Showing 51001 words to 54000 words out of 86718 words

Chapter 18 - SAIFUL-ISLAM Book Complete by miss xoxo (2).pdf

06 Jul 2025

2084

auren take. Kuma kaga naji Baban ku na cewa ma kila
muma cikin shekaran nan mu dawo Abuja, Saboda yana so ya dawo da asibitin sa nan.”

Cikin murna Saifullah ya d’aga kansa alamun yayi na’am. Haka dai tashiga yi masa nasiha da
dabarta masa yadda ake zamantakewar aure, yadda zai rike y’ar mutane da amana, ta ‘kar’kare
da,

“Na bawa Abbas sak’o idan zaka je gidan naka sai ka karba. Tashi kaje ka shirya, Allah yayi
muku albarka, yasanya alkhairi da farin ciki a rayuwar ku.”

Kad’a kai Saifullah yayi yana goge hawayen daya zubo masa, Haj zuwairah ta dafe baki kawai
tana daria,

“Ah lalle ango da kukan barin gida, Lalle auta na ya kafa tarihi.”

Ta fad’a tana mai mayar da nata hawayen daya taho. Zai fita daga dakin Khaled ya tunkaro kai
yana sallama, ganin Saifullah yasanya shi fad’ad’a murmushin sa,

“Iyye Angon Is..”

Harara Saifullah ya wurga masa, yana furta kalmar da ta zamar masa ta dolen fad’a.

“So...s..”

Be karasa ba Khaled ya riga shi yana
“Suffocating mutamina!”

Ficewa Saifullah yayi yana tsaki, shi kuma Khaled ya samu waje ya zauna bayan ya gayda Haj
Zuwairah. Sun ‘dan fara magana Fatima da Humaira suka shiga ‘daukar kayan Islam na ra’aki
da kususuram. Bayan sun fita dasu ne Haj zuwairah ta dubi Khaled dake sake sunkuyar dakai
kasa kamar sabuwar amarya, tuni ta gano jirgin sa amma ta danne,
“Yawwa ina jinka Khaled”

“Aunty...Temako na zaki yi”

“Temako kuma?!”

“Eh aunty dan Allah wallahi ba kiji ‘kirji na ba”

“Subhan’Allah Khaled baka da lapia ne?”

“Kusan hakanne Aunty, akan Fatma ne”

“Matar ka?”

“Eh ita Aunty..Dan Allah ba wanda zan iya kawo wa ‘ko’kon bara na ya amsa min sai ke, ki dubi
girman Allah Aunty, kiwa su Ummah magana su bani...”

“Matar ka Fatma”

Sosa ‘keya yayi, yana wasa da gashin carpet. Murmushi kawai tayi kafin tace.

“Khaled kenan, gata fa akai maka, sanin kanka ne gidan da zaku zauna anan garin yanzu ake
yinsa,an kammala fenti kawai yarage, abunda yasaka aka dakatar kuma kace kai ba anan zaku
zauna ba sai Spain. Yanzu so kake ka ‘dauki yarinyar mutane kuje hotel? Ga manya a gidah, ka
naso ka janyo abun da za’aita kananan maganganu ko?”
“Aunty .. Ni fa ko fuskarta an hana na gani, k..”

“Shikenan kawai, Bari zan turo maka ita yanzu sai ku gaysa.”

Dadi kashe Khaled, mikewa Haj Zuwairah tayi ta fita, mintina kad’an sai ga Fatma ta shiga tana
sunkuyar da kai ‘kasa. Kasa hak’uri Khaled yayi, yayi hanzari janyota jikin sa yana wani shegen
murmushi. Jikin sa sai rawa yakeyi, cikin kunya fatma tace,

“Ina yini..?”

“Ya rouh.! Wane yini kin gasa ni, har ramewa nayi na rashin ganin ki”

“Jiya ne fa kawai love..”

“Say no more! Dole ki karba hukunci.”

Ta shiga kiciniyar kwace jikin ta, ya riko hannun ta, yana sinsinar kamshin jikin ta, hannun sa
d’aya kuma na karakaina cikin rigar ta....

*6:30pm*

Zaune Islam take, kanta a ‘kasa tana tsakiyar su Daddy (prof Khaleel) da Ya Bala, da Inna
bilkisu, gefe kuma Hansa’u ce da Haj Aysa, can ‘k’arshen ‘kurya kuma bodara Yafendo ce, da
alama dai mutuniyar taku ta nisan ta kanta don gudun abun kunya. Sosai aka shiga yiwa
amarya Islam fad’an yi nayi bari na bari, kuka kawai take yi tana jan majina, Haj Aysa dake gefe
lokaci zuwa lokaci itama take fakar idonsu ta goge nata hawayen. Haka ma Prof Khaleel shima
idanuwansa cike suke taf da hawaye.

Haka dai kowannen su ya yiwa Islam fad’a, sosai take kuka, jikin ta har rawa yake yi. Ta
rungume Daddy tana kuka yana kuka, sai da Yafendo ta raba su dakyar. Sannan aka komar da
Islam sashen Haj Aysa, wanka ta ‘kara yi, ta sanya wata atamfa datasha stones blue, mahaifin
Haj Aysa tun na aure shi aka yafawa Islam kamar yadda Aysan ta qudura, ba’ai mata makeup
ba amma ba kadan ba tayi kyau cikin royal blue shigar ta, dai-dai stairs Haj Aysa ta hango
Islam, da hanzari ta sulale zata gudu don kada su hadu Islam tayi saurin rikota tana kuka, duk
mutanen dake wajen sai da suka koka, domin ba kadan ba xasu baka tausayi.

Dakyar dai aka ‘banbare Islam daga jikin Haj Aysa, sannan aka sanyata a mota, suka fara zuwa
gidan su Haj zuwairah, gaisuwar surukai, tsabar sonta da Haj Zuwairah keyi rungumota tayi jikin
ta, tana shafa bayan ta, kamar ta maida ta ciki haka take jinta, da alama dai soyayyar auta
Saifullah ta fara shafar Islam. Sai gud’a ke tashi.
Motoci a convoy suka nufi unguwar Asokoro kai Islam gidan ta, Abbas ke tuka motar da Islam
take, gaban motar Helwa ce, baya kuma tsakiya Islam ce, gefe da gefe kuma Hansau da
Yafendo, sai sauran motoci dake ‘dauke da ‘kawayen amarya da ‘yan uwan amarya. Yan uwa
na kaita suka mata sallama suka tafi bayan sun yaba akwatunan ra’aki da kususuram da aka
jere su a drawer, gidan sai tashin ‘kamshin turarukhan wuta yake.

A ‘dakin ‘kasa aka zaunar da Islam, sai kuka takeyi, yan uwa duk sun dare, sai ‘kawaye dake
jiran tawagar ango, Ai kuwa ba’a jima ba abokan ango suka shiga, aka tsadance kudin siyan
baki suka biya, da yawa daga ciki sun karbi nambobin juna, Riri ma taci sa’a wani ya ‘kyasa ya
karbi tata, sai 10 sannan suka watse, duk abun nan Saifullah na mota yana danna waya. Sai da
ya mula yasha iska sannan ya fito, sanye cikin yadi kalar madarar ruwa, bai sa hula ba,
kwantaccen gashin kansa ya kwanta luf, sai tashin ‘kamshi yakeyi, Abbas dake gefe ya ciro
wasu ledoji a bayan boot ya mik’a masa yana jaddada masa da,

“Gashi Mami(Haj Zuwairah) tace lalle na baka, nasan kuma ta sanar maka, My G Allah ya baku
zaman lapia ya kawo ‘kazantar ‘daki.”

‘Kwatar ledar Saifullah yayi sai kace fada, Abbas yai murmushi kawai yaja kan motar sa ya fice,
Cikin takun ‘kasaita Saifullah ya shiga ciki bakin sa dauke da sallama, kamshin turarukhan wuta
suka doki hancin sa, ya lumshe idanu cikeda Jin dadi. Sama ya hau, ya shiga wani ‘daki da ke
dauke da furnitures blue and white, murmushi yayi ganin dagaske Mami ashe ta shrya masa
dakin sa tamkar na Lagos. Bandaki ya fada yayo wanka da alwala, sallar nafila yayi ya karanta
alqur’ani yayi addua ya shafa. Har ya mike akan gado ya tuna ledar da akace lalle yabawa
Islam. Dauka yai ya bude tafarko kaji ne da gurasar larabawa da sauce, sai ta biyu kuma
yoghurts ne da drinks. Tabe baki yayi ya fita.

Dakin dake kallon inda yake ya shiga batanan, ya bude dayan na kusada corridor nan ma ba ta
ciki, ‘kasa ya sauka, kansa tsaye ya shiga ‘parlorn kasa ya murza dakin ciki, can yahangota a
gefen gado tana karanta littafin addu’oin 40Rabbana. Ga wani sihirtaccen kamshi dake tashi a
cikin ‘dakin. Dama fitilar dim ce saita ‘karawa dakin wani annurin haske, gyaran murya yai,
hakan yasanya Islam daga kai ta dube shi, sai kuma tayi ‘kasa dashi tana cigaba da karatun ta.

Cikin takun sa, mai cike da samartaka da nuna isa ya ‘karasa wajen ta, dadda’dan turaren sa na
Hugo boss ya daki kofofin hancin ta, shima fa ana sa ‘bangaren khumran jikin ta yasa shi
lumshe idanuwa. Ja baya tayi, ya bita sai da suka kai ‘k’arshen bangon ‘dakin sannan ta tsaya
tana kauda fuskarta gefe, siririn tsaki ya saki kafin ya dire ledar a gabanta yana mai nuni da
ledar,

“Ga shi nan, Mami tace a baki.”

Yana gama fada ya sa kai ya fice, nannauyar ajiyar zucia Islam ta sauke, tana raba idanuwa.
****

_HASKE WRITERS ASSOCIATION_
_HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS_

_YAN UWA MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE, KU MATSO KUSA GA NAKU, HA’KI’KA
HAZIKAN MARUBUTAN SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WASU DA’DA’DAN LITTATTAFAN
MASU TAFIYA CIKE DA;_

_DARUSSA_
_WA’AZANTARWA_
_NISHADANTARWA UWA UBA_
_SOYAYYA...KADA KU BARI A BAKU_ _LABARI KU ZO A DAMA DA KU. _

_ZAFAFA BIYAR DAGA YAN BIYAR NA CIKIN TAURARUWAR ‘KUNGIYAR HASKE, (BATCH
B)ZASU ZO MUKU NE DAGA GWANAYEN KU KAMAR HAKA,_

_DAGA TASKAR *MAMU GEE* MARUBUCIYAR TARAYYA A WANNAN KARON ZATA ZO
MUKU DA LITTATTAFINTA DADDAD’A MAI SUNA *BURI D’AYA*._

_SAI TASKAR *SAFIYYA ABDULLAHI HUGUMA* MARUBUCIYAR KUNDIN KADDARA
ZATAZO MUKU DA ZAZZAFA MAI SUNA *DAURIN BOYE*_

_SAI TASKAR HAFSAT RANO, MARUCIYAR GUGUWAR SO DA RUHI DAYA ZATA ZO MUKU
DA SABO MAI CIKE DA SOYAYYA MAI SUNA *SAUYIN ‘KADDARA*.. _

_SAI TASKAR BILLYN ABDUL MARUBUCIYAR RAINA KAM DA MUTUM DA DUNIYAR SA
ZATA ZO MUKU DA WANI SABON SALON SO MAI SUNA *WUTSIYAR RAKUMI* ._

_SAI NI NANA HAFSAT WADDA KUKA FI SANI DA *MISS XOXO,* MARUBUCIYAR NAUFAAL
(THE CHARMING) DA SAIFUL_ISLAM, A YANZU, ZAN ZO MUKU DA WANI SABON MAI
CIKE DA ‘KAUNA MAI TAKEN, *KAI MIN HALACCI* _


_WANDA DUKA BIYAR DIN ZASU ZO MUKU A SABUWAR SHEKARA ME KAMAWA INSHA
ALLAHU (2020). A WATAN JANAIRU, KADA KU BARI A BAKU LABARI. MAI SON DAYA ZAI
BIYA 200 NE, MAI SON BIYU 350NE, MAI SON HUDU ZAI BIYA 450 SAI MAI SON BIYAR DIN
ZAI BIYA 500._
_KADA A MANTA HAZIKAN MARUBUTAN SUNE:_
_MAMU GEE_
_SAFIYYAH ABDULLAHI HUGUMA_
_HAFSAT RANO_
__BILLYN ABDUL_
_MISS XOXO_

_LOVE YOU ALL FISABILILLAHI❤_





_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_


*_NA*_

_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_
_BILLYN ABDUL_


*_SHAFI NA 40-42_*

_WANNAN SHAFIN NA KI NE YAYYA NABEELAH ❤, MY BIGGEST SUPPORTER.
ILYSM SIS,MAY YOU BE FOREVER BLESSED_

_nanahafsat.wordpress.com_

Tunda Islam takoma Lagos gaba d’aya cikin k'uncin rayuwa tasa kanta, kullum addu'ar ta shine
Allah yasa afasa auren nan nata da Saifullah. Ta matsu ma ayi resuming school don ta cigaba
da harkokin ta, Kamar kullum yau ma tana zaune takaicin duniya ya taru ya tsaya mata a
ma’kogaro. Riri dake k'asa tahau sama tana ‘yan wak’e-wak'en ta. Ja tayi ta zauna a kusa da
Islam tana cewa,

“Wani guy nakeso a twitter, yaron nan yayi, komai yaji nake gaya miki, kyau da kud'i da
background abun ba’a cewa komai. matsalar shegen ko following d'ina back yaki yayi, ku...”

“Dan Allah Riri ki kyale ni, can ta matse maku ke dashi, ni meye nawa aciki?”

Bud'e baki Riri tayi ganin har yanzu Islam taki sakkowa daga doron fushin data hau, masifar yau
daban, ta gobe daban. Mikewa tsaye Riri tayi tana mik’a had'e da tab’e baki tace,

“Toh kizo dai inji Baba yana neman ki, yace na kira ki yanzu.”

''Daman aiko ki aka yi amman kika tsaya yi min zancen banzar nan.?'' Riri ta tafa hannu tana
cewa.

''Islam kece kika d'auki wannan maganar ta banza saboda ke baki waye ba har yanzu.''

Tsaki Islam taja, tana gaba Islam na biye da ita suka tafi sashen Haj Nabeelah matar Ya Bala,
wato marikiyar Riri. Shi kadai ne a parlorn yana kurbar kunun gyad'a. Ganin Islam yasanya shi
fad’ad’a murmushin sa yace.

“Baba barka da rana..”

“Barkan mu Islam.. Kina lapia?”

“Lapia Alhamdulillah Baba.”

“Masha Allahu... Ammh! Ina wannan matar abokin nawa dana ce miki tana kawo kayan amare
daga k'asar waje?”..

“Eh Baba na gane ta.” Cewar Islam kanta a ‘kasa.

“Yawwa toh, ya kirani jiya yake cewa tace kije shagon nata ki zabi abinda kikeso, nashi
gudunmawar kenan.”

“Allah sarki! Nagode k’warai.”

“Fareeda ai ke kinsan shagon nata ko?!”

“Nasani Baba..”

“Yawwa ki rakata kuje tare please!”

Kad’a kai Riri tayi sannan suka koma d'akin su ita da Islam. Cikin fushi Islam ta sauya kaya
zuwa doguwar rigar A shape ta atamfa mai zanen akwati ja da bak'i ta yafa mayafi akanta, da
yake hannun dogone har gwiwar hannunta. Bata d'aura d'ankwali ba amma ta rufe kanta ruf da
mayafin. Malam ubale direba shine yaja su zuwa can unguwar surulere dake lagos inda shagon
matar yake. Kamar ta maida Islam ciki haka Haj Binta take ta nan-nan da ita, kwarai ta kwanta
mata arai har takasa hak’uri sai da tace.

“Yanzu daman Alhaji nada sauran budurwar yarinya be gayamana ba sai yanxu da aka rigamu?
Allah yayi rabon wani ce ke da na had’aki da d'ana Mus’ab..”

Murmushi kawai Islam tayi tana jin dama a fasa auren ta da saifullah ayi da Mus’ab d'in watakila
shi zai darajata ya bata mutuncin ta na ‘ya mace. Cikin tunanin data fad’a Riri ta zungure ta, nan
suka shiga duba kayan, kusan Riri ce ta d'aukar mata komai, ita Islam kasa zab’a tayi. Sun d'an
jima suna hira da Haj Binta kafin su d'auki hanyar gidah. Dai-dai wani joint kafin a k'arasa
unguwar su Riri tace su tsaya ta sauka, cikin fushi Islam ta dubeta,

“Haba Riri ai kya bari dai mu koma gidah idan yaso sai ki dawo ke, amma ya za’ai mun fito tare
kice a saukeki..” Cikin rashin damuwa Riri tace,

“Toh sakko mu shiga tare.”

Harara Islam ta wurga mata, Riri tai murmushi tana d'aga kafad’a alamun kin yiwa kanki, Malam
ubale zai ja mota kenan wani bayarabe ya d'an k'wank'wasa masa motar,

“Megida motanka na hayaki..”

“Subhanallahi ya Allah..”

Cewar Malam Ubale, da sauri suka fito daga motar shi da Islam, Riri dake tsaye a bakin k'ofar
wajen ta k'araso tana tambayan Malam ubale,

“Meya faru Malam Ubale?”

“Hajia wallahi banduba ruwa ba, shine take hayaki, Kinga har wata roba tafara narkewa..”

Islam dake gefe ta ja ta tsaya a k'ofar joint d'in tana kamo addu’oi a baki. Riri ta kalli Islam ta
gefen ido sosai a firgice take, gashi bata san ta b'ata mata Ap data had’a. Cikin dak’ilewar
murya Riri ta cewa Malam Ubale,

“To ya xa’ai kenan yanzu?,Kai ma ka dinga dubawa saboda irin haka.”

“Insha Allahu Hajia..” ya cewa Riri kafin ya d'anje nesa da Islam yana rissinar da kai,

“Hajia bari naje na duba baya ko za’a samu bakanike yazo ya d'an duba mana, ayimin afuwa.”

“Tohm ba komi..”

Shine kawai abunda Islam tace, Riri ta k'arasa wajanta tana cewa,

“Mu shiga ciki to kafin a gama gyarawa.”

“Nanma ya isa..”

Kad’a kai kawai Riri tayi alamun shikenan toh, sannan tasa kai ta shiga cikin joint din, takaici
duk ya kama Islam na rashin madafa. Ta juya nan ta juya can, haka taita yi, lokaci zuwa lokaci
kuma takan saki tsaki. Cikin haka kuwa wani matashi ya fito daga cikin joint d'in cikin shigar
‘balman’ kayan duk a yayyage wai nan gayu ne, rabin wandon ya zazzago ta baya wanda
akewa laqabi da ‘ass down’, gashin kansa kuwa a saisaye yake rabi da rabi sak kan zakara.

Yana tafe yana wak’a, hango Islam dayai yasa shi sakin lallausan murmushi. Nufota yayi
gadan-gadan tayi hanzarin mikewa tana ja da baya-baya dashi, saurin riko mayafinta yai taja da
karfi da yake k'arfin ba ‘daya bane hakan ya sanya matashin mai suna 4gig k'wace mayafin
Islam sai gashi a hannun sa, neman kare jikin ta tashiga yi, shi kuwa 4gig k'ara gigicewa yai
ganin siffar Islam. Cikin sumbatu yace,

“Oh baby pls...”

Riri ganin 4gig bai dawo ba yasata fita waje da sauri, ganin yana neman cakumar Islam dake
hawaye shab’e-shab’e duk sai Riri ta rud'e sosai ta shiga yiwa 4gig bayanin Islam fa ba ‘yar
hannu bace, amman kememe yaki bada mayafin Islam d'in, yana ganin bakin ciki Riri ke yi
masa dan taga zai shana. Dai-dai Lokacin kuma Saifullah da Abbas sunzo shiga wani gidan
kallon ball dake kallon joint d'in dasu Islam suke, kamar ance ya juya idanuwan sa suka mai
kyakkyawan tozali da Islam da Riri dama wani gardi a kusa dasu, gardin na k’ok’arin yafawa
Islam d'in mayafi ajikin ta, alokacin kuma hak’uri 4gig ya shiga bata ganin dagaske ba ‘yar
hannun bace bata saba ba, dai-dai lokacin Islam tai murmushin takaici tana kwatar mayafin
tana yafawa akanta, Saifullah idanuwan sa suka sake d'akko masa hotan da Islam ke
murmushin tana lullube jikin ta da mayafi.

Gaba d’aya sai tunanin sa ya nemi d'aukewa, ashe kallon sokuwa yakewa yarinyar ma gaba
d’aya ta zarce tunanin sa. Da kyar yai kwafa yabi bayan Abbas suka shiga cikin gidan kallon
ball d'in wanda gaba d’aya hankalin sa na kansu Islam, cikin murya ciki-ciki yace da Abbas,

“Aboki... Can joint din na meye ne?” Abbas dake sipping coke yace,

“Ina fa? Oh wai opposite nan wajen kake nufi? Wani joint ne naga su Dee na zuwa shi da
Shambo, Kamar clubbing ne haka ina jin ana d'an shan shisha ne akwai kuma swimming pool
awajen.”

Jinjina kai Saifullah yayi yana furzar da iskar bakin sa, hakan ya sanya Abbas dafa kafad'ar sa
yana tambayar sa lapia, ganin damuwa kwance k'arara akan fuskar Saifullahin.

“Meyasa ka tambaye ni Aboki? Wani abun ka gani ne?”

Saurin kad’a kai Saifullah yayi alamun a’a, yana k'ak’aro murmushin da yafi kuka ciwo, cikin
husky voice d’insa yace.

“Bakomi Aboki, kawai ina mamakin yawan irin guraren nan a Lagos ne, gaskiya sunyi yawa,
barin ma dai area d'innan, so suffocating.”

Haka dai suka shiga wata hirar da Abbas, can waje kuwa 4gig sosai ya k'ara bawa Islam hak’uri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login