Showing 129001 words to 132000 words out of 191310 words

Chapter 44 - ABU CIKIN DUHU BY MAKAWA By abooks.com.ng.txt

Ba bata lokaci mu shiga sai wani girma da suke bamu kamar yadda suke bawa ogan su bayan mun zauna a motar sai ga ya mamud da dan saurin shi yana fadin hjy kuje zan shigo zuwa an jima ko safe inda kuke ina son naga mami ne a yanzu.
Kada ka dami dani mamuda zauna da uwarku kada ta aikata abinda bai dace ba ga dan uwanka.
Saida safe sukayiwa juna suka kama hanya damu duk da kuka nake bai hanani kallon titin garin ba don ba fitan dare nakeyi ba a garin.
Wani gida da zance yafi na mami tsaruwa da komai ga motoci nan zube kamar wurin sayar dasu suka shiga damu gidan.
Bayan motar ta tsaya ne da sauri security din dake gaba ya fito daga motar ya bude mana muka fito daga cikin motar zuwa cikin gidan a tare da biyu daga cikin su sai faman nan nan suke damu kamar wasu manyan baki.
Gidane har gida don in tsaya fadan tsarin ginan zai bata muna lokaci yanzu ba zaka taba cewa wai a wanan kasan wanan ginan yake ba duk ko da lokacin darene don goma dare har ya dan gwauta a lokacin.
A falo muka zauna a daidai lokacin da sako ke shigowa wayan wanda nake gani shine babban su ya duba tare da daukan jakkar hjy da nawa zuwa sama.
Bai dade ba ya dawo da sauri falon suka fita ina makale a jikin hjy har lokacin don kamar dumin jikintane zai tsimakamin ga abinda nakeji a rayuwana.
Muryan hjy ne ke fadin kinga dagani haka kada ki karasani yar nan ina yanzun dai komai yazo karshe a wurin ki.
Ban daga din ba sai kara shiga jikinta danayi a lokacin bata kara tanka min ba illama tausayina daya kara shiga jikin ta a lokacin.
Sun dawo dauke da ledojin abinci a hannayen su tare da abinsha dayan da ban taba tsamanin yana jin hausa bane yake fadin hjy ga abinci oga yace mu kawo maku kuci mu tabbatar da kunci kun koshi kafi mu fita yana magana cike da bada umurni a gareni.
Kaiya dan nan wani abinci zamu ci a wanan halin kaimu inda zamu yada kan mu kafin gari ya waye mu kama gaban mu ko yanzu don darene da zance ka kaimu tasha kawai mu shiga motar kaduna zuwa gida.
Don nasan idan Allah ya saukemu kaduna lafiya gida ba zaiyi wahala a garemu ba.
Umurnin ogane mu sa kuci abincin nan kafi ku kwanta ya fada yana kokarin bude abincin dake gaban mu da sauri yaci gaba da fadin ki taimakemu tsohuwa kuci abincin nan kada mu samu matsala ga aikin mu don Allah.
Jin abinda ya fada yasa jikin hjy sanyi ta dago habana tana fadin kinga tashi koba dadi ya zama dole muci abincin nan don wanan mai kiran samudawan yabarmu mu zauna lafiya gidan nan.
Abincine irin na gani na fada sai kamshi ke tashi kallon abincin nayi na kawar da kaina daga kallon shi ina kokarin komawa in kwanta.
Kinsan duk wanan abin don ki nakeyin shi don haka kada ki bari mu samu matsala dake a wurin nan hjy ta fada batare da ta kalloni ba.
Dole na mike na sauko daga sama kujeran zuwa kasan wani kafet mai laushi dake shimfide a falon komai na gidan abin kallone.
Jin abinda hjy ta fada yasa na fara kai abincin a bakina a hankali duk da ba komai nake diba ba sosai a spoon din.
Bai wuce sau uku ba ina kaiwa a baki sai ga amai na shirin zubo min ganin hakan yasa hjy fadin ki barshi ida bakyaci kada ki jawa kanki wani matsala kuma.
Haka yasani tashi daga wurin na koma inda nake kwance da farko na kara nadewa a cikin hijjibin da Allah ya taimakeni na dauko kafin in bar gidan mami din daga shi sai rigar dake jikina kawai na fito dashi gidan da mami tayi min koran kare akan laifin da bani na aikata ba.
A can gidan mami kuma bayan fitar mu daga gidan tare da hjy mami ta kasa furta komai ga yaranta sai shiru da tayi tana faman karkada kafafuwanta a hankali.
Ita kadai tasan irin yanayin da take ciki a lokacin don yanayin da take jin kanta zuciyar ta zai iya bugawa take a wurin idan tayi yunkurin yin magana a lokacin.
Ya mamud ne daya dawo daga rakamu yake fadin mami da baki bar hjy sun tafi ba a cikin daren nan wanan abu bai dace ba mami hjy fa tai fushi dake sosai mami tunda har ta iya sa kafa ta bar gidan nan.
Jajjayen idanuwan ta ta dago tana fadi da kyat mamud ya kake son inyi da hajiyan mu a gaban ka akai komai amma kaji irin hukuncin da hjy ta yanke min a karshe.
Yau an wayi gari saboda wanan yarinyar mahaifiyata tayi fushi dani haka a rayuwana don kawai, , , ,
No mami don Allah ki daina fadin don zeey ce hjy tayi wanan don yaya J ne gashi a zaune badon zeey hjy tayi fushi dake ba mami jamal ya fada a cikin bacin rai.
Mami kina saurin fushi yanzu wanda hakan bai dace ba idan munyi maki haka ba zaki taba jin dadi ba a rayuwan ki don me zaki bari har wanan zancen ya kaiku haka da hjy .
Aurene dai an riga an daurashi a bisa jagorancin kawu hamza da baffa sulaiman da sauran yan uwa da abo, , , ,
Mamud zaka bace min a wurin nan kafin rayukan ku ya kai ga baci ko sai na saba maku gaba dayan ku wurin nan zaku fice ku bani wuri.
Mikewa tayi kokarin sai kafanta ya kasa daukan ta da sauri jalal ya karaso inda yake ya kamata zuwa daki ko kallon inda sauran suke bata kara yi ba.
Saida ya kaita daki ya zaunar da ita saman gado tare da tambayan ta ko akwai wani abinda zai mata a lokacin.
Kai kawai ta iya girgiza mai ya juya yana kokarin fita daga dakin yaji ta ambaci sunan shi haka yasashi juyowa gare ta.
Jalal ta sake fada ina son kai min aikin siri a gidan nan kayi kokarin bincika min inda yayan ku yakai hjy da yarinyar nan.
Haka kuma ka saka ido ga duk wani motsi na yayan ku har idan ya bar gidan nan ya fita kamar yadda na haneshi dayi ka fada min.
Yace insha Allahu mami zanyi abinda kikace yanzu kuwa zan saka ido ga duk wani motsi nasa Allah yai maka albarka ta fada tana kokarin hawa saman gadon da kyau tare da fadin ka turo min Aisha yanzun nan yace angama mami ya fita.
Ya turo mata Aisha shi kuma ya fice wurin dan uwanshi don yasan yana can yana jiranshi don bai ganshi a falo ba inda ya barsu.
Yana shiga ya samu jamal kwance rigingine yayi filo da kanshi ba tare da ya dago ya kalli dan uwan ba yake fadin.
Yanzu kaine dan leken asirin mami ashe a gidan nan kallon shi jalal yayi da sauri yana fadin yaya akayi ka sanda hakan yana kaiwa zaune gefen shi.
Nasan hakan zai faru kowama yasan da hakan ya dago yana fuskantar dan uwan tagwaicin nasa kafin yace dashi.
Amma kasan idan ka fadawa mami wani zance kan ya jafar kajawa kanka matsala a gidan nan ko ?
Hauka nake da zan fada mata wani abinda zai kara jefata a cikin damuwa komai ba zan fada ba koda kuwa nasan inda suke din .
Kaje ya j na kiranka ya fada yana komawa kwance bai tsaya ba ya nufi part din dan uwan nasu.
Ya sameshi yana waya don haka ya dakata a wurin har ya kare wayan shi inda ya fahinci dan uwan nasu yana shirin barin kasan a lokacin.
A hanku zan bar hjy da yarunyar nan don ni zan koma wurin aikina ina da aiyukan da suke jirana a can ya fada ba tare daya kallo dan uwan nasa ba dake gefen shi.
Amma bro in mami ta fahinci hakan zamu shiga cikin fushinta muna don yanzu ta ban assgment a kan ka da inda kuka kai hjy din.
Fine yana da kyau ka fada mata ai ban kaisu ko ina ba sai gidana da ba wanda ya sani nan cikin garin abuja .
Akwai wani abu kuma ya fada yana dago kai don kallon fuskan jalal din dake tsaye a gefen shi.
Zamu kulasu yadda kakw so saidai nasan mami zata saka ido muma a kan mu why not ka wuce da yarinyar nan gaba daya ku bar kasan nan a tare.
Ba yanzu ba ya bashi sa yana mikewa zai shige bedroom din shi ya barshi a wurin amma bro in har ma, , , ,
Ka iya bakin ka ya fada a gagauce ya shige ya barshi wurin tsaye girgiza kai yayi ya fita tare da rufo masa kofa ya bar dakin.
Mami kan wanan daren yadda taga safiya haka daren yazo mata don hankalinta a tashe yake har lokacin abinda zuciyar ta ke bata shine nine na jawo komai tsakanin mahaifiyar ta da danta.
Taga laifin anty safiya yafi dubu a wanan daren daga baya kuma ta fara hangen nacin jafar ne ya jawo wanan matsalan haka.
Don me su baffa zasuyi mata haka har su daurawa danta aure da wata yar aikinta ba tare da sanin ta ba ma,ana dai sun goyi bayan yayi mata rasgin biyayya ke nan ko me ?
Idan ko hakane zata nuna masu itace uwa a gareshi ba su ba don wanan auren yadda suka daurashi dolene su warwareshi da kansu kamar yadda sukaje aka daura din.
Washe gari haka ta tashi babu karfin jiki a tare da ita har hakan ya jawo mata saukan kasala a jikinta ta kasa fita zuwa office wurin aiki.
Kiran da ake mata a waya baya shiga yasa hjy maria nufo gidan mami din tsit ta samu gidan don ranan harsu kande sun shiga hankalinsu a gidan gani irin tashin hankalin da kowa yake cikin sa.
Don a gaban su komai ya wakana tsakanina da mami din da kuma hjy da irin hukuncin da hjy ta yanke a karshe wanda hakan ya kara daga masu hankali suna ganin wautar mami din data yarda har hjy tabar gidan dani.
A falo mami ta samu bakuwar nata ba tare da an kawo mata komai na motsa baki ba gaban ta wanda da ina gidan da yanzun na gama cika gaban bakuwar mami din da abin motsa baki koda kuwa ba zata taba komai daga ciki ba.
Duk da mami na a cikin fushi hakan bai hanata kwalawa sabuwar mai aikin ta kira ba tana tambayan ta dalilin rashin kawowa bakuwar ta ruwa.
Tace hjy kiyi hankuri bansan da zuwan ta bane tafi ki ban wuri da wanan magana kina ina har ayi bako baki sani ba meye aikin ki a gidan nan maza ki dauko mata kafin ranki yakai ga baci.
Ta juya wurin bakuwar data rike haba tana kallonta da mamakin abinda ke tafe da ita hjy maria kin taso ashe ta fada tana kaiwa zaune.
Na taso hjy maryam keda wanan labarin daya karade garin nan ko ince kasan nan baki daya jiya ke kuma ga wayan ki a kashe.
Tsuki mami taja tana fadin yaron yanzun aisai ka barshi inda ka ganshi ni yanzu ba zancen shine abin damuwa ba a gareni sai zancen hjy na data sha min yaji kan wanan maganan.
Subbahanallahi ta fada da mamaki tare da fadin mama din tayi fushi akan me kuma har hakan ya faru ?
Kan dai zancen nan daya fada don me zan dauki mataki hjy tace tare da nuna fushin ta a gareni.
Dama abinda yake so ke nan a tsakanin mu ai ya aikata hakan don yasan zata kama mashi ba hjy ba kawai could you imaging wai har da yayana da kanin mahaifinsu yaron nan yabi ta baya suka tsaya mai aka daura mai aure ban sani ba.
Kai ki bari don Allah hjy maryam suko don me zasu mana haka yaro da gatan shi ai mashi wanan aure na mumuke kamar mara gata.
Mami tace ai sai su san yadda zasuyi su walwale wanan auren don bai dauru ba wallahi indai nina haifi abina.
Hakkuri za ayi abi abin a sannu tunda an riga da an daura a yanzu sai dai in wanda zaki maine ya biyo bayan wanan din.
Kai ina nerve hakan ba zai yuyu ba ina fada maki ni har yanzu ai ban gama yanke shawara kan zancen ba don uffan bance da shi ba har yanzu.
Ranan dai haka kawayen mami sukai ta zuwa gidan wai da sunan zuwa tayata murna jin danta yayi aure ashe basu sani ba kowa dai da irin gulman dake kawo shi gidan.
A karshe dai mami tace duk wanda yazo masu gadi suce ta fita wani meeting sai dare zata dawo gidan.
Bata ga shi ba kuma bata tambaya ba saima da darene ya mamud ya shigo da likita tana falo a lokacin ya tsaya gaida ita yake fada mata ya dauko likitane ya duba Jafar tun safe yana kwance a dakin shi.
Bata tsunka mashi ba balle Allah ya sauwaka har suka shiga suka dubashi suka fito likitan yai mata saida safe.
Tana kallon yadda yan uwan shi ke sintiri a part din shi a karshe ma tashi tayi daga falon ta shige dakin ta da zuman ta kwanta ta huta ko zata samu barcin da batayi ba a daren jiyan.
Sai kuma ta samu dakin ba a gyare ba taja tsuki da masifa ta nufo waje tana kwalawa hannatu mai aikinta sabuwa kira da dan karfi.
Sai gata da sauri tun kan ta karaso mami ke fadin wai ke ko kinsan aikin ki a gidan nan kuwa.
Hjy nayi wani laifin ne kuma meya hana ki gyara min daki mami ta fada cike da takaici a fuskan ta a daidai lokacin ne kuma jamal yazo yana fadin.
Mami ya J fa baya jin dadi sosai tun safe yau a kwance yake bai kuma ci komai ba har yanzu.
Jamal ka ban wuri da wanan shirmen yaje ya kashe kansa idan zai iya indai kan wanan zancen ne ba zan taba yarda ba.
Amma mami ai da kin je kin, , , , jamal na fada maka ka kauce min a wurin nan kafin ranka ya baci kaima.
Jin hakan jamal din ya wuce a fusace ya nufi part din yayan nashi don ya kara duba halin da yake ciki.
Zama tayi a falon tana jiran Hannatu mai aiki ta karasa gyara mata dakin inda ba a dauki dogon lokaci ba hannatun tafito tana fadin hjy na gama.
Ta dan dago kai tare da fadin ok kawai ta mike don komawa dakin ta zauna saidai tana sa kai a dakin wani irin arm odor ya daki hancun mami kamar a lokacin hanne ke cikin dakin nata don hamamin warin hammatan dake tashi a dakin.
Da sauri mami takai bakin mirrow ta dauki room fresh tana fesawa a dakin a cikin takaici ta aje ta nufi bandakin don ta dan kewaya.
Bata saba ganin wurin nata a haka ba yasa bata tsaya jiran komai ba tafito ban dakin baya ta daure ta kewaya a matse.
Cikin takaici ta zauna bakin gadon ta tana jan tsuki tare da fadi a fili wanan banyi tsamanin zamu kai ko ina da ita ba.
Wanan gyaran daki kamar mahaukaciya ko yaro yana wanan aikin haka tana fada tana karasa shirin kwanciya matawa tayi ta dauko kwalin maganin ta da take sha duk dare kafin ta kwanta barci.
Tsuki taja tana bata rai tare da jin wani bakin ciki a ranta take ta fara tunanen wani abu a wurin wanda ya kara bata mata rai maganin dai a ranan mami bata shashi ba haka ta kwanta don kiuyan da takeji zuwa falon .
Baku zata iya kiran hanne yar aikinta takawo mata maganin don wani irin tashi da dakin kanyi idan yar aikin nata ta shigo dakin.
Mukan tun safe muke saka idon ganin wani daga cikin su yaya bamuga kowa ba hankalin hjy ya tashi don tacewa dayan security din ya kaimu tasha mu shiga motar kaduna..
Yace aiko bakin kofan gidan ba a bashi daman ya barmu mu taka do ance ya kulada mune sosai


ZAINAB IDRIS MAKAWA










🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅


3️⃣9️⃣


ZAINAB IDRIS MAKAWA


FATAN ALHERI GAREKU YAN UW MUSULMAI UBANGIJI YA KARA MUNA IMANI A ZUKATAN MU AMIN, , , , ,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login