Showing 75001 words to 78000 words out of 191310 words
Chapter 26 - ABU CIKIN DUHU BY MAKAWA By abooks.com.ng.txt
shi yayi datti.
Su Rufaida iyaka ta dasu gaisuwa in suga dama su amsa in basuga dama ba su kyaleni sai ko idan na gilma idan ba mami kusa su sakar min magana mai zafi sai dai kawai in hadiye ban fadawa kowa kamar yadda mami tace in fada mata idan sun min wani abu.
Ya safiya ma zuwanta biyu da muka zo tana wuni gidan a karshe kuma su kwasa da mami su fita don tunda mukazo da wuya mami ta zauna a gida.
A bakin Aisha nake jin wai kafn mu tafi za a karrama mami nan jahar ta ita da wasu manyan jahar da suka samu mukamai shine dalilin ma da zamu kara sati daya nan gaba.
Nikan naga sai manyan mutane ke shigowa suna fita gidan maza da mata suna ganawa da mami wani lokaci da yaya mamud don kome mami zatayi shine gaba wuri aiwatarwa a gidan sai dai shi baida daure fuska iri sauran fuskan shi a sake yake ko yaushe gayin ba,a da raha.
Sai ince wanan shirin dinner kamar yafi wanda aka hada masu a abuja haduwa don irin shirin da naga anayi da kudin da ake fitarwa.
Don kawai wana shagalin da za ai mata ake wanan barnar da kudin nake fadi a raina sai ga hjy itama tana fada kan hakan.
Andace rana bata karya saidai uwar diya tayi kunya har gashi ana gobe buki sai faman tanadar abinda zasu saka babba da yaro sukeyi a gidan.
Ina kallo sai kiyasta abubuwa nake a raina idan naji suna ihun da shewa yasu yasun a falin har anty Aisha da yanzu kan wanan abin takan dan zauna tare dasu wani lokaci.
Da farko hakan bai damuna abu ga mace kuma mai karancin shekaru irina a lokacin don haka na saka damuwa har na gaji na bakaina lafiya danayi wani tunanen cewa kilama badani za a tafi wurin dinner din ba kamar wancan na Abuja da yaya ya taimaka min ya tafi dani naga shagali kuma na samo abin bukin da har yau nake boyon su in kaiwa innar mu a gida idan zan tafi.
Muna daki da hjy ta gama cewa in bata ledan goro taci na dauko mata na zauna ya shigo dakin suka fara gaisawa ni dai banyi gigin gaidashi ba don ko na gaidashi din ba amsawa yakeyi ba.
Bai dade da zama ba sai ga Aisha dakin tana fadin hjy ni zan fita zuwa gyaran kai hjy tace shi jan ma har sai anje gun gyaran shi kamar wata kafira can dake ina dai irin gyaran kafirai din nan kike nufin zuwa.
Kaji hjy kuma da wani zance bros ni zan tafi daga inda nake bansan lokacin danace anty Aisha nima zan tafi.
Hjy ta jiyo inda nake tana fadin kema zaki tafi ai maki wanan banzan gyaran kanbna zamani yar nan a cikin mamaki take magana .
Ballema ina zan tafi dake haka zainab don me ba zaki da ita ba ya fada fuska daure karbi nan kuje ai mata itama.
Hjy tace balle yau daine da tayi sha,awan wanan abin ai, ina nan kuke ta sha,anin ku iyakarta ido ko dinkin nan bata samu albarkan ai mata shi ba gidan nan ina kallon hankalin iyami duk da aiyuka sun mata yawa.
Har dai muka fita daga dakin bayan ya cikawa Aisha hannu da kudi masu yawa da suka sani mamaki a cikin raina.
Aisha tayi mamaki kwarai lokacin da aka bude kaina da kullun yana cikin katon hulan da nake dunkule gashina a cikin sa ko kafi aula dubara baka taba ganin gashin kaina a gidan mami.
Don haka ba wanda yasan wanan sirin dana barwa kaina sani ni kadai ba a gidan mami ba kwai ko a garin mu inna tace kan dunkula min a daki da dare.
Aisha na kallon ikon Allah wayan ta yayi kara ta dauka ta kara a kunnen ta ni sai naji tana fadin to yaya daga nan din zamu wuce can insha Allah.
Ashe ya Jafar ne ya kira ta ya umurce ta kaini wurun sayar da kaya a zaba min don hjy ta fada mashi ba a samu yu min dinkin fitar bukin bani don mami bata zauna ya kara da fasin kin san kuma tunda hjy ta fadi dole ayi basai mami ta sani ba tunda aiyuka sunyi mata yawa ranakun nan .
Muna gamawa driver na waje na jiran mu don bata jan mota ita saboda mami bata yarda da hakan ba wai bata gama sanin garin ba.
Ina mamaki idan ta dauko kayan yadda take gwadawa a jikinta kafin ta gwada a nawa jikin kayane masu kyau kala biyar babu na yarwa a cikin su.
Ina kallo ta biya bayan ta hada da jakka da takalmi ko wani kayan muka dauki hanyan gida mami ko sai kira takeyi wai mun dade a waje ga hjy na fadan haka kuma.
Dakin ta muka shiga da komai da muka sayo na wuce zuwa dakin mu ina shiga hjy fada sosai ta hau ni dashi wai na biyewa Aisha munyi dare a waje.
Kala bance ba don ba dabi,a na bane babba na magana ina bashi amsa lokacin sai bayan mun idar da sallah magariba har isha i har lokacin na kasa sakin jiki a dakin har hjy ta kare abinda takeyi ta juyo inda nake tana fadin
Yi hakkuri yar nan kin san garin kaduna ba kamar sauran garuruwa bane girma ga kuma yan daukan amarya a sasssan shi.
Shine yasa kukaga hankali bai kwanta ba don Allah ku daina fita kukai yamma garin nan.
Hjy kiyi hakkuri in Allah ya yarda ba zamu karan hakan ba tace ya wuce a cikin wani sauti dake nuna bacin ranta har lokacin.
Ni dai nayi shiru gefe daya nasha jinin jikina nasan tunda hjy ta hasala haka damu na mami sai yafi nata zafi.
Aikuwa ban gama tunane ba mami ta shigo dakin fada sosai mami tayi min a dakin kafin ta juya ta fita .
Duk sai naji ba dadi a raina duk da nasan ba nice mai laifin ba amma kuma anga laifina a hakan ko sun mata da ni yar rakiyace kawai.
Sai washe gari na samu hjy ta dan sake mun fuska muka koma daidai a dakin da ita har tana jana da hira tana fadin wanan gyaran kan danayi ya kara fitar min da suran fuskana a fili.
Yar nan ashe haka kike da kyau kike munanta kanki baki gyara don Allah ki rika gyara kanki kina kwalliya kina fitar da suran ki waje.
Ni dai sai dan murmushi nakeyi ina jin dadin yadda tsohuwar ke yabani koba komai dai na samu wace ta nuna min kauna nima kamar kowa.
Hankalin kowa ya dauke gaba daya a gidan ma kuma cike yake da mutane don haka na makale daki tare da hjy sai jefi nake zuwa in leka dakin mami indanyi wani abin.
Karfe bakwai kamar kowa jira yake yayi don dai shiga wanka akeyi ana shiryawa saiga anty Aisha ta shigo tana fadin ke zainab na manta da kayan nan ai da sauri na dago ina kallon kayan da take magana akai.
Kayan jiyane dana rakata ta sayo take miko min da sauri na karba ina fadin Anty nikika sayawa dama ?
No bani ba ya J ne ya bada kudi a saya maki jiya bayan fitar mu ai mantawa nayi na baki tun jiya wanan tsohuwar tasa mami na muna fada kawai kamar yara kanana ne mu.
Nikan banbi ta nasu ba hankalina yana gurin kayan duk na rikice don murna har ta gama ta fita ba,a jima ba ta aiko kirana nazo.
Da sauri na mike nabar hjy da muke kallon kayan a dakin mu tare na nufi dakin Aisha watace ke mata kwalliy a fuska ina shiga taks ce min zauna a gyara maki fuska ba tare data dubo in danake ba.
Wurin na samu na zauna saiga mami ta leko tana fadin kin san fa tare dake zan fita ki shirya ku fito mu tafi haka yasa akaiwa anty Aisha a gurguje ta shirya ta fita ta barni a dakin da mai kwalliyan.
Ina mamain yadda mai kwalliyan ta zauna ta shiryani kafin in fito gidan har ya koma shiru duk an watse zuwa wurin buki.
Raina naji ya baci ina raya ni yanzu wa zanbi kuma tunda wayanda na sani sun wuce sun barni a gida ba tare da kowa ya kulani ba.
Rigar da mai kwalliyan ta shirya ni aciki nake faman tatarawa don kada in fadi kasa don yayi min dan tsawo saidai tace dana saka takalma zai zauna daidai a jikina .
Har tafiyan da zanyi da yadda zan rike jakka ta nuna min ni dai sai dariya take bami a raina ina fadin wa zai tsaya kallona a wurin
balle yaga tafiyana.
Takon takalma da kamshin shi ya dawo da hankalin mu surin da muke jiyo takon ya fito naji matar na fadin sir mun gama you can go now.
Thank you yace da ita nikan na nufi dakin mu tunda naji sun fara magana ban tsaya ta kansu ba tunda naga mai tafiya dani yau ko bai amsawa zanyi kundun bala in daure in tambayeshi ya tafi dani.
Sai gashi dakin yana sallama hjy ke fadin a,a miskili kafi gaban gaiya ba,a fita ba ashe yace sai yanzu hjy ko munyi sauri zuwa ba farawa zasuyi da wuri ba.
Ke fito mu tafi ya fada fuska daure hjy tace dan albarka kamar ka sani yanzu ta shigo tana min korafin an tafi an barta har ina shirin kiran uwarku ta turo a dauke ta yanzu.
Mun tafi sai mun dawo ya fada ba tare daya tsaya ya bata amsa ba don da alama sauri yake kada ya makara a wurin taron.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
2️⃣3️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
UBANGIJI ALLAH KA SADAMU DA ALHERIN DAKE CIKIN WANAN RANAN KA KAREMU DAGA DUK WANI ABIN CUTARWA DUNIYA DA LAHIRA AMIN.
Ba a karanta min labari idan baki bani dan na saka data ba don posting idan kin karanta na biki bashi zaki biya.
Gabana ya fadi don jin abinda ya fada ba shiri na mike nabi bayan shi saida hjy tace takalman fa na dawo na saka na dauki dan jakkar hannun na rike.
Tsaye yake a falo na zata zan gansu da wanan mai kwalliyan sai naga babu ita babu labarinta wurin.
Sai shi kadai yana kallon kofan fitowa jin takona tafe ya fara tafiya saida ya fita daga kofan falon yaja ya tsaya wuri daya.
A nan na same shi ba tare daya kalleni ba ya fara magana kamar haka ki kama kanki ki natsu fiye da yadda kowa ya kama kanshi a wurin banda kauyanci da kalle kale duk abinda nayi maki ban son musu ko gardama so be cool kamar yadda na umurce ki.
Duk da hausa yakeyi wai saidai kamal turanci yayi yawa ga maganan shi amma ba laifi ga dan turancin dana iya ina fahintar shi hakana.
Ma,ana dai akwai abinda ke shirin faruwa a wurin yake min indirect akai wanda na kasa fahintar hakan a raina.
Har ya fara tafiya naga yaja ya tsaya sai na tashi karo dashi wani wawan tsuki yaja yana fadin idan kikai min wanan wautar taki wurin nan tun acan zan balbalaki.
Saboda haka kada ki bari in kara wuceki tunda ba dodo nake ba kuma ba sauri nakeyi ba.
Ya takalman kafanane ban iya tafiya dashi don ban taba saka irin shi ba kallon kafan nawa yayi ya kawar da kai don gaba daya shigar tawa ya tsorata shi wurin sai take ganin bani bace a gaban shi.
Kamar yadda yace hakan muka jero gabana sai faduwa yake min kamshin shi kamar a hancin na aka zuba turaren.
Security din shi suna hango mu mun fito sukayo kan mu suna gaidashi tare dani tunda sun gani tare dashi.
Umurni naji ya basu cikin turancin da baikai can ba suka amsa da yes boss da sauri wani daga ciki ke bude motar maimakon ya shiga sai kawai naji ya riko min hannu sai da gabana ya fadi uku uku don tsoro da bazatan da yai min lokacin .
Kofan da zan zauna ya nufa ya bude min na shiga ya ya rufo a hankali sai ya juya ya nufi dayan bangaren da daya daga cikin security din ke rike da kofan yana shiga aka rufe motar suma suka shiga nasu.
Mami dake zaune cikin taron duk rashin ganin shi hankalinta bai kwanta ba duk da ga sauran yan uwansa a gurin.
Table daya aka ware mata daga ita sai diyan ta sai anty Nuriya da ban san da zuwan taba a gurin, kujera biyu ya rage shine kujeran da Jafar zai zauna tare da matar dayace wa mami yau zai nunawa kowa a gurin wanda mami ta rigada ta gama sanarwa MC ya fada tun dazun kuma yake faman sanar da yau dan mami din nan matashi da duniya ke ji dashi saboda ilimi da nagartan iya sarrafa computer zai bayanawa kowa abin kaunar shi.
Haka yasa mami zaran ido kadan kadan ta kalli hanyar shigowa don ganin bai karaso ba yau dai tana son ganin wanan yar mai sa, a haka a duniya da har ta iya sace zuciyar danta dake gudun mata.
Wanda har ta fara zargin kodai aljannu ne suka aure shi bata farga ba don duk yar data nuna mai sai yace batai mashi ba shi.
A lokacin kuma shima yana faman tunane a ranshi ne yadda mutane zasu dubi zabin nasa yadda aka kwallafa rai da cewa diyar wani kusa zai kawo ko diyar wani hamshakin mai kudi a kasan .
Yes yasan ba mami ba kowa ma a wurin zai iya ganin rashin dacewan su to saboda me ita din ba mace bace kamar kowa tunda mami ita ta matsa mai sai yayi aure .
Wanan itace kadai zai zaba ya zauna lafiya a rayuwan shi don zabin mami sam yasan ba zasuyi daidai.
Lumshe ido yayi yana gyara zama kodai ya fasa wanan shirmen da yake shirin aikatawa ne idan hakan zai kawo masu matsala da mami.
Shin meye laifin shi har in ya gabatar da wanan yarinyar a yau a matsayin macen da zai aura.
Itace yaji rashin ya kwanta da ita a matsayin abokiyar rayuwa kamar yadda mami ke shan fada mashi kullun idan tana masa nasiha yayi aure.
Shi gaba daya ya yarda da hakan har zuciyar shi da gangan jikin shi ya amince da wanan zabin nasa matukar zasu zauna lafiya.
Yasan yarinyar is pretty shi ba wanan yabi ba nashi tsarin ne a hakan aure dai akace yayi kuma ita din zai aura yasan ta hanyan shi yarinyar itama zata zama wani abu a duniya muddin dai tana tare dashi.
Ya dan muskuta kadan tare da gyara zaman shi yaci gaba da tunane yace a ransa yasan ko bai samu goyon nayan kowa ba zai samu na hjy matukar ba mamice ta zugata ba funda itace ta fara kawo mai wanan idea din a falonta.
Yasan amsan da zai ba duk wanda ya tun kareshi da rashin yardan wanan zabin nasa duk na kowa bai damesa kamar na mami ba.
Ko ita din a yanzu ya tanadi hujjojin da zai bata idan idan har ta nuna bata yarda ya auri yar nan nata ba.
Ido ya kara lumshewa a hankali yasan dole akwai aiki ja a gaban shi ba shi kadai ba yanzu har wanan yarinyar ya jefata a cikin dabon tashin hankali don dole ta fuskaci kalubali daga mutane da dama daga yau .
A yanzu kan yayi niyar hakan bayajin kiran kowa ko dakatarwan wani bai damu da duk abinda wani zai furta akan hakan da zaiyi ba.
Ya shirya daukan duk wani rigiman da zai taso na barazana a kan mu duk yadda mutane zasu kalli abinda zai aikata din shi a shirye yake .
Wurin ya hadu da manya da yara da masu ruwa da tsaki a gwaunati tarone na yan boko da suka amsa sunan boko a wurin.
Haka motar ta danno kai a cikin get din wurin inda hankalin yan sa ido ya dawo garta akwai daya a gaban mu sai wace muke ciki a tsakiya dayana bayan mu ma,ana dai sun saka mu a tsakiya ke nan.
A daidai lokacin da motar ta tsayane driver ya fita da sauri sai ya rage dagani sai shi a motar .
Ya dan ja lokaci ba tare da yai magana ba sai can ya danyi gyaran murya yana fadin ke ina son ki kara saurarena da kyau kiji me zan fada maki.
Na dan daga kai a cikin tsoro kamar kadangaruwa ya furzu wani iska kamar abinda zai fada ansashi ya fada dole ne lokacin.
Ya fara magana a cikin muryan nan nasa mai fidda wani irin amon sauti ya