Showing 15001 words to 18000 words out of 86718 words

Chapter 6 - SAIFUL-ISLAM Book Complete by miss xoxo (2).pdf

06 Jul 2025

2076


*SADAUKARWA GA:*
_ASY KHALEEL💕_

*TUKWICI NE GARE KU:*
_YA HAJJAH CE😝_
_BILLYN ABDUL😘_



*SHAFI NA 14-15*

_This chappy goes to you *MISS HAFSY* favorite co-writer and a dearest friend of
mine_😻🌹❤

nanahafsat.wordpress.com


Saurin d'aga kansa Dr Khaleel yai, yana duban Inna Bilkisu. Jaddada kai yai alamun yayi na’am
da zancen, Murmushi ya fad'ad’a akan fuskar sa yace,

“Wannan abu yayi Inna..Wallahi yayi, dama na jima ina son had’a Saifullahi da wata acikin
yaran nan, sai dai duba da su d'in duk yara ne duka- duka sha biyar suke, kuma ko gama
makaranta basu yi ba.”

“Haka ne.. Amma ai ana aurar wa ko k'asa da hakan, sai dai yanzun ba kamar lokacin mu bane
tunda inaga Islam ce ma kawai tayi shekaru goma sha biyar ko?”

“Eh haka ne Inna, ashe akwai tazarar shekara d’aya tsakanin su da Hafsat, ita Hidaya ce dai
suke sa’anni da Islam.”

“Eh..To amma fa ba cewa nayi lallai ba, ba kuma cewa nayi dole ba, kuyi shawara da d'an uwan
naka yadda kuka ga ya dace sai ayi hakan.”

“Haba Inna, ai wannan kyakkyawar shawara kika bayar kinga dama fa aiki yake yi, duk sa’annin
sa sunyi aure, kuma shine dai-dai da Nusrah, saboda kinga ta gama komai na karatu, rantsar
da su kawai xa’ai watan gobe su zama lauyoyi..”

“Masha Allahu, Allah ya sanya albarka a abinda aka karanta. Munyi waya da wannan yaron, (Ya
Bala) yace shima yau zai shigo Habujan, amma ban sanar masa ba tukun sai yazo sai ayi
komai a gama ko?”

“Kwarai kuwa Inna.. Hakan yayi wallahi sosai, Allah ya k'ara miki lapiya da nisan kwana mai
amfani, Allah ya jikan Malam (mahaifin su) yasa aljannatul firdaus makoma ce agare shi.”

“Ameen ya Allah.. Allah yayi muku albarka”

“Ameen Inna..Bari naje ciki na gaya musu a yiwa Ya Bala girki kafin ya k'araso.”

“Eh hakan yayi. A gaida su”

“Za suji Insha Allahu, yau mazajen naki basu shigo miki bane Inna?”

“Ni nace abarsu garin ya d'an rufa tukun na, sai akawo min su, kaga yanzu da d'an sanyi yau.”

“Eh haka ne kam.. Toh bari naje Inna sai na dawo.”

“Yawwa d'an tsaya..”

Gani yai ya tsaya daga tafiyar daya soma yi ya dawo ya tsugunna cike da girmamawa yace.

“Maganar su Karimatu ne, dan Allah nasan kana adalci sosai a tsakanin su, kar ka gajiya da
hakan, ka cigaba . Allah yayi maka albarka.” Kansa a k'asa cike da girmamawa yace,

“Insha Allahu Inna..Na gode k’warai”

Mikewa yai ya fita bayan ya mata sallama, ko bata fito ta fad'a ba, sarai yasan kishi ne ya rufe
idanun su jiya suka zo suka yi masa sharri. Murmushi kawai yayi yana cewa,

“Mata.. Kai Allah ya shirya mana zuri’a”

Sashen Helwa ya fara shiga don anan yake, ita kadai ce sai ma’aikatan ta don 'yan biyun ta ma
kullum a sashen Haj Aysa suke wuni, sai dai bacci ya dawo dasu. Wani lokacin ma acan suke
baccin.

Sun d'an taba hira nan yake sanar mata zuwan Ya Bala. Kitchen ta shiga bayan fitar sa don yin
abincin tarbar yayan mijin nasu. Daga nan ya nufi sashen Haj Aysa, ya jima yana d'auke da 'yan
biyun sa, gefe kuma su Arfat sai d'ane k'afafunsa suke yi, Islam dake kusa dashi ta zumburo
baki,
“Daddy...”

“Na’am Mamana”

“Daddy yanzu kafison su Areef. Sam baka sona kaman da” Ta k’arasa fad'a tana shagwabe
fuska.

Murmushi yai yana riko hannun ta da yake a kusa dashi take, cikin muryar lallashi yace,

“Haba nina isa?! Mamana ai kece gaba da komai, kawai dai kinga su ne ‘yan fari a maza amma
kuma ai kece 'yar auta a mata ko?” ‘Daga kai tayi tana murna.

Sai da ya jima sosai anan har Haj Aysa ta fito daga wanka ya sanar mata zuwan Ya Balan, kafin
ya shiga wajen Haj Karimatu tana zaune tana aikin taunar cingam (chewing gum) dan ya zamar
mata al’ada.

Gefen ta kuma Hafsat ce tana kwance rigingine sai shek’ar bacci take.Tashin ta yayi yace ta
koma d'aki ta kwanta had’e da jaddada mata karta sake kwanciya a rigingine ba kyau, duk
abunnan da yake haj Karimatu danna waya take, sai daya mike zai tafi ne ya dubeta yana
fad’in,
“Sai faman danna waya kike, Wai ni ban gaya miki cewar hasken waya na cutar da ido ba ko
kuwa?”

“Alhaji wani littafin hausa nake karantawa wallahi, ba kaji dad'in sa ba”

Jaddada kai yayi yana mamakin wannan k'arfin halin nata,

“Toh Ya Bala dai yana nan tafe, anytime from now, za’a d'akko shi a airport..”

“Toh.. Allah ya kawo shi Lapiya”

“Ameen!” Kawai yace, yai ficewar sa sashen Yafendo.

Tana zaune itada Nusrah sai rusgar kuka suke yi, shi abinma dariya yaso ya bashi wallahi, abu
ya k'ici ya k'i cinyewa, zama yai kusa da Nusrah, gaishe shi sukai dukkan su, ciki harda Hidaya
data fito daga kitchen da indomie a hannunta,

“Daddy ga indomie..”

Kallon ta yayi ita da indomien, murmushi yai yana kad’a kai,

“Nagode Hidaya amman na koshi, indomie sai ku ‘yan indomie generation”

Daria Hidaya ta kyal-kyale da ita tana zuba lomar indomie a baka,

“Daddy kenan, Allah indomie na da dad'i amma kai baka so”

“Zaki koya munci ne?”

“Eh Daddy..” Ta fad'a tana dawowa kusa dashi da plate a hannun ta,

“Haa bakin ka to daddy” Murmushi yayi kafin yace,

“A’a ba yau ba fa sai wani lokacin. Yanzu kije d'aki zamu yi magana dasu Umman ki” (Yafendo
da Nusrah).

Amsa mishi tayi da toh, kafin ta haye sama abun ta. Juyawa yai yana fuskantarsu baki d’aya.

Ajiyar zucia ya sauke mai nauyi, hakan yasanya su juyawa su maida kallon su gare shi.

“Nusrah..”

“Na’am Daddy.!”

“Kisani shifa komai na duniya muqaddari ne daga Allah, Wallahi bamu da tsumi ko dabara ta
canza yadda komai yake tafiya a rayuwa face Allah ya yadda da hakan, Ina ilimin ki ya tafi?
Common and Islamic law kika yi, Duk Ina tarin tauheedin da ku kai yabar kanki? wallahi tunda
kikaga haka Allah ne zai musanya miki da mafificin alkhairi, ita rayuwa baka isa ka tsarawa
kanka yadda kake so ba, komai kud'in ka, ko mai k'arfin mulkin ka, kai kowacce irin sarauta ce
gare ka wallahi sai Allah ya yi ikon sa akan ka, saboda haka ki kwantar da hankalin ki, Insha
Allahu rabbi alkhairi ne wannan abu daya faru, dama can shi d'in ba mijin ki bane, kisa hakan a
ranki, ki cire damuwa kina jina ko kuwa da iska nake maganar?”

Saurin kad’a kai tayi,

“Abba duk naji, na kuma gode Insha Allahu zan sanyawa zuciata hak’uri.”

“Masha Allahu.. Ni kuma na miki alqawarin wata babbar kyauta nan ba da jimawa ba, zan cika
maki ita da yardar Allah..”

Murmushi tayi cike da murna tace,

“Daddy Nagode, Allah ya saka da alkhairi”

“Yawwa..” Ya fad'a yana maida duban sa ga Yafendo data rafka uban tagumi ta dulmiya duniyar
tunani,

“Aminah(Asalin sunan ta kenan)”

“Na’am Alhaji.”

Rausayar da kai yayi, hakan ya sanya Nusrah saurin tashi ta basu waje, kalamai masu dad'i
yake yi mata, had'e da qarfafa mata gwiwa akan ribar hak’uri, ya jima kafin ya tashi yana fad'in,

“Yawwa, Yaya Bala zai zo yau a kowa ne lokaci zaku iya tsammatar sa”

“Allah ya kawo shi lapia..”

''Ameen.'' kawai yace yasa kai ya fice.

Wurin matan Yaya Bala yaje suka gaggaysa, duk sun caba ado suna jiran mijin nasu ya shigo,
shi abinma dariya ya bashi ganin yadda sukai ado kamar wad'anda zasu zab’en kyau. Ya jima
suna hira kafin ya koma sashen sa yana nazarin (research) wasu litattafai.

***

Karfe 4 dai-dai Yaya Bala yana parlorn Dr Khaleel, an shirya masa abinci kamar wani
restaurant, ya d'anci ba laifi, nan Inna Bilkisu da ke gefe ta shiga sanar masa da komai akan
Nusrah kuma kwarai yayi na’am da xancen domin fuskar sa ta nuna hakan,

Shafa sank’on kansa yai, cike da murmushi yace,

“Inna wallahi wannan zance yayi min dad'i ba kad’an ba, shi yasa yau na tashi duk zuciya ta
tana dad’i, ashe abunda xai faru kenan, to ni Ina ganin me zai hana kawai a had’e ayi gaba
d’aya da nasu Mudasser da Mu’utaseer, don suma sunzo sun sameni da maganar yaran da
suke nema, wasu yara ne anan Abujan, ita yarinyar da Mu’utaseer ma yake nema yace k'awar
su Marwa ce, Toh Kamaludden ma dama ina shawarar had’asu da Aysha 'yar Hansa’u, Toh
kuma ga maganar Saifullahi ma daddad'a tazo. Toh zan yiwa Nuradden magana ma kan lalle ya
tsayar da wadda yake so, shi kuma Shamsudden tunda naga mata basa gaban sa, Ina ganin a
had’asu kawai da Shema’u, duk mu’aurar dasu mu huta Inna, Kinga nan gaba da an tashi nan
da wasu shekaru sai na su Islam, su ukun suma sai a had’e ai nasu ko kuwa ya kuke gani?”

Hansa’u dake gefe sai gud’a take tana rangad’awa jin wannan daddad’an labarin,

“Abu zai yi dad’i, idan yaran zasu bada had'in kai”

Cewar Hansa’u cike da farin ciki, don dama a kauyen 'yar gaya 'yan uwan mahaifin su
Shema’un sai gulma suke yi suna yada maganar yara sun zama gand’ama-gand’ama amma
taki ta aurar dasu, bayan ga sa’oinsu nan sun tara ‘ya’ya, dan tsabar iskanci ta kwashe su sun
koma legas sun iskance gaba d’aya.
“Mu fa muka haife su ba su suka haife mu ba, aure tamkar anyi angama ne da yardar Allah
babu mai kawo cikas a cikin su, kuma watan gobe farko ko tsakiyar sa Insha Allahu xa’ai bikin,
kowannen su ya tare a gidan sa, Alhamdulillah tunda kowa yana nan ba sai ance a jira wane
ba.”

“Allahumma Ameen! Allah ya sanya albarka, ya bamu sa’a a cikin wannan lamarin.”

Cewar Inna Bilkisu wadda fara’a gaba d’aya ta cika mata fuska. Su hud’u ne dama a parlorn,
daga Ya Bala, Dr Khaleel, Hansa’u sai Inna Bilkisu. Tsaida shawara sukai kan anjima za’a yi
General meeting don a shaidawa kowa abinda aka yanke....



_Munada biki jama’a..💃🏿🥰❤ anko na kece raini za’a fitar🤗_








_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO_🧕🏼

[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...💕*_


*_NA*_


_*ŠNANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


ÂŽ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL💕_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE😝_
_BILLYN ABDUL😘_

*_SHAFI NA GOMA SHA SHIDA(16)*_

_Wannan shafin na kune ‘yan *SAIFUL_ISLAM💕FANS GROUP* Ina son ku, kuna ‘karamin
‘kwarin gwiwar rubutu, Musanman *Aunty Bilk😘, Juwairiyya Ummee*_da *Mamuxee Sule and
Ummuh Islam*_ _kai da duk ‘dauka cin ku, Fatan Alkhairi gare ku hazik’an makaranta🙏🏾
jazakum Allahu khairan🤗❤💕__
_nanahafsat.wordpress.com_

Bayan sallar isha’i rankatakaf ‘din yan gidan kowa ya hallara, jikoki kawai aka cire, sai su Arfat
da ba wani gane kan zancen zasuyi ba, duk suna sashen Haj Aysa, wajen Yakolo, Safa ce
kawai wadda bata nan itada mijin ta Mubassher. Amma dukda hakan anayin live video call
dasu, tamkar dai suna wajen.
Addu’a aka fara, gaba d’aya banda su Dr Khaleel babu wanda yasan akan mai taron zai
gudana, duk ‘dauka suke labarin fasa auren Nusrah za’a bayar, Shiysa kowanne su bai wani
bada full attention ba,

Da maganar fasa bikin Nusrah aka fara, sannan aka fara lissafo marassa aure agidan. Tuni jikin
su Shamie baby ya d’au rawa, dan akwai wani Alhaji mai tumbi ga shegen muni a legas da ya
kafe kan lalle ita yake so, ita kuma bata son shi, amma ya nace sai ya aure ta, don baba ma (Ya
Bala) har fada yai mata, Kan lalle ta dinga saurarar sa, shi mijinka bakasan wanene shi ba,
babu kyau wulaqanta mutane, jikin ta sai rawa yake yi, Shikenan ita kam tata ta bushe, duk tulin
shekarun data ‘dauka tana dakon soyayyar Shamsudden (Dan Ya Bala)a ranta yanzu shikenan
ta tashi a banza kenan? Ai batasan sanda zancen zucin yafito fili ba, cikin zunduma uban ihu
tace,

“Wayyo shikenan ni Shamie Baby, tawa ta ‘kare, Alhaji Tulu(wai dan yanada uban tumbi) ka
cuce ni, Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un na kad’e”

Duk sai kallo ya koma kanta, Islam ta gimtse dariar data taho mata, Nan Saifullahi ya juya yana
kallon ta, had’a ido sukai ya zabga mata harara, Ya Bala dake gefe ya dubi Shema’u yana
murmushi, shi duk ya gano abunda yasa ta zauce haka, duk dan akan ‘Alhaji Lawwali Mai Nera
ne’, danne dariar sa yai yana zare mata idanu,
“Lapia Shema’u?”

Saurin rufe baki tayi, ganin katob’arar da tayi, murya na rawa tace,

“Ba komai Baba, da zucia ta nake.”

Daria falon ya ‘dauka dashi, banda Nusrah da Saifullahi wanda gaba d’aya kowanne da abunda
zuciar sa take sakayo masa,

“Toh ki cewa zuciar taki, ta baki nutsuwa tayi hak’uri, mu ‘karasa, sai ku cigaba da ganawa idan
muka gama ko?”

Cewar Dr Khaleel don akwai shi da barakwanci, dukkansu ma haka suke har Ya Bala. Kada kai
Shema’u tayi tana kukan zuci. Ciki harda tsinewa Alhaji Tulu da takeyi.

Gyaren murya Ya Bala yayi, duban su yake dukka ahalin nasu. Yasan Kowanne da abunda
zuciar sa ke ayyana masa, ‘dan sosa hanci yayi yana kurbar ruwa, yafara da basmala kafin
yace,

“Sai abu na biyu, wanda ni da mahaifiyar mu da ‘yan uwana muka yanke, wanda duk duniya
indai ba Allah ne yayi hakan baxai faru ba, to babu mahalukin daya isa ya sa a fasa wallahi, da
farko dai. Kai Mudasser da Mu’utaseer su waye kukace kunaso anema muku auren su?”

Suka kalli juna, cike da kunya Mudasser yace,

“Baba ni wata ‘kanwar wadda muke aiki a company din kace, wannan staff din naka y’ar nijar?
To kanwar ta nake nema ‘Rama’ tana can nijar, amma idan tazo hutu muna hadu wa,”

Kad’a kai Ya Bala yayi, alamun ya gamsu, Mu’utaseer yace,

“Baba ni kuma, ‘kawar su Marwa ce, wata yarinya ‘Miss Hafsy’ tana karantar agriculture”

“Madallah..Duk za’a nemo muku auren su da yardar Allah, amma sai na fara bincike, a yau
‘dinnan ba sai wani lokacin ba.”

“Mungode Baba” suka hada baki suna fadar haka.

Ruwa Ya Bala ya sake kwankwada, yana duban Kamaludden, da cikin sa ya hautsine ganin irin
kallon da Baban ke masa. Gyaran murya ya sakeyi yana nuna Kamaludden da yatsa,

“Kai kuma kamalu, ga ‘kanwar ka nan na hadaku aure da ita, daga yau ku fara fuskantar juna”

Duk yan matan parlorn sukai tsuru-tsuru, musanman su Hidaya. Murya na rawa Kamaluddeen
yake cewa,

“Ba..Baba wa kake nufi wai?”

“Wa kuwa? bayan kai da Aysha gata nan kusa da kai,”

Sanyi Aysa taji aranta, amma bata nuna ba, Shema’u wani kuka ne taji ya taso mata, take, ta
dinga jero addu’oi harda tashiga bandaki.

“Shikenan Baba..Na karba Allah ya sa albarka” cewar Kamaludden, bawai dan yana son hakan
ba, kawai dai sai dan bin zab’in iyaye”

“Allah ya muku albarka..”

“Ameen”aisha tafada tana wani sussunne kai, da alama y’ar banzar ta fara kunyar Ya Bala,
wayaga uban miji hehe.

“Kai kuma Shamsudden” cewar Ya Bala, sai kuma ya tsaya yana saka wayar sa a silent ganin
irin ‘karar da masu kira suka ishesa.

A razane Shamsudden ya dago yana kallon Ya Bala, sai kuma ya mayar ‘kasa yana kukan zuci,
ganin da girman su ana sadakar dasu, a auren dole.

“Yawwa Shamsudden, Kai kuma na had’aka aure da Shema’u..”

Babu kunya Shema’u tayi sujjadar godia ga Allah, tana riko kafar Ya Bala, sumbatu take tayi,
da’di kasheta,

“Baba,Nagode! Allah ya saka da alkhairi.” Cewar Shema’u.

Daria aka kwashe da ita, Banda wanda aka had’a auren dole, su wa’enann kukan zuci suke.

“Shikenan Baba, Godia muke.”

Shamsudden ya fad’a ko ajikin sa, domin ya ‘kudiri niyyar anayin biki ba da jimawa ba, zai ‘kara
wani auren son ransa, tunda ita Shema’un zab’in iyayen sa ce.

“Ameen.Allah ya muku albarka.. Sai abu na ‘k’arshe, Nusrah!”

Dago kai tayi a razane tana kallon Ya Bala, ba ita kadai ba du yan parlorn kallon sa suke yi,
musanman Yafendo da ta gwalalo idanuwa tana jiran jin wanne hukunci za’a yanke akan tata
‘yar. Dakyar ta iya furta,

“Na’am Uncle B”

“Y’ar albarka kenan, Kiyi hak’uri da ‘kaddarar data faru akan ki, kan auran ki da Aliyu, Kuma ki
sani ba xamu tab’a miki zab’in da ba nagari ba, kamar yadda ‘yan uwanki kowannen su ya
yadda kada ki bamu kunya, bayan baki isa ko wani naki ya hana ba ma..”

Shiru yai yana duban yan parlorn, Sosai yake had’e ransa don yasan yanzu xa’a kwashi
ruguntsumi. A hankali Nusrah ta furta,

“Toh..Uncle B”

“Yawwa! kai saifullahi ,na had’a auren ka da Nusrah, sai ku fara fuskantar juna,”

A razane Saifullah ya d’aga kai yana kallon mahaifin sa, sosai ko a mafarki bai taba xaton haka
xata faru ba, yarinyar da ya tsana, ya rena ‘kirarta, wata sad’o’do da ita, domin shi mutum ne
mai muguwar sha’awa, kuma yafison dirarriyar mace, komai yaji ishasshe, Islam ce tafad’o
masa arai, yasan ba sonta yake ba, amma tabbas yana sha’awar yarinyar, ko’ina cikakke ne a
jikin ta, komai nata yayi mai. Ya juya yana kallon Islam, kansa ya sauka akan ‘kirjin ta da yake
mugun tafiya dashi. Dakyar ya iya janye kansa yana saukar dashi ‘kasa.

“Ko bakuji bane,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login