Showing 24001 words to 27000 words out of 86718 words

Chapter 9 - SAIFUL-ISLAM Book Complete by miss xoxo (2).pdf

06 Jul 2025

2077



“Kayi hak’uri, abunne da ‘dan rudani aciki, at first mun ‘dauka menstrual cramps ne, to se
bayan da cikin ya ‘kara hautsinewa muka fara ‘k’ok’arin mata scanning, nan kuma jini yafara fita
daga ‘kasanta, atakaice dai tayi ‘barin cikin dake jikin ta, da mukai scanning m..”

Katseta yai, yana ‘daga mata hannu,

“Look Dr Hindu, Hidaya dai yarinya ta da tagama secondary satin baya? She’s just 17.. No it
can’t be.”

Murmushin takaici Dr Hindu tayi,
“Kayi hak’uri, amma wannan kasan aiki na ne, Gynecologist ce ni, baxanwa yarinyar ka sharri
ba, wallahi ‘karamin ciki tayi ‘barin sa, domin inaga kamar ya ‘dan fara kwari ma.”

Gaba d’aya ji da ganin Dr Khaleel sai suka ‘dauke na ‘yan wasu da’ki’kai....





_Have a blessed weekend ahead_





_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_
_BILLYN ABDUL_


*_SHAFI NA 21-22_*

_Shafin yau naku ne ‘yan *RANO ONLINE NOVELS*, Ha’kika duk wata writer da ke cikin group
‘dinnan kuna ‘kara mata ‘kwarin gwiwa da da’da’dan comments ‘dinku,Nagode k’warai da yadda
kuke bibiyar littafin *SAIFUL_ISLAM*. Allah ya saka da alkhairi_

_nanahafsat.wordpress.com_

Tuni numfashin sa ya fita, ji kake tim ya fad’i a ‘kasa, cikin kidimewa dr Hindu ta kira drs maza
suka dauke shi aka fara bashi temakon gaggawa, ita kuwa Hidaya tana can tana bacci saboda
allurar da akai mata,

Jin shiru basu koma ba, yasanya Haj Aysa kiran wayar sa, bai ‘daga ba domin tana silent,
director din asibitin ta kira inda yake sanar mata Ai da shi da y’ar duk an kwantar dasu, cikin
firgici ta shirya ta nufi asibitin itada Yakolo. Sai dai har lokacin Hidaya da Dr Khaleel basu farka
ba sai washe gari,Duk wani gwaje-gwaje anyi masa babu wani abun da ya same shi
sakamakon bugar da yau, kawai dai yasamu rauni a gefan goshin sa, da kuma ‘dan yatsan sa
na hagu da yai targad’e.

*WASHE GARI*
Da safe tuni asibitin ya cika da yan uwa, ganin duk sun farfad’o ba wani matsala, yasanya likita
sallamar su bayan yabasu magunguna.

Hidaya dai batasan me ke faruwa ba, haka ma Dr Khaleel babu wanda ya fad’awa, sai da suka
warke sukai ras lokacin da sati ya zagayo duk yan uwa sun hadu xa’a fara bikin Nuraddeen ‘dan
Ya Bala da ya’yan Hansa’u su biyu Kabeer da Ibrahim banda autan su Yusuf. A time din Dr
Khaleel yace yanason ayi general meeting bayan anyi isha’i.
Ya kuma kira Yafendo da Helwa kan lalle su dawo a ranar, dama ita Karimatu da safe jirginta ya
sauka, tayo siyayya fal. Kafin lokacin meeting, Yusuf ‘dan Hansa’u yaje sashen Inna Bilkisu,
matashi ne ba canba amma, domin baifi shekaru ashirin da biyu ba.

Bayan ya gaisheta, ya sa hannu yana shafa ‘keyar sa, Tana lura dashi, ‘dan murmushi tayi kafin
tace,

“Me ke tafe dakai Yusuf”

“Inna dama..Dama” sai kuma yayi shiru, kansa a ‘kasa.

“Dama me?! Fad’i ina jinka, kaga ba kowa daga ni sai kai sai Allah”

Cikin rawar murya yace,
“Inna dan Allah.. Dama so nake kiyiwa Baba(Ya Bala) magana, Dan Allah ni..Nima ai mun
aure.”

Baki bude Inna take bin Yusuf da kallo, sai kuma ta rufe tana jinjina kai,

“Toh shikenan babu damuwa, amma yanzu kai Yusuf kanada wacce kake so ne? Shin zata iya
auren ka, alhalin yanzu kake bautar ‘kasa ko aiki baka dashi?”

Cikin dakewa ya ‘daga kai,
“Eh inna ina da ita, domin iyayen tama sun amince sunce na turo manya na.”

“Dakyau..” Inna tafada tana daria.

Sosa ‘keyarsa yayi yana saurin mikewa ya fice,

Kusan karo sukai da Ya Bala da Dr Khaleel dake k’ok’arin shiga parlorn wajen Inna, ganin su
yasanya ta fad’ada murmushin ta,

“Yawwa ku kira Hansa’u ma tazo, zamuyi magana”

“Tohm Inna” dukka suka amsa a tare.

Dr Khaleel ne ya daga waya yakira Hansa’u, mintina kalilan sai gata tashiga wajen su,
gaggaysawa sukai aka taba hira, sannan inna ta sako zancen Yusuf.

“Yawwa wannan yaron, Dan Allah inaso a had’a auren nan ayi dana Yusuf..”

Gwalalo ido sukai dukkan su kafin ya Bala cikin kidimewa yace,

“Inna! Yusuf dai Yusuf namu?” Yafada yana nuna bakin kofar da suka hadu fa Yusuf,tamkar
Yusuf dinne awajen.

“Eh shi dai..”cewar Inna..

Hansa’u da Dr Khaleel suka hada baki wajen cewa,

“Inna meyasa kika yanke hukuncin haka?”

Ajiyar zuciya inna ta sauke kafin tace,
“A har kullum idan yaro ya nuna yana son aure gwara ayi masa, kafin ya janyo abun kunya.
Domin duk yaran da kaga ya bude baki yana cewa ai masa aure to lalle gwara ai masa, domin
ya matsu ne, kuma gata ne sannan ‘kara kamalar su ce da shirya kai dama ceto rayuwar su
daga fadawa kogin halaka, da ace anayin haka da yawan zinace-zinace ya ragu.. Yadda ya
fadamin ma yace iyayen yarinyar ma sunce ya turo magabatan sa, kunga kuwa Alhamdulillah”

Jinjina kai sukai, kwarai sunyi na’am da xancen, Dr Khaleel yace,

“Masha Allahu, kwarai naji dadi, kuma ni nayi alqawarin daukar dawainiyar auren sa, gidan da
xai xauna ma ya xabi apartment d’aya a estate din da su Mu’utaseer suke. Allah yasanya
albarka”

Addu’a sukai gaba d’aya duka, suna ‘kara mamaki. Sai da aka nisa sannan Dr Khaleel yace,

“Toh inna dama nima abunda ke tafe dani zancen Hidaya ne, na so sanar da ku kuma , sai kika
kwanta zazzabi na har maganar duk sanda kika wartsake sai na sanar da ku duka..”

Shiru sukai suna sauraron sa, hakan ya bashi damar ci gaba,

“Toh Nide satin baya ne, nadawo daga tafiya na babbawa yaran nan tsabar su banga Hidaya
ba, na aika akirata akace batada lapia, to na sata dai a gaba mukaje asibiti..” shiru yai yana
‘dan tari hade da sauke nannuyar ajiyar zuciya. Hawaye fal idonsa yake karasawa,

“Mukaje asibiti likitoci sukai gwaje-gwajen su, Na karkare zance dai Hidaya ashe ‘bari tayi, wai
ciki ne d..”

Be k’arasa ba, suka hada baki wajen fadar,

“Ciki?!”

“Kwarai ciki, amma tayi ‘barin sa” ya karasa fada hawaye na zirarowa daga idanun sa.

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un..” shine kalmar da suketa maimatawa,

Gaba d’aya sai parlorn yai tsit sai kakarin kukan Hansa’u da Dr Khaleel, Ya Bala ne yai ‘karfin
halin magana,

“Amma meyasa sai yanzu ka fada Khaleel?! Shin wane mataki ka ‘dauka a kai kenan?”

Cikin kuka yace,
“Yaya wallahi gaba d’aya na kasa samun nutsuwa, ni da anawa shirmen na dauka irin wannan
abun sai mutum ya aikata zina ne ake ramawa akan ‘ya’yan sa, wallahi kwana da kwanaki
tunanin da nakeyi kenan, shin ko na tab’a aikata irin wannan mummunan zunubi ne a baya,
batare da na sani ba?”
Girgiza kai Ya Bala yayi, cikin muryar ban hak’uri yace,

“Wallahi a’a Khaleel, babu nutsatstse kaf dangi irin ka, kanada ladabi, biyayya, da zumunci ,
wallahi qaddara ce kawai da dama can muqaddari ne daga Allah, wanda bamu isa mu canxa
ba, sai dai yanzun abunda na keso na sani shin ina ita Hidaya take?”

Hansa’u taja majina, kafin tace.
“Amma Wannan yarinya ta cucemu, Allah dai ya..”

Katseta Inna Bilkisu tayi ta hanyar ‘daga mata hannu,

“Kowa da tasa qaddarar Hansa’u, kuma xai iya yiwuwa ko fyade aka mata, tunda ciki lokaci
d’aya yake shiga ,Toh kila anan tasamu”

Girgiza kai Ya Bala ke tayi yana magana shi kadai, kafin ya dubi Dr Khaleel yace,

“Shin ko hakanne yasa kace akwai general meeting yau?”

Kada kai Dr Khaleel yayi alamun eh.
Waya Ya Bala ya janyo ya kira Yafendo, bugu biyu ta ‘dauka yasa ta turo masa Hidaya sashen
Inna Bilkisu.

Hidaya bata dauki lokaci ba, tashiga ciki bakin ta dauke da sallama, bata kawo komai aran taba,
domin batasan ma anyi hakan ba, shigar cikin, samun sa ballantana ‘barewar sa.

Gaishe su tai, sannan ta nemi waje ta zauna tana fadin,

“Uncle B! Gani.”

“Hidaya..” Ya Bala ya kirata

“Na’am Uncle B.”

Ya sake maimaitawa har sau biyu,kafin yace.

“Sau nawa na kira ki Hidaya?”

“Sau uku Uncle B”

“Yawwa...Shin inaso ki gayamin gaskia tsakanin ki da Allah waye yayi raping dnki?”

“Rape..?!”

Ta maimata a fili, kada kai Ya Bala yayi yana nazarinta,Babu alamar tsoro a tattare da ita, domin
da hakanne jikin ta zai nuna, ‘dan yatsina fuska tayi kafin tace,

“Uncle B. Wallahi ba wanda yai raping dina.”

“Okay likitoci ‘karya suke yi miki kenan? Ke!” Ya daka mata tsawa.

Jikinta ya hau rawa, tana jin sanda fitsari ya zirara a pant ‘dinta. Maka mata harara yayi, tuni
launin fuskar sa ya canxa, jijiyar goshin sa ta ‘dad’daga ya sa yatsa yana mai nuni da ita,

“Kinga Hidaya , ki kuka da kanki idan har baki fadamin gaskia ba.”

Kuka tafara tana yarfe hannuwa,
“Uncle B, dan Allah kuyi hak’uri.”

“Hakurin uban ki, xaki bude baki ki gayamin wanda ya miki ciki ko sai na kira makarantar da
kaina na tambayi da wane shegen kike mu’amala..”

Nan tagano ashe Hilal ne, abunda suke aikatawa shine ya sanya ta awannan halin da take ciki,
Hawaye d’aya nabin ‘d’aya, majina na kwarara daga hancin suna y’ar tsere akan fuskarta, tasa
hannuwa alamun ban hak’uri tafara magana,

“Uncle B! Wallahi tallahi saurayin Hafsat ne, tun farko da.. da..”

“Da uban uban ki, xaki gayamin ko sai na karairayaki?”

Cikin kidimewa ta hadiye wani kakkauran yawu kafin tace,

“Wallahi tallahi Uncle B.. Sas..Saurayin Hafsat ne da farko da ita suke yi, yana taba nononta
wai tanaso suyi girma sufi na Islam, shi.. shi..Shine nima na sameshi nace inaso nawa su fara
girma nima yamin haka, kuma...Kuma shine daga baya yafara saka...”

Bata ‘karasa ba Ya Bala ya bata kyawawan mari guda uku a jere, ji kake ‘tas tas tas’ ,duhu ne
ya mamayeta kafin tafara jin kamar tsuntsaye na zagaye kanta, tsabar xafi sai da taga wuta a
mari na biyu , Ana ukun kuma kunnuwan ta suka toshe.

A zuciya Ya Bala ya sa aka kira Hafsat , gabanta sai faduwa yakeyi tashiga parlorn. Gaidasu
tayi tana xama nesa da Hidaya, jikin ta yabata itama yanzu xatasha nata dukan, ganin Hidaya
wadda aka canxawa halitta lokaci d’aya tamkar ba ita ba.

“Ke..”Ya Bala ya dakawa Hidaya tsawa,

Dawowa tayi a razane hannunta dafe da kuncinta,

“Maimata abunda kika fad’a.”

Maimaitawa tayi,Hafsat tuni jikin ta yafara rawa, Ya Bala ya dubu Hafsat yana cewa,

“Wanene yaron, kuma ‘dan gidan uban waye shi? Tinkiyoyo kawai, da har kuka tsaya, tsatso
d’aya kuka fito amma namiji guda d’aya ya ‘bata rayuwar ku, wannan wane irin dabbanci ne?
Idan aure kuke so ayi muku mana, tukunna ma dukda dai bana tunanin haka, kuma bana fatan
hakan,babu Islam acikin wannan abin naku ko?”

‘Daga kai sukayi, Hafsat jiki na rawa tace,

“Wallahi Uncle B, ni dai sau d’aya ne muka...Mukayi, Nace banaso kada ya sake saboda wani
wa’azi da naji, shine fa ya koma kan Hidaya kullum kullum..”

“Ya isa” cewar Ya Bala, gaba d’aya yaran sun fara bashi tsoro.

“Wanene yaran?”

“Sunan sa Hilal ‘dan gidan Ambassador Umar Gumi ne”

Gwalalo ido Ya Bala yayi yana maimata sunan Amb Umar Gumi, cikin in’ina yace,

“Amb Umar Gumi dai recent Amb dake wakiltar Nigeria a Johannesburg?”

Gyadai kai suka Hidaya da Hafsat suka yi, Ya Bala ya juya suka hada ido da Dr Khaleel, a
hankali ya furta,

“The mafia kenan... Subhan’Allah”

Sallamar su Hafsat da Hidaya Ya Bala yayi, sun jima a parlorn kowa da abunda yake saqawa a
zuciar sa, ajiyar zucia Inna Bilkisu ta sauke kafin ta dubi Ya Bala tace,

“Wannan yaron(da ke ‘dan fari ne) yanzu ya xa’ai kenan?”

“Inna wato a zahirin gaskia mahaifin shi yaron da sukai wannan babbar ta’asa, Idan duk duniya
zasu taru suce ga abunda ‘dansa yayi wallahi baxai yadda ba, ‘dan rigama ne Inna, Idan kinji
ana ‘The Mafia’ Toh shine, hatsabibancin sa ya xarce tunanin mutum wallahi..”

Hannu dafe da hab’a inna tace,

“Toh Allah ya kyauta, domin acikin su ma ba’asan wa ya fara jan ra’ayin wani ba. Allah ya
shrya..”

“Ameen” suka baki d’aya.

“Ni ina ganin had’a su a aurar dasu baki ‘d’aya shi yafi muhimmanci, Tunani nake ma acikin
yaran nan wa za’a had’a a rufawa juna asiri.” Cewar Ya Bala.

Sun jima suna tattaunawa, tareda bawa Dr Khaleel hak’urin wannan bakar ‘kaddara data afka
masa. Ya Bala da kansa ya tasa qeyar Hafsat da Hidaya ciki harda Islam zuwa asibiti. Gwajin
farko aka fito da Islam virgin ce ita komai ruf a muhallinsa. Hidaya kuwa har ‘dinki akai mata

sannan sun samu mummunan virginal infection Hafsat da Hidaya, sanadiyyar fingering da Hilal
yake ma muka hannunsa acikin gaban su. Su biyu dai result yafito ‘baro ‘baro su ba virgin bane,
kuka wiwi kowaccen su tayi, banda Islam da taka godewa Allah daya tsameta bata fada wannan
mummunan ‘kaddara ba.
Bayan sallar isha’i aka fara meeting, da maganar auren su Nuradden aka fara, inda Nuraddeen
xai auri wata y’ar ‘kanwar gwamnan kaduna, Kabeer da Ibrahim kuma ‘yayan mutum ‘d’aya
xasu aura amma kowacce babar sa daban, uba suka had’a. Daganan aka dakko maganar
auren Yusuf, kowa yayi mamaki amma an tayashi fatan alkhairi. Sai aka ‘karkare da zancen su
Hidaya.

Karimatu na gefe ta lailayo wani ashar, tana kumfar bakin wallahi sai dai sihiri aka jefe ‘yarta
dashi, ko kuwa ture akai mata na gardi ya keta mata haddi a makarantar, Hakama Yafendo da
ke ta kama sunan Haj Aysa tana qullalliya suka shirya dan kawai araba yaran su da budurcin
su, a zuciye Dr Khaleel ya mike yaja niyyar basu ragowar sakin su, dakyar Inna Bilkisu ta
haneshi, domin har sai da ta mike tana rike kafadar sa, gaba d’aya idanuwan sa sunyi jajir shi
kadai yasan tashin hankalin da yake ciki.

A lokacin Ya Bala yace su Hafsat kowacce ta maimaita abunda yafaru, babu kunya suka
fayyace komai, Haj Aysa dake gefe har kukan tausayi tayi, tana ‘kara jaddada girman ‘kaddara,
na irin tsaron da Dr Khaleel yakewa yaran sa amma ace haka tafaru? Kuma iya xamanta dashi
tasan baida wani mummunan hali na bin mata ko akasin haka.
Fada sosai Ya Bala ya shiga yi, ta inda yake shiga, batanan yake fita ba, ya ‘karkare xancen da,

“Saboda haka satin sama ne bikin su Nuradden, mun yanke shawara wanda Idan duk duniya
xasu taru su hana, Indai ba Allah ne ya ‘kaddara hakan baxai faru ba, wallahi summa tallahi sai
mun had’a auren su Hafsat a satin.”

Gaban Islam ya yanke yafadi, tuni jikin ta ya soma rawa, Ya Bala ya cigaba da cewa,

“Saboda haka zamu had’a auren Hafsat da ‘Alhaji Saminu Taura’ na kano, Hidaya kuma..”

Bai ci gaba ba, Karimatu tai hanzarin katseshi tana hawaye,

“Yaya kayi hak’uri dan Allah, Alhaji saminu fa, wannan tsohon mutumin mai mata biyu?
Fisabilillahi ka duba lamarin nan Yaya”

Tsaki Ya Bala yaja yana kauda kansa gefe, cikin fushi yafara magana,

“Idan ba shi ba wa kikeso a bawa? Shi dinma shine tun kwanaki yace yanason d’aya daga cikin
yaran gidan nan, kuma itace dai-dai domin ai ba budurwa bace yanzun, shima temaka mata
xaiyi”

Rufe baki Karimatu tayi tana kuka, Sosai da hawaye, Hafsat dake gefe tai shiru itama hawayen
na fita daga idanun ta, domin ko a mafarki bata tab’a xaton haka rayuwa xata canxa mata ba.
Yafendo kuwa kasa kunne take tana jiran taji wane hukuncin xa’a yanke akan Hidaya.

“Yawwa sai ke Hidaya. ‘Alhaji Muzammil Rimi’ dake Zaria, shi muka yanke hukuncin baki shi a
matsayin mijin ki, kun san shi dai wanda yazo ya duba Inna rannan, yanada mata uku kece ta
hudu, zai ajiye yi agidan sa dake Zaria.”

Tusar wannan karan da Yafendo ta saki kowa yaji ta, a fusace Ya Bala ya juya yana dubanta da
duk ma yan parlorn,

“Haba Amina, wannan wane irin abune wai? learn to growl up pls” cewar Dr Khaleel had’e da
wurga mata harara.

A kidime Yafendo ta rarrafo kusada Ya Bala dayai hanxarin toshe hancin sa da hannu ‘d’aya,
domin warin tusar data saki ba karamin babban bomb bace, Rokansa tashiga yi, kan ya janye
ra’ayin sa, ita kuwa Hidaya dake gefe tunani take ina nema Zaria,saurin rufe baki tayi tunanowa
da suna tsayawa a garin suyi sallah Idan xasu kano, kuma sun tab’a zuwa dubiyar matar
mutumin, sam gidan baiyi mata ba, don mutumin ba mai kudi bane kamar Dr Khaleel (To ai
dama hakane, dan mahaifinka mai kudi ne bai xama lallai sai ka auri mai kudi ba, ita dunia ai
Up and down ce, kuma dama life is dynamic).

Ya Baka ko takan Yafendo dake bashi hak’uri ya janye ‘kudurin sa bai bi ba, sai ma sanya ‘kafa
dayai ya shure hannun ta, dake makale da ‘kafar sa, gyaran murya yayi, kafin yace.

“Saboda haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login