Showing 39001 words to 42000 words out of 86718 words

Chapter 14 - SAIFUL-ISLAM Book Complete by miss xoxo (2).pdf

06 Jul 2025

2095

ajiye shi a zuciarta sai dai ta
daure tace,

“Ni wai Yayya Islam har yanzu shiru? Ba wani a k'asa ne?”

Haj Aysa dake gefe ta sauke nannauyar ajiyar zucia kawai bata ce komai ba. Yakolo ce ta
dank'arawa Yaburra harara kafin tace.

“Sai akai yaya? Wai ke bakisan aure lokaci bane? Ko kuwa duk dangin mu da sun tasa aure
suke yi? Haba mana, ni fa bana son k'ananan maganganu da gutsiri tsoma, sai inci...”

Hanzarin katseta Yaburra tayi da sauri tace.

“Kai! Wallahi ni ba da wani abu na fad’i haka ba, kawai dai naga ina ‘yar ya Fanna ta Askira? To
itama kusan hakan ne issue d'in, sai da abu yai tsamari aka gane wai ashe jinnul-Ashiq ne.”

Dogon tsaki Yakolo taja tana maida d'ankwalinta kanta, kyakkyawar harara ta k'ara bankawa
Yaburra kafin tace,

“Duk naji, Toh kina nufin kice Islam aljanine a jikin ta ko me?”

Girgiza kai Yaburra tayi, tana k’ok’arin wayarwa Yakolo kai, wadda sam tak’i yadda, ganin
hayaniyar tasu na neman caza mata kai ya sanya Haj Aysa dakatar dasu cikin sanyi tace,

“Ku bar zancen dan Allah! Allah ne kad’ai masanin gaibu, ke kuma Yaburra tunda kin kawo
suggestion ki kirawoshi ya mata tambayoyi idan sune Allah ya mata maganin su, idan kuma
basu bane Allah ya gaggauta kawo mata mafita ita da duk masu matsala irin tata.”

“Ameeeen!”

Suka amsa gaba d’aya. Bugu biyu kuwa Ustaz Aliyu ya d'aga wayar, zaiyane masa komai
Yaburra tayi cikin harshen kanuri, ya shaida mata gashi nan Insha Allah bada jimawa ba don
dama basu dad’e da dawowa daga tafiya ba shida amaryar sa Jiddah. Ba’a d'au lokaci ba kuwa
sai gashi duk sun gaggaysa dashi kafin a kira Islam dake sama tana bacci, sai data watsa ruwa
kafin ta sakko sanye cikin hijabi. Gaishe shi tayi ya amsa cike da fara’a, ya d'anyi naxarin ta na
d'an wasu lokuta kafin yayi addu’a yafara magana cikin sanyayyar muryar sa.

“Idan aka ce Jinnul Ashiq, ana nufin Aljanin da ke zuwa da daddare yana saduwa da matan
mutane, ana kuma samun Aljana mai zuwa da dadddare ta dinga saduwa da namiji. Akwai
kuma Ashiq dake bibiyar ‘yan mata ta hanyar ture (sihiri) ko kuma sun yi wasarere ya shiga jikin

su. Su irin wadannan Aljanu suna aurar mace ne ta yadda za su dinga kwanciya da ita a duk
lokacin da suka ga dama suna kuma k’ok’arin hana ta aure, in kuma tana da auren sai su dinga
k’ok’arin kashe mata shi. Su na kuma k’ok’arin hana mace samun ciki ko kuma in ta samu cikin
sai su zubar mata da shi. Sukan ma biyo yaron da matar ta haifa ya zamo tun daga haifar sa za
a ga alamun jinnu a tare da shi. Irin wannan nau’in Aljani shi muke kira...JINNUL ASHIQ ﻦﺟ
ﻖﺷﺎﻌﻟﺍ,

“Wani lokacin irin wannan Aljanu suna shiga jikin mace ko namiji ne idan an saka su, wato ta
hanyar Sihiri kenan. Wani lokaci kuma gamo ne, alamomin shafar aljana mace ta b'angaren
maza sune; rashin sha‘awar aure ko jima’i sam-sam, k'in mikewar gaba sanda kai nufin yin
jima‘i alhali kuma haka kawai ma yana tashi, k'in fitowar ruwa yayin jima‘i, domin Aljanin yana
iya zama a cikin marainan mutum, saurin gajiya yayin jima‘i da rashin iya komawa, jin motsi
kamar tafiyar wani abu a ga6o6in haihuwa yayin jima‘i, rashin cimma bukatar jima’i in ka yi nufin
yin jima‘i sai bacci ya d'aukeka, da ka yi niyyar yin jima‘i kawai sai ka ji ka kawo tun kafin ka
fara, komawar gaba da maraina su shige ciki, yawan ciwon kai, 6acin rai mara dalili,

“fad'uwar gaba da dai sauran su, haka kawai sai ka ji ka tsani matar ka, yawan mafarki kana
saduwa da wata matat, yawan samun matsaloli a duk inda ka je neman aure sai maganar ta
lalace, Za ka dinga mafarkin wata tana wasa da kai, Matsananciyar sha’awa da tsoron mata da
dai sauransu.,
_YADDA MACE ZATA GANE ALJANI YA AURETA_

“Yawan ciwon ciki mai tsanani da jin motsi a cikin, a duk lokacin da sukai nufin saduwa kawai sa
ta ga jini ya zo ma ta alhali ba lokacin al’adarta bane, jin zafi yayin jima‘i da rashin samun wata
fa‘ida, suna gama jima‘i sai maniyyin da mijinta ya zuba ma ta ya dinga dawowa ba zai shiga
mahaifar ta ba, matsanancin ciwon baya ko kwankwaso, kin yarda da jima‘i za ki dinga yawan
mafarkin wani na saduwa da ke, da siffar mijinki ko da wata siffa daban, yawan yin mafarkin kin
haihu wataran ma har da taron suna, ganin wani a mafarki ko a fili ya nutsa hannun sa a cikinki
ya fizgo wani abu,

“Musamman idan kina da ciki, yawan yin 6arin ciki ba tare da wani sanannen dalili ba. yawan
mafarkin ana bin ki a guje ko ana kokawa da ke, jin motsi a cikin ki, wani lokaci ma har yana
dad'a girma amma in likitoci suka auna za su ce ba su ga komai ba, rashin son yin magana da
kowa da jin haushin mutane haka kawai, tsanar mai gida haka kawai alhali za ki ji kina sha’awar
wasu mazan,

“Jin wari mara dad'i yana fito miki ko kaykayin gaba da kurajen gaba Idan budurwa ce, duk
wanda ya zo neman aurenta to in ya tafi ba zai dawo ba. Idan mutum ya dage yana so ya
aureta ita kuma sai ta ji ta tsaneshi, In ta fita unguwa zata dinga ganin alamun maza suna so
suyi mata magana amma sai su kasa, wasu za su dinga fad'ar cewa wance kwarjini take musu,
za ta dinga yawan zama a duhu da zama ita kadai da rashin son magana da mutane, Idan
yarinya tana zuwa makaranta za'a ga k'ok'arin ta yana raguwa kuma tana ramewa, yawan

ciwon kai da yin jiri, fad'uwar gaba, musamman idan Magriba ta kusa. Idan mace ta fara bacci
sai ta ji an zungureta ta farka. Da dai alamomi da yawa. Ya k'ark'are da cewa,

“Mafita shi ne ka ziyarci mai Rukiyya don ya d'ora ki akan tsarin maganin da ya dace da ke.
Kuma ki dinga zama da alwala da addu‘o‘in safiya da maraice. Idan kuma wannan matsala tayi
karfi, to dole sai an yiwa mutum rukiyyah, an nemi Aljanin an kona shi ko kuma a had'a
magungunan da za su kashe shi. Ko’a sami garin harmal, ad'ebi cikin karamin cokali d'aya
azuba a cikin ruwa babban kofi d'aya, sai a tofa ayoyin ruqiya ciki a dinga sha sau uku ayini.
sannan a had'a man zaitun, man habbatussauda, man hulba, man gelo, man tafarnuwa, man
na’ana'a, man Khisdil Hindi, Turaren za’afaran,

“Turaren miski, turaren wardi, Garin khaltit. Sai a had'a su duk awaje d’aya, a tofa ayoyin ruqya
aciki, ana shafawa sefe da kuma dab magriba. Insha Allah za’a dace”

Daganan ya shiga yiwa Islam tambayoyi ko zai gano alamun ko ta kamu da shafar jinnul Ashiq,
amma kemad’agas ko alamu babu. Ta amsa komai tiryan-tiryan babu matsala, hamdala yayi,
kafin yace ta samo biro ya babbata wasu addu’oi, Daganan yace ta koma sama abunta, ruwan
da aka ajiye agabansa yasha kafin yace.
“Toh hajia Alhamdulillah domin gaskia ‘yarku bata da matsalar Ashiq, kawai jinkiri ne da zai
zamto alkhairi Insha Allahu, tunda yadda na d'auka ma ashe ba hakan bane, domin yarinya ce
har yanzun, Insha Allahu zata samu abunda ake buk'ata da yardar Allah, kawai dai shine ta rike
addu’oi, azkhar na safiya da maraice dana kwanciya bacci. Kullum ta zamto cikin alwala, lalle
ne kuma ya zama wajib idan zatai bacci ta kwanta da alwala, ta kuma dinga yin addu’o'in dana
bata sannan ni zan mata wani tofi a ruwan zam-zam Allah yasa mu dace.”

“Ameen..” suka fad’a baki d’aya. Fuskar Haj Aysa fad’ad’e da murmushi.

Zungurar Yaburra Haj Aysa tayi da k'afa tana mata alamun nawa za’a bashi? Murmushi Yaburra
tayi kafin tace,

“Malam Aliyu, Toh mahaifiyar Islam d'ince ke tambayar nawa za’a bayar na lada dana zam-zam
d'in?”

Murmushi Aliyu yayi yana mikewa tsaye, hannunsa d'auke da ragowar ruwan sa, cikin muryar
sa mai dad’in sauraro yace,

“Haba Yaburra. Ladan addu'a fa kikace? Haba Allah ya kiyaye, ni dan Allah nayi batun zam-zam
kuma idan nagama yi zan aiko a kawo, fatanmu koma menenen ya warware cikin sauqi,
ballantana ma k'alau take, kada kusa komai a ranku wallahi lokaci ne kawai bai yi ba, Allah
yana sane da komai, ba kuma wai dan baya sonta ba, sam ba haka bane, wani lokacin ma
jarabawa ce daga gareshi ya gani shin zata iya cinyewa ko kuwa? Toh Allah ya bata ikon cinye
jarabawar ita da duk masu jinkiri irin nata”

“Ameen..” suka fad’a baki dayan su.

Har bakin k'ofa Yaburra ta rakashi kafin ta dawo ciki, Haj Aysa tai mata godia itada Yakolo. Nan
suka sake zaman hirar Aliyun da irin kirkin sa, har maganar matan sa ta shiga ciki, Yaburra
tace.

“Wallahi matan sa biyu, Maimuna itace uwargidan sai Jiddah ta biyun, amma naji ance yana
neman ta uku a kano.”

“Haba?” Cewar Yakolo da Haj Aysa.

Jinjina kai Yaburra tayi cikin gasgata abun da take fada tace,

“Haka naji, kai dagaske nema domin yace min da kansa yana neman ta uku a kano, wai kinji
sunan ta ‘Miss xoxo’ shine nickname d'inta, yace wai ta WhatsApp suka had’u a group d’insa na
ilimi-haske ne. Ya ma sunan ta na gaskiyar..? Yawwa Nana-Hafsatu.”‍♀

“Allah sarki, Allah ya basu zaman lapia, ya sanya alkhairi.”

“Ameen” cewar Yaburra.

Basu tashi daga wajen ba sai da suka gama list d'in komai na biki, da sati ya zagayo kuma a ka
raqashe bikin Yakolo, kamar wata ‘yar budurwa, rana d’aya akai wushe-wushe a farfajiyar gidan
su Helwa ne akan komai. Aka kai amarya nan gidan ta dake unguwar Asokoro.

*LAGOS*

Tunda Saifullah ya dawo, ya fara shirye-shryen tafiya bautar k'asa (NYSC), ya gama komai. Jira
kawai yake yaga inda za’a tura shi, ranar Monday da safe kuwa Mail ya shigo masa na
anturashi 3weeks camp a Abuja. Sam bai so haka ba, domin yaso kudu aka kaishi, aganin sa
wai zaifi samun life experience. Kwana biyu nayi ya d’aga zuwa Abuja bisa jagorancin Khaled,
wanda vissa d'insa zata fito nan bada jimawa ba. Camp ya shiga, yanayin yadda ‘yan mata ke
rushing d'insa ya sashi kasa zama, sannan shi mutum ne mai son tsafta, amma yanayin
band'akin camp d'in sam bayi masa ba, beside gurin ma gaba d’aya is too noisy acewar sa. Nan
yai ciku-cikun sa yai exeat from camp. Yakoma gidan su Khaled yana jiran fitowar ‘yan camp
d'in don ganin shin za’a canza masa gari(relocation) ko kuwa?.

Sanyayyar safiyar asabar ce ya fito da damuna, garin yai luf-luf dashi, Sam ba hayaniya
korayen bishiyu sunyi shar dasu ni’ima na busawa ta ko’ina. Da kyar ya fita daga gida domin
daily exercise d'in daya saba. Yana tafe yana d'an had’awa da gudu ya rufe kansa da hular
sanyi. Yanayin na matukar ratsashi sosai yake jin dad’in yadda yake motsa jikin nasa.

A lokacin ne kuma Islam tafito daga gida itama, don yin exercise, aganinta saboda yana da
kyau yana gyare jiki musamman kuma don ta rage yanayin jikinta dan sam bata san yadda
mutane ke bin jikinta da kallo, shi yasa a school kullum cikin hijabs/jilbabs ko Abaya take. Tafe
take tana tafiya tana had’awa da gudu. Riga da wando ne a jikinta kasancewar da sassafe ne
ba wanda ya fito tunda weekend ce, kuma d'ai-d'ai kune ke fita exercise din. Ba kowane zai
ganeta ba, amma ta yane kanta da mayafin abaya, kunnuwanta saqale da earpiece tana
sauraren karatun alqur’ani mai girma na k'ira’ar shureim. Medicated glasses d'inta kalar kayan
jikin ta, ta bayan gidan su ta fara zuwa gaban layin su.

K’ok’arin rage volume take yi lokacin data shawo kwanar gidan su Humaira, kanta a akan wayar
ta sam bata kallon gaban ta, hakama Saifullah dake tafiya da baya-baya, wai shi kwarewa cikin
rashin sani ji kake garau, goshin su ya had’u dana juna. Tuni wayar hannun ta, ta sulale tafad’i a
k'asa cikin azabar zafi Islam ta dafe goshin ta tana fad'in.
“Ouch! Ya Salam!”

Saifullah dake rik’e da nasa goshin yana mulmulawa ya sakar mata wata uwar harara, yana
fad'in,

“What the fuck... hey watch it.”

Dago dara-daran idanuwanta tai tana duban mai fad’ar haka, ya bigetan sannan ya fad’a mata
haka? Ba ko ban hak’uri. Dake blurred take ganin fuskar mai maganar sam batasan ya kalar sa
take ba. Girgiza kai kawai tayi ta duk’a k’asa tana d'aukar wayar ta. Ko takansa bata biba tai
wucewar ta gidah cike da haushin arrogant fellow d'in da suka had’u yanzu. Har ta wuce wa
ganinsa yana bin bayanta da harara tamkar tana ganin sa. Cikin shagwababbiyar muryarsa
yace,

“Annoying piece of shit...!”




_SAIFUL_ISLAM...!_
_perfect strangers_
_(Labarin tacacciyar soyayya marar gauraye..._)‍♀

_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_

[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_
_BILLYN ABDUL_


*_SHAFI NA 32-33_*

_SHAFIN YAU NA KU NE GROUP ‘DIN sis UMMI AISHA, NA *DUNIYAR MAKARANTA
GROUP*, FATAN ALKHAIRI AGARE KU, GODIA CIKIN KWANDO GA FIRDAUSI
ABUBAKHAR, DAMA ‘DAUKACIN MAKARANTA SAIFUL_ISLAM_

_nanahafsat.wordpress.com_


D'an k'aramin tsaki yaja, tare da harar hanyar da yaga tabi sannan ya juya shima ya tafi, yana
tafiya yana mulmula wajan da suka yi gwaran dan ba k'aramin zafi yaji ba shima. Kai tsaye
bedroom d'insa ya nufa ya cire kayan jikin sa, ya zamana daga shi sai boxer da bak'ar vest ya
nufi bathroom dan yin wanka, haka kawai yaji yana mamakin yarinyar, wato su mata idan suna
so suyi wani abun da kai duk ta hanyar da suka san zasu samu abin sai sunyi, yana kyauta ta
zaton wannan yarinya ta bigesa ne kawai dan ta tab'a jikinsa, kamar yadda yasan mata suna

sha'awar yi masa hakan dan dai baya basu fuska ne kawai.

A ‘bangaren Islam, kuwa da gudu ta shiga gida duk a tunanin ta zai biyo ta gashi unguwar babu
mutane kartaje ya danneta ya cuceta, tunda taga ita haka samari da magidanta suke yi mata,
wani kallo na a huta da ita, ba wai kallo na kauna ko soyayya ba bare akai ga yin aure.

Numfashi taja mai tsawo tare da furzar da iskar da ta shak'o tana k'ok'arin warware tufk'ar da
tayi ma gashinta, cilli tayi da ribbon d'in a kan gado sannan ta karasa ta d'akko towel ta d'aura
ta nufi wajan madubi ta na kallan fuskarta zuwa sassan jikinta da inda sukayi gware da
Saifullah, ta mulmula gurin yafi sau biyar kafin ta murgud'a baki tace a fili.
“Wallahi da ace inaji da rashin kunya babu abinda zai hanani yiwa mutumin can ita, dan iskanci
kana ganin mace na tafiya baka sani ba matar aure ce, ko budurwa ko kuma bazawara kawai
kazo ka bigeta dan salan iskanci, hmmm wallahi kaci sa'a da babu abinda zai hanani sharara
maka mari a duka kumatunka sakarai kawai.'”
Tayi maganar tana yatsina fuska tamkar da wani take yi a wajan, ta d'auki comb ta shiga toilet
ranta duk babu dad'i babban haushinta yadda boobs d'inta suka tab'a kirjinsa wannan abun yayi
mugun b'ata mata rai sabida gani take kamar ya sake rage mata farashi. (Wa yaga sakarai).

Hutun mid semester suka samu, a lokacin kuma saifullah ya gama sati ukun sa na camp, ya tafi
Lagos. Duk meyiwuwa yayi kan yakoma Lagos yayi one year service d’insa abu yakiyi, place of
primary assignment d’insa still Abuja ne. Nan SMEDAN branch dinsu na wuse. Lagos Islam tayi
tafiyar ta hutu, a lokacin Saifullah shima ya koma gida kafin ya dawo ya fara ppa d’insa.
Unguwa d’aya suke gida biyar ne tsakanin gidan Ya Bala dana su Saifullah. Su saifullah idiroko
12b, su Ya Bala kuma 17b.

*LAGOS IDIROKO*


Haka suka ci gaba da fita motsa jiki anan lagos ‘din. kullum shi Saifullah yana ganinta ko zai tafi
ko kuma ya dawo, yarasa wane irin naccacciya ce, acewar sa da ganin sa saboda shi tazo
lagos ‘din. sab'anin ita da tun ranar da abin nan ya faru tsakaninsu a Abuja bata sake had'uwa
dashi ba, sai wasu mazan daban wad'anda suke tare ta a hanya suna nuna mata wasu
banzayen d'abi'u amman bata basu dama, Saboda yanzu itama tsoro takeji kar wani ya lalata
mata rayuwa, daddyn su yayi mata aure da abokinsa kamar yadda aka yiwa su Hidayya da
Hafsat 'yan uwanta.

Yau dai kam tare suka fito exercise d'in wato Saifullah da Khaled, jere suke suna d'an yin gudu
kad'an-kad'an suna 'yar hira cikin tsantsar mamaki Khaled ya kalli can gefensa inda yake hango
wata kamar Islam wadda suke tare da Riri ,sai ture-ture suke yi duk sun takurawa kansu
wannan tana cewa ana tureta wannan na cewa Islam na takata dan kar su wuce junansu. Sake
murza idanunsa yayi tare da kad'a kai ya kalli Saifullah tare da cewa.

'”Waccan yarinyar kamar Islam.'”

'”Wacece islam?”

'”Gata can nasan ta a abuja 'yar gidan makocin muce.'”

Mtscew Saifullah yaja tsaki, jin abinda Khaled ya fad'a, wai 'yar makocinsu a can abuja amman
shine yake ta wannan fara'ar tamkar yaga wani abun daya shafesu. Kamar ance ya juya
Saifullah ya kalli inda Khaled ya nufa kawai sai yaga wannan yarinyar ce da ta bigesa, wane
tukukun bakin ciki ne ya tokare masa makogaro? Ya tab'e baki. tare da ci gaba da abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login