Showing 72001 words to 75000 words out of 86718 words
yayar ta ta, Haj Nabila matar shi Uncle Bala din.”
Kad’a kai yayi alamun gamsuwa kafin yace,
“Ina ganin ta ai a Lagos, Meye alak’ar su da Islam?”
Murmushi Humaira tayi, kafin tace
“Ba komai, sai zumunci kawai, tinda idan da kara kaga ai ta zama y’ar uwar su, tunda tun tana
‘karama take gidan Uncle dinsu.”
“Yadda na lura kaman ‘kawar ta ce sosai..”
“Kawai zumunci ne Yaya, nothing beside that, ‘kawayen Islam daga Lee sai ni, sai su Hafsat da
Fatima, suma kuma duk sunyi aure, acikin su ma ni kadai ce banyi ba.”
“Allah zai kawo nagari sis.”
Cije ieb’e yad’an yi kafin ya sake cewa,
“I heard ita da Khaled sunyi soyayya ko?”
Ya canza maganar, ware idanuwa Humaira tayi kafin tace,
“Soyayya da yayan? Anya? kai a’a gaskia, na san dai itada yaya suna mutunci sosai, So ni I
thought son ta yakeyi, Saboda duk cikin friends dina ba wanda Yaya yake mutunci da ita kamar
Islam, so sai nagaya wa Umma, nace soyayya suke yi, na kuma dinga pressuring Islam kan
Yaya na sonta, ya kasa fad’a mata ne, Saboda a lokacin anyi auren step sister’s dinta ba
dad’ewa, saura ita kadai kawai, So shine ta gaya mishi fa, kuma Islam nada masu son ta da
yawa, tanada farin jini, ko a school baka ga yadda classmates dinsu suke cewa suna sonta ba,
Saboda ni ina art class amma mazan ajin mu ma suna sa muna kancewar su dai suna son
Islam.”
Ta ‘kara da ‘y’ar ‘karyar ta, Don bataso Saifullah ya rena ajin Islam din, jin ta gama yasa shi
jaddada kai, alamun gamsuwa da zancen ta, kafin yace,
“Oh okay.. Thank you sissy!”
Mikewa yai zai fita, har ya kai ‘kofa Humaira tace,
“Ya Saif, Ka dena zargin Islam da aikata wani abu, wallahi nasan wacece Islam, duk inda
descent mace takai, Islam ta kai, ta zarce ma.”
Kad’a kai yayi kawai, yafi ce batare da ya tanka taba.
On a cold Thursday evening, Haj Lateefa taje gidan Haj Zuwairah, suka tattauna akan
maganar Saifullah da Islam, domin Saifullah ya takura mata da zancen, ta fadawa Haj Zuwairah
komai akan maganar da sukai da Saifullah, ciki harda zancen Riri daya gansu da Islam a joint.
Lokacin Fatima tazo ganin gidah, a parlorn gidan aka shiga maida maganar kowa yana tofa
albarkacin bakin sa, Fatma ta shiga ‘dakin da Islam take ta hilato ta suka fito parlorn, a lokacin
Saifullah yazo shima, Don Fatima ta kira shi tana san ganin sa, duk suka hallara a parlorn,
Fatma ta shiga jan hira da Islam, domin ta naso ko yaya su samu evidence, wanda zai kau da
zargin da Saifullah ya kewa Islam.
Sosai ta shiga bugun cikin Islam, Islam ta fada mata komai dangane da zaman su da Saifullah,
nan dai Fatima ta shigar da zancen joint na lagos da sanda 4gig ke yafa mata mayafin. Don
Saifullah ya bata labarin komai, A wayonce take tambayar ta wanene shi meye alaqar su?, dan
saurayin ‘kawartane a Lagos. Kuma ita tagan su, and kawar is feeling uneasy. Fatma ta
‘kark’are da,
“yanzu ya za’ai mu samu information dinsa, tunda kince ko sunan sa baki sani ba.”
Islam ta ‘dakko wayarta tayi dialing number Riri, bugu biyu ta ‘dauka, a speaker Islam ta saka
Riri, sai da suka gaysa kafin tace,
“Riri ni kuwa time din da motan mu ya lalace, a bayan plaza dinnan na idiroko ya sunan wajen
please?”
“Oh time din da mota ba ruwa dinnan, ba canai ki shiga ba kika ki? Mena tambaya na ynxu?”
Islam tayi murmushi tace,
“Dallah wannan wanda yake tsokana na dinnan ne naga wani kamar shi a live show yanzu”
“Oh wai 4gig daya kwace miki mayafi ya ‘dauka ke ki ‘y’ar hannu ce? Sunan sa Basher, wallahi
rannan kuwa yake cewa wai na ‘kara baki hak’uri daya ja mayafin ki.. Ni kwa nace masa ai kai
ka fiya renin hankali, tunda ba gani kai ta shigo ciki ba, a waje ka ganta dan ma motor dinsu ya
lalace ne, nace masa ke y’ar Abuja ce, wallahi ya isheni wai sai na ba shi number dnki ya baki
hak’uri, nace kinyi aure amma zan gaya miki on behalf of him. So kiyi hak’uri pls, Basher yayi
lefi then, amma inaga shi dinne a live show din dan cousins dinsa singers ne.. That aside, ya
gidah Lam-lam? Hope everything’s going on smoothly??”
“Alhamdulillah Riri, Yasu Mom?”
“Lapiar su lou, ki gayda mai gidan, ana kirana, later.”
“Alright bye, take care..”
Nan aka shjga kallon-kallo, Saifullah ya sunkuyar da kansa, kunya duk ta kama shi, deep down
he’s feeling guilty, Fatma tai murmushin takaici, kafin ta dubi Islam tace da ita,
“Islam ki koma ‘daki, zan zo na same ki”
Islam tai nodding kanta, sai yanzu ta gano, bugun cikin ta akai ta fadi gaskia al’amari. Murmushi
tayi daya nuna taji dad’in wanke kanta da tai awajen su, and finally Saifullah zai dena zargin
daya ke mata, sai yanzu take recalling duk bakaken maganganun da yake gasa mata duk akan
zargin ta da yake yi ne, wasu zafafan hawayen bak’n ciki ne suka shiga reto a kyakkyawar
fuskart ta.
_A gurguje plls_
Dare ya zama safiya, safiya ta zama yammaci, yammaci ta koma dare, Lalle Allah mubuwayi ne
gagara misali, cikin haka kuwa akai sati biyu da wannan zancen, Saifullah kullum yana jelan
gidan su Mami da Aunty Latifa, gashi daga baban nasa har uncle Aji Mommodu duk basa
sauraren sa, Islam dinma bata bashi fuska, duniya dai tayiwa mutumin ku zafi, ya rame kad’an
saboda rashin cin abinci da kwanciyar hankali, damuwa tayi masa yawa. Haka dai adaddafe
yake tafiyar da aikin wurin ppa dinsa..
Ranar wata asabar da yammaci, ya je gidan su, ya tarar mahaifin sa na nan, yana kallon
kwallo na La liga, tsakaninmu club din real Madrid’ da kuma Barcelona. Hankali kwance ya
cigaba da kallon sa bayan ya amsa sallamar Saifullah, ‘karasawa Saifullah yayi yana gayda
mahaifin nasa cikin girmamawa, nan mahaifiyar sa Haj Zuwairah ta shiga parlorn ta zauna,
gaishe ta yayi, ta amsa kai a sama, domin batasan ma ta kalli kwayar idanun sa yabata tausayi.
Kai a ‘kasa Saifullah yace da mahaifin sa,
“Daddy wurin ka nazo..”
Juyawa mahaifin na sa yayi ya dube shi kafin yace,
“Ina jinka, meke tafe da kai?!”
Cikin rawar murya kai a ‘kasa yace,
“Daddy a... a... akk...akan maganar Islam ne, na ga kuna fushi dani, dan Allah kuyi hak’uri, in
sha Allah bazan kara kamanceceniya haka ba”
Alhaji Faruk ya kurbi tea din dake hannun sa, kafin ya fara yi masa fad’a, ta inda yake shiga, ba
ta nan yake fita ba, Sosai yake jan kunnen sa akan laifukan da yayi, ya ‘kark’are da,”
“Kasan meye matsalar ka?”
Saifullah ya girgiza kai alamun a’a. Alhaji Faruk ya murmushi kafin yace,
“Zargi, kana zaton abun da ba haka yake ba, Allah mad'auka kin sarki yana cewa,
]30:22[ نمو هتايآ نأ قلخ مكل نم مكسفنأ اجاوزأ اونكستل اهيلإ لعجو مكنيب ةدوم ةمحرو ۚ نإ يف كلذ تايآل موقل نوركفتي
And (one) of His Signs (is this), that He has created wives for you from among yourselves that
you may find peace of mind in them, and He has put love and tenderness between you. In that
surely are Signs for a people who reflect.
“Kuma akwai daga ayoyin sa, ya halatta muku matan aure daga kan ku, domin ku samu
nutsuwa a gare su,kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakanin ku, Lalle wannan alama ce ga
mutane masu tuba/hankali.,
“Sannan akwai wata ayar cikin suratul hujrat aya ta 12, inda Allah mad’aukakin sarki yace, Ya
ku wa’danda kuka yi imani, ku nisanci abu mai yawa na zato, Lalle sashen zato laifi ne,
“Lalle zato shine ake nufi da zargi a addinin musulunci, idan har miji yana zargin matar sa da yin
wani shu’uminci, kuma bai dai na zargin ta ba, to anan ba’a ma bukatar sai miji ya furta kalmar
saki, rabuwar aure ta tabbata a gare su, Imamu Abu Dawooda ya rawaito cewa; Manzon Allah
SAW yace: haramtaccen abu wanda Allah yake qi shine saki (divorce), Don haka idan har zato
ya shiga cikin aure, to rabuwa tafi amfani, domin zargi yanada illa sosai da sosai, Toh Allah
yasa mu dace, ya kuma ‘debe mana munanan zato daga zukatanmu...”
Gyaran murya Alhaji Faruk yayi, ya ‘kara sipping tea 'dinsa kafin ya mai da duban sa ga
Saifullah, cikin muryar umarni yace,
"Yanzu ba sai anjima ba, Ina so ka rubuta takardar sakin Islam, ka bani. Ga biro nan a kusa da
kai, Ungo nan ga paper, rubuta ka bani.."
Dai-dai lokacin da Saifullah ya 'dago a razane yana kallon mahaifin sa, A dai-dai lokacin a
'bangaren Islam kuma, wayar tace tayi 'kara, a razane ta jiyo muryar Saifullahi cousin dinta yana
sanar da ita...........
*****
XAFAFA BIYAR;
DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOXO
ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka
litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*
_*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_*
[1/3, 10:54 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_
*_NA*_
_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_
_*®HASKE WRITERS ASSO._*
*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_
*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_
_BILLYN ABDUL_
*_SHAFI NA 67_*
_nanahafsat.wordpress.com_
‘Difff...... Numfashin Saifullah ya ‘dauke, wata razananniyar ‘kara Islam ta saki tana ‘dora
hannuwa akai, Alhaji Faruk ya kira Mami ta janye Islam. Su kuma shi da Aji Mommodu suka
‘dauki Saifullah kamar gawa aka ‘dora shi akan kujera, ruwa aka yayya fa masa amma ko motsi
ba yayi, Haj Zuwairah sai kai da komowa take yi a parlorn, tana adduar Allah ya tashi kafad’un
Saifullah, ahankali numfashin sa ya dawo amma iya ciki kawai, cikin gaggawa suka ‘dauke shi
sai asibiti, dayar motar kuma Haj Zuwairah ce da Islam sai Fatima yayar Saifullah itama da
tsohon ciki, haihuwa ko yau ko gobe. Ana shigar da shi asibiti likitoci sukai kansa, suna bashi
temakon gaggawa, ai kuwa da taimakon Allah da oxygen da aka sanya masa yafara numfashi
normal, amma jikin nasa is weak, Dr Jalaludden, shine likitan da ya duba Saifullah, a tsaye ya
samu su Daddy sunyi cirko-cirko, Islam kuma na daga can baya ta kifa kanta tana kuka, Dr
jalaludden ya nufe su yana murmushi, Aji Mommodu yai hanzarin cewa,
“Dr ya jikin Saifullah, ya farfad’o kuwa?”
Dr ya zare face mask din dake hancin sa kafin yace,
“Alhamdulillah ya farfad’o, sai kuyi wa Allah godia, dan gaskia condition dinsa bamu saka ran
numfashin sa zai dawo normal ba, saboda sanda kuka kawo shi har ya shiga coma stage, Toh
kuma dai Masha Allahu, numfashin sa yadawo normal, amma acikin ku waye mahaifin sa?
Inaso muyi magana ne..”
Aji Mommodu yace,
“Nan duk iyayen sa ne, waccen yayar sa ce, ta ‘k’arshen can kuma matar sa ce.”
Ya ‘karasa fad’a yana nuni da su Fatma da Islam. Likita yace,
“Allah sarki, Toh idan ba damuwa inason muyi magana da ku biyu mazan.”
Kad’a kai su kai, suka bi bayan sa har ofishin sa, guri ya basu suka zauna, kafin shi ma ya
zauna yana duban su da kyau, sannan ya fara magana da,
“Toh kamar yadda na fada muku Saifullah yana cikin critical condition gaskia, jinin sa ya hau da
yawa, sannan akwai alamar dimbin damuwa atare dashi, ba ma wannan kad’ai ba, harda
chronic ulcer. Garin yaya kuka bar matashi haka da wa’ennan tarin cututtuka dake barazanar
‘karar da rayuwar sa akoda yaushe?”
Aji Mommodu ya dubu Alhaji Faruk, sukai kallon kallo, kafin Alhaji Faruk yace,
“Hau hawar jini fa kace likita...?”
Dr Jalaludden ya jaddada kansa alamar tabbatar da zancen da ya fada hakan yake. Aji
Mommodu yai ajiyar zucia kafin yace,
“Amma likita a iya sanin mu babu wani abu da yake damun Saifullah, da har zai sanya kansa
cikin damuwa haka..”
Alhaji Faruk ya girgiza kansa yana kallon agogon hannun sa, kafin yace.
“Toh ko zancen Islam ne?”
Dr Jalaludden yai hanzarin cewa,
“Wacece ita Islam ‘din?”
“Matar sa ce, wadda muka nuna maka ita a waje...” cewar Aji Mommodu.
Dr Jalaludden ya jaddada kai kafin yace,
“Ko zan san meyasa matar sa ta zama wani ‘bangare a sashen shiga matsalar sa?”
Alhaji Faruk ya hangame baki zai magana, Aji Mommodu yai hanzarin cewa,
“Da akwai y’ar matsalar da aka samu ne, shine muke tunanin rabuwar su zai fi, akan suci gaba
da zama a inuwa d’aya..”
Dr Jalaludden yai shiru, yana kallon su, ya cire biron dake bakin sa, Daga kai yayi sama, kafin
ya sake mai da duban sa gare su yace,
“Shin matsalar babba ce da har kuke maraba da ita? Yaron ku ya kamu da rashin lapiar dake
barazanar farautar rayuwar sa, why.. why?”
Daga Aji Mommodu har Alhaji Faruk shiru sukai, suna raba idanuwa, dr Jalaludden ya saki dan
karamin tsaki, kafin ya sake cewa,
“Toh ni dai abun da yasa na kira ku kenan, idan da hali dai ku ba shi matar sa pls, idan lefi yayi
ku ke neman hukunta shi haka kuyi hak’uri dan Allah, rayuwar yaron ku itace gaba da komai
agare ku yanzu, kuyi tunani akai Alhaji..”
Yana gama fad’a ya mike yana duba agogon dake daure a wutsiyar hannun sa, kafin ya sake
cewa,
“Bari na koma wajen sa, maybe ko ya farfad’o.. Excuse me pls”
Cewar dr Jalaludden ya fice, rataye da stethoscope. Aji Mommodu ya dubi Alhaji Faruk, su kai
kallon kallon, ‘Ina mafita?’. Alhaji Faruk yai ajiyar zuciya kafin yace,
“Ya kake ganin za’ai, an ya idan muka tilasta yarinyar nan bamu cuceta ba?”
“Gaskia kam, sai ya d’au dangana, komai ‘dan hak’uri ne, dama ba komai da kake so kake
samu ba, akwai hills and valleys a rayuwa.. Allah ya zabi ahunda yafi alkhairi..”
Cewar Aji Mommodu, ya fad’a yana jinjina kansa, Alhaji Faruk yace,
“Kwarai kuwa, zab’in Allah shine mafificin alkhairi.. Muje Modu..”
Mikewa sukai, suka fita.. Yadda suka bar su Haj Zuwairah haka suka gan su yanzun ma, Islam
still kanta a ‘kasa, Dr Jalaludden ya fito yana zare safar hannun sa, kafin yace.
“Toh.. Alhamdulillah, Saifullah ya farfad’o and yana tambayan wata Islam, so please Islam taje
kafin mu san matakin da zamu sa shi a kai..”
Haj Zuwairah ta dago Islam itada Fatmah, zasu shjga ‘dakin dr Jalaludden ya girgiza kansa,
alamun a’a, kafin yace.
“Mama kuyi hak’uri, Islam first,before anything else..”
Jaddada kai su kai, suka ja baya, ita kuma Islam ta shiga dakin gabanta na tsananta fad’uwa,
ido hudu sukai da Saifullah, ya miko mata hannun sa a hankali , dr Jalaludden dake kallon su
yai wani shegen murmushi, kafin ya janyo musu ‘kofar ya kulle..
‘Karasawa tayi, taki kallon sa bare hannun daya ke miko mata, ta mai da kallon ta ga window, a
hankali tace,
“Ya jiki?!”
“Da sauki..”
Ya furta can ‘kasan mokoshi, kallon sa tayi, idanuwan su suka sarqe dana juna, ta ‘dauke da
sauri saboda kwarjinin da yai mata, shi kuma ya shagala da kallon ta, mikewa tai zata fice ya
rik’o hannunta, murya ‘kasa kasa yace,
“Please stay...Please...Islam’”
Mutuniyar ku har cikin magudanar jininta taji dad’in yadda ya furta sunanta, ya ja laaam ‘din
kamar wani balarabe, dan bata rai tayi kafin tace,
“Me zan maka ne?”
“When you leave, I swear I can't breathe, Do you really care Islam?”
Kwace hannun ta tayi, zata gudu yai saurin jan mayafinta, luu tafada akan sa, baiwar Allah ta
shiga neman kiciniyar kwace kanta, mutumin ku ya hana, ya kara mannata a jikin sa, yana
shakar kamshin jikin ta, tsoro ya kama Islam jin saifullah na ajiyar zucia, zata tashi ya sake
damke ta ajikin sa, cikin kunnenta ya shiga rad’a mata,
“Please calm down, gimme just 3mins..”
Shiru Islam tai, tana lafe a kirjin sa, jin kamar za’a turo k’ofa ya sa ta, saurin kwace kanta, suka
shiga kallon kallo, ya saki lallausan murmushi, ta yatsina fuska tana kallon gefe kafin tace,
“Kar ka sake yi wa matar wani haka”
“Matar wani kuma?”
Yafad’a yana ware idanuwa, jaddada kai tayi alamun da gaskiyar ta ta fadi haka, murmushi
kawai yayi, kafin ya sa hannu ya dafe saitin zuciyar sa, cikin lumshe idanuwa yace,
“Kece maganin zuciata Islam, I love you more than life itself. Pls kakki bari