Showing 27001 words to 30000 words out of 86718 words
duk sati mai kamawa za’ai ‘daurin auren, Ke kuma Islam sakamakon irin
k’ok’arin ki, da yanayin tarbiyarki da kyawawan ‘dabi’unki da kike dashi, baki zubarda mutuncin
ki ba, ha’ki’ka kin cancanci babbar gudunmawa daga gare mu, amma duk da haka nan bada
wani lokaci ba zamu aurar dake, saboda haka da xarar kin samu me son auren ki, ki fada sai
ayi bincike ayi auren, sannan yanzu bayan anyi ‘daurin auren su Hafsat, zamu nema maki
gurbin karatu a jami’a anan garin, zancen fita waje kuyi karatu yanzu an soke shi, Kiyi hak’uri
Insha Allahu xamu cika miki burin ki, Medicine xakiyi da yardar Allah, sannan inaso ki je ki nutsu
kafin sakamakon ki yafito muji wacce makaranta zaki yi, idanma a Lagos wurina kike so, to duk
ba matsala. Allah yasa albarka..”
Haka Inna Bilkisu ma ta sake yin fada mai ratsa jiki sosai, sannan aka watse akabar su Inna
suna tsara yadda al’amarin bikin zai kasance.
***
Rana bata ‘karya, sai dai uwar ‘diya taji kunya, domin ranar asabar da yamma bayan anyi
‘daurin auren Nuradden da safe a kaduna, da rana aka ‘daura na su Ibrahim, Kabeer, Yusuf. Sai
na ‘Alhaji Saminu Taura da amaryar sa Hafsat Khaleel Mai Mota, sai ‘Alhaji Muzammil Rimi’ da
amaryar sa Hidaya Khaleel Mai Mota. A satin ne kuma Nusrah matar Saifullahi ta haihu, tasamu
‘diya mace, aka sanya mata Nabeelah sunan mahaifiyar Saifullahi, amma xa’a dinga kiran ta da
Nana.
Yawan mafarkai kala-kala da yawan firgita su Haj Aysa keyi akai-akai , gaba d’aya ta zabge,
sihiri ba karya ba kallo d’aya xakai mata kasan jifanta akeyi, hakan yasanya Yakolo yiwa Dr
Khaleel shawara kan ya canzawa Aysan gidah. Domin kishiyoyi sun sata a gaba, Hakana Helwa
data samu ciki sai ya b’are. Ganin haka yasanya Dr Khaleel gyara wani gidan sa dake kusada
gidan su Humairah wato gidan Alhaji Mommodu Mele. Nan ya mayarda Haj Aysa da Helwa, Ai
kuwa sun sami sauk’i bayan anyiyyi musu add’uoi sun kuma yi amfani da ganyen magarya. Can
gidan kuma yakoma daga Yafendo sai Karimatu, wanda har yanzu ba su sauke ‘damarar shiga
malaman da suke yi ba.. Abun dai sai dai muce Allah ya kyauta kawai...
*GIDAN ALHAJI MOMMODU MELE*
Shiirye-shryen tarbar dawowar Khaled ake daga ‘kasar Spain, masu aikine keta kara-kaina........
_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_
*_NA*_
_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_
® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_
*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_
*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_
_BILLYN ABDUL_
*_SHAFI NA 22-23_*
_SHAFIN YAU NA KUNE ‘YAN GRP DIN *HAJJAH CE NOVELS*, MUSAMMAN
*@MAMANSADEEQ & @PRETTY JIDDAHLURV_ *._INA GODIYA ‘KWARAI DA
YADDA KUKE BIBIYAR LITTAFIN *SAIFUL_ISLAM*_
_nanahafsat.wordpress.com_
*GIDAN AJI MOMMODU MELE*
Shirye-shiryen dawowar Khaled akeyi daga ‘kasar Spain, gaba d’aya masu aikin gidan ne keta
kara-kaina a kitchen suna had’a masa abinci komai atsare. Lokaci zuwa lokaci Haj Latifa
(mahaifiyar sa) kan shiga kitchen ‘din don ganin anyi komai a tsare, kuma cikin tsafta.
Haj Latifa na tsaye jikin kitchen cabinet, tana gyarawa wata mai aiki yadda xata hada ‘coleslaw’.
Humaira tashiga cikin kitchen ‘din, tana tafe tana gyara zaman agogon ta dake ‘daure a
wutsiyar hannunta. Sanya take cikin abaya baka tayi rolling kanta, hannun ta rike da y’ar purse
‘dinta.
Hannu tasa ta ‘dan gutsiri maras da ake yayyan kashi ta jefa a bakin ta, kafin tace,
“Umma. Zanje gidan su Islam, zandawo kafin a ‘dakko Ya Khaled a airport.”
Kad’a kai Haj Latifan tayi, kafin tace,
“Karki jima Humaira, nasan halin ku idan kuka had’u da Islam.”
“Insha Allah Umma.. Sai na dawo” ta fada tana ficewa daga kitchen din
“Allah ya tsare... “
Sai kuma ta juya wajen Kande mai aiki, tana gyara mata yadda take ‘kokarin danna naman
akan abun gashi.
“Ha’a Kande ki bari naman yayi marinating kafin kiyi grilling mana haba.”
*DR KHALEEL’s*
A kitchen Humaira ta tarar da Islam tana tuk’in tuwo, ta rage gas tana jiran ya turara ta sauke
shi, da gudu Islam tai hugging Humaira cike da jin dad’i, Humaira ta yatsine fuska tana bin Islam
da kallo,
“Ke kam kinason girki, ‘karama dake kike girki? bayan ga masu aiki.”
Girgiza kai Islam tayi, tana jaddadawa Hari mai aiki ta kwashe tuwon, cikin murmushi tace da
Humaira,
“Babes, wallahi tun banaso sai da na koya, Ammi tace hakan nada kyau idan nayi aure na
huta, Ai kuwa tuni yanzu kinga yadda na iya abinci kala-kala kuwa?”
Tabe baki Humaira tayi, kafin tace.
“Hu’uhm! Ni kuwa na tsani girki, kuma idan nayi aure masu aiki Umma xata dakko su dinga yi
mun”
Kad’a kai kawai Islam tayi, taja hannun ta sukai sama, dakinta suka shiga, Animation cartoon ta
saka musu na ‘princess and the frog’. Suna cikin kalla Lee tazo, nan suka kafa dabar hirar
school, zancen auren su Hidaya ya shigo, Humaira ta tsunture da daria tana rufe baki, kafin
tace.
“Naga mazajen su Hafsat a album na ‘daurin aure, wannan ai sun haife su.”
Lee ce ta amshe tana,
“Maganin su kenan, sun janyo at early age anyi musu aure.”
Islam dake gefe ta katse su tana daga hannuwa,
“Abeg abeg, enough. Su ai yanzu sun huta tunda sunyi auren su.”
Lee da Humaira suka tafa, suna kyalkyala daria, kafin Lee tace.
“Kowa zeyi ai, ni kin tunomin ma Dawood ya isheni da maganar aure wallahi, nace mishi ni ba
yanzu xanyi aure ba yaki yadda”
Humaira ta kwashe da daria,
“Wallahi nima Yaseer ya isheni, nace mi shi sai na zama accountant tukun sa..”
Lokacin jin Islam ya dauke, tuni ta fada duniyar tunani. Ita kam haka xata xauna ba xatai aure
ba kenan? Shin me tayiwa maza da ba sa sonta haka?, Ta jima tana tunani sai da zazzafan
dundun da Lee ta zuba mata a baya ya dawo da ita dunia. Cikin daria Lee tace,
“Haba girly, tun daxu muke magana kinyi shunning dnmu, bama wannan ba tashi mu raka
Humaira gidah, brother dinta ya dawo.”
Mikewa Islam tayi, a tare suka sauka kasa parlorn Hajia aysha suka mata sallama, sannan suka
tafi gidan su Humaira.
*GIDAN ALHAJI SAMINU TAURA*
Zaune Hafsat take tana tsiyayar da hawaye agefen murhu, tunda aka kawo ta gidan take
aikatuwa, Haj Larai babbar matar Alh Saminu ta takura mata da tsangwama, yau ma dakyar ta
iya ‘karasa tuka tuwo a babbar tukunya mai cin kwano biyar, duk ya ‘kone ya koma tamkar
amala.
Daga ‘dakin ta Haj Larai tafito, da yake kowannen su ‘daki d’aya da parlor ne mallakin sa, sai
yammata xagada xagada ‘yayan Haj Laran, wanda kowannen su ya girmewa Hafsat nesa ba
kusa ba. Rissinawa Hafsat tayi tana cewa,
“Aunty na kammala..”
Ashar Haj Larai ta lailayo ta ‘durawa Hafsat, Tare da bata kyakkyawan ranqwashi a ‘kwanyar
kanta,
“Yanzu ke a gidan uban ki haka ake tuwo? Okay na tuna fa ke shafaffiya ce da mai, renon
kwanfilas (cornflakes), to bari kiji bar ganin Alhaji na rawar takashi akan ki, wallahi tallahi idan
kika ci gaba da ‘kona abincin gidan nan sai na lahira ya fiki jin dad’i.”
Cikin tsawa ta sake cewa,
“Wuce ki bani waje, banza mamugunciya, jia kin dafa taliya ta koma tamkar kunu, yau kin
maida tuwo kamar..”kasa ‘karasawa tayi tana haki, cikin iko tasa babban hannun ta tana
dungure mata kai.
Bata hak’uri tayi had’e da yin sum-sum ta mike ta koma ‘dakin ta, lokaci xuwa lokaci hawaye ke
y’ar tsere akan fuskarta, a hankali cike da tausayi take mai-maita,
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un”
*GIDAN ALHAJI MUZAMMIL RIMI*
Hidaya ce tsaye a tsakar gida tana tular wankin braziers da su pants na ‘yammatan Haj Deluwa
matar Alhaji Muzammil, tana yi tana d’aga hannayenta tana share gumin dake kwararo mata,
“Ke..” Fareedah babbar ‘yar Haj Deluwa takira Hidaya,
“Na’am” Hidaya ta amsa jikin ta na ‘bari.
“Ungo nan ban had’a miki da shi ba, yanzu na cire shi, kisa hypo ya wanku tatas..”
Sa hannu Hidaya tayi ta karba tana kukan zuci. Domin pant ne gaba d’aya ya jike da jinin
al’ada, sai ‘karni yake.
A ruwa ta jikashi tana mai canza mai ruwa lokaci zuwa lokaci. Sosai tafara hawaye ganin
Fareedah tabar wajen. Ko’a mafarki bata tab’a tsammanin irin wannan rayuwar ba, ita kanta
panties dinta a washing machine take sa su lokacin da take Abuja, amma yau wai itace mai
wanke na wasu mai ‘dauke da jini, jinin ma na al’ada. Wani abun takaicin ma Haj Deluwa idan
‘yan rashin kirkin suka tashi har sakar ‘duwawu takeyi ta narka uban kashi ta kuma tashi ta
barshi, Hidayan kuma ya xama dole ta kora ruwan(flushing). Da dare kuma Alh Muzammil ya
maida ita sex machine, budurinsa yake akanta, ko tunanin ita ‘din yarinya ce baya yi.
*BAYAN WANI LOKACI*
Sosai Islam shakuwa ta shiga tsakanin su da Khaled , takanas yake zuwa har gidan su suyi
hira, ko kuwa ya kira ta wayar Ammin su yaita janta da hira, hakan ya sanya Islam sawa a ranta
lalle khaled sonta yake da aure kuma.
Ganin irin muguwar shakuwar da sukai, Humairah ta tseguntawa Umman su wai soyayya Islam
da Ya Khaled suke yi, cike da jin dad’i Haj Latifa ta samu Khaled da maganar Islam, tashin farko
ya kwaso rantsuwa ya dire tare da ‘doriyar,
“Tab! Umma kenan. Ni wallahi ba son Islam nake da aure ba, na ‘dauketa tamkar Humaira a
zuciata, kuma yarinyar she’s fun to be with. Tanada ‘ko’kari..”
“Naji-Naji... Amma duk wannan alamun soyayya ne Khaled, wallahi yarinyar mutuniyar ‘kwarai
ce, kuma mahaifiyar ta baka ga yadda muke mutunci ba..”
Daria Khaled ya shiga yi harda rike ciki, harara Haj Latifa ta xabga masa ,hakan yasanya shi
rage sautin dariar sa, cikin gaskiyar sa yace.
“Allah Ummah.. Dagaske ba son Islam nake ba, already ina da wadda nake so wallahi, kuma
har munyi alqawarin aure”
Fushi Haj Latifa tayi da Khaled, ta mike tai ficewar ta, shi daria ma abun ya bashi wai suna
soyayya da Islam, yana cikin daria wayarsa tafara ‘kara, Islam shine sunan dake yawo akan
screen din wayar sa, ‘dagawa yayi ya kara a kunnensa,
“Hello Ya Khaled” zazzak’ar muryar Islam ta doki kunnen shi.
“Sisto!” Yafada yana ‘kara gyara kwanciyar da yai akan pillow.
“Ya Khaled inason maka wata magana.”
Mikewa yayi yana gyara button din rigar sa,
“Magana sis? Yaushe kikeson gani na?”
“Ko yanzu ma.” Tafada tana jan ‘maa din.
“Okay I’m on my way.”
Ya katse kiran bayan sunyi sallama, a gaggauce ya canxa kayan jikinsa ya fesa turaruka, da
kafa ya tafi gidan su Islam domin ba wani nisa. Yana zuwa ya kirata. A parlorn baki ta same shi,
sanye take cikin laffaya baka tayi kyau sosai. Cikin salon maganar sa dake tafiya da ‘yammata
yace,
“Kinyi kyau Mi lady.”
Murmushi tayi tana wasa da zoben yatsanta. Cikin shagwababbiyar muryar ta tace,
“Ya Khaled ina yini?”
“Lapia lou kanuri babe.. Ya su Ammi?”
“Ammi tana parlor, lalle ake mata”
Kad’a kai yayi yana sipping ruwan data kawo masa, yasha sosai kafin yace.
“Toh Mi Lady gani ko”
In’ina (stammering) tashiga yi,
“Ya Khaled da..Dama.. ca..nai”
“Menene Mi Lady uhm?” Yafada yana sake komawa kujerar dake kusa da tata.
Rufe fuska tayi, kafin cike da kunya tace.
“Ya Khaled, dan Allah kazo muyi aure, tunda kaga muna soyayya da kai.”
Baki bude yake kallon Islam, inde shirin da suke ta dauka soyayya ne, lalle ya yadda batasan
meye soyayya ba, ba kuma tafara taba har yanzu. Cikin dakewa yace,
“Ni zaki aura? You are not serious” Yafada hade da mikewa tsaye.
Durkusawa tayi tana k’ok’arin zubar da hawaye,
“Wallahi Allah ina sonka Ya Khaled, dan Allah ka yadda ka aure ni kar ayimin auren dole, Na
yadda ko ranar daurin auren ne kace kafasa aure na dan Allah, ko kuma ka...”
Dakatar da ita yai, ta hanyar ‘daga mata hannu, cikin ‘dagawar murya yace,
“Haba Islam, dududu shekarunki nawa? Idan kinyi nisa kiyi sha takwas, shirin da muke irin na
yaya da ‘kanwar sa shi kika ‘dauka a matsayin na saurayi da budurwa? kowa da kike gani idan
har Allah yayi yanada rabon aure wallahi zeyi, kuma wani baya auren matar wani, haka zalika
wata bata auren mijin wata. Duk inda kike a fadin dunia wallahi mijin ki na nan zuwa, Kiyi hak’uri
Islam, wallahi ni ba son aure nake miki ba, na daukeki a zuciata tamkar Humaira. Kisani cewar
slowly but surely khairan Insha Allah... Naki readymade din mijin na nan zuwa, wanda yafini
komai da izinin Allah. Kiyi hak’uri pls , ki yafemin dan wallahi inada wanda naiwa alqawarin
aure.”
Yana gama fada ya fice yana goge hawayen dake neman zubo masa, Islam kuwa tuni ta sulale
awajen tana kuka mai tsuma zuciyar duk wanda ya saurara, a yau takara tabbatarwa ita din
bakin jini ne da ita, wanda lokaci d’aya ta cire soyayya da son aure a ranta. Dakyar ta iya
mikewa ta koma sama, Ya Bala takira a waya ta sanar masa da tananan zuwa wani satin
Lagos, zatai hutu kafin su fara lectures a nan Nile university dake Abuja.
***
Khaled yana komawa gidah ya hada kayan sa a akwati, sallama yaiwa Umman su kan zaije
Lagos gidan Uncle Faruk( wan babansu) ya ‘dan kwana biyu kafin Vissa d’insa tafito ya koma
Spain ‘karo karatun Masters.
Bata hana shi ba, domin fushi take dashi, ita ta dauka akan maganar da sukai da ita ne daxu
yasan yashi ‘kaura daga garin, Batasan yayi hakanne don ya baiwa Islam lokaci ta cire sonsa a
ranta.
*LAGOS*
Karfe 5 dai-dai jirgin su ya sauka a airport din Murtala Muhammad dake Lagos. Dakyar Khaled
ya ciro waya ya kira Uncle Faruk cewar ya iso azo a ‘dauke shi.
Dake weekend ce Alhaji Faruk Muhammad(Uncle Faruk) yana gida da iyalin sa, matar sa Haj
Zuwaira ita kadai ce sai ‘ya’yan sa mata biyu, da maza biyu.
Aisha, Fatima, Adnan sai ‘dan autan su dake karatu a America mai suna... *SAIFULLAH*
_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER; MISS XOXO_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_
*_NA*_
_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_
® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_
*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_
*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_
_BILLYN ABDUL_
*_SHAFI NA 24-25_*
_SHAFIN YAU NA KI NE *ZEE YABOUR* xeexeecism Habeebtyn-Habeetyn baby
YasmeenAllah ya ‘kara basira ki cigaba da wantsalo mana FETTA_
_nanahafsat.wordpress.com_
Alhaji Faruk Muhammad ‘dan uwan Alhaji Mommodu Idris ne.Yaya ne ga Alhaji Mommodu
domin iyayen su daga tsatso ‘d’aya suka fito. Ma’ana ‘dan wa da ‘dan ‘kani suke. Mahaifin Alhaji
Muhammad Idris shine Yayan mahaifin Alhaji Faruk Muhammad. Zaman sa ya koma hannun
mahaifin Alhaji Muhammad, domin iyayen sa duk rasuwa sukai. Anan yai karatu, har Allah ya
kai shi babban matsayin da yake na likita, (surgeon).
Ya hadu da Mahaifiyar su Saifullah, wato Hajia Zuwaira a garin kano,’ bangaren galadanchi, a
asibitin Aminu kano. Lokacin ita kuma sun kawo mahaifin su baida lapia, anan ‘kauna ta’dore
mai tsanani har ta kai ga aure.
*4:00pm*
LAGOS (IDIROKO, MARYLAND)
Zaune Islam take, hannunta rik’e da Novel ‘din, ‘chasing Red by Isabelle Ronin’. Kusan kullum
hakan take ko dai kaga Qur’an, ko littafin daya ‘kunshi harkan medicine, sai kuma novels, da
suka zamar mata addiction.
Farida (Riri) ‘kanwar Haj Nabeelah ce, a gidan take a zaune tun lokacin tana ‘karama, domin
sa’ar su Islam ce, tashiga ‘dakin da Islam take, zama tai akan gadon tana duban Islam da sam
batasan shigowar tata ba,
“Peek a boo” Riri tafada da ‘karfi tanawa Islam gwalo, Ai kuwa Islam din ta ‘dan tsoro ta,
harararta tai cikin wasa tana tura baki gaba,
“Toh shagwab’abbiya, ke kam mijin ki yaga ta kansa da tsagwaran autanci, to ni dai tashi maza,
zamu ‘danje outing kiga gari.”
‘Dan yatsina fuska Islam tayi, kafin tace.
“No, not today pls, banason katse karatu na”
“Ke wallahi baki isa ba, Haba yarinya sai kace kunkuma, sannu matar ustax. Kullum kina ‘daka
kamar sabuwar amarya, da anyi magana kice this and that, abeg tashi muje nan kusa ne ba
jimawa zamuyi ba.”
Takaici kamar ta shak’e Riri haka take ji, a dole ta shiga band’aki ta ‘karayo wanka. Doguwar
riga ta saka mai launin sararin samaniya, ta yane kanta da mayafin rigar. Fita sukai itada Riri’,
domin su kad’aine ‘yammata a gidan yanzu, duk kowa ya watse. Mazanma sai dai ‘yan uwa na
‘y’ar gaya ko ‘yan uwan matan Ya Bala ‘din.
Riri ce ke driving, wani joint suka je, ba abunda akeyi sai zuk’ar shisa, joint ne daya amsa sunan
joint, domin clubbing ne na maza da mata, sai raye-raye akeyi ana busar shisa. Gefe d’aya
kuma kayan ‘kwalam da ma’kulashe ne. Gaba d’aya Islam kallo d’aya xakai mata kasan a
matukar tsoroce