Showing 75001 words to 78000 words out of 86718 words

Chapter 26 - SAIFUL-ISLAM Book Complete by miss xoxo (2).pdf

06 Jul 2025

2078

a raba auren mu

Islam, nasan ada nayi kuskure amma wallahi yanzu na gyara, fiye da tunanin ki. Dan Allah ki
bani last chance...Kinji?”

Yatsina fuska tayi, duk da har cikin zuciar ta takejin dad’in kalaman sa amma afili kuwa
kemad’agas tayi, tamkar bata sauraren sa, adai-dai lokacin akai knocking, Dr Jalaludden ne ya
shiga shi da su Mami.....


________

XAFAFA BIYAR;

DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOX

ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka
litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*


DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE

SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOXO




_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_
[1/3, 10:54 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


_*®HASKE WRITERS ASSO._*


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_
_BILLYN ABDUL_


*_SHAFI NA 64-66_*

_GAISUWAR BAN GIRMA GARE KI *TAWAN (BILLYN ABDUL)*,LITTAFIN SAIFUL_ISLAM,
GABA ‘DAYA TUKWICI NE AGARE KU KE DA (YA HAJJA CE), FATAN ALKHAIRI A GARE KU
KE DA UNCLE ABDUL, INA MIKI SON SO FISABILILLAHI, TUN WHATSAPP BA
KALAALLAH YA BARKI DA UNCLE ABDUL ABADAN DA’IMAN, KI DAD’E KIYI ‘KARKO
UWARGIDAH/AMARYASHAFIN YAU NA KI NE TAWAN, KI SHALLARA SHI DUK INDA
KIKE SO❤_

_nanahafsat.wordpress.com_

*A* razane Islam ta jiyo muryar Saifullahi cousin ‘dinta yana cewa,

“Hello Islam, dan Allah number DOCTOR SAMEER AMEER( littafi na) malamin physiology ‘din
ku zaki bani, Kinga an kai Nusrah ne zata haihu a asibitin sa, Kuma wai baya kusa suna
meeting ne, ni kuma bana garin, yanzu haka ina kaduna naje duba nuraddeen ne, Wai duk
nurses din tsoran kiran sa suke yi, ni kuma da inada number ‘din sa, amman babu yanzu. Dan
Allah ki turo min please, tunda shine level coordinator d’inku..”

Cikin rawar murya, cike da tausayawa halin da Nusrah take ciki. Tace dashi,

“Eh shine, Bari na turo maka, Allah ya sauke ta lapia. Ameen!”

Cike da hanzari ta nemo number a contact’s log ‘dinta, ta tura masa, bakin ta ‘dauke da adduar
Allah ya sauki yayar ta ta lapia.

‘Bangaren Saifullah kuwa a razane ya ‘daga idanun sa yana kallon mahaifin sa, cikin rawar
murya yace,

“Saki? Daddy saki fa kace.”

Ya fada a ‘dan razane, jaddada kai Alhaji Faruk yayi alamun tabbacin da gaske yake, cikin
rawar jiki Saifullah ya ‘kara matsawa kusa da mahaifin nasa, yasa hannuwan sa duka biyun
yana rik’o ‘kafafuwan mahaifin nasa, sai kace mai neman gafara, gaba d’aya ko Ina ajikin sa
rawa yake, tamkar mazari na kad’a shi..Cikin rawar baki yace,
“Dan Allah Daddy kuyi hak’uri, hukuncin ku yayi tsauri, wallahi wallahi Daddy bana zargin
Islam, kafin muyi aure ne dai tunda na gan ta a bakin wani joint, shi... shine zucia ta take zaton
ko bata jin magana ne, amma Allah bayan nan Daddy wallahi ban ‘kara zargin ta ba, ko dana
ganta a school dinsu da wani thou nasan shi a wani wajen, Allah banyi mummunan zato akan
haka ba, kawai dai bana sakar mata fuska ne, wai ko rashin sakin fuskar zai sa ta hankalta ta
de na, k...”

Kafin ya ‘karasa Alhaji Faruk ya ‘daga mai hannu alamar ya dakata, cikin yatsina fuska yace
dashi,

“Daga ganin sarkin fawa sai miya tai dad’i? Kenan daga ganin ta a bakin joint sai kai mata
kallon mummunan zato? Wallahi kabani kunya Saifullah, da ilimin ka da komai kake jahiltar
abu? Wannan wane irin duhun kai ne da kai? Meyasa da kake zaton hakan baka same ta ka
tambayeta ba? Sai kabar abu acikin ranka kana muzguna mata, shashasha, sakarai, sullutu
kawai, wanda ilimin sa bai ‘kare shi da komai ba sai bakar zucia da duhun kai. Sakar min kafa
ni, kafin nasa d’aya na ham’bare ka.”

Saifullah yaja baya a hankali yana zare hannuwan sa daga kan ‘kafar Alhaji Faruk. Cikin muryar
tausaya wa yace,

“Abba dan Allah kuyi hak’uri, wallahi wallahi Ina son Islam yanzu, da ‘dinma shed’a...”

“Kar kayiwa she’dan sharri Saifullah, wallahi wannan wata aqidar kace ta daban, andeji kunya
wallahi, Allah ya kyauta”

Cewar Hajia Zuwairah, ta ‘karasa fada tana zabga masa harara. Shi dai Saifullah hak’uri kawai
yake ta basu, gaba d’aya bashi da kuzari, ambaliyar hawaye ne ke reto a kyakkyawar fuskar sa
na nadama da dana sani, cikin haka Islam ta fito daga ‘daki, batasan da zuwan Saifullah ba,
kusa da Haj Zuwairah ta xauna daga ‘kasan ta, kafin tace da Alhaji Faruk kanta a ‘kasa,
“Daddy barka da rana..”

Murmushi kwance akan fuskar sa yace,

“Barkan mu Islam, kina Lapia?

Kanta a ‘kasa tace,

“Alhamdulillah Daddy..”

Saifullah ya zuba mata idanuwan sa yana kallon ta ‘kasa-k’asa, ta dauke kai kuwa hade da
shan kunu, dan karma ta gaishe shi, Haj Zuwairah ta dubeta tana fadin,

“Auta, na zo ne?”

Cikin rad’a rad’a islam ke cewa da ita,

“Mami dama sis dina Nusrah aka kwantar a asibiti, yanzu naga anata maganar a family group
‘dinmu, condition din nata is critical, kuma dama kafin nan ma Ya Saifun gidan mu yakira ni
neman number Dr Sameer malamin mu an kai ta asibitin nasa.”

“Ayyah.. Allah ya sauke ta lapia, itace matar Saifullahi ko?”

“Eh...”

Ta bata amsa kanta a ‘kasa, Mami ta mai da dubanta ga Saifullah da ya mai da Islam tamkar
television, gaba d’aya hankalin sa da nutsuwar na kan ta, cikin tabe baki Mami tace dashi,

“Kai..”

Daga kai yayi yana dubanta, alokacin kuma Alhaji Faruk ya mike ya bar wajen yana waya, cike
da muryar tausayawa Saifullah yace,

“Na’am first love.”

“Auta ta, zata je asibiti dubo yayar ta.”

Kansa a ‘kasa yace,

“Toh first love..”

Ganin Islam ta shiga ‘daki, ya sashi mikewa jiki ba ‘kwari yace,

“First love na tafi..”

“Allah ya raka taki gona..”

Kawai Mami tace, ta mai da duban ta ga tv dake nuna shirin ‘sons of the caliphate’. Fita yayi ya
shiga mota ya tayar da ita, ya fita daga gidan yai parking daga nesa daga gidan, alokacin Islam
kuma ta fito da tata motar, da sauri ya tsaida ita, kamar ba zata tsaya ba sai kuma ta tsaya,
buda gaba yayi ya shiga, wani kallon wulakanci ta jefa mai, kafin tace,
“Malam ya haka?”

Bai amsa taba, sai wani botton daya danna kujerar sa tayi baya, ya kwanta yana lumshe idanu,
tsaki ta saki, ya dago yana duban ta, a hankali kamar mai rad’a yai nuni da bakin ta yana cewa,

“Clean that shit..”

Kamar zatai kukai, haka tayi rau-rau da idanuwa, kafin tace,

“Vaseline ne fa nasa, lips dina naturally red ne.”

Tab’e baki ya yi, ya koma ya kwanta yana fad’in...

“Do you believe in love?!”

Shan kunu Islam tayi, ta cigaba da driving ‘dinta, har suka kai asibiti yana zuba mata magana
amma bata tanka shi, ita mamaki yake bata ma, dama yana magana haka?! Tana shirin zare
mukullin yai hanzarin rik’o hannun ta, cikin muryar na dama ya fara mata magana,

“Bilkisu... Dan Allah ba dan ni ba kiyi hak’uri, kinji?”

Ya shiga murza hannun ta, ta kwace tana dankara masa harara, kafin tace,

“Wanda ka keso shine idan ya maka laifi kake adana shi a kundun zuciya, Saboda haka zargi

na da kakeyi ni wallahi ko a jiki na, zaman takarda ta nake yi, domin ashirye nake na au...“

Rufe mata baki yayi da hannun sa dake tashin ‘kamshin Black oud, lumshe ido tayi tana shak’ar
‘kamshin, cikin rok’o ya fara mata magana,

“Dan Allah Islam, ba dan ni ba, wallahi wallahi Allah ya jarabce ni da son ki, So mai tsanani,
nasan nayi lefi a baya, amma inaso ki ‘dau hakan ki ajiye a matsayin sharrin shed’an, wallahi ba
wai zargin ki nake da aikata fasiqanci ba, a’a wallahi, kawai kishi ne, idanuna sun rufe, Believe
you me bilkisu, wallahi da gaskiyata nake miki magana.”
Ya karasa fada yana langabar da kansa, agogo ta kalla, kafin ta gyara ‘daurin ture kaga tsiyar
dake kanta tace,

“Ka gama?”

Ya kad’a kai kamar kad’angare, ta kalle shi ta watsar kafin tace,

“Toh fita zan kulle mota ta..”

Kamar yaron ta haka yafito yana raba idanuwa, a hankali ya furta,

“Why do I feel so suffocated?”

“Kace me?”

Cikin hanzari ya kad’a kansa yana saurin cewa,

“Ban yi magana ba.”

“Fine..”

Tace kawai, tasa motar ta a key, tai shigewar ta cikin asibitin,

Saifullah ya tsaya ‘ki’kam kamar wanda ya had’iye muciya, tunawa yayi da mahaifin su bai
sallame shi ba, da sauri ya tafi titi ya tsare cab/taxi. Yana shiga gidan su kuwa gaban sa ya
cigaba da fad’uwa, ganin harda motar Aji Mommodu mahaifin Khaled, addua yake ta faman yi
kar Daddy ya tambaye shi ina da ya tafi?
Bai rufe bakin sa ba kuwa, Alhaji Faruk yai gyaren murya kafin ya dubi Saifullah dake raba
idanuwa, kamar daga sama Saifullah ya jiyo muryar mahaifin sa ta doki kunnen sa da,

“Ina kaje kuma? Daga tashi naje nai waya na dawo mahaifiyar ka tace kace mata ka tafi?”

Saifullah ya sa hannu ya sosa ‘keyar sa, kafin yace,

“Na.. Naje nan bayan layi ne, wurin wani aboki na..”

“Madalla, Ina abun da nace ka rubuta?mikomin sauri nake yi.”

Saifullah ya sunkuyar da kansa, ya sake matsawa can kusa da mahaifan nasa, kamar zai shiga
cikin su, ya fara kwararo magiya gwanin tausayi ya ‘kar’kare da,

“Daddy wallahi tallahi ba wai ina zargin ta bane, ko sanda naganta a Lagos ai lokacin ba aure a
tsakinmu Daddy, kawai...Kawai nayi kuskure Daddy, Baba ka sa baki please, wallahi Allah na
cancanci kowanne lefi fyace na saki, ba .. baz..Bazan iya rayuwa ba ita aciki ba Baba..”

Aji Mommodu yaja majina, yana kara kwakula tissue a hancin sa, kafin yace,

“Wacece kuma ita...”

Cikin rawar baki Saifullah yace,

“Matata... Ita Islam ‘din, dan Allah Baba, wallahi Allah ina sonta yanzu, ko da dinma sharrin
shedanne..”

Sai faman zance yake zubawa, kamar sabon tabin hauka, Aji Mommodu yai ajiyar zucia, kafin
yace.

“Toh Masha Allahu! Bi sa ga shawarar da mukai, mun yanke hukuncin Is...”

Bai ‘karasa ba, Saifullah ya riko k’afar sa yana rokon sa da,

“Baba dan Allah kakka ce na rabu da islam, wallahi I truly love islam, with all my heart and
soul.”

Tsaki Daddy ya saki yana mikewa, can dispenser yaje ya tatso ruwan sanyin sa, ya koma ya
harde kafofi . Aji Mommodu yayi murmushi kawai yana sake maida duban sa ga Saifullah daya
makalkale masa kafa, cikin muryar umarni yace,

“ba zamu yiwa yarinyar tilas ta koma gidan ka ba Saifullah, kaga auren had’i aka muku, ba
wanda ke son ‘dan uwan sa, yanzu kazo da maganar kai kana sonta, ta iya yiwuwa ita har
yanzu ba ‘digon son ka azuciar ta, Saboda haka babu tilashe a zancen komawarta ‘dakin ta,
id...”
Be karasa ba Islam ta shigo parlorn bakin ta dauke da sallama.. dake parlorn idan zaka shjga
ko fita dole seka bi tashi, tsugunnawa tayi tana gaishe su, Aji Mommodu yace ta zauna dama

yanzu yake shirin aikawa a kira ta, murmushi fad’ad’e akan fuskar sa yace,

“Islam..”

Kanta a kasa tace,

“Na’am, barkan ku da yawwa”

“Barkan mu..”

Daga haka, Aji Mommodu ya shiga labarta mata komai kan yadda sukai da Islam, kuma zab’i
suka bata, idan tanaso ta koma ruwan ta, idan bataso nanma ruwan ta, Saifullah sai jifanta yake
da kallon ‘karki min haka’ , ta ‘kasan ido suka had’a ido ta zabga mai harara, kamar daga sama
taji yo muryar Aji Mommodu yana cewa,
“Zaki ci gaba da zama da shi? Ko kuwa ya sawwake miki?”

Sau uku yana maimaitawa, Islam kanta a ‘kasa tana murza hannuwa, cike da kunya tace,

“Baba ya sawwake min...”

Take ji, da ganin Saifullah suka ‘dauke, na’urar memory card din kansa ta chake, subscription
din yayi expire, duk wani gig take tattare zance yayi ‘dif daga bakin sa, a hankali ya sulale a
‘kasa ya fadi.... ji kake d’if, numfashin SAIFULLAH FARUK MUHAMMAD ya tsaya chak.....

XAFAFA BIYAR;

DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOX

ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka
litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*


DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOXO




_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_
[1/3, 10:54 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


_*®HASKE WRITERS ASSO._*


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_
_BILLYN ABDUL_

*_SHAFI NA 69_*

“Zan koma ‘daki na Baba..”

“Masha Allahu, Toh Allah yasa ki koma a sa’a, Allah ya kad’e fitnah a tsakanin ku, ya baku
zaman lapia mai ‘dorewa, ya baku zuri’a ta gari, mai ‘dimbin albarka, Ameen”

Kanta a ‘kasa, cike da kunya tace,

“Ameeen...”

A lokacin kuma Alhaji Faruk suka shigo shi da Abbas, Bayan su kuma Saifullah ne. Da alama
‘dakko su yayi daga asibiti, garin kallon Islam da Saifullah keyi sai da yayi tuntub’e zai fad’i,
Abbas dake nazarin sa yai saurin rik’o shi yana daria kafin yace,

“Aboki! Easy mana...”

Gaishe su tayi kanta a ‘kasa, Abbas yayi musu sallama ya tafi gidah, parlor yadawo daga Aji
Mommodu sai Aji Faruk da Saifullah, sai Islam dake gefe, Haj Zuwairah ta fito daga mab’oyarta
da Fatma wadda ta haye sama, ita kuma Mami tashiga parlorn tana murmushi kafin tace,

“Sannun ku da dawowa, ya jikin na ka?”

“Na warware first love”

“Masha Allahu! Allah ya ‘kara afuwa”

“Ameen” suka amsa baki dayan su

Alhaji Faruk ya ajiye robar ruwan daya kwankwad’a kafin yace,

“Toh sai mu ‘dora daga inda muka tsaya ko?..”

“Akan me fa?!”

Cewar Aji Mommodu dake gefe yana ajiye wayar dake hannun sa, Alhaji Faruk ya nuna Islam
yana cewa,

“Ta Islam, tunda tace gwara ya s...”

“Tace zata koma ‘dakin ta ai, mun gama magana..”

“Alhamdulillah abu yayi kyau, Toh Allah ya tsare gaba.”

Alhaji Faruk ya fada, murmushi fad’ad’e a fuskar sa, Saifullah dake kan kujera ya sauka daga
kai yayi sujjadar godia ga Allah, abisa wannan daddad’an labari daya doki kunnen sa, cikin
hanzari ya mike yana cewa,

“Mungode Allah ya saka da alkhairi, Tashi mu tafi.”

Ya karasa yana mai nuni da Islam wadda kunya ta mamayeta ganin idon Saifullah ya rufe ya ma
rasa agaban su wa yake, su Haj Zuwairah kuwa baki bude suke kallon sa, Sai itace ma ta ‘dan
bata fuska kafin tace,

“Wai ni auta ina ka kai kunyar ka ne? Agaban namu kake cewa ta tashi ku tafi? tukunna kai ka
kawo ta ne? Toh ba zata tashi ba sai..,”

Aji Mommodu ya dakatar da ita, ta hanyar daga hannun sa da yai mata alamun ta dakata kafin
yace,

“Toh tunda yace haka ku bashi itan mana..”

Suka ‘kyalkyale da daria dukan su, Saifullah ya fara sosa ‘keya da alamun ya manta a gaban su
wa yake, Haj Zuwairah tayi murmushi kafin tace,

“Zata je ma gidan barkar matar yayan su data haihu, anan Ganges street dake maitama ko
auta ta?!”

Cike da kunya Islam ta ‘daga kanta alamar Eh, kafin tace.

“Eh Mami..”

“Yawwa to ga abinci can a dinning, Daddyn su da Abban Khaled ku ci kar yai sanyi dan Allah..”

Mikewa sukai su ka nufi dinning area, Haj Zuwairah ta shiga serving ‘din su abincin, Islam tai
kitchen tana had’o musu lemonade Saifullah ya shiga,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login