Showing 69001 words to 72000 words out of 86718 words
wasa da car key din hannun ta, Sosai ta ke
jin Peace of mind a gidan ba kamar prison din da take ba a da wato gidan saifullah, zata fice
daga gidan ne a bakin kofar da zata sa da ka da babban parlorn gidan su kai gware da
Saifullah, wanda shigowar sa kenan. Ita tana tafiya kanta a ‘kasa bata lura, shi kuma yana tafe
yana danna waya, ji kake ‘kauu’, sun gwara kai, Kowanne acikin su yaja baya yana mulmula
goshin sa, tare suka zabgawa juna harara, Saifullah ya shagala da kallon Islam sam bai lura da
ta fice ba, bin ta yayi a baya yana sauri, zata bude ‘kofar motar ta shiga ya rike handle ‘din kofar
yana kallon ta sama da ‘kasa, ba kadan ba tayi masa kyau, sai kace ‘Black Ethiopian’. Ganin ba
shi da niyyar matsawa, yasanya ta turo baki gaba, cikin shagwaba tace,
“Dan Allah ka matsa, zanyi late a lectures fa..”
Kissable lips dinta ya kalla, yana licking lips ‘dinsa kamar maye, bata fuska yayi, kafin yace.
“Me nace miki akan shafa jambaki?”
“Jambaki kuma?”
“Eh gashi nan kin shafa”
Ya fad’a yana mai nuni da lips dinta da hannun sa, saurin gocewa tayi gudun karya tab’a mata
labbanta, da sauri ta shige cikin mota, tana k’ok’arin tashin ta ya bude ya shiga shima, cike da
mamaki Islam ta bude idanu tana kallon sa kafin tace,
“Malam ya haka?!”
Hararar ta yayi, yana gyara zaman seat belt ‘dinsa, kafin yace.
“Hakan ce ta kawo haka malama.. just drive”
Yatsina fuska tayi, had’e da tabe baki,
Ta manni motar a ‘dari tai hanyar makarantar su, So yake ya mata magana amma miskilancin
sa ya hana, itama kuwa taja mutuncinta tana sake ‘dage kai, hannunta d’aya na kan sitiyarin
mota dayan kuma ta d’ora shi akan volume na cd, tana ‘karo muryar wakar ‘tarhani’.
Har suka ‘karasa cikin school, ‘faculty of medicine’ nan tayi parking, Tana k’ok’arin zare mukullin
motar ya riko hannunta, ta fizge tana yarfe hannuwan ta kaman ta tab’a kashi. Cikin zare idanu
yace mata,
“Me kika gayawa first love akai na? Meyasa zaki shiga tsakani na da mahaifiyata?! Uhm?”
Kallon tara saura kwata ta watsa masa, kafin ta fice daga motar, fitowa yayi shima, tayi hanzarin
saka lock tayi gaba abunta, ya fara binta da takadar dashi ta hanyar ‘daga hannunta, cikin
takaici tace,
“Wanda aka damu dashi, shi ake kai wa ‘karar sa, ni wallahi Idan na raina kasuwa ko sautu
bana bayar wa. I’m done”
Tana gama fada, tayi gaba abinta tana sakin tsaki, Saifullah ya daskare a tsaye jin kalaman
Islam, Sam bai bi takan yammatan dake maitar kallon sa ba, domin inda sabo ya saba, Uber ya
kira ta kai shi wajen ppa dinsa.
_*KANO_*
Karimatu sai tauna hakoranta take, tana gatsa harshen ta, tana neman cire kayan jikin ta, sai
wasu irin surutai take faman yi tana sakin kashi da fitsari a zaune,
Kawu Amadu ya jinjina kai, cike da tausayi yake duban Hajjan Karime kafin yace,
“Toh wai ina Sidiya ne?”
“Amadu Sidiya fa jia da rana auren ta ya mutu..”
Kawu Amadu ya sake dafa ‘karfen gadon asibitin da Karimatu ke kai kafin yace,
“Kina nufin ki ce garzali ya saki Sidiya itama?”
Hajia dafe da kuncinta hannu bibiyu tace,
“Wallahi saki uku ma yayi mata, ya gano wai tanabin malamai, shine ya dankara mata saki har
uku, ya kuma ce idan bokayenta sun iya asiri su bokance shi ya maida ita, cin mutunci dai babu
kalar wadda beyi ba”
Tabe baki Kawu Amadu yai, kafin yace,
“Ai ga irin ta nan, abunda aka hanesu da kada suyi, ai ‘ki sukayi, yanzu gashinan wa gari ya
waya?”
Ajiyar zucia Hajia ta sauke, kafin tace,
“Amadu ‘dan kira yaron kirkin nan ka gaya masa yadda ake ciki, ka dubi girman Allah ka kira
shi, don zumunci zakai ba don Karimatu ba.”
Kawu Amadu( Kawun Karimatu)ne yai ta maza ya kira Prof Khaleel, bugu biyu ya ‘dauka, sai da
suka gaysa cike da mutuntaka, tukun sannan Kawu Amadu ya shiga maganar abunda yasa ya
kira Prof Khaleel tun farko. Ya ‘kark’are da,
“Toh yanzu haka maganar nan da muke da kai, Karime na can a yashe, ta kamu da cutar
mutuwar jiki duka, da shan inna, kamar harda farfad’iya ma, wallahi yarinyar nan ba dan
albarkacin mahaifiyar ta ba, bazan taba temakon taba, to ‘dan abunda yan uwa suka tara duk
ya ‘kare akanta, wanda ‘yayanta suka aiko shima babu, shine mahaifiyar ta tace, dan Allah idan
da temakon da zaka iya mana, ko da ta ‘bangaren ganin babban likita ne. Wallahi tana cikin
wani hali Alhaji, Kayi hak’uri dan Allah..”
Ajiyar zucia Prof Khaleel ya sauke, Wanda kawu Amadu ya jiyo ta, ta cikin sifikar (speaker)
wayar. Ya jima kafin yai magana, dakyar yace.
“Ba damuwa kawu, akwai wani neurologist anan asibitin Aminu kano, zan ki rashi, yanzu kuna
gidah ko asibiti ne?”
Cikin rawar murya kawu Amadu yace,
“Muna nan asibitin murtala, dakta zai bamu sallama yanzu.”
“Okay toh shikenan, yanzu idan kuka gama sai ku wuce can asibitin Malam bangaren
speciality, ni kuma zan kira likitan na sanar masa, Allah ya bata lapia. Ameen”
“Ameen Alhaji, Mungode Allah ya saka da alkhairi.”
“Ba komai kawu, zan turawa likitan komai na jinyarta, Allah ya tashi kafadunta..”
Nan kawu ya shiga yiwa Prof godia, shi dai katse kiran yayi ya cigaba da abunda yake yi.
(Dama hausawa sun ce idan zaka gina ramin mugunta, gina shi gajere, domin baka sani ba
wataran ko kai zaka fad’a ciki, ‘Yan uwa kunga yadda ‘k’arshen Karimatu ya kasance, mugun
halinta shi ya janyo mata, Sannan ga ‘bangaren Hillaal ma, yayi k’ok’arin ganin ya samu
kintsattsiyar mace mai tarbiya, yasan mai ya shuka a baya, sai dai kash Allah baya bacci, domin
shid’in mubuwa yi ne, gagara misali, cikin hukuncin sa da sarautar sa yasanya Hilaal girbe
mummunan aikin daya shuka, hakama ‘bangaren su da Hidaya, Toh Allah katsare mu, ka nisan
ta zuciyar mu daga aikata aikin haram, kayi mana katangar ‘karfe daga sharrin masu sharri,
Allah ka kara kare mu daga sharrin shed’an la’ananne. Yan uwa muyi taka tsantsan, domin
KOMAI NISAN DARE GARI ZAI WAYE, ALLAH ZAI BAYYANA MAI GASKIA)
_*ABUJA_*
Gaba d’aya ranar, Saifullah a wajen ppa baya mai da hankali, closing hour na cika kuwa ya
mike yai ficewar sa, gidan su ya koma dake anan ya bar motar sa da safe, Daganan yabi Islam
school dinsu, shysa a zuwa da dawowa (to and from) duk a Uber yai yawo. Bai ga motar Islam
a parking lot ba, hakan yai masa nuni da bata dawo ba kenan, bakin sa ‘dauke da sallama ya
shiga parlorn. Haj Zuwairah ce kawai a zaune a parlorn sai y’ar aikin ta a gefen ta a ‘kasa, suna
kallon wani tsohon hausa film. ‘Sangaya’.
Haj Zuwairah ta amsa sallamar aciki ciki, ganin sa yasanya ‘sumayya mai aiki’ ta fi ce da
sauri tabar wajen, tana susar kanta. Harara Saifullah ya watsa mata, yaki jinin y’ar aikin tasu,
kazama ce, yarasa me yasa Mami ke sonta, sai kace ‘yarta, tai ta gatan tata. Shi kuma
‘kazantar yarinyar ne ke bashi haushi, wanka sai an sata dole take yi, idan kuma ba’ a tursasa
taba to sai jumu’a-jumu’ah. Durk’usa wa yayi yana cewa,
“First love barka da rana...”
Hajia Zuwairah dake hakimce akan kujera ta dube shi a yatsine, tana ‘kara danna
tufar(Apple)hannunta a baka. Sai data had’iye, sannan ta dube shi, yana tsugunne, sanye cikin
shadda blue anyi mata dinkin hannu Golden color, ba hula akansa sai pcap golden color da aka
rubuta S a jiki, cikin tabe baki tace,
“Barkan mu..”
“First love.. Dan Allah ki dena fushi da ni, wallahi I’m ready to amend my mistakes, please kiyi
hak’uri first love.”
Dogon tsaki Mami taja kafin tace,
“In dai abunda ya kawo ka kenan tashi ka fita, tashi ka tafi bana buk’ata.”
Rarrafawa yayi zai rike kafarta ta goce tana dankara masa harara, be hakura ba ya dafa kujerar
da take, Sosai Mami ta hango damuwa a idanun sa, ta danne kawai, Don so take ta kankarowa
Islam mutuncinta.
“Zaka matsa ko sai na sharara maka mari..?”
“Allah ya baki hak’uri first love”
Ci gaba tayi da kallon ta, hankali kwance, ya ‘kara saisaita murya yana fad’in,
“Toh first love zanci abinci pls”
Sai daya maimaita sau uku kafin Mami ta mike tana barin wajen, sai da tabar tsakiyar parlorn
kafin tace,
“Ba agidan su Khaled kake cin abinci ba?! Wane taohon kinibibin ne yasa kazo nan zaka ci?!
To babu, abinci, na iya mu na dafa ban had’a da na waje (outside)ba, idan ka fita ka janyomin
k’ofar.”
Jiki ba ‘kwari Saifullah ya mike ya fita waje, farfajiyar gidan ya tsaya yana kallon sararin
samaniya kawai, duniyar fa tafara yiwa mutumin ku zafi. Gefan famfo ya zauna a wani ‘dan tudu
yana wasa da wani tsinke a gefe, azahirin gaskja zancen zuci yakeyi, ‘nan Islam ta danno
hancin motar ta, har ta kashe motar bai dena kallon ta ba, ta ‘dora lab-court akan rigar ta, tana
tafe tana k’ok’arin cire ta, Saifullah ya sha gabanta, cike da takaici tace,
“Malam matsa zan wuce..”
“Idan naki fa?”
“Karka so ma wannan kuskuren, dan wallahi sai nayi maka ihun gardi.”
“Waye gardin?”
Yafada yana ware idanu, cikin yatsina fuska tace,
“Waye gardi anan bayan Kai, excuse me pls..”
Ta fada tana wuce wa ta gefen sa, Saifullah ya saki baki yana kallon ikon Allah, Duk abun nan
Mami na kallon su ta sama, Islam na shiga ciki ya tada mota a zuciye yabar gidan, ya ‘dauki
hanyar gidan su Khaled. Sai da Islam tayi wanka taci abinci ne Mami ta sameta da maganar
abunda yasa tadawo da ita gidan, ta ‘kar’kare da,
“Kada ki sakar masa fuska ya ‘kara rena ki, nasan halin auta na, Kiyi duk me yiwuwa ya fara
binki ya baki hak’uri ba ke ki bishi ba, kingane nufi na?”
Cike da kunya Islam ta d’aga kai alamun eh, a sanyaye kuma ta furta,
“Toh Mami Insha Allah..”
Haj Zuwairah na fita, Islam ta dakko wayarta ta gayawa Lee yadda ake ciki, itama ta ‘kara
‘dorata akan network din da zatai subscription din Saifullah. Sun dan taba hira da Lee, kafin
ta shiga groups din hausa novels din favorites writers ‘dinta a WhatsApp. Wato (RANO ONLINE
NOVELS na Hafsat Rano, da HOME OF NOVELS na miss xoxo &HAJJAH CE NOVEL GRP na
Ya Hajja), Sosai take jin dad’in groups din musanman da za’a fara littafan ZAFAFA BIYAR, na
DAURIN BOYE na Huguma, BURI DAYA na mamu gee, SAUYIN KADDARA na Hafsat Rano,
da WUTSIYAR RAKUMI na tawan billy, sai KAI MIN HALACCI na matar sheikh Aliyu wato miss
xoxo , tana gama karanta ‘dan’danon kowanne tayi musu transfer din dari biyar 500, aka
sanyata a grp din ZAFAFA BIYAR.. da haka wani daddad’an bacci yai awun gaba da ita, cike da
mafarkan yadda za’a sha ruguntsumi a cikin wannan dad’adan littattafai, masu dinbin
darussa....
———-
Ina kike AYSHA KANYA? Sak'on ki ya iso gare ni, Ina fatan an baki ma'anar suffocatingna
gode da yadda kike bibiyar littafin SAIFUL_ISLAM, tate da 'yan KUNDIN HASKE duka
_______________
XAFAFA BIYAR;
DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOXO
ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka
litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*
_*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_*
[1/3, 10:54 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_
*_NA*_
_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_
_*®HASKE WRITERS ASSO._*
*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_
*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_
_BILLYN ABDUL_
*_SHAFI NA 61-63_*
_GAISUWAR BAN GIRMA GARE KI *YA HAJJA TAH*, LITTAFIN NAN GABA ‘DAYA TUKWICI
NE A GARE KU, KE DA TAWAN (BILLYN ABDUL)FATAN ALKHAIRI A GARE KI, OUM IHSAN
WA AREEF❤INA MIKI SON ‘KAUNA FISABILILLAHI, ALLAH YA BARKI DA UNCLE ABADAN
DA’IMAN. WANNAN SHAFIN NA KI NE KE KAD’AI., KI YI YADDA KI KE SO
DASHI♀_
_nanahafsat.wordpress.com_
Saifullah na barin gidan ya nufi gidan su Khaled kansa tsaye, jijiyoyin kansa duk sun tashi,
bugun zuciar sa ya canza, Sosai kansa yake ciwo tamkar zai bar gangar jikin sa. Ko gyara
parking dai-dai bai yi ba, yai fitowar sa yana mikawa driver Aunty Lateefa mukullin, da hannu yai
masa alama da yai parking dinta, kansa tsaye ya wuce part din Khaled na da, wanka yayi ya
‘daura alwala ya yi sallar nafila, ya jima zaune akan prayer mat yana addua, kafin ya mike jiki
sanyaye ya nufi sashen Aunty Lateefa. Samun su yayi a zaune itada Humaira, suna shan fruit
salad, zama yayi a kujerar mutum biyu dake kusa da wadda Haj Lateefa take, Humaira ta
gaishe shi ya amsa, ta mike ta haura sama abunta, bin bayanta yayi da kallo, sai yanzu ya lura
fushi take dashi, sunku yawa yayi yana gayda Haj Lateefa, ta amsa murmushi fad’ad’e a fuskar
ta kafin tace,
“A kawo maka abinci auta? Favorite dinka a kai, faten dankali, wannan karan an saka kifi.”
“Okay Aunty, a zubo amma kad’an.”
Mikewa tayi ta shiga kitchen din su dake k’asa, mintina kadan tadawo da food flasks guda biyu,
da plate da serving spoon, sai wani jug dake cike da zab’o da yasha kayan had’i aciki anyi
decorating dinsa da ice blocks. Zuba masa tayi yace ya isa, ya ‘dan caccakuna ya barshi, tana
hankalce dashi, zobon ya sha sosai, ya goge bakin sa da tissue yana hamdala kafin yace,
“Aunty! Wajen ki nazo fa”
“Toh auta, Allah yasa alkhairi ne”
Murmushi yayi, yana shafa ‘keyar sa, kafin yace.
“Aunty..a..Akan maganar Islam ne”
“Islam kuma? What about her?”
“Aunty nasan kin sani, dan Allah temako na zaki yi, ki bawa Mami hak’uri.”
Murmusawa Haj Lateefa tayi kafin tace,
“Auta ka daina zurfin ciki kaji? Damuwa na damun ka, ka samu wani kuyi shawara, sai kaita
barin abu a ranka, sai yaci yacinye ka sannan kazo kana magana a ‘kurarren lokaci, in dai akan
Islam ne gaskia bani da abun da zan fada maka, Tunda zance ya koma wajen manya.”
“Aunty kiyi hak’uri, ni fushin da Mami take dani yafi damuna akan komai wallahi.”
“Wato auta har yanzu baka fara saka Islam a cikin ranka ba kenan? Kuma fushin da Mamin
keyi ai duk akan hakane, ni banida abunda xan iya maka auta, kai zaka dage, fight for ur dear
self, kayi lefi admit it, shikenan fa, amma duk wannan ‘kunbiya-‘kunbiyar da kake ba zai maka
amfani ba..”
Tana gama fada ta mike ta shiga kitchen, domin halin Saifullah na ‘kona mata rai, gashi ta
sanadiyyar ta akai auren, ko kadan ba taso hakan ya kawo ruguntsumi ko rabuwar kawuna.
Tana shiga kitchen ya hau sama wajen Humaira, a parlorn sama ya tarar da ita tana danna
waya, kallo d’aya tai masa ta mai da kanta kan littafin da take karantawa. Zama yai a kujerar
dake kallon tata kafin yace,
“Humaira...”
Ya fada cike da damuwa, ‘daga idanu tai ta dube shi, kafin ta ajiye littafin agefe tace,
“Ya saif..”
“Kin san meyasa nazo wajen ki?”
Girgiza kai tayi alamun a’a, ya jaddada kai shima kafin yace,
“Akan ‘kawar ki ne Islam, deep down na san kina ‘boyemin wani abu, ki fadamin me na yi
mata? Ita Islam din.”
“Babu komai Ya Saif.. Allah ni Islam bata fad’amin komai ba”
“Toh waye ya gaya miki? Ki dena nuna bakisan komai ba, kin san halina dai sarai.”
Sanin indai ya canza yanayin sa bazata ji dadi ba, yasanya ta saurin bashi labarin abunda taji
game da maganar da Islam suka yi da Lee, ta ‘kark’are da,
“Kuma Ya Saif, wallahi nasan wacece Islam duk zargin ta da kake wallahi ba haka halin ta yake
ba, wallahi duk inda kamilar mace ta kai, Allah Islam ta zarce, ba wai dan ‘kawata bace, ko
kuwa dan yanzu matar kace, tsakani na da Allah nake gaya maka, idan hankali da nutsuwa ne
ma wallahi tafi ni, nasanta tun primary school, childhood friend dina ce, Saboda haka bayan ni
da Lee ba wanda yasan halin Islam kamar mu.”
Tana gaya masa halin Islam yana ‘kara ganin ‘kimar Islam din a zuciar sa da gangar jikin sa,
Humaira ta tsaya tana kallon sa ganin yana murmushi shi kadai, sai da yai mai isar sa kafin
yace,
“Wannan Riri din, wacece ita?”
“Sunan ta Farida, sister din matar Uncle dinsu ce da yake a Lagos, tun tana ‘karama take wajen