Showing 3001 words to 6000 words out of 86718 words

Chapter 2 - SAIFUL-ISLAM Book Complete by miss xoxo (2).pdf

06 Jul 2025

2071

masu sharri, ya Allah kasau keni lapia da ni da duk wanda haihuwa tazo wa,
ya Allah kafini sanin abunda yasa ka azurtani da wannan babban arziki, rabbi kasa...”

Bata k’arasa ba sakamakon wani azababban ciwo daya taso tun daga tafin k’afarta xuwa marar

ta, dakyar tasamu ta sakko daga kan kujera tana k’ok’arin danna intercom dake kan center
table, dakyar ta danna cikin wahalalliyar murya take cewa,

“Falmata..”

Falmata mai aiki dake can sama tana mopping parlorn sama tajiyo muryar Haj Aysaa, dake
tunda haihuwar tazo kusa Haj Aysa tadawo dakin kasa taxama tana jiran Allah ya sauketa
Lapia, da sauri Falmata ta saki moo tasheka k’asa a guje don dajin muryar Hajian kasan ba
lapia ba,
Temakawa Hajia Aysan tayi tasaka hijabi suka k’arasa wajen mota a waje, driver ya bude hajian
ta xauna kafin Falmata takara shekawa a waje ta dakko akwatin kayan fa suka tanada na baby
unisex (wanda xa’a iya sawa mace ko namiji) suka siya dan hajian taki yara tayi scanning, a
cewar ta wannan Duk harkar yarinta ce, ita data manyanta tacire ran haihuwa tuni kuma saiga
Allah yayi ikonsa, Allah kenan qadirun ala manyasha’u,

Ta window Haj Karimatu taga fitar su, dogon tsaki taja kafin takoma kan doguwar kujerar datake
xaune tun farko ta xauna,

“Allah ya raka taki gona, ya kara miki yan hudu mata akan ukun dakike dasu, domin aikin
Malam na dotsa kamar yankan wuka yake kuma ya tabbatar mun hakanne xai faru, mu zuba
mu gani, la’ananniya” duk maganganun nan Haj Karimatu ita kadai takeyin su babu kowa a
parlorn, tamkar dai sabuwar tab’i, tanayi tana k’ok’arin neman wata number a waya da alama
kira xatai.

Zanklin asibiti sukaje dake nan kusa dasu ba awani dau lokaci ba aka shiga da Haj Aysa
maternity room, sunyi sunyi akira mijin agaya masa don qa’idar sa ce tunda regular patients
dinsu ne Ha Aysaa taki, kan lallai yana can senate board meeting na d’aya daga cikin university
din da yake lecturing.
Cikin hukuncin Ubangiji domin shidin mabuwayine gagara misali ya sauki Haj Aysaa lapia,

“In yaaa” shine kukan jarirai har biyu yan maza zankad’a zankad’a sukeyi, dayan na tsotson
hannun sa dayan kuma na mimmike jikin sa, hakan ya yi nuni da lapiyayyu ne , kallo d’aya
xakai musu ka sake maida kallon ka kansu domin healthy babies ne kuma kyawawa, sai dai
muce TubarkAllah kawai,
Tuni bacci yai awun gaba da Haj Aysaa yaran sai tsala Kuka sukeyi, babu shiri dr James ya kira
lambar dr khaleel bugu biyu ya daga bakinsa dauke da sallama kafin yace,

“Yes dr James..”

“Sir! Congratulations”

Dr Khaleel yana zaune a meeting ya mike yana,

“Congratulations?! I beg your pardon”

“Oh sir! I mean your wife safa’s mom..”

Be karasa ba dr Khaleel ya katse kiran a kidime ya fice daga board meeting ko takan sauran
board members be saurara ba dake dakatar dashi,

A 330 ya karasa asibitin, da Falmata ya fara cin karo tana ta murmushi, tana magana cikin
harshen kanuri da alama Allah takewa godia,

“Álà bárgà càkkó,Álà bárgà,Álà kámbò”

“Alaji hajia ta sauka lapia,”

“Alhamdulillah ya Allah,Tana cikin dak..”

Shiru yai sakamakon nurses biyu da suka nufo shi da babies a hannun su mika masa su sukai,

Kasa magana yayi sai kallon ikon Allah daya tsaya yana kallo, saurin sujjada yai tagodia izuwa
rabbis samawati mamallakin komai daya azurtashi da wannan babban rabo daya jima da
hakurin haka a zuciyar shi,

Dagowa yai daga sujjadar ya karbi yaron be wani dau lokaci ba yayi musu kuthba, ya kira sallah
a kunnuwan su tareda tauna dabino yai addua yai drop kadan a bakin su, a take ya sanya musu
suna,

“Allah ka raya mana Abubkhar (sunan mahaifin Hajia Aysa ‘Alhaji Bukar Goni’) da kuma sunan
mahaifin sa marigayi Malam Muhammad Tasi’u”

Dakin da Haj Aysaa ke bedrest ya shiga tana kwance tana bacci, numfashin ta yana futa a
hankali da alama tasha wahala domin an dade ba ‘a haduba..

Gefan ta ya zauna yana gyara mata dankwalinta cikin murya cikeda farin ciki yake shafa
fuskarta yana fadin,

“Allah ya miki albarka Aysa, kinbiyani kin cikamin burina duk abunda kike bukata a duniyar nan
kigayamin komai tsadar sa xan cika miki burinki ko menene ko mai tsadar sa”

Mutumin naku dai sai surutan sa yake ,Falmata dake waje dadi kashe ta yau Hajian su tacikawa
oga burin sa,

Cikin lokaci kankani ya kira yan uwa da abokan arziki ya gaya musu wannan daddadan labari,
kafin minti 30 asibiti fa yafara cika da yan uwa da abokan arziki,amma duk abunnan babu keyar
Haj Karimatu da Haj Yafendo, Helwa ce kawai taje amaryar, da kuloli shake da abinci,

Tuni Haj Aysa ta tashi daga bacci don masu xuwa barka sun hanata yin baccin, dr Khaleel
kuma yak’i barin a karbi yaran minti kadan da an dauke su xaisa a miko masa su, yanzu ma Haj
batul matar kawu Ndume kawun Haj Aysaa ce ta karbi Abubkhar tana gyara masa diaper, dr
Khaleel yace Falmata ta karboshi babu ko kunya bare kawaicin sirikace fa inda kara,
Ai kuwa ta hana da ike itama y’ar neman rigima ce,

“Ni fa nayi sabon ango dakta, daga yau har mu bar asibitin nan”

Daria yayi yana shafa k’eya ganin ta gano shi, dakyar dai da kuma yadda aka yanyame dakin
yasashi ficewa bayan ya jaddadawa Falmata kan lallai,
‘Ta goya d’aya ta bawa iya Amuna (dayar mai aikin su) dayan su goya su.

Ita dai Haj Aysa murmushi kawai take, Ashe abunda Allah zai azurtata dasu Kenan?Lallai da
tayi babban kuskuren lokacin datai wautar zubar da cikin. Mama tabasu suka sha suka koshi
bayan sunyi video call dasu safa, likita ya kara mata allura kafin zuwa washe gari su tattara su
tafi, don sosai likitan karakainan surutun masu zuwa barka sun isheshi, shiyasa ya rubuta musu
discharge leave kan da safe su ware gidah kawai ta karasa bedrest din acan.

Zagaye parlorn tashiga yi, zaninta a dage, gashinta duk awaje se surutai take kamar sabuwar
tabi,

“Ina..Baxai yiwuba walahi, makirci ne walahi..”

Yafendo ce takaraso parlorn Karimatun tana sallallami kafin tasamu waje ta zauna ta zabga
uban tagumi,

“Malam na dotsa ya tabbatar mun da taurarin jarirai biyu yagani mata, anya ba musanye
tsinanniyar nan tayi ba” cewar Karimatu cikin kidemewa

“Hmm yaya walahi nima sakawa nake Ina warewa, domin ni kaina falalu na kan tudu haka ya
buga kasa ya fadamin, ai Kadan daga makircin su nifa yaya gani nake yi xuwa tai a ka cire
wa’incan aka saka mata maza biyu”

“Allah ko?!” Cewar Karimatu cikeda gasgata abunda Yafendon tafada,

“Yo abune da yaxama ruwan dare, zuwa kake a sa maka yaya, ke kinji muryar Alhaji kuwa daya
kirani yana sanarmin ta waya walahi yadda kikasan ansashi cikin aljanna”

“Bar can d’aya gaula sallamamme, yanacan yana rawar duwawu uwargidah ta sauke masa
abunda yake muradi..” Karimatu takarasa tana Jan tsaki a karo na ba’adadi

“Hmm walahi kam, ana haihuwar dan yan mintuna shegiyar can (Helwa amaryar) tafice zuwa
asibitin waya sanima ko bakin su d’aya”

Ashar Karimatu ta lailayo ta dura shi tareda sauke kwandon tsinentaka akan sunan Haj Aysa da
Helwa,cikeda huci take cewa,

“Bar dangin asiri ai tsatson su d’aya Allah wani lokacin ma ni gani nake da saninta Alhaji ya
auro ta, gaba d’aya saikace itace ta haifeta sai wani binta take tana mata biyayya”

“Ni bama wannan ba, yanzu yaya Meye abun yi?!”

“Rabasu da iska shine babban buri na Yafendo” Karimatu ta karasa ko gezau babu a furucin ta,

Gwalalo idanuwa Yafendo tayi cikin kidimewa take,

“Yaya kisa, kisa fa kikace?! Tukunna ma wa kikeson kashewa Aysan ko helwan”

“Ana maganar serious kina sako wasa da kashe su Xanyi tuni Van aiwatar da kudurina ba.Da
yan biyun da aka haifa nake, natsanesu walahi,Baxan iya hakura Ina numfashi a gidan nan da
gilmawar yaran nan ba”

“Tab yaya kenan, Ai kwa wannan abune da baxai taba yiwuwa ba Kema I san yanzu yaran nan
ko quda Alhaji ba zai so yataba su ba”

“Yafendo kenan. Wani lokacin kikan manta da irin hatsabibab cina,to kizuba ido ki kallo”

“Toh yaya Allah ya baki iko” Yafendo ta karasa murya a raunane,

Tafada duniyar tunanin har ga Allah batasan abunda Karimatu xatai silar barinta daga gidan nan
domin igiyar auren ta saura biyu karimatun kuma saura d’aya, kuma Karimatun ce tajanyo
abunda aka sausu.. Fisabilillahi tasaba da jar miya anan ina xata iya rayuwar rugar su, baxata
mantaba lokacin da aurenta ya mutu na saki d’ayan da girman ta baffah Ardo xaisa ta tatso
nonon shanu,kuma kullum abincin su furace sai dan abunda ba rasaba na fulanin jaubawa,
gaskia baxata sabuba, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin tace,

“Yaya ki sake shawara gaskia..”


******

*B* *N* *A*

Islam ta wanke undies dinta tana shanyawa, Hidaya dake ta saman hostel dinsu ta hangota
bata bata lokaci ba ta zunguri bucket dinta dake cikeda underwear’s ta sauke kasa wajen famfo,
don ana musu wanki kayan ciki (underwear’s) kawai suke wankewa,

Saida gaban Islam ya fadi ganin Hidaya , mugun murmushi Hidaya tayi kafin ta muka mata
bucket din hannun ta, hannu Islam din tasa ta karba, cikeda nuna isa Hidaya ke cewa,

“Ki wanke su ki goge mun kayana kafin karfe 9 saboda xanyi bacc...”

Bata karasa ba Hafsat Rano kawar Islam ta karaso da gudu tana haki,

“Lam Lam guess what?”

“HR! Munci biology test duka?”

“Wrong ..yanzu Mrs Daniel tace agaya miki maman ku ta haihu yan maxa”

Ai Islam bata karasa jin HR ba tabar wajen da gudu HR na biye da ita, ai Hidaya ma bata tsaya
ba ta wuce wajen Hafsat dake zaune itada Hilaal (yaran da ake yayi a sch din)suna hira
hannunsu sarqe dana juna,

Bata rai Hidaya tayi don itama fa tana son Hilal dinnan gashi dan ajin su nema amma saboda
tsabar yadda take shakkaar Hafsat ko kadan bata nunawa sai dai Idan Hafsat din bata wajen,
shi kuma yafison Hafsat saboda takoya masa taba jikin ta.

Murya cikeda haushin ganin su tare tace,

“Maman Islam ta haihu yau, maza”

“Kutmar ubancan, Karya kikeyi” cewar Hafsat da lokaci d’aya ta burkice idanunta sun rufe sak
dai irin halayyar Haj Karimatu..





*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO*
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...*

*NA*


*©NANA HAFSAAT*
*(MISS XOXO)*


*®HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*SHAFI NA UKU (3)*


*B N A*..


Elizabeth Arden’s hostel...

*Z*aune Islam ta ke, hannun ta rik’e da littafin chimamanda mai suna ‘purple hibiscus’,
kasancewar dare ne tuni yawan cin ‘yan dakin sunyi bacci, da yake kowan ne d'aki mutum shida
ne ciki. Da Ita kanta a cikin d'akin sai Lee da Hafsat da suke uba d’aya, sai Hafsat Rano da
suke kira da HR, sai kuma Fatma bichi da suke kiranta Zarah, sai Iffy kawar Hafsat kanwar
Islam sune a d’akin su 6, gabas da yamma kudu da arewa na dakin ko Ina gado biyu ne inda
yayi making 6 bed kenan.

Had'add'an d'aki ne kai kace gida ne idan ka shiga, harda d'an parlorn su da tv a ciki, can gefe
kuma study ne da bookshelves ajiki, kowa gadon sa da kalar sa, da mini cooler fridge kowan ne
da nasa, ga kuma yalwataccen band'aki wanda yaji komai abun dai sai sam barka kawai, Domin
makaranta ce mai karshen kyau, kuma ta amsa sunan ta don kwarai matuka suna samun
karatu, kama daga na boko zuwa arabi ciki harda k’arin karantar harshen faransan ci (French).

Kasancewar shi harshe na biyu da ake ji dashi a duniya bayan English saboda mahimman cin
sa a duniya ko a international court of crimes na duniya daga French sai English kawai ake yi.
Wannan kenan.

Haleema Sameer Ameer ‘kawar Islam itace ta fito daga band'aki, da alama wanka tayi dan
gashi nan tana tsane kanta da karamin towel kafin ta d'akko dryer tana drying gashin kanta,
duban Islam take da gaba d’aya hankalin ta na kan littafin da take karantawa, da alama ma ba
ta san Haleeman ta shiga band'aki ba balle kuma fitowar ta.
“Aikin dai kenan” cewar Haleema ta ajiye dryer tana k’ok’arin daure gashin ta da ribbon..

“bae boo”cewar Islam tana k’ok’arin cigaba da karasa karatun ta,

“Wallahi baki isa ba”Lee ta fad'a tana wafce littafin daga hannun Islam,

“Ki dinga hutawa dan Allah, Shi kenan ke bakida aiki sai karatu ne?ko gajia bakya yi, beside ke
fa ba Art student bace for heaven sake..”

“And so, reading is one of my fave hobby yarinya” Cewar Islam had'e da rolling idanuwanta cike
da tsoka na,ta mika hannunta ta kwace littafin ta, hade da saurin mikewa tabar wajen Lee.

“Zaki dena ne..Ni bama wannan ba bari na dakko physics ki kara sa coaching dina”

Kad’a kai Islam tayi, ita kuma Lee ta tashi ta shiga study wajen karatun su inda books d'insu
yake..

Tashin ta keda wuya Hafsat ta shigo d'akin tana wake-waken ta, sosai gaban Islam ya shiga
fad'uwa don batasan yau kuma da wanne kalar rashin mutunci Hafsat din zatai mata ba.

Bata karasa tunanin da take ba, Hafsa ta dire mata plate akan littafin ta, har cheese na
fallatsuwa a idanun Islam, da sauri Islam tasa bayan hannunta tana goge idanun ta, gashi tana
da ciwon idanu lokaci d’aya ya karade ya zama ja..

Kwan chewing gum Hafsat ta saki guda uku lokaci d’aya ji kake k’as-k’as-k’as kamar tsohuwar
karuwa. Hannu d’aya kuma tana danna waya, gashi an hana amfani da waya a sch din. Idan
aka gani ma seizing ake yi, amma Hafsat da Hidaya asace suka zo da tasu, bayan ko agidah
ma Dr khaleel bai basu daman rike wayar ba. yace kowannen su sai ya gama secondary school
zai rike waya,

“Reheat that for me..”cewar Hafsat ga kuma harara tana makawa Islam din,

Islam bata ce komai ba ta ajiye littafin ta a gefe, ta mike da plate d'in a hannunta cheese burger
ce akai, tafiyar daba tayi taku goma ba ta isa ga microwave d'in su dake gefen tv stand, tana
k’ok’arin saka plate d'in aciki Lee ta fito daga study room.

Tsayawa tayi tana duban Hafsat, kafin ta maida kanta ga Islam dake danna minutes ajikin
microwave, ganin idanunta sunyi ja ya sanya Lee tsarguwar ko dukan ta Hafsat tayi? Domin
hakan tasha faruwa in bata wajen sai tana nan nema Hafsat din ke sarara mata, Da sauri ta
karasa wajen Islam tana tambayar ta.
“Dukan ki tayi ne?!”

Girgiza kai Islam tayi alamun a’a, tana murmushin karfin hali, Zafi burger din yayi Islam taciro
tana mikawa Hafsat.

“Water..”cewar Hafsat dake sake gyara xaman ta akan gadon Islam din tayi male-male akai,

“What the fuck..Mehn cut this shit up, dan tsabar rainin hankali itace xata miko miki ruwan
bayan ga ki ga mini cooler din a kusa dake?”

“Don’t let me repeat my self..”cewar Hafsat tana wa Islam kallon tara saura kwata, kallo d’aya
xakai wa Islam kasan tana cikin tashin hankali.

“Ba xata dakko ba”Lee tabata amsa tana k’ok’arin dakatar da Islam daga d'akko ruwan,

“Bari Lee, Kiyi hak’uri ki bari na d’akko mata.” Da sauri ta karasa ta dakko ruwan tana mikawa
Hafsat.

‘'Bud’e shi..” Hafsat ta sake bata order. Karba Islam tayi ta bud'e ta mik’a mata,

“Banza loser, bumbling idiot kawai, tana kanwar ki tana baki order.”

Lee nagama fad'a ta koma study room cike da haushin Islam. Sum-sum Islam ta fice parlor
bayan ta dau littafin ta,

Dariar mugunta Hafsat ta shiga yi sai da tayi mai isarta sannan ta mike ta shiga bathroom,
wanka tayi tasa pajamas dinta ta kwanta akan gadon ta,

Ko takan plate d'in dataci burger din batai ba gashi kaca-kaca tayi da sashen Islam din, ta zubar
da burger da gani da gangan tayi, kafa d’aya Kan d’aya take chatting da wayar ta hankalinta
kwance, guntun message ta turawa Hidaya(wadda suke uba d’aya),

“Just made the loser shed tears again, turn dnki ne yanxu sissy..”

Bata wani jima ba bacci ya dauke ta bayan ta boye wayarta a maboya. Sai past 12 Lee tafito
daga study tana hamma sosai bacci take ji, batabi takan Islam ba dan har yanzu haushin ta
takeji ta karkad'e kan gadonta ta kwanta bayan tayi addu'a.

Sai alokacin Islam ta dawo dakin ta ajiye littafin a bookshelves ta shiga band'aki tayo alwala, sai
da tayi sallar nafila, sannan ta koma ta gyara kan gadonta, ta kunna turaren wuta a burner,
komai ya kintsu sannan ta koma kusada Lee tana dan bubbuga bayanta a hankali cikin sautin
rarrashi tafara mata magana ,
“I’m so so so sorry best fren”

Buge hannun Islam Lee tayi tana Kara matsawa can gefe,

“Leave me alone, yeye fowl”

“Habba mana dan Allah..The one who forgives owns the biggest heart. kiyi hak’uri pls”

Shiru Lee tayi tana kumburo baki ita adole tayi fushi da yawa,

“Oh plss babes..”

“Fine joor,na hakura”

“Yay that’s my better half” Ta fad'a had'e da hugging Lee.

Milkshake Islam ta hada musu suna sha suna suna ci da cookies, tuni baccin yai kaura daga
idanuwan su, basu kwanta ba saida suka yi tutorials na physics da xasuyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login