Showing 63001 words to 66000 words out of 86718 words

Chapter 22 - SAIFUL-ISLAM Book Complete by miss xoxo (2).pdf

06 Jul 2025

2075

of a shoulder to lean on, kin samu miji da akai mai
auren dole, kin nemi alfarma kin samu, kuma daga antemaka miki shine zaki wani tsiri kukan
wofi... Stop crying abeg, grow up..”

Yana fada yai gaba yana nanata kalmar,

“So suffocating...”

Hawaye Islam ta goge na irin bakaken maganganun da Saifullah ya gasa mata, dakyar ta goge
labbanta tana furta kalmar ‘Allah ya sakamin’. Ta gyara jikin ta ta zuri kayanta tai gate, ba motar
sa, hakan yayi nuni da ya tafi kenan. Motar ta tashiga ta tasheta ta fita, ta dawo takulle gate din,
ta wuce school...
Ko a school dakyar Islam take concentrating akan abunda ake koyar wa, bayan fitar malamin
‘dietetics’, ‘Dr Saifullahi Bala Muhammad’ ya shiga. Wato Saifullahi cousin din Islam. Sosai
Islam tayi mamakin ganin sa, ashe dagaske Lee take, da tace xai fara koyar dasu, Ai kuwa
yadda ta tsammata hakanne domin sun sha tambayo yi, yau Islam duk batai concentrating ba,
shiysa daya basu open test batai wani abun arziki ba, Ai kuwa ana tashi daga lectures ta bi
bayan sa cikin sauri, Don ko kadan batasan ta samu matsala a harkar karatun ta, tanason ta
wuce komai successfully, Saboda withdrawing ake yi ko change of faculty’.

“Ya Saifu”

Cewar Islam, tana maganar ne, tana hadawa da sauri, domin kamo Saifullahi dake tafiya,
hannun sa rike da waya yana karata a kunnensa, da alama waya zai yi. Ja tayi, ta tsaya daga
bayan sa jiran yagama, Yana gama amsa wayar ya juya yana kallon ta, ‘dan rissina kai tayi,
kafin tace.

“Ina yini Ya Saifu?!”

“Ah Amarya..Ya mai gidan naki?”

Ware idanuwa tayi, jin abunda Saifullahi ya ambata, lalle aure yana kankaro maka mutuncin ka,
yana kuma ‘kara maka daraja da ‘kima a idanun mutanen da suka mai da ka ‘bawon albasa.
Cikin kunya ta sunkuya tana murmushi kawai. ‘Dan darawa Saifullahi yayi, kafin yace,

“Menene matsalar ne? Nasan ba zata wuce open test dinnan ba ko?”

Cikin azama Islam ta ‘daga kanta alamun Eh, murmushi yayi yana gyara tsayuwar sa kafin
yace.

“Kakki wani damu, attendance ce kawai zan mai da ita, nafison taking attendance sosai akan
tests, saboda attendance kowane ‘dalibi zaifi zama serious baya missing sch. Tests kuwa har
makeup anayi, and I don’t tolerate such shits kin sani ke ai.”

Daga kai Islam tayi tana murmushi, kyakkyawar wushiryar ta, ta bayyana, Shima Saifullahi
dariar yake yi, a dai-dai lokacin Saifullah mijin Islam ya shigo school ‘din karbar mukullin gidan,
Don ya manta bai dauki na gate ba, gashi tace xata jima a school yau, kalle-kallen inda zai
hango Islam yakeyi, kamar ance ya ‘daga idanun sa, ya hangota itada Saifullahi ‘dan uwanta,
gashi yasan fuskar sa gayen a wani waje, amma yakasa tunano a’ina ne.

Wani abu yaji ya tokare masa maqoshi, Lalle yarinyar nan batajin magana, juya kan mota yayi,
ya figeta kawai, ganin kusan minti biyar da tsayawar sa, bai ga sun dena hirar ba, a lokacin
kuma Saifullahi shi Islam ce ma take masa maganar Nusrah don takusa haihuwa yau ko gobe,
cikin ta ya tsufa, tana sake karbar number Nusran saboda batada ita yanzu. Da wannan
Saifullah yaja mota sai gidan su Khaled. Ran sa a matukar ‘bace, domin duk ‘daukar sa Islam
bata dena kule-kulen mazan da yake zargin tayi a baya ba. Nan ya tarar da Khaled suna shirin
tafiya Spain shida amaryar sa dr teemah, daga ‘k’arshe dai shiya kai su airport din, bisa
umarnin Haj Latifa, dan tsabar iskancin Khaled kuwa a baya suka hakimce shida matar sa, suka
kwantar da kujerun bayan. Duk abunda sukeyi Saifullah na jiyo su, minti kadan ya buga brake
yana na-nata,

“So suffocating..”

Yana sauke su a airport aka fara yayyafi, Khaled dake janye da akwatunan su yace da Saifullah
cikin murya ‘kasa ‘kasa,

“Aboki na yanayin nan yayi fa, shar da kai, ana ruwan nan, Allah yaso kanada mata, ta zama
lapiyayyan bargon ka nake gaya ma, acan-acan da kai wallahi, dama gashi nan fuskar ka ta
nuna alamar desi..”

Cikin sauri Saifullah ya katse shi yana matsar da fuskar Khaled daga kunnen sa,

“Abeg ja boxes dinka kuyi gaba pls, you are very annoying..”

Murmushi Khaled yayi yana jan hannun Nusrah, sai da sukai nisa kafin yace,

“Ka dai ajiye girman kan nan, kada kayi irin na mutumin ka NAUFAL(THE CHARMIN, littafi na),
wallahi Allah yasa Islam ta gasa ka, kamar yadda Ayush ta gasa the charming, and kakka soma
zuwa waje na neman favor.”

Tsaki Saifullah yayi, yana girgiza kai, ba karamin dadi yaji ba fa tafiyar Khaled. Domin ya
takurawa rayuwar sa, shi matar Khaled din cema ke bashi tausayi, Sam Khaled din baya sarara
mata, kullum yana ‘kwakwume da ita a ‘daki, Sam baya bari ta huta. Mota ya koma ya jata ya
nufi gidah, domin yasan duk yadda akai yanzu Islam tadawo, akwai wasu zanen hostels daya
keson ya ‘dauka, wani mutumi na neman contract a inda yake aikin PPA.

Islam kuwa tana shawo hanyar gidan ta, ta hango Saifullah akan mota yana danna wayar sa,
gabanta yai mugun fad’uwa hango fuskar sa, kwarai matuka yanayin sa ya sa ta tsorata, hango
motar ta yasanya shi dirowa daga kan motar sa, ya gyara parking yadda zata wuce, da kansa
ya bude gate din ta shiga ya rufe, ta zura mukulli ta bude kofar parlorn suka shiga atare, bakin
su dauke da sallama da adduar shiga gidah,

“Barka da dawowa”

Idan Saifullah ya amsa, bangon parlorn ya amsa, ko kallo bata isheshi ba, ya haura sama
abinsa yana tsaki.

“Ikon Allah.. Yau kuma da wannan salon ka dawo kenan”

cewar Islam, hade da tab’e baki. Dakin ta tashiga, tayo wanka, ta zura riga marar nauyi. Ta
kukkuna turaren wuta a ko’ina hade da karatun suratul baqrah’, a wata madedeciyar speaker
dake gefan corridor. Kitchen ta shiga, rasa abunda zata dafa tayi, cikin sauri ta ‘dau ra’ayin dafa
Italian spaghetti, cikin kankakin lokaci kuwa tagama, sunada cat fish tagasa shi, Tare da
hadadden iced tamarind juice.(Yunwa nake ji) Ta debi iya nata, ta jere sauran a dinning. Har
tagama zamanta Saifullah bai sakko ba. Daki takoma don yin assignment dinta, tana kuma
labartawa Lee amarya yadda lectures din ranar ta kasance don ita bata zuwa kwana biyu.

Da asubah ma da Islam ta fito, ta tarar da abinci yadda ta ajiye shi, ko kadan Saifullah bai ci ba,
anasa bangaren kuwa dakyar yai bacci, wannan kiss dayayi ya janyowa rayuwar sa alaqaiqai,
minti kadan ya tuno da yanayin labban Islam, shape dinsu da tastes dinsu, yayi salati yafi cikin
carbi, tsaki kuwa ko dangin tsaka sai haka, kalmar so suffocating kuwa daren ranar ko
dictionary albarka. Yai dana sanin aikata haka yafi sau dubu, har sallar nafila yayi, hade da

adduar Allah ya cire masa tunanin wannan sabon al’amari mai cike da almara. Gefe d’aya kuma
wata sabuwar tsanar ta ce ta sake dasuwa a zuciar sa akan Islam da Saifullahi daya hango
dazu. Dakyar ya iya tashi da safe ya shirya ya sauka ‘kasa don tafiya wajen ppa dinsa.

Nan ya tarar da Islam tsaye tana mopping dinning area, ko kallo bata ishe shi ba, ya sa kai zai
fice, da sauri ta bi bayan sa tana cewa,

“Barka da fitowa, An tashi lapia?”

Kallo d’aya yai mata, idanun sa suka sauka akan lips dinta da suka sha lip gloss sai glowing
sukeyi, ya dauke kansa yai ficewar sa, batare da ya amsa taba. Jiki a sanyaye Islam ta koma ta
zauna, hawaye suka shiga reto a kyakkywar fuskarta, Kamar da wasa ba sai Saifullah ya dau
mummunan fushi da Islam ba, ya dena kulata ko kad’an, duk yadda zatai ya amsa gaisuwar ta
yaki, ta tambayesa me tayi mishi nanma babu amsa, a satin ne kuma aka kawo musu mai gadi,
Saifullah ya tsiri dadewa a waje, dukkoda rabin hirar yanayin ta ne a gidan su Khaled.

Washe-gari, tun da safe Islam ta shirya ta kintsa ko’ina na gidan, cornflakes kawai tasha, dake
General holiday ne hakan yasanya, daga Islam har Saifullah babu inda kowannen su yaje, suna
gidah, shi yana sama ita tana ‘kasa. Sai wajajen sha biyu saura ya sauka ‘kasan yana kumbure
fuska, zai fita, Islam tayi saurin cimmashi tana,
“Dan Allah Ya Saif.. Kayi hak’uri Idan na yi maka wani abun unknowingly, wallahi bansani ba,
kaji?”

Shiru Saifullah yayi yana cizan ‘kasan lips dinsa, har ga Allah bayasan kallon fuskar ta,
idanuwan sa sauka akan mayen lips dinta da suka zautar dashi, kusan kullum da tunanin abun
yake kwana yake tashi,

“Kaji?...”

Ta ja jiiii din, tana k’ok’arin riko ‘kasan rigar sa, Don a tsugunne take, ya rufe idanuwan sa gum
don karya kalli labbanta, cikin sarkewar murya yace.

“Don’t you dare.. Sakar mun riga , with ur dirty hands. Gerrit off me or else..”

Cikin rawar jiki Islam ta cire tana hawaye, ita kuma tata qaddarar kenan? tana kallo ya fice yana
bugo mata kofa, yana fita ba ajima ba Lee tazo gidan, duk da Islam tayi k’ok’arin danne kukan
ta amma hakan yaci tura, tana bukatar shawara, Don haka Lee na tambayar ta meya faru? Ta
zayyane mata komi. Mamaki Lee tayi tana ware idanuwa, ganin irin zurfin cikin Islam, Wannan
ai ba abun da za’a barwa ciki bane ayi shiru,

Ashe duk zancen nan da suke Humaira na jin su, ta yiyyi sallama basuji ba kai yana kayuwa, ta
kad’a kai ta koma gidah ranta duk babu dadi, Tana tsara yadda zata shawo kan al’amarin anata

‘bangaren. Lee kuwa ta gyara zama tashiga bawa Islam shawarar yadda zata shawo kan
komai, ta ‘kar’kare da,

“Long story short, dai Ya Saif na zargin ki kenan ko? na biyu kuma baya ganin darajar ki, na uku
duk abunda ya fito daga hannun ki baya ci, ke karan kanki ma baki dame shi ba, hmm Lam lam
duk tsawon watannin nan ace auratayya ma bata tab’a shiga tsakanin ku ba? sai kace
katakwaye, Ina bazai yiwu ba wallahi.. bude kunnuwan ki kiji matakin da zamu ‘dauka, ke
wallahi sai ya zubar miki da hawaye, yana kneel down a qasa yana rokon ki zaki hakura..”

Nan dai Lee tashiga bawa Islam shawarwari ta ‘kar’kare da,

“Kema can d’aya banza, sai kace matar Malam kullum cikin kaya burum-burum, Ina shegun
‘kananan kayan da na baki kwanaki? ki dinga showing near nakedness dnki, kuma ki nuna
badan shi ki kai ba, baza gashin ki, Ina turarukan ki masu girgiza mutane, shafa su, ki juya
mazaunanki da malamalan ki sosai,(gaba da baya), ki bani kayan ki na dnko miki wasu styles
na garari, ke abincin ma tun da bayaci dafa iya naki da mai gadi kadai, kidenayi da yawa yana
lalacewa babu kyau, tunda mai gidan baci yake ba, zanturo miki wasu sirrin ta WhatsApp, for
now ki gwada wa’innan, ki dena shiga shirginsa tawaje na, watsar da shi a dustbin, keda kike
classy chiclada, Ina ajin ki ya tafi? nuna masa ‘bawon albasa yafishi mutunci a idanun ki. Zaki
bani labari wallahi, yadda kike da dirin nan, figure 8 ga kyau TubarkAllah, namiji ya isa ya rena
ki ne?..”

Ta ‘karasa maganar tana jan tsaki a karo na ba’a dadi, Haka dai Lee ta babbawa Islam
shawarwarin yadda zata shawo kan komai, sai ishai mijin yazo ya dauketa, Ai kuwa Islam tafara
amfani da hudubar Lee, domin Saifullah ya jima yana buga ‘kofa bata bude ba, sai data mula ta
sha iska, sannan ta mike tana yan ‘kwana, wata shegiyar rigar bacci ce a jikin ta, armless, gaba
d’aya ana ganin santala-santalan cinyoyinta a waje, kirjin ta kuwa tamkar zai fito ta gaban rigar,
tayi parking gashinta a tsakiya, cikin narai-narai da manyan idanuwanta kamar mai bacci, ta nufi
‘kofar zata bude masa, a bangaren Saifullah kuwa ya gama ayyana irin kwandon rashon
mutuncin da zai shuka mata, na barin shi da tayi a waje tun d’axu, sai kace ‘dan aike ya kawo
sak’o....
...
_Ikon Allah na tsinci maganar wai na dakatar da yin SAIFUL_ISLAM,, Saboda zan fara KAI MIN
HALACCI, Na kuma gode da kwandon zagin da wasun ku suka sauke min�, tunda haka ku ke
so, Shikenan! Na dakatar sai APRIL inda rai da rabo‍♀, kuma wannan Page din nayi ne shi ne
kawai dan ‘yan group din SAIFUL_ISLAM fans grp�_
*
_D’AN-D’ANO daga cikin_
_*KAI MIN HALACCI!_*


“Wai dan girman Allah karatun bokon nan shi za'a tambaye mu a kabarin mu? ahh nace na

gama neman ilimin boko dole sai nayi ne? gaskiya ni babu wata *Dabo English academy* d'in
da zanje bare na b'atawa kaina lokaci, idan naje guri ban iya turanci ba dan Allah a zageni ko
ayi min dariya, ba dai abinda mutum yake ji dashi zai yi amfani ba? toh ayi min turanci sai nayi
hausa dan shine yare na.”
“Ni kake yiwa rashin kunya Shamsu? Umma kinji yaron nan ina cewa yayi abu yana cewa ba
zai yi ba dan raini, to idan kayi wa zaka yi mawa? Kar Allah yasa kayi kudina ma sun huta kaje
kayi duk uban da zaka yi sakarai kawai shashasha.”

Tashi yayi yabar gurin yana k'unk'uni, kawai yaya Garzali yazo ya b'ata masa rai sabida wani
buri nashi can, yace baya so ba sai a kyalesa ba ko dole ne, sai kace fita daga addini duk yabi
sai yab'a masa magana yake yi harda cewa yayi masa rashin kunya dan sharri...

******

Cikin takun ta na cewa itama fa yanzu 'yan mata ce kuma budurwa, tazo wucewa ta gaban
shagon sa, yana zaune akan kujera a k'ofar shagon nasa. Yayin da daga cikin shagon kuma
wak'ar *alagidigo* ce take tashi ta cikin speakers hannunsa rike da game yana ta faman yi.

Muryarta kawai ya jiyo kamar yadda ta saba duk lokacin da ta hangoshi a guri ko cikin mutane
abokansa ne sai tayi masa waka, tun lokacin da tsautsayi yasa shi furta mata kalmar SO.

Satar kallanta yayi yaga yauma ta cokaro d'aurin d'ankwalin nan nata wato ture kaga tsiya,
mayafin nan a kafad'arta ta tsaya dai-dai shagon, kusa da wata mai suyar awara ta rike kugu
tana karkad'a jiki bakin nan yasha kanta kile, cunoshi take tana waka.

_''Allah ya tsine wa saurayin kusa da gida, shekaran jiya yazo.., jiya ma yazo..yauma kuma
zaizo...!''_

Kamar yayi shiru ya kyaleta kamar kullum idan tayi, amman yau zuciyarsa tana son ramawa
dan bai ga dalilin da zai sa k'aramar yarinya dan yace yana sonta ta dinga gasa masa magana
a fakaice ba, dan haka shima yana danna game d'in ba tare da ya kalleta ba yace.

_''Allah ya sakawa saurayin kusa da gida, shekaran jiya yakai an k'arb'e.., jiya ma yakai ta
karb'e.., yauma kuma zai kai, indai da gaske ne ba'a son 'yar kullum idan ya kai yau kar a
karb'a...!''_

Da sauri ta kallesa domin ba tayi tsammanin martani ba daga bakinsa, murgud'a baki tayi tare
da bugun cinya da hannunta ta kallesa, shima dai-dai sannan ya d'ago suka had'a ido ta
dank'ara masa harara, yayin da shi kuma ya mayar mata da lafiyayyan murmushi, mai awarar ta
kalla tana cewa.
“Aikin banza, Sa'ade soya ki bani ta hamsin.” Sa'ade dake zuba awara cikin mai tace,

“Toh.” Shi kuma da yake gefe yana jinsu yace.

“Sa'ade dad'a mata ta wata hamsin d'in, ta d'ari kenan zan biya ki”

Tab'e baki tayi maimakon tayi masa, godiya amman cikin ranta fess domin ko sisi daman babu a
gurinta, saboda tasan zai iya biya, shi yasa tace a bata ta hamsin dan ta kare yawa a gabansa,
da mamaki ya bita lokacin da aka gama soyawa aka mik'a mata ta karb'e ta juya zata tafi tace.

“A duniya dai akwai wahalallu, Sa'ade Allah ya sa a rage kud'in waken suya(soy beans), kinga
kuma kun huta masu saidawa kuma sun kwaso asara.”

“Kai Aliyah Shamsu mafa yana sai dawa kuma a gurinsa nake auna, so kike shima asarar ta
same shi bayan kuma gashi ya siya miki awara har ta naira d'ari”

Dariya Aliya tayi tana kuma sauyawa ledar awararta hannu, saboda zafin da d'ayan yayi, sai da
ta kalli inda Shamsu yake zaune sannan tace.

“Oho ke wacce kike so a amsa miki a cikin addu'ar tawa? A kara kud'in waken suyar, ko kuma a
rage kuma dole ku siya a haka wanne kika fi cewa amin?” Da sauri Sa'ade tace.

'”A'a nafi son a rage amman ai su Shamsu ne zasu yi mugun asara fa Aliya.”Cikin saurin baki
Aliya tace.

“Haka nake so ai Sa'ade kinsan wasu a wahale suke duk abinda zaki musu toh ba ganewa zasu
yi ba, ni na wuce sai anjima.”

Murmushi Shamsu yayi yana girgiza kai, sosai Aliya take bashi mamaki, gashi yayi-yayi
soyayyar da yake yi mata ta fita daga ransa, amman abin ya faskara yarinyar duk tabi ta raina
shi, yakan jure duk wani wulak'anci da zata yi masa, sannan yana lodar kayan ‘kwalam da
makulashe ya bayar akai mata bata tab'a dawo masa dashi ba, amman duk lokacin da yaje tad'i
gurinta bata fitowa haka kuma baya fasa komawa gobe.

—-
DOMIN MALLAKAR LITTATTAFAN _ZAFAFA BIYAR, ZAKU IYA TUNTUBAR LAMBOBIN MU,
KAI TSAYE XASU SADA KA DA LITTAFIN DA KAKE SO KO MALLAKAR DUKA BIYAR DIN A
DARI BIYAR DUKA KACAL_

*ga mai buqatar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login