyau kema ni dai murmushi nayi kawai ina kawar da kaina gefe.
Sai dai ke har yanzu dadina dake kinki sake jiki a gidan nan ki nuna nina haifeki kamar kowa .
Kullun kina abu kamar bakuwa a gidan nina rasa wanan halin naki kodai bakijin dadin zama da mune zainab ?
Da sauri na dago kai ina fadin mami ina ji haka dai yanahina yake ko a gida nan ma aina sake ke nan .
Sai tayi dan murmushi tare da fadin a hakan da kikeyi sai na dinga tunane ko bamu kyauta makine wani sa, an.
Shigowan Rufaida dakin ne a daidai lokacin da nake kwashe kayan zuwa wardrobe din mami kamar yadda ta umurceni inyi.
Rufaida tayi sallama ta shigo ina jin suna gaisawa da mami din take fadin kunga dama kun tashi ke nan yau weekend kun samu wuri kun kwanta kuna ta barci ina sauran mashiriritan suke basu tashi bako har yanzu ?
Ban dubasu ba ta bata amsa gefen hjyn naga ta zauna ysyin da nazo wurin da niyar incewa hjy din akwai wani abinda zan matane ko in wuce.
Kafin in furta Rufaida ta daka min wani uban tsawa malama may kikeyi kuma a nan bakin gama aikin ki ba ki fita magana nake son yiwa mami yanzu.
No no no Rufaida na fada maku bana son wanan hattaran da kukewa yarinyar nan bari ganin tazo tana aiki a karkshin mu.
Ku dauka hakan gazawa ne ko wani abu ni da kaina na rokota hannun iyayyen ta kuma aikaimin karamci aka ban ita don haka duk daya na dauke ku gareni don jinta nake kamar diyar cikina itama.
Bana son wanan halin da kuke nuna mata a gidan nan to ai mami biyan ta akeyi bata daya damu ai.
Na fada maku ban son hakan da kukeyi nan aikin ta yake tare dani dole kuma ta shigo dakin nan tunda abinda tazo yi ke nan a gidan nan.
Baki Rufaida ta zunburo wai ita an mata fada ni dai ina tsaye ina sauraren su can nace mami da wani abinda zan maki yanzu ne wanka na fito dama ?
Yamm yamm yamm don Allah fita kiba mutane wuri inda aikin ma zan karasa mata shi amebo kawai.
Nidai na juya na fice daga dakin raina bai min dadin hakan ba ko kadan yadda yan matan nan suke min a gidan gashi naga duk da mami na tsawata masu sai dai bata son ransu ya baci ko kadan.
Yanzun na gama waya da yayan ku yana son ya raina min wayau wai ba zai samu zuwa rantsar damu ba da za ayi.
Abinda naji mami tana fada ke nan lokacin da zan fita daga dakin bayan korar da Rufaida tayi min.
Dakina na koma na karasa shirina duk da ba wani shiri bane dan dongon rigar da anty safiya ta sai min sune nake sakawa yanzu saidai naji hjy tana wakan tana son a samu lokaci aje a sai min kaya don tana kunyar wanan kayan da nake sakawa haka.
Ban sa raina ba sai na gani balle zumudin hakan ya hana zuciyana shakat da damuwa na fito na nufi kitchen don samawa cikina abin karyawa.
Ruwan shayi da soyayyen dankalin turawa nagani a cikin kula shina diba na hada tea na dawo inda Larai ke gyara kayan miya na zauna kusa da ita na fara sha ke nan naji muryan Rufaida na kwala min kira da yar aikin hjy don sunan da suke kirana dashi ke nan dashi a gidan in ka debe hjy dake ce min zeey sai su mama kande da suke kirana da zainab.
Amsawa nayi da na,am tana karyawa Larai ta fada yadda zata iya jiyo ta tana karyawa shine ba zata zo ba Rufaida ta fada.
Dole na mike zuwa amsa mata kiran a tsakiyan falo na sameta tsaye ta rike kugu tana jirana a hasale.
Ina zuwa take fadin ke don uban ki zan kiraki kice kina karyawa haba Rufaida wanan zagin fa haka ?
Muryan Anty salma ce dake zaune wurun dinning tana karyawa lokacin ba dole in zage ta ba don daukan kanta take daya damu wanan yarinyar.
Kin san dan kauye bai iya samun wuri ba dama idan yaga ya waye sai yake gani yafi kowa waye wa ki shige dakina kaya na nan na tara a bayi na ki wanke min ta fada tana juyowa inda nake tsaye ina kallon ta da idanuwa da suka ciko da hawaye don zagin da tayi min.
Bazaki tafi yin abinda nasaki bane ta fada cikin tsawa da sauri na juya na nufi hanyar dakin nata don kwaso kayan datace din.
Saurara ta fada naja na tsaya cak wuri guda ina saurarenta kada ki fara ki satar min wani abu a dakin nan don ranki zai baci sosai idan kinyi hakan.
Haba haba hakan baida kyau fa Rufaida and kuma kinsan mami ba zataji dadi ba idan tasan da hakan anty salma tace.
Mami kina nufin banda right din sakata aiki ko warning dinta akan kayana tana yar aiki gidan nan.
Nidai na juya na wuce ina shara hawaye don abu biyu ga zagin dana samu ga kuma zargin sata yanzu.
Dakin na shiga na same shi a ya mutse kamar ba mace ke kwana a cikin sa ba don daki babu gyara ko kadan yadda na ganshi.
Bai da banbanci da dakin da nake bambancin su dai wanan mirrow shi cike yake tab da kayan shefe shafe sai manyan akwatuna dake gefe ajiya ga kuma tv bango babba.
Duk a fakaice na kalli dakin nasan da hakan don wanan ne shigana na farko wani daki daya shifi gidan in kin debe na mami da kullun ina cikin sa.
Mami bata taba ce min wani abu game da dakinta da zanga kudi ko agogo ko sarka da sauran su sai dai in dauka in mayar inda take aje sarka ko agogo kudi kuma zan daga filo in aje mata shi yadda suke.
Ina shiga ban dakin idona ya fara arba da pant din ta saman kayan su rigan nono da bujen ciki kai kaya daine na unders da mace ke sakawa a jikin ta ta tara gudan masu yawa a wurin.
Tattarawa nayi na a bucket din dana gani a bayin nafito tana tsaye tana kokarin cire rigan dake jikinta take fadin ki tsaya ki gyara min daki kafin kije wankin.
Dole ba yadda na iya tunda nazo cin arziki ne gidan su na fara gyaran dakin ita kuma ta shige bayi don yin wanka kafin ma ta fito na gama na bar dakin.
Can baya naje inda ake wanki da sauran aiyuka na wanke na shanya mata tunda wanan ba aiki bane a wurina.
Na gama na dawo na samu ruwan tea di dana aje har yayi sanyi haka na dauka nakarasa shan shi da sanyi.
Fitowa nayi da niyar komawa dakina na samu yan matan gidan zaune da kawayen su a falo zaune.
Zuwa nayi zan wuce ba tare da nayi masu magana ba nakai tsakiyan naji muryan Nazifa na fadin amma wanan yarinyar bata kunya.
Sai duk suka dawo da kallon su wurina wanan wacece yaushe tazo gidan nan cewar wata daga cikin bakin.
Rufaida dake cin chewing gun ta tabe baki tana fadin a kauye mami ta dauko ta .
A hakan mami ta dauko yar aiki wanan wani aiki zata iya kazama da ita haka ga ruwan kauyanci ko ina tare da ita.
Gaba daya suka sa dariya lokaci guda ke zoki gaidasu ki shige salma ta fada a dake ba tare da tayi dariya ba ita.
Nazo gaban su na tsuguna ina gaidasu basu amsa ba sai dayan ke fadin kina gani ta nan idan ta waye sai duk kun girgiza a gidan nan.
Amma dai kin gama damu Laila wanan din ne zamu girgiza don tayi clean .
Oh kina raina irin kauye ke nan ai barsu yadda kika gansu ba wani zancen clean gareta don tana clran aurin nan ba karamin taksici zakuci ba duk wanda ya zo kanta zai tsaya rabu da mutum ka barshi a ranan da yake kawai don idan kace zaka kaishi innuwa shiko yana turaka rana .
Salma ta kalleni cikin takaici tace ba kingaida su ba me kike jira kuma a nan yanzu ?
Sai ta gama jin abinda muke fada mana Rufaida tace tana watsa min harara na mike ba bar wurin ina jin bakin na fadin ke wanan ai idan tayi clean ko yaran gidan nan ba zasu barta ba tana hakama yaya aka kare da suranta duk mai hankali yasan anyi halitta a nan ai.
Ire iren haka yasa nakan shige daki in zaune in dai ba mami ke gida ba dole ina falon don aike ko wani aiki da zan mata.
Yan matan basu bar gidan ba har mami ta dawo daga unguwar data tafi tana shigowa ta samesu a falon gaisawa suka farayi bata ko amsa masu ba ta fara fadin ina wanan yarinyar zeey take ne ?
Sai kawai ta shiga kwala min kira ina cikin daki na kulle kaina naci kuka har na gaji naji an bankado min kofan dakina da karfi .
Haka yasa na dago kai ina kallon mai shigowa dakin lokacin ba kowa bane sai Nazifa ke kina nan zaune to mami tana kiran ki.
Mikewa nayi da sauri ban ko tsaya share fuskana daya gama dan hawa ba saboda kukan da nasha.
Mun iso falin daidai mami ta dauki ruwa zata kurba nake fadin sannu da dawowa mami ta dago kai ta kalleni sai ta furzo da ruwan lokaci guda daga bakin ta.
Gaba daya hankalin kowa ya koma kanta don ganin me ya faru tana fadin zainab mamana kuka kikayi ne ?
Kaina na girgiza mata kafin in ce a a ahankali ina wasa da yatsun hannuna haba bana son inganki cikin damuwa ko kadan.
Shiru ta danyi ta mayar da hankalin ta ga wayan ta kafin tace kwashe kayan nab ki kai min daki.
Na duka na dauki kayan zuwa dakinta kallo ta bini dashi tana fadin na rasa me yake samun wanan yarinyar taki ta sake jiki damu har yanzu.
Cikin ko in kula salma tace mami tambayi yaran ki don su suka bata mata rai suka kirata da yar kauye a gaban ta dazu nasan shi takema kuka dai.
Salma haka take bata shiga harkan kowa kuma bata boye gaskiya fadin shi takeyi komai dacin sa a cikin su.
Amma na fada maku tun randa yarinyar nan tazo kan ku kiyayyeta a gidan nan ko ban fada ba ranan kan mami tayi masu tas a kaina a gaban kowa don sauran ma ashe ba baki bane duk yan gidane suma.
Wanan fadan ne ya kara jawo mi bakin jini a gurin su sosai suka saka kafan wando daya dani dole idan mami bata gidan ina daki ko wurin kande.
Haka kuma bai hanasu sakani aikin wahala da suke gani suna ban ba gashi mami bata zama gida yanzu don shirye shiryen da ake na zuwa rantsar dasu Abuja.
Wanan ya dauke mata hankali daga komai dake faruwa a gidan ba wankin unders ba har tufafin su yanzu suke bani in wanke wai nafi mai wankin gidan iya wankin kaya sufita a cewar su don mugunta kawai.
Ranan ina dakina kwance mami ta kirani kande aka aiko ta kirani nazo da sauri tare da wani na samesu ina zuwa ta nuna mashini tana fadin ka ganta nan duk ita zaka dinkawa kayan .
Kallona tellan yayi yana fadin bari a aunata ke nan da sauri hjy tace tana daga mai hannu ina warning din ka da wanan awon da kukewa mata yana daga cikin aikata alfashan zama koda kuwa namijine dan uwanka ko mace yar uwar mace haramun ne yin hakan.
Hjy za,a kiyaye ya fada yana dan sosa kai tare da dan jin kunyan abinda hjy ta fada mai sai kuma ta dago yana fadin kayab zasu matse ne ko a danyi mata su free ne.
Kafin mami ta bashi amsa na karbe da fadin free nake so kada ya matseni don Allah.
Ji mun yarinya kin san abinda yake nufi ke nan ko ni dai nayi dan murmushi kawai ina dukar da kaina kasa cikin kunya.
Kudi masu yawa taba tella ya tafi yana mata sallama tare da godiya gareta wuri na samu sama kafet din dake tsakiya a daidai inda mami ta dora kafanta tana zauna cikin limtsetsen dogon kujeran falon.
Hjy ta kalleni tayi murmushi kafin tace min wai zee yaushe zaki daina wanan hali naki ga kuja zaki wani zauna a kasa kamar marainiya.
Dama ina son jin wani abu a dangane da rayuwan ki mahaifiyar ki tana da rai ?
A bazata tambayan yazo min da sauri na dago kai na kalli hjy kafin ince tana da rai sai kuma tace mahaifin ki fa ?
Shima yana nan na bata amsa kai tsaye kuma suna tare da babar ki kai na gyada mata wanan karon idanuna yana kawo hawaye.