Showing 96001 words to 99000 words out of 191310 words

Chapter 33 - ABU CIKIN DUHU BY MAKAWA By abooks.com.ng.txt

Ita iyamin ta fada maki hakan na gyada mata kai kawai ba baki idan ma har ta fadin hakan ai yanzu bake kika bishi ba shi ya biyo ki ko sai tayiwa danta fada shida ke binki.
Dakin mami ya nufa direct ba tare da jin komai a zuciyar shi ba duk da hjy ta fada mai mami ta leko dakin mu yana ciki yasan kuma ta ga halin da muke ciki a lokacin.
Da sallama ya leka dakin ba,a ansa ba haka yasa kai ya shiga dakin mami ya hango a zaune gefeb gado tayi tagumi da hannayen ta dukka biyu kamar wacce ke cikin tsananin damuwa.
Ta rasa abinda ke mata dadi a duniya yaron nan wani abin kunya haka yake son jawo mata ne duk ita a zaton ta ya bar wanan zance ashe shi yanzu yakema ga zancen wata namiji dai sai a barshi ga abinda yake so ya kwallafa rai kuma.
Kallon mamaki yake mata har ya karasa bakin gadon da take zaune a kai yace mami lafiya kuwa na ganki a haka ?
Wani abu ya faru ne ko wani abin kike tunane haka ke kadai a daki kinyi tagumi.
Ido mami ta dago ta gallamai harara da idanuwan ta da suka kade sukai ja tankar zasu fado.
Ji take kamar ta wanka mai mari da tana iyawa a yanzu so yake ya tozarta ta ya kunyata ta a idon kawayen ta tozarta.
Maganan hjy da take tunawa guda biyu shike taka mata burki ga koran yarinyar nan ta koma kauye.
Saidai idan ta tuna da kalamin hjy da take fadin idan ta kori yarnan a gidan ta sai danta yaje gun iyayyen ta a bashi ita ya aure muddin yaje da waliyan shi makusanta ita kuma a barta tana hargowa a gida.
Ga kuma barazan hjy data ita kuma idan ta matsa sai ta dauke yar ta koma da ita wurinta ta inganta rayuwan ta fiye da tsamanin ta to me hjyn ke nufi da hakan.
Hannun ta ya riko don yaga ko a yanzu da take kallon shi hankalinta na ga tunanen da takeyi a lokacin.
Riko hannunta yayi yana fadin haba mami meye zai sakaki irin wanan damuwan haka kinsan fa yanzu aiki na maki ya, , , ,
Baiyi aune ba yaji saukan mari a lafiyayyen fuskan shi lokaci guda ya dago kai da mamaki yana kallonta da kyar ya iya furta mami you slap me ?
Ko zaka ramane tunda yanzu ka girma har bakajin umurnina kake ganin kaika isa har yanzu kake mamakin na mareka ko ?
Allah yasa yanzu da idona na gama ganin ku da kazaman yarinyar nan a dakin hjy ba wani ya tsegunta min hakan ba.
Yanzun kai bakaji kunya ba ace kamarka jafar kamar kafa kamar kake rugumar wanan kazaman yarinyar zainab yarinyar da wani lokaci ma tsami takeyi da wari.
Da sauri ya dago kai a karo na farko tun bayan marin data kwasheshi dashi ya dukar da kanshi bai daga ba yana dafe da wurin cikin mamaki.
Wari mami wari fa kikace yarinyar nan tanayi ban taba jin haka ba a tare da ita asalima ni yau wani kamshin ma naji a wurin ta.
Mami nifa kome takeyi ina sonta hakana da don itace zabina a duk yadda take ya fada yana kokarin mikewa tsaye.
Jikin mami ya sake yaraf kaman ruwan sanyi a gabanta yau jafar ke wanan magana kan mace macen ma wai yar aikin gidan ta wanan wani irin lalacewa ne ya kama dan nata haka?
Ganin ya soma batrin dakin don tafiya don marin ma datayi mai shiko a jikinshi ya yadda nunata take ta soma magana tana fadin.
Yau da uban ka yana raye jafar zakai min haka ince ga wace nake son ka aura kace kai ba hakan ba yaushe ka fara wanan halin banzan na kafi ban sani ba ?
Mami daddy , aiko daddy yana raye ba zai hanani zaban abinda hankalina ya kwanta gareshi don dama daddy yana raye aida yanzun akaiga matsaya ga zancen nan don shi daddy ban taba ganin ya kyamaci wani a rayuwan shi ba
And mami kin san koda daddy yake da rai mun fi shakuwa dake fiye da daddyn mu
Mami kin kasa fahintana ne kin kasa tausa zuciyar ki akan yarinyar nan why mami zaki hanani abinda nake so.
Ba zaka aure ta ba nace bazaka aureta ba ko dole zakai matane mu gani idan zaka iya No mami ba dole amma nasan itama tana sona don naga alaman hakan tare da ita.
Tsoron warning dinki gareta ne take amma ba matsala zan gwada sa, a ta tunda kinban dama a yanzu.
JAFAR mami ta fada da karfi ya fice dakin ba tare daya juyo ya kalleta ba tunda mami take da danta haka bai taba faruwa a tsakanin su ba sai akan wanan dalili.
Me yaron nan yake nufi dani da wanan kalamin nasa tursasa yarinyar nan zaiyi taso shi tunda a yadda ta samemu a dakin da alaman tsoro shi a fuskana don kuka ta samu ina masa.
Ma,ana dai shi jafar din ne ke bibiyan ta a dole meya gani ajikina har ya mace ga son yar nan haka.
Yarinyar da saida tazo nan ma tadan yi wanan clean din da yake rudin shi ta runtse idanunta tana mai fadin kada Allah yasa so ya rudi yaron na ya aikata wani abinda zaija mata kunya ga idon mutane.
Ya zama dole ta jashi a jiki tasan hanyar data bi ta lalashi da lalama ya janye kudirin shi akan yarinyar na don koranta gidanta baida wani fa,ida a yanzu idan tayi amfani da maganan hjy.
Zeey bata da laifi ta sani amma wanan dalilin ya jawo mata tsanar yarinyar ba gara ba dalili taji yarinyar ta fita mata rai ga baki daya ta wanan dalilin.
A dakin mu hjy ta samu ta lalabe ina kwance lamo sai faman ajiyan zuciya nakeyi ga tunanen abinda ya faru tsakanin mu yaki fita a rai.
Duk motsi nayi sai inga kamar a lokacin abin ke faruwa dani uwa uba ga kamshin turaren jikin shi daya dameni a hancina yana kokarin saukar min da kasala a jikina.
Mikewa nayi zubur hjy dake zaune ta kalloni tare da fadin ina zaki ban daki zan shiga inyi fitsari na fada.
Na shiga ta bini da kallon tausayi tana gyada kai Allah kadai yasan yadda take ji a zuciyar ta kan yaranan a yanzu.
Na dan jima a ciki kafin in fito rike da digana dana cire ina daure da tawul a jikina wanda nake kewayawa dashi don a dakin muka same shi wani babba haka dashi fari mai kyau da yan flawer a jikin shi kanana a gefe.
Dogon rigar yar katin da anty safiya ta saya min da zanzo gidan mami na jawo na zauna saman kujera ina dan shafawa jikina mai don kada in bushe.
Au yar nan wanka kikayi gabanin magariban nan kudai yaran yanzu baku da tadan lokacin yin abu.
Hjy na magana tana kallon gashina da har lokacin yana tuke babu kitso a kaina sai fibon dana daure gashin dashi ta bayan kaina.
Kafin ta mayar da kallonta da kyau a inda nake tanaci gaba da fadin yadda kike nan da tsari irin hakane mutanen boye ke so su shige jikin mutum a sauke.
Mutanen boye kuma hjy na fada ina juyowa gareta tace kwarai kuwa yar nan ai su abinda sukw so ke nan urin wanan sakacin da kukeyi a yanzu take sun shigeka suyi maka illa.
Kinga mu a zamanin mu duk irin wa yan nan abubuwan musanshi iyayyen mu na fada muna mukiyaye don tsaron lafiyan mu.
Hjy daga yau na daina ba zan sake kewaya a wanan lokacin ba in Allah ya yarda tace dadai yafi maki kam.
Waini meya hadaki da mutumin naki ne dazun kike ta wanan kuka ina saka riga a jikina da sauri don maganan da tayi naji wanan maganan.
Juyowa nayi da a daidai ina karasa saka rigan na dauki hulan dana dora saman gado na dawo kusa da ita na zauna tare da dan marairaicewa nace hjy ki taimake ni ya jafar yafita daga tsabgata a gidan nan don Allah idan ba haka ba mami zata koreni ta fada.
Kin taba ganin inda aka cirewa mutum rai ga abinda yake so farat daya wanab sai uwarku da take ganin tana iya hakan.
Wai yau dai ki fada min yar nan shin kina son jafarin nan ko bakya son shi inji da sauri na dago kai na kalli tsohuwar sai kuma na dukar da kaina kasa don bansan amsan da zan bata ba.
Ince ina son sa in kaishi ina ko ince banson jinin ta kiri kiri haka a gabanta anya zataci gaba da sona nima duk da nasan tun kan haduwan mu da jafar din tsohuwar take nuna min kauna sahihi.
Sai kuma yanzu da take nuna min kauna tankar itace ta haifi iyayyena ta san zafina fiye da kowa ta yaya zan iya bude baki ince banson jikanta mafi soyuwa a gareta ido da ido haka.
Nasan wani abu yanzu ma saboda shine ta tsaya min take tsare min komai a gidan yadda ya dace.
Murmushi naji tayi tana fadin to ai abu yayi kyau takwara shiya nake kara sonki saboda halin nan naki na alkunya ga kuma girmama mutum saidai iyami taki gane hakan .
Ke din wani baiwace a garesu takwara naso iyami ta gane hakan amma idonta ya rufe ta kasa hangon hakan da kanta.
Nidai har ta gama maganan daidai ana kiran magariba ga agogon dake dakin namu ta mike da sauri zuwa bandaki do bata wasa da ibanda ta kiran sallah kawai ta kan jira ta mike ko wani lokaci.
Bayan kowa ya kammala komai aka fito cin abincin dare kamar yadda aka saba da kyat hjy ta shawo kaina na yarda na fito daga dakin.
Mun samu mami a falon har ta fito tana zaune tunda muka tun karo wurin ta dago kallo daya tayi min ta kawar da idon ta gareni tana fadin hjy kin fito yanzu nake zancen ko lafiya yau baki fito da wuri ba haka.
Muna daki nida mutumiyar ina bata labari mutanen da can yadda suke rayuwan su ga wuri hjy ki zauna tana fadawa mahaifiyar nata cikin girmamawa gareta.
Kafin ta dago kai inda nake tana fadin cikin bada umurni ke jeki aka hijabi a jikin ki baki ganin gidan nan akwai samari ne kike fitow haka dake.
Ya ilahi nikan ko me zanyi mami a yanzu bata ganin haske na na juya naji hjy na fadin zancen banza ke nan yo ai shigarta yafi naki dana yarki mutuntuwa bakiwa wanan mai zama kamar arniya a gida ba haka kai babu hula ko dan kwali sai wanan da jikkn ta yake a suturce.
Hjy mu muharamin si ne ita fa irin shigar da ta dauko yi ke nan har yaro nan ya jefa kanshi a tarkon ta.




Ita yar nan din tasan ta danawa wani tarko da ace hakan take da baki fada ba da bakinki yanzu don da kin gane kabewa ruwane.
Tsohuwar ta juyo gareni tana fadi jeki ki saka hijabin ki dawo muci abinci nikan ina shiga dakin ban kara fitowa ba na neme wuri na kwanta ina sharan kwalla.
Abuja ba kaduna bane don ko sunan uguwanin su ban gama sani ba sabanin kaduna da tun ban shigo shi ba nake jin sunaye unguwanin cikin shi a bakunan mutanen kauyen mu.
Ina barin wurin mami ta mike ta nufi dakin dan lelen ta a karo na farko tun dawowa shi Nigeria don ba dabi,an ta bane zagaya dakin samari nata.
Kofan dakin yana rufe ta murda taji shi a ruwa saidai karan tv dake aiki ana wasan kwallo tana dan iya jiyo hayaniya daga inda take tsaye.




ZAINAB IDRIS MAKAWA






🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅




2️⃣9️⃣




ZAINAB IDRIS MAKAWA


LITTAFIN KUDINE DON ALLAH KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA YAR UWA DON TURA KUDINSA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN DARI UKU KACAL A WANAN LAYIN 08036959257 NAGODE GA WANDA YASAN ZAFIN ABINDA NA FADA.




Da mamaki ta juya don a zaton ta yana cikin dakin sai dai bataji alaman mutum a part din ba haka ta dawo dakin ta ta nufa direct .
Har ta zauna ta bude system dinta da niyar tayi aiki a cikin sa sai zuciyar ta ba zai barta tayi abinda take so ba a lokacin.
Har dare duk wanda ya shigo gaida ita tana tambaya idan ya dawo sai suce basuga shigowan shi ba kuma security din shi basa nan saidai ga wayan shi na shiga kuma karshe taji wayan a kashe.
Washegari wanan dalilin ya hana mami fita aiki da wuri ni dai nagama mata komai tana bandaki kafin ta fito na karasa na fita daga dakin shiryawa nayi a gurguje kar driver dake kaimu school ya jirani.
Mami ta gane me nake nufi don ta fahinci tun jiyan ina gudinta don ban fito ba ita kuma bata tambaya ba duk ta san banda laifin kan hakan amma zuciyar ta ya kasa daina jin haushina.
Zazzabi mai karfe gaske yake ji a jikin shi tunda ya falka da safe da kyat ya iya shiga bandaki yai wanka ya fito yayi sallah asuba ya koma ya kwanta.
Mami ta fito daga dakinta ta samu hjy zaune a falo ita kadai tana kallo wa,azi da takance kafin mu kai mata kafin mu fita da safe.
Mami ke fadin hjy tun jiya banga shigowan jafar ba ko kinga fitan shi da safen nan da mamaki hjy ke fadin yanzun nake maganan shi a raina ni kadai.
Ko tafiyan yayi babu salma kuma wanan karo ma mami ta dan yi tunanw tare da fadin anya don bai dade da dawowa ba da wuya ya sake fita.
Part din shi ta nufa tana fadin bari in dubashi ko yana ciki har yanzu idan ba fita yayi ba.
Murda kofan tayi taji kofan a bude yake haka ya bata daman shiga dakin kai tsaye tsab falon yake kamar kullun sai kamshin dake tashi a cikin sa.
Cups har biyu ta gani aje saman dan table din glass din dake gaban kujera sai fararen takardu dasu laptop a gefen kujera aje.
Kai tsaye ta nufi dakin kwanan shi ta fara kwankwasa kofan ta fara kwankwasawa sai gana ukune ya amsa da kyar ya iya yin magana ya tambaya da waye ?
Nice ta bashi amsa a gadarance ba tare da ta kara furta wani abuba a kai.
Kofan a bude yake ya fada yana kokarin cire bargon dake jikin shi rufe mami ta tura kofan ta shiga daga cikin dakin.
Ta hango shi yadda yake kwance saman gado ya dan rufe rabin jikin shi da bargon.
Lafiya kake kwance haka a rufe tun dare baka leko muba baka kuma shigo da safen nan ba mami ta fada tana karasawa bakin gadon nasa tana zama.
Sai daya dan dago daga kwancen cikin yanayin yamutsa fuskan shi yace yau bana jin dadi ne amma yanzun nake son in shiga.
Baka jin dadi shine zaka kwanta a daki kai kadai haka ba wanda ya sani kamar karamin yaro mami ta karasa fadan nata da tambayan wai meke damuwan kane.
Cikin dauriya yai magana da kyat yana dafe kirjin shi mami ina jin kirjina na ciwo da zazzabi.
Wani kallo tayi mashi kafin tace dashi ai saika tashi kaje likita ya dubaka ko ?
Mami ba sai naje asibiti ba nasha magani dazun da zan kwanta tace ka karya ne da kasha maganin ?
Baida matsala mami yanzun zan fito ya fada yana maida kanshi ga filon da ya dago akai.
Ido mami ta dan kura mai kafin tace zaka jawa kanka matsala akan wanan yarinyar har da kwanciya ciwo don kawai na fadama gaskiya.
Murmushi kawai ya danyi tare da lumshe idanun shi ba tare daya iya mata magana ba ta mike tana fadin idan ba zaka iya fitowa insa lami ta kawo ma abin karyawan ka nan ka tashi ka karya ko zakaji saukin jikin.
Sai lokacin ya iya magana yace ba sai ta kawo min ba mami zan fito da kaina ai ya sake lumshe idon shi a hankali.
Mami a cikin dakewa take da karfin hali a lokacin don gaba daya hankalinta ya tashi ga halin data samu dan nata a ciki wanda take tunanen maganan su najiyane yaja masa wanan kwanciyar haka.
Hjy na zaune falo tana dakon fitowan hjy sai gata tun kan ta karaso take tambaya kin same shi a ciki ?
Yana nan hjy wai ashe baya jin dadin jikin sane yakw kwance daki shi kadai bai fadawa kowa ba.
Subbahanallahi me ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login