Showing 33001 words to 36000 words out of 86718 words
ku, sannan akwai Munafukai, masu cece-kuce, idan da ace kishiyoyi za su
daina daukar guzuri-zoma, ta yadda idan suka ji magana za su tabbatar da ita kafin su yi
hakunci ga kishiyarsu da hakan ya rage kawo matsaloli. Amma ku duk kunyi fatali da wannan
idanuwan ku sun rufe, kun ‘dauki zugar shed’an kun d’orawa zuciyar ku, kuna aikata shirka,
domin wallahi had’a Allah da wanin sa shirka ne, zuwa wajen duba, da yan tsibbu suna gaya
muku ‘karya da gaskia, kuna zama akai, kun cusa mummunar ‘dabi’a aranku, kun ‘dau wani
qudri na ganin kunyi mai yiwuwa kun fidda wasun ku daga gidan, to ku gayamin da ta tada
rigima kar a auro ku, Allah ba za’a yin ba, dandai bakusan k’ok’arin da baiwar Allahn nan tai
muku bane da har ta bari aka auro ku,
“Dan ni ‘dinnan da kuke gani, ca nai sam a’a, kada ya ‘kara aure, Aysa ta isheshi zaman dunia
da ‘yan ‘yayan su, yace rufa muku asiri zai yi, barin ke Karimatu” inna bilkisu tafadi hakan tana
mai nuna da Karimatu, Kafin tace,
“Bazawara ce ke, mijin ki ya miki duka ya sakeki, Allah ya temaka babu rabon ‘yaya a tsakin ku,
kawun ki ya samu Khaleel da zancen ki, ya rufa miki asiri ya aure ki, Ke kuwa Amina(Yafendo),
ta tallan nonon shanu, Allah yai auren ku zai had’u, ta sanadiyyar kad’e ‘kanin ki da drivern sa
yayi, yaji tausayi bayan an kammala komai, yace xai aure ki ya temakawa Baffan ki da hidimar
ku, ganin kunyi yawa awajen sa, amma duk hakan bai isheku yin hankali, kun zauna da abokan
zaman ku lapia ba, Sai tada fitina da neman yadda zaku fiddasu daga gidan, Ku na jifansu da
sharri da sihiri kala-kala, wanda duk daga ‘k’arshe idan da zakuyi nazari kan ku yake dawowa,
kukan kurciya jawabi ne, mai hankali ke ganewa. Ko kunsan,
“Hukuncin sihiri, da bokanci da abunda suka ‘kunsa? To ku sani baya halatta ga ko marar lapia
ya je wajan bokaye da suke ikirarin sanin abubuwan da ke boye, wai don ya gano masa rashin
lafiyansa, kamar yadda baya halatta ya gasganta su cikin abinda su ka bayar da labarin sa ba,
domin su suna maganine ko kuma su kirawo aljanu domin su taimaka mu su akan abinda su ke
so, to wadannan hukuncinsu shi ne ‘kafirci’ idan sun yi ikirarin – ilimin gaibi, hakika Muslim ya
ruwaito cikin ingantaccan littafinsa, lallai Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
ya ce;
نمEE ىتأ افارع هلأسف نع ءيش مل لبقت هل ةالص نيعبرأ FFاموي
Ma’ana: “Duk Wanda ya je wajan dan’duba sai ya tambaye shi wani abu to ba za’a karbi sallar
sa ba ta kwana arba’in”. Kuma daga Abuhuraira Allah ya kara masa yarda daga Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata agareshi yace:
نمEE ىتأ انهاك هقدصف امب لوقي دقف رفك امب لزنأ ىلع دمحم ىلص الله هيلع .FFملسو
هاور وبأ دواد هرخو لهأ ننسلا هححصو مكاحلا نع يبنلا ىلص الله هيلع ملسو ظفلب نمEE ىتأ افارع وأ انهاك هقدصف امب لوقي دقف رفك
امب لزنأ ىلع دمحم ىلص الله هيلع .FFملسو
“Ma’ana: “Duk wanda ya je wajan boka sai kuma ya gasganta abinda ya ke cewa, to hakika ya
kafircewa abinda aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi”. Abu dawud ya ruwaito shi kuma ma’abota littattafan sunnah hudu sun fitar da shi, kuma
Hakim ya ingantashi daga Annabi tsirada amincin Allah su tabbata a gareshi da lafazin: “Duk wanda ya je wuri dan’duba ko boka sai ya gaskanta abinda yake cewa to hakika – ya
karficewa abinda aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agare
shi”.
Kuma daga Imran dan Husaini Allah ya karama sa yarda ya ce: Manzon Allah tsirada amincin
Allah su tabbata a gareshi ya ce:
سيلEE انم نم ريطت وأ ريطت هل وأ نهكت وأ نهكت هل وأ رحس وأ رحس ،هل نمو ىتأ انهاك هقدصف امب لوقي دقف رفك امب لزنأ ىلع دمحم
.FFﷺF><><><.)<>><><><><><ه<>><><><><><ر<>><><د<>
“Ma’ana: “Baya cikimmu duk wanda ya ke yin camfi ko a ke yi masa camfi ko ya yi bokanci ko
ake yi ma sa bokanci, ko ya yi sihiri, ko ya sa ayi mishi sihirin, duk kuma wanda ya je wajan
boka sai ya gaskantashi a aduk abinda yake cewa to hakika ya kafircewa abinda aka saukarwa
Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi”. Bazzar ne ya ruwaito shi da
Isnadi mai kyau.
“ saboda haka ku sani, A cikin wadan nan hadisai masu girma akwai hani game da zuwa wajan
‘yan’duba da bokaye da masu sihiri (asiri) da makamantansu, da kuma hukuncin tambayarsu da
kuma hukuncin gasganta su da bayanin narkon azaba akan haka. Domin hakika manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi hani akan zuwa wajan su da kuma tambayar
su da gaskanta su, domin abinda ke cikin haka na muni maigirma da hatsarin da ya ke babba
da mumunar makoma kuma domin lallai su makaryatane fajirai, kamar yadda ya ke cikin
wad’annan hadisai dana baku, wadannan Hadisai dalili ne cewa boka kafirine da mai sihiri
domin su biyun basu cimma manufar su sai ta hanyan yi wa aljanu hidma da bauta musu koma
bayan Allah kuma wannan kafurcewa Allah ne da kuma yi masa tarayya – tsarkakken sarki,
“Kuma mai gasganta su cikin abinda su ke cewa na sanin gaibu ya kasance kaman su ne, kuma
dukkan wanda ya karbi wadannan al’amura na abinda su ke bayarwa to hakika Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi ya barranta da shi, kuma baya halatta ga musulmi ya yarda
da abinda su ke rayawa cewa magani ne. Domin lallai wannan yana daga cikin bokanci da
rudar da mutane, kuma wanda ya yarda da hakan to hakika ya taimaka musu akan barnarsu da
kafircin su,
Hakanan kuma baya halatta ga wani mutum musulmi ya jewajansu – domin ya tambayesu
gameda wanda. Zai aurar da dansa ko wani makusancinsa ko kuma abunda ke iya kasancewa
tsakanin ma auratan biyu da danginsu na soyayya da cika alkawari ko kuma kiyayya da rabuwa
da makamantan haka;domin wannan yana daga cikin gaibi wanda babu wanda yasansu sai
Allah tsarkakke mada’au kaki.
“Kuma sihiri yana daga cikin abubuwa haramtattu na kafirci kamar yanda Allah mai girma
dad’au kaka yace cikin sha’anin mala’I kunnan biyu cikin suratul Bakarah: ﴿ْاوُعَبَّتٱَو اَم ْاوُلتَت ُنيِطَيَّشلٱ ىَلَع
ِكلُم َنَميَلُس اَمَو َرَفَك ُنَميَلُس َّنِكَلَو َنيِطَيَّشلٱ ْاوُرَفَك َنوُمِّلَعُي َساَّنلٱ َرحِّسلٱ اَمَو َل
ِ
زن
ُأ
ىَلَع ِنيَكَلَملٱ َلِباَبِب َتوُرَه َتوُرَمَو اَمَو ِناَمِّلَعُي نِم ٍدَح
َأ
ىَّتَح اَلوُقَي اَمَّنِإ ُنحَن ةَنتِف اَلَف رُفكَت َنوُمَّلَعَتَيَف اَمُهنِم اَم َنوُقِّرَفُي ِهِب َنيَب ِءرَملٱ ِهِجوَزَو اَمَو مُه َنيِّراَضِب ِهِب نِم ٍدَح
َأ
اَّل
ِإ ِنذِإِب ِ
هَّلل ٱ َنوُمَّلَعَتَيَو اَم
مُهُّرُضَي اَلَو مُهُعَفنَي دَقَلَو ْاوُمِلَع ِنَمَل ُهىَرَتشٱ اَم ُهَل يِف ِةَرِخألٱ نِم قَلَخ َسئِبَلَو اَم ْاوَرَش ِهِب مُهَسُفن
َأ
وَل ْاوُناَك َنوُمَلعَي١٠٢ ﴾
Ma’ana: “Kuma basu sanar da kowa ba balle suce: mu fitina kawai ne, saboda haka ka kafirta,”
balle har suke rarrabwa tsakanin mutum da matarsa dashi daga gare su. Kuma su (masu yin
sihirin) basu zama masu cutar da kowa da shiba, face da iznin Allah. Kuma suna neman ilimin
abin da yake cutar da su, kuma baya amfaninsu, kuma lallai ne, sun sani tabbas wanda ya saye
shi, baya da wani rabo lahira. Kuma tir da abinda Suka sauar da raukansu da shi, da sun
kasance suna sani)). Suratul Bakara, aya ta: 102,
“Sai kuma waccan ayar maigirma da ta yi nuni akan cewa lallai masu sihiri suna raba tsakanin
mutum da matarsa. Kamar yadda ta yi nuni kuma cewa lallai sihiri baya tasiri don karan kansa
ta fuskar amfanarwa ko cutaruwa, sai dai yana tasiri ne da iznin Allah wan ya riga ya kaddara
kuma ya kasantar, domin lallai Allah tsarkakke madaukaki shi ne ya halcci alkhairi da sharri,
hakika cutar ta yi girma kuma zaluncin ya yi tsanani ga wadannan masu kirkirar, wadanda su ka
gaji wadan nan ilimomi daga mushrikai su ka zo suka rikita masu raunin kwakwale da su, lallai
mu daga Allah mu ke kuma lalle mu gare shi zamu koma, Allah ya isar mana kuma madalla da
wakili wanda yake shi ne Allah.,
“Ma’aikin Allah ﷺ Ya sake cewa kuma
نمEE ىتأ افارع وأ انهاك هقدصف امب لوقي دقف رفك امب لزنأ ىلع دمحم ىلص الله هيلع .FFملسو
“Ma’ana: “Duk wanda ya je wajan danduba ko boka sai ya gaskanta shi da abinda ya ke cewa
to hakika ya kafircewa abinda aka saukar wa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su
tabbata agare shi”.
“Anan zan dakata, ku sani duk wannan ayoyi da hadisai na kawo su ne domin ku, saboda ku
tabbatar abunda kukeyi ba mai kyau bane, babban shirka ne, ko da nan gaba hakan zai zamto
silar shiryuwar ku, Ta haka har Allah yasa ku janyo ra’ayin masu hali irin naku, zuwa turbar
gaskia. Abunda na fada dai-dai Allah yabamu ladan, kura-kuren dake ciki rabbi yayafe min.”
“Ameen...” suka had’a baki d’aya wajen cewar hakan.
Ya Bala da Dr Khaleel ne suka ce da Inna Bilkisu,
“Toh! Inna Allah ya saka da alkhairi, mun ‘karu muma gaskia..”
Sannan Ya Bala ya ‘kark’are da,
“Toh Karimatu da Aminatu yanzu zamu ji daga bakin shi mai gidan naku kan wane hukunci ya
yanke abisa hakan. Domin a zahirin gaskia ni na cire hannuna a harkar ku, babu ruwana, baxan
dinga tilastashi ya hakura ba, akan yadda kuke cutar dashi. Saboda haka Khaleel ka yanke
hukuncin ka kawai, bansan Inna ba dai, amma ni duk hukuncin da ka yanke, Ina bayan ka,
domin sun cancanci kome kayi musu wallahi.”
Dr Khaleel ya ‘daga kai yana kallon su, Dan murmushin takaici yayi, kafin yace,
“Toh inna ni da na yanke hukuncin sallarmar su kawai, domin baxan iya xama suna cutar da ni
da ahali na ba, nan gaba bamusan mai zasu aikata ba.”
Wata gigicacciyar ‘kara suka saki, cikin zabura Karimatu ta fara sumbatu, Yafendo kuwa
rarrafawa tayi ta ‘riko ‘kafar Inna Bilkisu,
“Inna kiyi hak’uri, mun tuba, ba zamu sake ba wallahi, ni de.. Ni.. dai dama Yaya ce ke sa ni
aikata duk wani mummunan aiki, tace idan ba haka ba zata fiddani daga gidan..”
ashar Karimatu ta lailayo ta ‘dura mata, kafin kace me? Tuni duk sun to nawa kansu asiri,
baram-baram sukai da junan su, kowanne yana kwashe wa ‘dan uwan sa albarka. To dama
ance komai nisan dare gari zai waye, Allah zai bayyana mai gaskia, a ranar dai gaba d’aya duk
wani b’oyayyen al’amari sai da suka bayyana shi, har da yanda aka qullawa Safa makirci. Duk
kansu sai suka koma suna hararar junan. Dama haka ne rana dubu ta ‘barawo ce, d’aya kuma
dal ta mai kaya.
Inna Bilkisu tai hanzarin girgiza kai, kafin cikin dattako tace,
“Kar kai haka Khaleel, nasan kayi hak’uri, kana kanyi ma, karka zamto sauran maza masu
saurin yanke hukunci Khaleel, kayi hak’uri ka dubi girman Allah, ka sauqaqa hukuncin da za kai
musu, su ci darajar ‘ya’yan dake tsakanin ka dasu. Kayi hak’uri Khaleel, mata sunyi yawa yawa
agari, yan mata da zawarawa, hakika duk sanda akai saki, al’arshin ubangiji girgiza take, kaga
kuwa ba ‘karamin abu bane. Kayi hak’uri Khaleelu, Allah ya dubi hakurin da kai, ya cika maka
burikan ka, dunia da lahira, Allah ya muku albarka, ya tsare ku ya ‘kara kareku daga sharrin ma
sharranta.”
Sam Dr Khaleel bai so ba, amma ya xaiyi? Hakika zab’in iyaye shine zab’i nagari ba son rai ba.
Cikin taushasshiyar murya yace,
“Ameen Inna. Sun ci darajar ki, da wallahi hukuncin da na ‘dauka shine sawwake zaman mu
dasu tare, Allah yasa zab’in da kikai shine mafificin alkhairi, na janye qudurina, amma zamana
dasu a Abuja ya ‘kare Inna. Ita Karimatu zan mayar da ita can Bauchi inda gidan gona ta yake,
ita kuma Amina zata koma jigawa, saboda zan fara part time lecturing acan. Ina ga idan akai
haka, komai zai yi sauki, tunda zama waje ‘d’aya shine yakawo had’uwar kan su, dama cusa
mummunan ra’ayi a zukatan su.”
Jinjina kai Inna Bilkisu da Ya Bala sukai, alamun sun amince da hakan, Karimatu da Yafendo
kuwa sun ‘danji sauki a ransu. A washe-gari kuma aka ‘dakko su Hafsat daga kano, hade da
Hidaya dake Zaria. Sosai sun canxa tamkar basu ba, dukkan su, suka rankaya gidan Haj Aysa,
takanas daga umarnin Inna Bilkisu wacce ke jagorancin tafiyar. Hak’uri sosai suka shiga bata,
tamkar basu Karimatu ba, duk sunyi laushi, fadakarwar da Inna Bilkisu tayi musu, ta matukar
canza su, sai dai duk da haka Karimatu da Yafendo sun ‘dau mummunar gaba a tsakanin su,
Dan ko d’aya na magana, d’aya bata saka baki. Haka suka dawo gidah, suka kara neman
gafarar, Dr Khaleel. Ganin hakanne yasanya Inna Bilkisu baiwa Dr Khaleel shawarar ya ‘dan
saiwa su Hafsa da Hidaya matsakaicin gidah kowacce a garin da take aure, saboda zama waje
‘d’aya da kishiya babu dadi. Hakan kuwa akayi, da sati ya zagayo kuma kowacce cikin matan
biyu, wato Karimatu da Yafendo, ta koma sabon gidan ta, Karimatu a bauchi. Yafendo kuma a
Dutse/Jigawa.
LAGOS IDIROKO.
Bikin Fatima, yayar Saifullah aka yi, aka kaita gidan ta dake port-harcourt. Da sati ya zagayo
kuma Islam ta koma Abuja, Don fara lectures din first semester na MBBS.
*USA *
Harvard University(Cambridge)
Sosai convocation hall ya cika da students ,parents da kuma teachers. Kowa ka gani da
graduation gown a jikin sa, can na hango Saifullah. Sanye cikin graduation gown, tayi matukar
amsar jikin sa, ba kadan ba, kyakkyawa r fuskar sa ta kamala ta ‘kara cika da annushuwa.
Chancellor ‘din makarantar ne ya kirashi, nan aka bashi award na, best student of the year. Da
kuma first call student na department of Architecture. Awards dai kala-kala haka aka dinga kiran
sa ana bashi, Muslim student society of Cambridge ma sai da suka bashi award na, Mufti of the
year. Kai abun sai sam barka kawai, ba’a cewa komai.
Saifullah faruk muhammad, saurayi ne ‘dan shekara ashirin da takwas a dunia, ya kammala
senior secondary certificate d’insa anan Lagos, inda ya tsallaka nahiyar turai ya karanci fannin
architecture a first degree d’insa (Bsc. Architecture), bai dawo ba ya ‘dora da degree na biyu a
matakin harkar kasuwanci, wato master of business administration (MBA) .
Fari ne, amma ba irin dau ‘dinnan ba, kallo d’aya xakai masa kasan Allah yayi kyakkyawar
halitta, dogo ne sosai, sannan ba shida jiki, sannan bai cika rama ba, zamu iya kiransa
moderate. Yanada yalwataccen gashin kai dana gira, domin girarsa ta kusa had’ewa ma, tsabar
cikar ta. Yana da kwantaccen saje a gefan fuskar sa, wanda turawa ke kira sideburns. Idanuwan
sa dara-dara ne TubarkAllah. Hancinsa kuwa tamkar shiya zana shi dan tsawo, bakinsa dan
‘karami ne jawur dasu kamar ya shafa jambaki. Kai bayyana yadda saifullah yake tamkar bata
Lokaci ne, sai dai muce TubarkAllah kawai. Allah yayi halitta.
Yana karbar certificate d’insa yai apartment d’insa, ko takan friends d’insa dake kiran sa
bai-biba, domin bayason hayaniya. Shiysa yace su Baba(Uncle Faruk) ba sai sunxo ba ya yafe,
burjik ya tadda gifts boxes kala-kala da kati, duk na tayashi murna,
Girgiza kai yayi, shi sam mata suna bashi mamaki, yadda suke gaya masa suna sonshi, ko su
rubuto masa wasik’a, yawancin gifts dinma duk sunan ‘yammata ne akai. Ko takan su bai-biba
ya tattake wanda suka tokare mai bakin ‘kofa yai wucewar sa ciki, bakin sa ‘dauke da sallama,
jefar da gown din yayi a kan sofa, yana sakin siririn tsaki, kafin yace.
“So uncomfortable...!”
_banyi edit ba,pls ignore all typos_
_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_
*_NA*_
_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_
® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_
*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_
*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_
_BILLYN ABDUL_
*_SHAFI NA 26-27_*
_An amazing page, goes to an amazing person, this page is dedicated with love and
appreciation to my day one niggurh, my sissy and always a favorite fan of my novels.. *MISS
PINKY*, _.
_nanahafsat.wordpress.com_
*ABUJA*
Kallo ‘d’aya zakai musu kasan a matuk’ar tsorace suke. Karimatu jikin ta in banda rawa babu
abunda yake yi, Mutuniyar ku, Yafendo kuwa sai sakin tusa take yi. Girgiza kai Dr Khaleel yayi
kafin ya haura saman Karimatu abun sa, duk jikin sa babu dadi yake jinsa, a ransa kuwa ya
qudiri niyyar yanke zama dasu Karimatu, don kwarai xasu iya kisa, sam basu da imani.
Cikin hanzari ya ‘dakko wani brief case a gefan gadon sa, takaddu ne fal ciki, dake ‘dauke da
transcripts na students ‘d’insa, ‘kasa ya sauka. Ko kallo basu isheshi ba. Secretary ‘dinsa mai
suna ‘Mamman’ ya bawa y’ar jakar, yana jaddada masa da,
“Dan Allah Mamman kakkai wasarai-rai da sak’on nan, a yanzu ba sai anjima ba, ka taimaka ka
kaiwa ‘senate board members’. Saboda nagaya maka a yanzu haka wani aikin ne agaba na.”
Gyad’a kai Mamman yake tayi, alamun girmamawa da kuma cika alqawari, cikin ladabi da jakar
a hannun sa yace,
“Insha Allahu oga yanzu zan kai musu, karkaji komai. Your happiness is what matters me
most.”
Murmushi Dr Khaleel yayi, kafin ya sake bashi hannu suyi sallama, sashen sa ya koma ya
xauna, addu’oi kawai yake ambata a bakin sa, hannuwan