Showing 42001 words to 45000 words out of 86718 words
ya fito
dashi har ya nufi gida ba tare da ya tsaya Khaled d'in ba, kasan cewar besan lokacin da zai
gama magana da 'yar makocin tashi ba.
A can kuwa Khaled ne yayi musu sallama duk suka d'ago suka kallesa, duk da cewar Islam taji
dad'in ganinsa amman sai da taji kunya da nauyinsa, lokacin da ta tuno furta masa buk'atar ya
aureta amman ya watsa mata k'asa a ido yayi rejecting d'in buk'atar ta.
Cikin dauriya da kawar da jin nauyinsa da take ji ta zaro ido tare da kama hab'arta tana cewa.
“Kai! Yaya Khaled kaine kuwa?'”
Murmushi yayi yana shafar d'an gemun sa,
'”Nine Islam ashe nan kika dawo shi yasa idan naje gida bana ganinki?''”
Farrr tayi da idanunta tare da d'agowa ta kallesa nan taga shima ita yake kallo irin kallon da
yake mata har tayi tunanin ko sonta yake yi a baya shi yake mata yanzu tayi saurin sanya
hannunta a kirji tana yatsina fuska tare da turo baki tana cewa.
''Eh wallahi yaya Khaled nazo nan ina hutu dai, sannan ina zaune a gidan uncle d'ina wato
gidan su wannan kaifa?''
Murmushi yayi yana kallan Riri wacce ta kafesa da idanu kamar taga sabon abu, ya sosa d'an
gemunsa daya fara tarawa tare da cewa.
“Nima nazo gidan uncle d'ina wato dai gidan su wancan..'”
Yayi maganar yana juyawa dan nunawa su Islam inda Saifullah yake tsaye yaga wayam babu
kowa cikin jin kunya ya malk'aye hannunsa tare da cewa.
'”Ashe yabar gurin da yake jiran nawa, gaskiya naji dad'in ganinki Islam sosai.'”
“Nima naji dad'in ganinka yaya Khaled, bari mu tafi gida kar aga mun dad'e ayi mana fad'a ko a
hana mu yi gaki d'aya, sai mun sake had'uwa Yaya.”
Murmushi tayi tana wasa da yatsun hannunta dan ita har lokacin ta kasa yadda da cewar shifa
Khaled ba auranta zai yi ba, gani take kamar yana sonta amman shi sai waskewa yake yi, ganin
yadda yake kare mata kallo me cike da ma'anoni masu tarin yasa ta kuma sanya hannu ta
rungume kirjinta sabida yadda taga Khaled yana kallonsu tace dashi.
'”Yaya Khaled sai anjima.'”
'”Kai Islam sauri haka? Toh ki bani address d'in gidan da kike watak'ila na kawo miki ziyara wata
rana.”
“Okay babu damuwa yaya Khaleed, Riri please ki bawa yaya na address d'in gidan ku yadda
zaifi ganewa.'”
'”Okay toh ka bani phone number d'inki sai na turo maka yadda ba zaka manta ba.''”
Cewar Riri domin gabaki daya guy din ya tafi da ajinta babban abinda yake damun ta shine taga
kamar akwai soyayya tsakanin Islam dashi duba da yadda taga suna yiwa juna wani irin kallo
na kauna da soyayya, but zata san yadda tayi ta b'arar da gwamnatin Islam a wajansa ta shigar
da kanta domin yayi mata sosai. Lambar wayarsa ya bawa Riri wadda take sake karairaya
jikinta shi kuma duk hankalinsa yana can wajan Islam suna sallama kafin kowa ya wuce gida.
A d'aki Khaled ya tarar da Saifullah yana ta faman harhad'a takardu, Khaled ya fad'a kan gado
tare da mirginawa yayi rigingine yana cewa.
“Gaskiya my friend baka da kirki shine ko kajirani mu taho tare.” Saifullah ba tare daya d'ago ba
yace dashi.
“Da ban tsayaka ba yanzu waye ya dawo da kai? Ko wad'annan 'yan matan ne suka kawo ka
gidan?”
Dariya Khaled yayi domin yasan haushi Saifullah yaji sabida yaga ya kula mata bai san cewar
Islam 'yar uwar su bace domin makocinka duk talaucinsa duk kudinsa indai kun zauna tare toh
ya zama d'an uwanka, cikin dariyar yake cewa.
“Basu suka kawo ni ba nine na dawo da kaina, sannan dan ka ganni naje wajan su sabida
nasan ta ne shi yasa, wallahi yarinyar tana bani tausayi domin 'yan uwanta duk sunyi aure ita
kadai ce bata yi ba kuma mahaifinsu yana bada lokaci ne idan matum bai fito da miji ba toh
shine yake fito musu dashi a cikin abokansa, Allah yarinyar tana bani tausayi domin da kanta ta
buk'aci na aureta ni kuma kaga inada wadda nake so.”
Mtwww Saifullah yaja tsaki wanda yasa Khaled d'agowa yana kallan sa yaga sam ba shi yake
kallo ba dan haka yayi tunanin ko da zuciyarsa yake. Shi kuwa Saifullah abin ne ya daure masa
kai jin cewar wai kamar yarinyar nan itace take zuwa gurin saurayi tace tana so ya aureta dan
lalacewa da rashin kamun kai, shin wai me yake damun mata ne akan son yin aure? Basu san
komai lokaci bane da baza su hakura ba har sai sun wulak'anta kansu a gurin mutane. Ya
karajin haushin ta ya kuma raina ajinta uwa uba yaji tsanarta a cikin zuciyarsa yana tunanin ma
'yar iska ce tunda har take cewa maza su aureta dan yasan ba wai Khaleed ta fara furtawa
hakan ba.
'”Wai kana jina sai nayi ta maka magana kana jina dan wulak'anci ko?'” Khaled yayi maganar
yana kallan inda Saifullah yake, sai da ya d'ago ya kalli Khaled sannan yace.
'”Yah ina jinka amman me kake son nace maka a cikin maganar taka? Kace min kana jin
tausayin kuma ta nuna maka buk'arta na son ka aureta kace kana da wata, toh ina tausayin da
kake mata ya tafi? Menene yasa ba zaka aureta ba kodan ka ceci rayuwarta daga fad'awa
auran sa'an mahaifinta?” Khaled ya kallesa da sauri yana zaro idanuwa yace.
'”Wai kana nufin na aure su duka biyun?”
'”Eh mana ai zaka iya tunda kanada ragowar imani.'” Da sauri Khaled ya fara girgiza kansa
alamun ba zai iya wannan b'arnar ba wadda Saifullah yake k'ok'arin cusa shi.
'”Bazan iya ba gaskiya, zan dai cigaba da yi mata addu'a Allah ya kawo mata mai kaunarta,
amman gaskiya ni ba auranta zanyi ba sabida akwai wadda ta shiga can cikin zuciyata.”
Tattare kayan Saifullah yayi tare da barin d'akin domin Khaled ya isheshi da surutun da shi
kansa bashi da mafitarsa, uwa uba kuma dama jiran lokacin da ya bashi ya gama magana ya
cika, fita yayi can zuwa study room dan nan ne kawai gurin da zaije yaji dad'in zama kuma
yasan Khaled ba biyosa zai yi ba domin ko ya biyosa yasan ba kulashi zai yi ba.
Can b'angaran su Islam kuwa gabaki d'aya Riri ta isheta da maganar Khaled, har zancen yasa
Islam ta fara zargin wani abun tace da ita.
'”Wai Riri menene a cikin zuciyarki daga ganin yaya Khaled?”
'”Ah mekika gani?'”
'”Ji nayi tun a hanya sai tambaya ta kike yi akansa, nace miki aure zai yi kwanan nan kuma
wallahi ba zai soki ba domin...”
Sai kuma tayi shiru ta kasa fallasa sirrin zuciyarta dan kar Riri ta sake rainata, cikin yatsina
fuska Riri tace.
'”Toh dan zai yi aure so what? Ni kawai so nake mu zama abokai dashi bawai muyi soyayya ba
na gansa zai kankaro min mutunci idan muna tare da kawaye na.”
'”Allah ya shiryeki Riri wallahi halinki sai ke ni bazan iya miki ba.”
Daga haka Islam bata sake kula Riri ba sai ma kwanciya da tayi akan gado saboda tayi bacci ta
huta.
*ABUJA*
Saukar sa kenan a garin Abuja, a gidan su Khaled ya fara sauka kafin yaje can inda zai
gudanar da aikinsa, Umman su Khaled sai murna take yi yau ga Saifullah a gidan ta dan ba
zuwa yake yi ba sosai ya dad’e, khaled yafi shi zuwa can lagos, koda yake yanayin su ba daya
bane kasan cewar Saifullah baya shiga cikin mutane komai da yake yi yana da lokacin yinsa
koda kuwa aski ne yana da ranar da yake yi da kuma lokacin yi bare kuma zuwa gidan 'yan uwa
da abokan arzuk'a.
Lafiyayyun girke-girke aka kawo masa duk da cewar basu san ranar zai zo ba, amman ya samu
abinciccika na alfarma wanda Umma bata rabuwa dasu ko ba'a cinye ba za'a bawa almajirai da
mabuk'ata basa zubar da abinci dan abban su Khaled bai bada kofar almubazzaranci ba a
gidan, hakan yasa kowa yake kiyayewa dan ko zubarwa kayi sai ka tsince ka cinye na kasan,
shi yasa kowa yake kaffa-kaffa da abinci idan ya zubo ko idan an jera a dining table ko wani
gurin inda aka tanada dancin abinci.
Bayan ya gamaci sun d'an tab'a hira da Umma dasu Humaira ya tashi ya nufi sashen Khaled,
kasan cewar shima yana da nashi key din ba sai ya nema ba kuma shima d'akinsa dake can
lagos Khaled din yana da key, kowa zai iya shiga ba tare da ya jira d'an uwansa ba. K'ananun
kaya yasa wando jeans baki da farar riga mai dauke da rubutu a gabanta an rubuta wonderful
da d'igo-d'igon stone a jiki baki da jah Saifullahi yayi kyau dama gashi masha Allah sai wanda
ya kallesa shine zai gama tabbatar da irin kyautar da Allah ya bashi. Kuma fitowa yayi ya koma
wajan su Umma da alama hira yake ji dan sai fara'a yake yi idan anyi abin dariya shima ya dara
abin gwanin ban sha'awa.
Kwanansa uku da zuwa garin abuja da sassafe bayan ya shirya ya fito motsa jiki ya had'u da
Islam abinda ya daure masa kai, kodai aljana ce wannan yarinyar ganin ya barota a lagos ya
dawo nan kuma sai ya sake ganinta, shin menene yasa bata bari sai ya koma ba sannan ta
dawo?ko dai Khaled ya sanar da ita cewar ya dawo nan?idan hakan ne to meye alak'arsu da
har zai fassara wannan had'uwar tasu? Dole ya dauki kwakwaran mataki akan yarinyar dan
yaga kamar kiruciya tana damunta gashi wani irin mugun tsanarta yake ji a ransa, amman dole
yana son koyar da ita wani darasi, yana son ya nuna mata duk macen da ta furtawa d'ah namiji
kalmar so a wannan zamanin toh ta siyarwa kanta wulak'anci da rashin ganin kimarta, dole yayi
amfani da wannan damar tasa wajan sanin kanta da kanta.
_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_
*_NA*_
_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_
® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_
*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_
*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_
_BILLYN ABDUL_
*_SHAFI NA 34-36_*
_SHAFIN YAU NA KU NE GROUP ‘DIN MAMMY NA (KAUTHAR M HASSAN) WATO ‘YAN
*MUSHA KARATU GROUP*, FATAN ALKHAIRI AGARE KU, MUSANMAN MAKARANTA
SAIFUL_ISLAM_
_nanahafsat.wordpress.com_
*ABUJA*
Lectures su Islam suke yi sosai, domin exams ma xasu fara ta first semester, gaba ‘d’aya ta cire
maza a ranta, aganinta bata da rabo, tana fatan Allah yasa hakanne mafificin alkhairi. Ta
‘Bangaren Saifullah ma ya mai da hankali wajen zuwa place of primary assignment ‘dinsa,
amma sam baya son wajen. Domin matan wajen sun uzzurawa rayuwar sa, sai kace shi kad’ai
ne namiji. Shi abun har mamaki yake bashi da takaici.
*5:35*
Yana gama idar da asubahi a masallaci ya fita jugging da ya saba, shine first morning routine
‘dinsa, alokacin itama Islam tafito tana da gilashin ta, tana tafe tana zikiri. Can Saifullah ya
hangota murmushi yayi, yana ‘kiyasta yadda xai mata magana, inde tabada Kai bori ya hau, to
tabbas she’s not classy, da shegen killer smile ya ‘karasa yana shawo gabanta, tsayawa tai tana
kallon sa, ganin bata san waye ba yasanya ta dan rissinar da kai, cikin kunya tace,
“Gud morning...”
Mamaki ne ya cika saifullah, tsayawa yayi yana duban ta da kyau, ba laipi for the first time in
history muryar ‘ya mace tayi masa dad’i. ‘kisisina’ ya furta a zuciyar sa. Cikin melodious voice
‘dinsa yace,
“Morning.. How was ur night?.”
Ta muryar sa tagane shine daya bigeta kwanaki har wayarta ta fad’i. Domin dama bataga face
dinsa a lokacin ba sai yau, rabawa tayi zata wuce ya kara tare ta,
“Ke kiddo!”
“Kiddo?!” Ta maimata tana kallon sa”
“Yeah ai itance.”
Girgiza kai kawai tayi, ta bar shi nan tsaye yana dubanta, yayi niyyar ya sake binta sai shima ya
basar kawai, yai tafiyarsa tare da cin alwashin sake tareta. Don so yake ya koya mata darajar
mace. Kullum sai sun hadu ya jata da magana, wata ta amsa wata ta basar, a kwana na biyar
lokacin sun gama exams washe gari suka hadu dashi.
“Little one...” ya kira ta da ‘karfi
Juyawa tayi tana kallon sa, mutumin nan ya takura mata da yawa, gashi idan ya tsaida ita ba
maganar arziki suke yi ba,
“What again?” Ta fada cike da ‘kosawa.
“Kiddo! Yau ba gaisuwa?”
“Morning..”
Tace tana kallon gefe, wani killer smile yayi, har saida dimple dinsa suka lotsa, cikin rad’a-rad’a
yace,
“How was ur night?!”
“Twas great..”
Tana gama fad’a tai gaba, binta ya shigayi kamar jela, tsayawa tayi tana kallon ‘kasa. Ganin
haka yasanya shi, langwabar da kai yana duban fuskar ta. A hankali yace
“Little one, Ina ne gidan ku?!”
Yana so ya tabbatar idan tanada aji ko batada shi, Shawara ta shiga yi da zuciyar ta,shin tafada
masa ne ko kuwa? Wata zuciyar tace ‘aa Islam kakki soma, kila yaudararki zai yi ko kuma jikin
ki yake sha’awa kamar sauran maza. Har tayi taku d’aya, d’aya zuciyar tace, ‘uhm uhm Islam,
kila Allah ne ya dubi zuciyar ki, ya kawo miki shi, duk da dai bacewa yayi yana sonki ba, kawai
dai kuyi mutunci., cikin shagwababbiyar muryar ta tace,
“Idan kayi corner ‘din can street din, first house by the left shine gidan mu.”
Girgiza kai kawai Saifullah yayi, cikin zuciyar sa yace, ‘ba aji’. zahiri kuwa ca yai,
“Oh ashe ba nisa da gidan su Khaled. By the way sunana SAIFULLAH... And you?!”
“ISLAM....” tafada tana ci gaba da tafiyar ta, shima juyawa yayi yai tafiyar sa gidah.
*BAUCHI*
A gajiye lik’is Dr Khaleel ya shiga harabar gidan sa, inda Karimatu take yanzu. Mai gadin ne ya
tafi a sukwane zai karbi jakar hannun sa, dakatar dashi yayi kafin yace,
“Basshi lawwali nagode, ai ba bu nauyi. Ya badai wata matsala ko?”
Sosa ‘keya lawwali ya shigayi yana sunkuyar da kansa a ‘kasa. Ganin haka yasanya Dr Khaleel
hanzarin shiga cikin gidan. Har ya fara hawa matattakalar bene ya jiyo muryar Karimatu da
Sidiya ‘yar uwar ta, yana mamakin taurin kai irin na Karimatu. Ya haneta da shiga harkar sidiya
amma taki yadda, duk wani shedananci Sidiyar ce ke ‘dora ta akai, wato saboda nan ba Abuja
bace, shiyasa take yadda taga dama kenan, no wonder lawwali yake inda-inda ashe ashe
makirar sidiya ce tazo. Dai-dai matattakalar bene na takwas ya jiyo muryar Karimatu na cewa,
“Sidiya kinga ni Alhaji ya hana fita, ballantama garin nan bansan kowa ba wallahi, Kinga ko
makota ma babu nan kusa, so nake duk yadda zaki ki fadawa mallam komai, jibi ni kuma zance
masa hajia ba lapia, yabar ni naje kano, nasan zai bani bugun Abuja. Toh dasu zan bawa
mallam ladan aiki, fatana ni dai Aysa ta haukace gaba d’aya, shegiyar ‘yar tata da suke tare ta
iskance ku...”
Bata ‘karasa ba dr Khaleel ya shiga cikin parlorn bakin sa ‘dauke da sallama, Sidiya sai ta fara
neman hanyar guduwa, gaisheshi suka shiga yi, Karimatu harda in-ina,
“Alhaji da..Dama zaka zo yau ne? Na dauka sai...jibi ai,”
“Karki damu wani unexpected abune ya kawo ni..”
Kad’a kai tayi tana fatan Allah yasa bai ji zancen da suke ba dai, Sidiya jiki ba kwari ta mike
tana gyara xaman mayafinta, kafin tace.
“To yaya ni zan koma garin mu, sai kinzo, jikin Hajia dai ya matsa.”
Murmushi Karimatu ta ‘ka’karo, kai da ka ganta kasan ba lapia, cikin dauriya tace.
“Insha Allah ina nan tafe, tunda ma ga Alhaji yazo, sai na sanar mai.” Juyawa tayi tana kallon
Dr Khaleel kafin tace.
“Alhaji jikin hajia (mahaifiyar ta) ya matsa, sai dai a kwantar a tayar, shine Kawu ya taso Sidiya,
yace tazo ta sanar mun, dama ina shirin kiran ka awaya sai ga ka.”
“Allah ya bata Lapia”
Abunda ya ce kenan, yana latsa wayar sa, a zahirin gaskia, yadda zai rabu da Karimatu yake
tunani, Don yaga alamar bazata tab’a canzuwa ba. A hankali ya ‘dan dubeta kafin yace
“Nima yanzu zan koma Abuja inada abun yi, idan zakije ki duba Hajian yau ma shikenan..”
Washe baki tayi, aganin ta baiji komai ba, cikeda murna ta shiga godia, ‘daki ya mike ya shiga,
yana shiga ya yagi takardar littafi ya rubuta,
“Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh, Ni Khaleel Muhammad Tasiu, na saki
matata Karimatu saki ‘d’aya, dama na mata saki biyu shekarun baya, ya kama saki uku kenan,
xaman mu ya ‘kare, Sakamakon wani babban dalili data aikata, Ina fatan hakan zai zamto silar
shiryuwarta nan gaba, Allah ya had’a kowa da rabon sa. Bissalam.”
Yana gama rubutawa ya linketa ya zura a envelop, ya kara ‘daukar wata envelop din ya zura
aciki, kafin ya dakko bandir din yan dubu d’aya guda d’aya ya had’a akai ya fito parlor. Sai
murmushi take yi, mika mata envelop din yayi yana jaddada mata,
“Wannan envelop ‘din Kawu zaki bawa, munyi magana dashi, sannan wannan kudin kuma
gasunan ko zakiwa Hajia siyayya..”
Ido ta bude tanabin kudin da kallo,
“Ah! Madalla angode Alhaji.. Allah ya saka da alkhairi.”
“Ameen..”
kawai yace ya koma cikin ‘dakinsa, gaba d’aya ya hakura da Karimatu. shiysa yaji bazai iya
sanar da su Ya