Showing 48001 words to 51000 words out of 86718 words
rannan na maka magana a WhatsApp, you shunned me!”
Khaled daya gaji da maganar ta yace,
“Ni? Anya.. ze iya yiwuwa na bude chats din amma ban karanta ba, I’m sorry”
“Issokay, yau zan ‘kara maka ai.”
Murmushi kawai yayi, Islam dake gefe ta danne dariar ta , sun ‘dan taba hira kafin su koma
gidah a ‘kara shan wata walimar. Saifullah kam cayai wa maman su Khaled shi baida lapia, dan
dazuma ita tayi forcing d’insa suka tafi.
Bayan kwanaki biyu aka fara maganar had'o kayan lefen khaled wanda murna ta gama cikawa,
yana son Fatima wadda ake cewa Dr Teema, wato wadda zai aure hakan yasa baya iya ganin
ko wace irin mace duk kyawunta duk dirinta yana ganin bekai na Fatiman sa ba.
Saifullah na gefe yana jin yadda suke shirya komai, amman ya kasa sanya musu baki ba
saboda a ganinsa ba huruminsa bane.
Sai da suka rubuta abubuwa da yawa kafin su ajiye da nufin idan an tuno da wani abun sai a
rubuta dan kar sai anje kasuwa a fara tunanin mai za'a siyo.
Maman su Saifullah aka bawai ragamar shirya kayan lefe, tunda ta fara take jin ina ma ace
harda yaronta saboda yanzu ba ta da burin da ya wuce ace Saifullah nada iyali, tayi nasihar tayi
fad'an amman kullum maganarsa shine bashi da wadda yake so har yanzu, duk kayan da ta
siyawa matar Khaled sai da ta sayi na matar Saifullah, Saboda tana so a had'a da nashi tunda
bashi da wadda yake so ita zata aura masa 'yar kawarta tunda ita yarinyar tana son shi.
Sai da ta gama had'a komai akwatuna arba'in ashirin na matar Saifullah ashirin na matar
khaled, koda aka kai kayan gidan su khaled sunyi murna domin komai yayi musu kyau, hatta
Islam sai da taje ta gano kayan tayi Allah ya sanya alkairi,Haj Aysa ma taje ta gano sunyi musu
murna sosai. Ana sauran kwanaki uku akai kayan khaled Maman su Saifullah tazo abuja domin
harda ita za'aje kano akai kayan auran wanda kowa yake jiran zuwan ranar bikin.
Zaune suke a cikin d'aki suna hirar duniya kowa yana fad'ar abinda yake damunsa Maman
Saifullah taja numfashi tare da kama kumatunta tace.
'”Ni yanzu damuwa tayi yawa, duk da cewar aure lokaci ne dashi amman ace Saifullah ko
zancen budurwa bayayi? Da naje had'a kayan lefen nan harda nashi nayo da nufin idan na
gama zan yiwa ‘kawata magana akan zamu had'a aure tsakanin 'yarta da d'a na, wallahi na
gaya muku sai da na gama komai na yi mata magana take shaida min ai yarinyar sickle ce da
ita, ban san lokacin da na fashe da kuka ba saboda tausayinta da kuma tausayin Saifullah
domin nasan idan ba yi masa auran aka yi ba, toh shi kam ba yi zai yi ba dan karankansa.”
'”Banda abinki menene na damuwa dan Allah? Auran Saifullah lokaci garesa, ita yarinyar itace
abar tausayi domin kafin a samu wanda zai aure ta za'a jima.”
Cewar mahaifiyar su khaled, haka dai suka ci gaba da tattaunawa har Umman su khaled take
cewa.
'”Ni kuwa da zaki gwada wata 'yar k'awata anan makotan mu take, wallahi yarinyar nan ita da
iyayenta suna da halin dattako har khaled na yiwa sha'awar yarinyar nan ya aure ta, toh kinsan
d'an yau ka haifesa hali kuma sai wanda aka zo maka dashi, wallahi k'ememe yace min shi
yana da wadda yake so, mai zai hana ki gwada Islam d'in kona rana d'aya ne kiga yadda take
da nutsuwa da kamun kai, watakila kiga sun dace da yaron namu.”
Cewar Haj Latifa tana murmushi yayin da Haj Zuwaira (mahaifiyar Saifullahi) ta gyara zama tare
da cewa,
“Uhmm kina ganin khaled ma yayi rejecting ina ga Saifullah mai tsattsauran ra'ayi? Kina ganin
zai so yarinyar ko kuwa kina ganin kawai nayi masa dole akan sai ya aure ta?' Haj Latifa ta
kad'a kai tare da cewa.
“A'ah Haj Zuwairah ba haka nake nufi ba, ina nufin zan kirata nan gida ki ganta idan yaso in tayi
miki sai ke kuma ki nunawa Saifullah ita kiji mai zai fad'a, mudai fatan mu Allah ya basu mataye
na gari masu kaunarsu da gaskiya”
“Toh shikenan hakan ma yayi, Allah yasa shi kuma idan nayi masa maganar ya amince.”
''Amin ya Allah.''
Haj Latifa ta kad'a tana sake gyara zama suka ci gaba da hirarsu.
Washe gari kuwa Haj Latifa tasa akaje aka kirawo mata Islam, tare da Areef suka taho ta
durk'usa har kasa ta gaida su tana murmushi tace.
'”Umma gani aka ce kina nema na?”
Cewar Islam tana gyarawa Areef zamansa akan cinyarta, Saboda duk tabi ta tsargu gani take
kamar kowa ita yake kallo, taji muryar Haj Latifa na cewa.
“Eh Islam cewa nayi a kiraki na tambayeki ko zakije kai kayan yayanku can kano saboda a
tanadar miki wajan zuwa.”
Nannauyar ajiyar zuciya Islam ta sauke jin ba wani laifi tayi ba, cikin sunkuyar da kai tana
murmushi tace.
“Lahh Umma wallahi naso zuwa amman yanzu babu hali sabida Ammi ba tada lafiya duk komai
yana kaina, ina musu fatan alkairi Allah ya kaisu lafiya ya dawo dasu lafiya Umma, idan lokacin
bikin yazo ayi damu.”
Ta k'arasa maganar tana dariyar ta mai burgewa, dama tunda ta shigo idanun Haj Zuwairah
yake kanta har zuwa yanzu da ta mik'e zata tafi tayi musu sallama suka bita da fatan alkairi.
“Toh Haj Zuwaira ya kika ga yarinyar? Kuma mahaifiyar ta ma y’ar Bornu ce, babarbariya ce”
Cewar Haj Latifa bayan Islam tabar gidan.
'”Gaskiya tayi hajiya ni kam ko Saifullah baya so toh ba zamu rasa yarinyar nan da shigowa
cikin family d'in muba.” Maganar suka bari da nufin idan Saifullah yazo zasu yi masa zancen
Islam d'in.
Sai da aka kai kaya aka dawo lokacin shima Saifullah yazo gidan a nan ne mahaifiyarsa tayi
masa zancen Islam, abu na farko da ya fara zuwa cikin ransa shine tazo tace asa shi ya aure
ta, ya rasa gane kan yarinyar akan son yin aure amman zai yi amfani da wannan damar wajan
auranta ya nuna mata cewar bawai kayi ta jarabar son yin aure ba shine a'a ka samu wanda
yake sonka yake tausaya maka yake jinka a can cikin ranka, sai da ta sake masa magana
sannan ya kauda kai gefe yace.
'”Allah ya nuna mana lokacin.” Haj Zuwaira tayi murmushin jin dad'i tare da cewa.
'”Amman fa mu san samu a had'a bikin da na khaleed kowa ma ya huta ko ya ka gani?” Sai da
ya yatsina fuska sannan yace,
'”Duk d'aya ne ayi hakan ma.'”
“Alhamdulillah Allah yayi maka albarka Saifullah yasa Abokiyar arzikinka ce, dama abinda nake
buri kenan naga lokacin da zan aurar da d'an auta na, gashi yanzu lokaci yayi ashe ma muna
tare da matar a kusa damu, wani abun dadin itama tanada jin bare-bari, kasan fa da a Al'adar
auren Kanuri ta samo asali ne tun daga lokacin da Kanurai suke karamar hukumar Kukawa ta
jihar Borno, a sannan a kan yi auren ne bisa umarnin iyaye wato kai tsaye iyaye ke yima
junansu kamun surukansu. Daga baya kuma da suka koma Dikwa sai kuma aka tsuri al'adar
cewa an daurawa yarinya igiya wato a wannan lokaci yarinyar takan san waye za ta aura shi ma
mujin zai san wadda zai aura. Amma bayan sun dawo Maiduguri sai abin ya sake daukar wani
salo na yadda yaro zai ce ya ga yar wane yana so kuma a shige gaba a nema masa auren,
Allah ya maka albarka auta, Ashe duk autoci ne, itama autar mata ce”
Duk aka yi dariya amman banda shi sai ma tashi da yayi yabar parlourn yana jin tsanar Islam,
tabbas zai shayar da ita ruwan mamaki domin sai ya koyar da ita illar zuwa neman wanda zai
aure ta da take yi, tsoransa d'aya karya aureta taga bata samun wasu abubuwan ta fito masa
da munanan halaye dan yaga alamar idan bata fara ba a yanzu da take, toh tabbas zata yi a
gidan sa, ai kuwa da taci kaniyarta domin kafin ya rabu da ita sai yayi mata shegen duka
sannan.
Da wannan tunanin yaci gaba da harkokinsa sam ba shi da labarin su Maman shi sunje gidan
Dr khaleel har sunyi maganar auran, kuma an bashi domin ta hanyar su Haj Latifa suka bi shi
yasa ba ai wani dogon lokaci ba aka basu Islam. Anyi sarte (sa ranar aure), anyi
tambaye-tambayen ‘sigga’ (yarjewa na anbada auren/ the act of asking and acceptance
between the family of the bride and groom and their witnesses)
Tuni har Yakolo sun fito da ankon dangashe da mandil (kayan wushe-wushe) na ankon Islam.
Ita kuwa Islam tun ranar da aka sanar mata da maganar Saifullah ne xai xamto mijin ta take
kuka, mai tsuma zuciar duk wanda ya saurara, sosai ta rame ta fad’a, Ganin haka yasanya Ya
Bala ‘dauketa ya kaita Lagos kafin ranar bikin suzo, acan ya kira ‘Madame Yerwa’ mai gyaren
jiki tun daga bornu tafara yi mata, duk abunda takeso yi mata yakeyi, domin har kano ya barta
taje bikin Hafsat Rano. Gaba d’aya Islam fushi take da kowa, ciki harda Lee da Humaira
,aganinta sune manyan munafukan da suka sanya xa’ai mata auren dole, auren dolen ma da
wanda bataso baya sonta, zaman doya da manja....
...,
Ni miss xoxo Nace wooo Balu tawan (billyn Abdul) Takusa xama ‘dakko riga, ta kusa xama
‘dakko wando, takusa xama tashi ki had’amin coffee... Ko ki gyara ko na sashi ya auro ta
biyu yasin don bazan auri shiekh Aliyu mai mata biyu ba, ke kuma SAIFU ke kadai ce
awajen sa, bayan ba sonki yake bakinyi mai yiwuwa kinsa an ‘ka’kaba masa ke, tawan ki ja
ajinki gaskia ko kiga aikin ahalin barebari
_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_
*_NA*_
_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_
® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_
*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_
*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_
_BILLYN ABDUL_
*_SHAFI NA 43-45_*
_nanahafsat.wordpress.com_
*KANO*
Tuni an sallamo Karimatu daga asibiti, domin kudin jinya ya ‘kare. ‘Yar wayarta tuni ta siyar da
ita, da wanda ‘yayanta suka tallafaa mata dasu duk sun ‘kare a magani. Kamar kullum a sheme
take kwance kamar shekararriyar saniyar dake jinya. Lokaci zuwa lokaci takan saki murmushin
takaici, da alama dai mutuniyar taku tuna baya take yi.
Wata waya ‘kirar nokia wadda akewa laqabi da rakani kashi ta ‘dakko a gefan inda take kwance,
tasha ‘dauri da kyauro, gefe da gefe kuma an nane da super glue. Can ‘k’arshen wajen chaji
kuwa an nannade da salatef (seal-tape). Duk screen ‘din ya faffashe kana hango cikin wayar,
madannan sun goge sai da biro aka zana kowacce lamba. Dakyar ta iya gano lambar Sidiya,
takira ta yafi sau goma kafin ta ‘dauka dakyar,
“Toh baxan ‘kara ba, sai kinzo.”
Shine kawai abunda Karimatu tace, ta ajiye wayar a gefe. Can wajen bayan minti talatin sai ga
Sidiya tana cika tana batsewa, kallo ‘d’aya taiwa ‘yan gidan ta ‘dauke kanta. Hajia dake gefe ta
tab’e baki kawai tana ci gaba da ‘kulla alala a leda. Kamar yaki Sidiya tashiga ‘dakin da
Karimatu take tana wani yatsina fuska, gashi ta tsaya ‘kerere akanta. Ganin ta yasanya
Karimatu ‘dan muskutawa ta gyara zaman ta dakyar.
“Ki zauna mana Sidiya.”
“Kai gaskia a’a, kin ji wani shegen zarni dake tashi a jikin ki kuwa, kuma fa nagaya miki kidena
kirana da yawa, fisabilillahi baban Gali(mijin ta) sai fad’a yakemin, nifa gaskia ba zaki kashemin
aure ba Karime”
Shiru kawai Karimatu tayi, tana sauraron masifar da Karimatu ke zazzaga mata, babu ma Yaya
da take kiranta a da, sai Karime gatsal. Tana cikin tunani, muryar Sidiya ta dawo da ita daga
duniyar tunanin data tafi.
“Wai me zan miki ne da tun asubahi kike dokawa waya ta kira?”
Cikin taushasshiyar murya Karimatu tace,
“Da..Da..Dama kudi zaki aramun asiyo min gurasa da...”
“Kutma.. Cab lalle ke dinnan ma, kiji da kudin lapiar ki ma a’a sai ta biyewa dad’in baki? To
wallahi bani dashi, ni idan kin samu ma ki biyani dari uku na ta shekaran jia, bazan iya da cin
bashin ki ba.”
“To ko zaki aiko mun da abincin da ki kai?”
Kyakkyawar harara Sidiya tayiwa Karimatu, kafin ta buga zani kawai, ta fice abinta, girgiza kai
Karimatu kawai ke yi, ganin yadda Sidiya ta juya mata a baya, ada itace gatanta, ta’dauke
‘dawainiyar ‘ya’yanta ma gaba ki d’aya. Tana cikin tuna baya, Alawiyya tashiga ‘dauke da kwano
sai ‘kamshin man ‘kuli ne ke tashi. Shinkafa ce da wake na gidan asabe mai abinci.
“Gashi inji Hajia..”
cewar Alawiyya, ta duk’a ta ajiye tafi ta. Cikin hanzari jiki na bari Karimatu ta bude kwanon
abincin, shinkafa da wake da yasha man ‘kuli da yajin tafarnuwa, sai yankakken tumatir da
albasa, ga maggi guda d’aya a gefe. Kamar mayunwacia haka Karimatu ta shiga ‘durawa
cikinta abincin, tana kad’a kai da alama yai mata dadi. Ashe Hajia duk taji yadda sukai da
Sidiya, uwa mai dad’i, ta ciri dari biyu cikin kudin alalar tabawa Alawiyya ta siyo mata abincin.
Ko kad’an ba tabada sigar da su Alawiyya xasu rena Karimen ba, dukkoda tarin abubuwan da
ta yiyyi musu. Tana gama ci ta koma ta kwanta da ‘d’ayan barin, domin ‘barin hagun ta baya aiki
sam. Shiysa takan sau fitsari wani lokacin a zaune idan robar fitsarin ta goce.
Gaba d’aya hakurin Khaled ya ‘kare, domin duk kawaicin da yake musu yaga basa ganewa, a
bashi matar sa an ‘ki, tun shekaran jia aka kawota amma ko fuskarta ‘kememe an haramta
masa ganin ta, zaune yake akan kujerar ‘dakin sa shida Saifullah dake sketching wani zane .
Sake sakin tsaki Khaled yayi a karo na ba adadi kafin ya turo baki gaba cikin tausayawa yace,
“Saboda tsabar an tsaneni ba, Wannan ai rashin adalci ne.”
Saifullah daya gaji da mitar Khaled ya mike yana tattara kayan sa zai bar masa ‘dakin, cikin
azama Khaled ya riko shi yana rausayar da kai,
“Dan Allah guy, kayi wa su Umma da Aunty magana su bani matata..”
Sakin baki Saifullah yayi yana duban sa, cikin tabe baki yace.
“Saboda mace kake mita awa da awanni dama?”
Kad’a kai Khaled yayi yana wani taune ‘kasan lips ‘dinsa,
“Ba zaka gane ba Guy, na shirya ne, a matse nake wallahi. Su bani ita mu tafi sunki wai sai
lokacin tafiyar yayi tukun na, sai kace ba mallaki na bace..”
Yakice hannunsa Saifullah yayi, yana goge wajen da handkerchief, Ganin haka yasanya Khaled
girgiza kai kawai yana murmushi,
“Toh ni meye nawa aciki?”
“So nake kayiwa Umma da Aunty magana su bani matata, hak’uri na ya ‘kare. Ita kanta nasan
a matse take.”
“Haka tace maka?” cewar Saifullah, Yana mai dubar agogon hannun sa.
“Lapiyayyar macece fa, wallahi itama nasan ta matsu, dan iska, kai saboda yau za’a kai maka
taka shiysa ai baka damu ba.”
“Wa?”
“Matar ka..Islam mana”
Tabe baki Saifullah yayi yana yatsina fuska, kamar an kira sunan kashi. Cikin nuna ko ajikin sa
yace.
“Kai mata suka dama..”
Mikewa tsaye Khaled yayi, yana wata y’ar iskar miqa, kafin yace.
“Tabbas mata sun dame ni wallahi, tunda ababen more rayuwa ne ku..”
Be karasa ba, Saboda wani dogon tsaki da Saifullah yayi.
“So suffocating...” ya fada yana barwa Khaled dakin gaba d’aya.
Saifullah na fita sukai kicib’is da Haj Latifa, da wasu baki dake shirin tafiya rakiyar amarya Islam.
Sosa ‘keya saifullah yayi, Haj Lateefa tayi murmushi kafin tace.
“Lalle Ango, shine kayi shigewar ka ‘daki kana ji su Gwaggo na tambayar ka, to kayi sauri dai
ka sauya kaya dan Allah..”
“Toh Aunty..”
shine kawai abunda Saifullah yace, yai gaba yana tura baki alamun shagwab’a. Dakin da yaga
mahaifiyar sa tashiga ‘daxu nan yayi, yayi sa’a kuwa ba kowa a dakin sai ita kadai tana shirya
wasu kaya a akwatuna, tana ganinsa ta fadada murmushin ta,
“Auta...”
Da sauri ya ‘karasa, yana dora kansa kan jikinta, shafa sumar sa ta shiga yi,
“Auta na..”
“First love..” ya furta cike da shagwaba.
“Auta, yanzu fa ka girma, gashi yau za’a kaika gidan ka fa. Kaga kayan amaryar ka ne nake
had’awa su Fatima su tafi dashi yanzu. Ra’aki ne da kususuram”
‘Daga kansa yayi yana duban akwatunan kalar hoda, guda hudu da Kit, shake da kaya harda
kwando cike da turaren wuta da khumrah. Cikin murya cike da tausayawa yace,
“First love ni dai gaskia tayi zaman ta a gidan su.”
Ware idanuwa Haj zuwairah tayi tana duban Saifullah, ‘kin yadda yayi su had’a ido. Murmushi
kawai tayi kafin tace.
“Saboda me zata zauna a gidan su? Bayan an daura aure, Duk adon mace ace tana gidan
mijin ta shine auta.”
“First love... Ni nufi na kowa acikin mu ya zauna a nasu gidan, If she needs anything...”
“Sai kace a garin gab’a-gab’a Auta? A’ina aka tab’a yin haka? Ayi aure miji da matar kuma
kowanne na gidan iyayen sa, anyi ba ayi ba kenan.”
Shiru yayi kaman zai yi kuka, Haj Zuwairah tacigaba da sha fa kansa tana bashi hak’uri,
“Kayi hak’uri Auta, haka dama rayuwar