Showing 81001 words to 84000 words out of 86718 words
isar sa kafin cikin gwada muryar Saifullah yace,
“First love da ma Islam aka bari..”
Ya shiga daria harda rike ciki, Saifullah ya zabga mai harara yana juya mai baya kafin yace,
“Ai ni an cuce ni wallahi, da za’a rasa wanda za’a had’a ni da shi sai kai, ‘katon banza da kai,
gwauro marar mata...Mts”
“Eh ana dai had’a, kuma dole da katon banzan zaku kwana a ‘daki d’aya, jarababbe bakada
lapiar ma sai ka ‘kwakwume yarinyar mutane, banza marar ta ido( kunya)..”
“Eh naji, ai halaliya ta ce, matata ce ai, So suffocating.”
Tsaki Abbas yayi, kafin ya shjga daria sai da yai mai isar sa kafin yace,
“Kai baccin ka kawai, angon Islam, autan Mami ‘dan gidan Uncle Modu bada kanka asare..”
Haka dai Abbas ya shiga tsokanar Saifullah suka raba dare suna abu d’aya... Cikin kwanaki
ukun nan Saifullah a daddafe yayi su, domin ko sau d’aya Islam bata sake zuwa ba saboda hot
practicals suke yi, kuma mostly night lectures ake musu,
A ranar da za’a sallamo Saifullah ne Aji Mommodu ya kira Islam ya tambayeta zata zauna da
Saifullah ko ya sawwake mata? Ya ‘kar’kare da,
“Kar kiji komai Islam, idan har bakyason Saifullah kar ki cu ci kan ki, idan kuma ki na son ki
koma ‘dakin ki to, duk dai zab’i ya rage na ki...”
Kanta a ‘kasa tana wasa da jelar hannun rigar ta tace,
“Zan koma ‘daki na Baba...”
Haj Zuwairah da Fatima da ke labe suna sauraron su, jin abunda Islam tafada yasa su sakin
lallausan murmushi......
——-
XAFAFA BIYAR;
DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOX
ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka
litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*
DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOXO
_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_
[1/3, 10:54 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_
*_NA*_
_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_
_*®HASKE WRITERS ASSO._*
*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_
*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_
_BILLYN ABDUL_
*_SHAFI NA 70_*
_*EPISODE FINALE (KARSHE)_*
_nanahafsat.wordpress.com_
“Toh..Zan danja hankalinki akan yadda ya kamata ki dinga tarairayar Auta ta siga daban-daban
kamar; kissa, jan hankali da kuma ladabi da biyayya kowanne xan daukeshi d’aya bayan d’aya
namiki bayani akansa, Kisani dukkan xamantakewar rayuwar aure ba xata yiwu ba saida kissa,
idan akace miki kissa ta kunshi abubuwa da yawa, kissa ta kasu kashi biyu akwai kissa marar
kyau akwai kuma kissa me kyau, Mara kyau itace ta shirye tuggu da makirci da sihiri, Za ki ga
kishiya ta kullawa kishiyarta sharri ko idan ta daidaici ta gama girki taje ta tsuga mata gishiri ko
yaji ko kananzir ko kuma tai k’ok’arin fitar da ita daga gidan ma gaba d’aya, zaki ga mace ta
shiga tsakanin d’an mijinta da mijin,
“Ta cikin dabara ko mace tashiga tsakanin mijinta da iyayensa da makamantansu wannan kissa
mara kyau sede muce tur da ita. Allah ka ganar da masu irin wannan kissa, Amma kissa mai
kyau itace kulawa da mai gidah da tarairayarsa kamar kwai wanda daga ciki akwai, Kissar
magana, kissar tafiya, kissar kwalliya, kissar abinci, kissar tsafta, kissar kallo mind you ba kallon
film ba to kallon miji nake nupi, yawwa se kissar shagwaba da kissar kwanciya se kissar kula da
jikin mai gidah suma xan d’auki kowanne nai miki bayani akansa Ina fatan kina ganewa?!,
Cikin k’asa da kai Islam tace,
“Eh ya Fati..”
“Kissar magana: idan xakiyi magana da mijinki ki kasance cikin nutsuwa da tauna magana da
xaki gaya masa kafin ki fadeta don gudun gaya masa maganar da baxai ji dadinta ba ko bata
masa rai, Ki dinga magana cikin sigar hankali karki dinga bud’e masa muryarki kala kala wani
lokacin ki maketa wani lokacin ki dan budeta wani lokacin ki dinga yi a hankali kamar bakyason
magana, wataran kuma idan kinason gaya masa magana mai dadi ko ta soyayya kice saiya
baki kunnensa xaki rada masa. Sai kissar mu ta gaba,
“Kissar tafiya; idan xakiyi tafiya kuma kin tabbatar yana gurin ko yana kallonki daga inda yake ki
dinga tafiyar da xata dauke masa hankalinki xuwa gareki misali ki dinga tafiya a hankali kamar
bakyason taka k’asa wani lokacin ki dinga tafiya kina karairaya kina dan jujjuya jikinki wani
lokacin kuma sauri sauri xaki dingayi kina juya maxaunanki idan ta gaba yake kallon ki kisan
yadda xaki dan dinga girgiza kirjinki cikin hikima bata sigar da xai gane ba, amma fa Islam
mijinki kad’ai xaki dinga yiwa wannan kala kalar tafiyar cux kikaiwa wani xaki dau zunubi ne,”
Cigaba da koyamata kissoshi tadingayi kama daga kissar kwalliya, da kissar abinci kissar tsafta,
da kuma kissar kallo ciki harda kissar shagwaba data kwanciya, wanda sosai Ya Fati taja
kunnen Islam akan kissar kwanciya ta kar kare mata da yadda xatai kissar kula da jikin mai
gidah,
“Hope kingane?!”
“Nagane Ya Fati” cewar Islam datai wiki-wiki da idanuwa wai yau Ya Fati ce take hira da ita,
hirar ma ta manya duk kunya ta davaibayetaa
“Yawwa to sai dan karin jan hankali daxan miki wanda idan kika dumfafi yinsa tabbas xaki xamo
shalele awurin mijinki yaxamto ba wacce yakeso da gani sai ke hanyoyin jan hankalin sune,
“Kula da duk wani abu da mijinki yafi so,ki kula sosai da duk wani abun da bayaso ki lura da
abinda yake damunsa da hanyar da xaki kula da iyayensa da danginsa da yadda xaki xauna
lafiya da kowa babu ruwanki da wani kishi na banxa da wofi wanda xe kaiki ga hypertension,
kishi dole ne ba ace karki ba amma akwai irin kishin da akeyi bana yanxu da yaxama na hauka
ba, kede babu ruwanki don baki taso kinga anayi a gidan ku ba...
Islam ta daga kai, tana tuno irin buga kishin da ake a gidan su, Fatima ta ci gaba da cewa,
“Na ga, ga Ammi nan da Maman Arfat kamar ya da kanwa haka suke abun sha’awa ba’a taba
jin kansu ba ina fatan kina ganewa?!”
Kad’a kai Islam tai tana wasa da yatsun hannunta cikeda nutsuwa. Ya Fati ta cigaba da yi wa
Islam jan hankali akan rayuwar gidan miji ta k’ark’are da,
“Abu na k’arshe shine ladabi da biyayya, babbar magana kenan domin duk abubuwan dana
fada abaya idan ba ladabi da biyayya yaxama na banxa don duk iya tafiyar ki ko iya farinki idan
bakya yiwa miji biyayya meye amfaninsa?! Misali kinyi kwalliyar jan hankali kinyi masa kalar
girkin dayake so jira kike ya dawo yaga kwalliya, Yaci abincin da kika tanadar masa amma
yashigo ba sannu da xuwa ba karbar kayan hannunsa saidai ki bishi ki dire masa abincin da
kika yi masa tana iya yiwuwa ma alokacin ki fara masa k’arar ko kudi da makamantansu toh tell
me tayaya zaiga kyan kwalliyar sannan kuma yaji dadin abincin?!,
“Ko kiga wasu matan miji na magana suna yi suna fada sosai fad’i in fada bai dace ba sam
kamata yai idan mai gidah yana fadansa kiyi masa shiru idan yagama sai ki bashi hak’uri idan
kuma ke aka batawa baxaki iya bada hak’urin ba tunda ranki yakai kololuwa a baci to kiyi shiru
kawai kuma ko menene yace kiyi masa koda kuwa ran naki a bace yake don kansa shima xe
sakko ku shrya, Wasu kuma matan xaki ga suna yawan korafi akan maxajen su don abinda ba
abin fada ba sai su rufe su da fada wasu ma kawai xakiga sun fice daga harkar matan kwata
kwata inkinga sun kusancesu to sede idan rabo ya tsinke yawanci kuma xakiga akan maganar
da mukai d’axu ne akan rashin gamsuwa damu da maxajen mu ba sayi xakiga mace har mace,
Kamar ita tai kanta don kyau sai kiga sun had’a kishi da wadda bata kaitan ba harma xata
xamto itace mai fada aji gurin mijin xakiga yana Allah Allah girki ya xagayo kanta don yafi
gamsuwa da ita xakiga wasu matan suna yawan tambaya to meyasa wata macen ake
gamsuwa da ita wata ba’ayi?!,
“Ba komai bane yake kawo haka kisani sai kowa da irin ni’imar da Allah yai masa misali
kowanne jinsin halitta akwai maza akwai mata kuma both ana samun farare da bak’ake dogaye
da gajeru mai kib’a da siriri ke kowanne abu dake jinsin bil adama xaki ga nawani yafi nawani to
haka ma ni’ima take ajikin mata da maxan wata macen tanada ni’ima sosai bata buk’atar kari
wata kuma tsaka tsaki ce wata ma bata da ita se d’an abunda ba’a rasa ba,
“Don haka Islam kisani kamar masu bukatar karin jini da ake cewa ga abubuwan daya kamata
suci haka ma matan masu neman k’arin ni’ima ajikin su akwai abinda yakamata suci domin
ance idan kanada kyau to kadad’a da wanka,sai dai wasu matan suna amfani da magunguna
barkatai wanda wasu ma basusan komeye ba sudai suci susha buk’atar su ta biya kawai
shikenan, Wanda xakiga yin hakan xakiga yana haifar da cututtuka barkatai ga mata,shawara ta
dake Islam karki xamto cikin irin wa’innan matan masu bankawa cikinsu kowane magani suka ji
ance yanayi aa sam karki soma kowaye yakawo ko yaxo maki dashi karki soma amfani dashi
kinji de na gargadeki domin hakan yana haifar da toshewar mahaifa,hana haihuwa ko canxawa
yaro kamanni kamar wata k’awata sumayya matar ma’aruf wallahi abinda yafaru da ita
kenan,Tahaifo yaro marar cikar halitta abun tausayi saboda ita komai cusawa take ta bankashi a
baki duk bamu sani ba se bayan da xata haihu a asibiti dr tace har cancer magungunan suke
sawa dakyar aka mata cs don kasa haihuwan tayi abu nabiyu ga kaikayin gaba wato
infection,Da kurajen gaba plus ciwon ciki ke da abubuwa da dama de kede ki lazimci shan fruits
kamar yadda kikaga ana saki sha anan su,
“Kankana,gwanda,ayaba,guava,lemo,tumatir,rake,aya,kwakwa,dafaffiyar gyada
xuma,nono,madara,madaran shanu gurji cukwi,zogale da ruman da inibi se tuffa da kuma xaitun
kina ganewa kuwa?!”
Nodding kanta kawai Islam tai gaba d’aya jikinta yayi sanyi se yanzu tasan tabbas aure aka
mata batare da ya fati tadamu da damuwar da Meenah tashiga ba tacigaba da maganar ta,
“Se abu na k’arshe naga lokaci na ja, Auta yana ji ranki a kasa,Addua wato kirik’e addua,
wallahi Islam addua makarin mumini ce ke duk wanda ya lazimci addua wallahi baxe taba
tabewa ba azkhr dinnan kidinga yawaita yinsu nataho maki ma da wasu littafin du’as din suma
ki rik’esu gidanki kullum yaxamto cikin karatun qur’ani musanman suratul baqra domin duk
gidan da ba’ayinta ance kamar kango yake, Ki yawaita yin addu’oi na neman tsari ga korar
shaid’an ya kuntata masu ya karyasu ke dama mutane ma sharranta masu nufarku da sharri,
addu’a tana jawo yardar allah ta’ala, suna gusar da bakin ciki da bacin rai a zuciya,suna
janyowa zuciya farin ciki da nishadi,suna karfafa zuciya da jiki,suna jawo arziki suna kara imani
da tawakkul da sabr ke sunasa komai na mutum ya daidata ya samu peace of mind ki kama
Allah Islam, kirike addua da qur’ani Insha Allah rabbi xaki bani labari,anan xan tsaya seki fad’i
tambayoyin ki karkiji kunya ta Islam, ko tsoro saki jikinki ki fad’amun abinda baki gane ba.,
Shiru Islam tai tana k’as k’as da yatsun hannunta kunya dukta isheta jin shirun yayi yawa ne
yasa ya fati sake tambayrta,
“Uhum Islam ina jinki”
“Ba..Babu komai ya fati duk nagode JazakillAhu khairan”
“Ameen..To shikenan dukde abunda baki gane ba ko kikeda karin bayani akai seki kirani awaya
yawwa nasanki dama ke sarkin kamshi ce amma ki kara xage damtse khumras dinnan na
wanka dana wanki da jiki dana moping duk fa kidage wajen amfani dasu kingade yadda mijin ki
ke son kamshi, ki sake kaimi da sauran turarukhan jiki dana tsugunno dana kaya dana gidah du
kulaccams dinnan duka kiyi amfani dasu, Idan sun kare kiyi waya ayo miki wasu koki had’a da
kanki irin kamshin da kikeso aikin iya ko?!”
“Eh ya fati”
“To shikenan Allah ya miki albarka ki shirya, ga kaya nan da laffaya inji Mami, wannan kuma
tsumin chad ne ki sha yanzu, karki mike sai bayan minti goma, wannan kuma cinye shi zaki tas,
idan kin gama sai ki sakko, Allah ya sa ki koma a sa’a ya kad’e fitnah, ya baku zuri’a dhayyi
ba...”
Cewar Ya Fati.. Ta karasa fada tana mai nuna mata komai da amfanin sa, a kunya ce Islam
tace,
“Nagode Ya Fati, Allah ya saka muku da alkhairi, ya sa ki sauka lapia, Ameen.”
“Ameeen”
Cewar Fatima, ita kuma Islam ta mik’e ta shiga shirya wa...Hankali kwance ta gama kintsawa,
tayi amfani da duk abun da Ya Fati ta bata tayi, admiring kanta ta tsaya yi ta cikin mudubi, ba
kadan ba kayan sun mata kyau, lace din pink ne laffayar kuma pusher pink. Ganin su kadai ne
ba kowa, yasa ta shafa pink jambaki, Ai kuwa ya mata kyau sosai, dan karamin bakin ta ya
kama sosai da jambakin, abun dai sai fadar; soo masha Allah. Kasa ta sauka tun daga nesa
Saifullah ya tsurawa Islam kallo, tamkar yau ya taba ganin ta, Haj Zuwairah da sauri ta ‘karasa
ta rik’o Islam, Islam kuwa ta ‘barke da kuka, Don ba kadan ba takeson Haj Zuwairah, ganin ta
‘dauke ta kamar ‘yar data haifa, tare suka dinga kukan, domin Fatima ma sai da tai hawaye, sun
bata tausayi, kuma ta lura mahaifiyar tasu na yiwa Islam din wani irin so tamkar ba sirikar ta ba..
Daga k’arshe dai Haj Zuwairah daki kawai ta shige ta rufe, Saifullah ya kama hannun Islam
suka tafi, dai-dai bakin kofa ta cije tana shesshekar kuka, Ai kuwa yai mata ‘daukar jarirai ya
direta a mota itada kayan ta...
A hanya ya tsaya ya sai kaji da kayan ‘kwalam da makulashe, suka nufi gidah yana aikin bawa
Islam hak’uri, ba abunda yake kara tunzura kukanta irin first night din da Lee ta tsoratar da ita,
Suna komawa gidah tai hanyar dakin ta, komai a killace a tsaftace, da alama Saifullah yasa an
gyare gidan. Wanka ta sake yi ta feshe jikin ta da turarukha, nan Saifullah ya shiga shima da
kayan baccin sa, dauke da plate cike da kaji da sauran mouthwatering kayan dadi, a hankali
yace mata,
“Love ga abinci sakko ki ci pls..”
Bin kazar tai da kallo ta ‘dauke idanun ta daga gare sa, durku sawa yai kafafuwan sa zube a
kasa yayi kneeling down, hawaye fal idanun sa, tuni suka fara wanke kyakkyawar fuskar sa,
kafin yace.
“Dan Allah love kiyi hak’uri, ki yafemin, hakika nayi kuskure a da, amma inaso ki dau hakan ki
ajiye a matsayin past life, love ko Allah da ya haliccemu muna masa laifi kuma mu roke shi ya
yafe mana, so pls ki yafemin Love, kwatankwacin haka ma bazan sake miki ba insha Allahu,
wallahi wallahi ni ba ma SO na ke miki ba ‘KAUNAr ki nake, domin ‘kauna bata karewa kullum
daduwa take yi, So kuma yana raguwa kuma wani lokacin har dena yin sa ake yi, Ina miki son
so, Ina miki son kauna, Ina miki tacacciyar ‘kauna marar gauraye...”
Shiru yai yana goge hawayen fuskar sa, ahankali Islam tasa hannu ta ‘dago shi tana goge masa
hawayen kafin tace,
“Ni ma Ina kaunar ka Zawj, I love you pass my mind beyond my soul, ni ban rike kaba dama a
raina, Allah ya yafe mu baki d’aya...”
Dadi Saifullah yaji, ya kama hannun Islam suka zauna, Kazar ya dakko ya sa mata a baki yana
cewa,
“Ki ci sosai Love, wannan itace kazar amarcin mu, ki dau yau tamkar itace ranar da aka kawo ki
gidan ki, kuma a yau ne zan shayar da ke zumar da tafi kowacce zaki, Ina fatan zaki bani hadin
kai?”
Islam tai gum da bakin ta, Saboda ta gano nufin sa, Ai kuwa ya saki murmushi yana cewa,
“Matsoraciya...”
“Eh dai...”
Caraf ya hade bakin su, dama tun dazu yake muradin haka, sun jima suna abu d’aya, kafin su
cinye kajin tas su ka kora da yoghurt, bandaki suka shiga atare sukayo alwala da brush, bayan
sun kurkure da mouthwash na mint, Su kai sallar isha’i, sun ‘dan tab’a kallo kafin su koma dakin
sama, Saifullah yace da ita,
“Love tashi muyi sallar nafila mu godewa Allah, abisa azurtamu da yayi na samun junan mu..”
Daga kai kawai Islam tayi, suka yi sallar, Saifullah yaja ya zauna a gabanta yana mata
tambayoyi akan addinin musulunci, ta amsa dai-dai gwargwadon sanin ta, gado suka haye
gaban Islam sai fad’uwa yake yi, Saifullah na hankalce da ita, janyo ta yayi jikin sa yana karanto
adduar bacci;
:“ َّمـُهَّللَا َكِمْساِب ُتوُم
َأ
”,اَيْح
َأ
َو
Can kuma ya ‘kara da adduar saduwa da iyali(du’a when having relation with wife):
:“
ِ
مْسِب اللَّه ، َّمـُهَّللَا اَنْبِّنَج َناَطْيَّشلا ، ِبِّنَجَو َناَطْيَّشلا اَم