Showing 60001 words to 63000 words out of 86718 words
tsaye a bakin ‘kofa, yanata ayyana yadda zai sauke wa Islam kwandon rashin
mutunci, na barin sa da tayi a tsaye tamkar ‘dan aike. Islam dake baje akan gado tana danna
waya ta ajiye ta a gefe, jin knocking din da yake ya isheta, cikin turo baki gaba ta nufi hanyar
‘kofa domin bude masa, gaba d’aya ta ‘dauki darasin Lee a kanta, chewing gum ne a bakin ta,
tana taunawa. Sanye take cikin wata shegiyar rigar bacci armless. Gaba d’aya santala-santalan
cinyoyin ta sun bayyana a waje, domin rigar shara-Shara ce, ‘kirjin ta kuwa tamkar zai fito ta
gaban rigar tsabar kamata da tayi.
A yangance ta bude ‘kofar tana yatsina fuska, Saifullah dake shirin zubo mata kwandon masifa,
ya bude baki kenan zai yi ya kasa, ganinsa da jinsa sai suka tsaya cak akan siffar Islam. Bin ta
yake da kallo, kamar ‘dan ‘kauye yazo birni. Yana ‘kissina abubuwa da yawa a zuciar sa. Tabe
baki Islam tayi, ta wuce abunta tana juya mazaunanta, wani kakkauran yawu Saifullah ya
hadiye, irin na kwadayin abun da kakeso aka hanaka ‘dinnan. Har ta koma daki bai dena kallon
taba, tundaga saman ta zuwa ‘kafarta. Jiki ba ‘kwari Saifullah ya kullo ‘kofar. Dakyar ya hau
sama yana hawa kowanne matattakalar bene yana bin dakin Islam da kallo. Ji yake wani abu
na ingiza shi, kan yaje gareta amma ya kasa.
Islam kuwa tana komawa ‘daki, ta shiga bawa Lee yadda sukai ta WhatsApp. Take bacci ya
‘dauketa bayan ta yi alwala ta sauya wani kayan baccin, Don dama wannan tasa ne don
tsokano Saifullah, Saifullah dake sama kuwa ya nemi bacci a idanunsa ya rasa. Yayi sallolin
nafilfili da addu’oi, amma sam bacci yak’i ‘daukar sa. Daya rufe idanu siffar Islam kawai yake
gani, Wani sabon yanayi yaji yana shiga jikin sa, tunani sosai ya shiga yi, cikin haka kuwa bacci
‘barawo ya sace shi...
*WASHE-GARI*
Islam bata fito ba sai wajen 10, dake weekend ce, sanye tafi to cikin sequence lace blue, dinkin
fitted gown, bata ‘daura ‘dankwali ba, tayi kalba guda biyu manya da suka zubo mata har gadon
bayan ta. Tasha jambaki. Tana fitowa sukai kicibis da Saifullah dake zaune a kujera ya saita
‘kofar dakin da zata fito da kallo. Kallo d’aya zakai masa kasan bai samu bacci ishasshe ba. Ko
kallon sa batai ba ta ‘dauke kanta, y’ar gaisuwar da yake tsammanin samu ma ranar batai masa
ba. Kitchen tashi ga, cikin ‘kan’kanin lokaci ta soya chips and egg, ta kira mai gadi a waya ya
karbi nasa. Kanta tsaye ta wuce ‘dakinta da nata plate din a hannu. Saifullah dake kan kujera ya
zama kamar wani mutum-mutumi. Ganin ko takansa bata biba, yau ko tayin abinci batai masa
ba. ‘Kwafa yai yana mikewa tsaye. Mukullin motar sa ya zira rai ‘bace ya nufi gidan su Khaled.
Lokacin kuma Humaira tagama bawa Haj Latifa labarin komai. Ita ma kuwa batai ‘kasa a gwiwa
ba ta buga tafawa Haj Zuwairah. Haj Zuwairah kuwa lokacin sunata shirye-shryen dawowa
Abuja a satin. Wayarta kare a kunnenta ta jiyo muryar Haj Zuwairah na ‘kark’are xancen da,
“Na baki wuk’a da nama auntyn su, ki dau duk matakin da kikaga ya dace, kafin mu dawo,
Insha Allah ni nasan me zan yanke akan al’amarin..”
A lokacin kuma Haj Latifa sallama takewa Haj Zuwairah, Ai kuwa Saifullah ya shiga parlorn
bakin sa ‘dauke da sallama. Haj Latifa tai murmushi kawai tana cewa da Haj Zuwairah ta cikin
waya,
“Kin ganshi ma ‘dan halak yazo. Okay to shikenan, Duk dai yadda ake ciki zan sanar miki.”
Cewar Haj Latifa ta katse kiran bayan sunyi sallama, Saifullah ya zauna a gefan kujerar da
Humaira take, mikewa Humaira tayi bayan ya zauna, fuskarta a had’e ta gaishe shi, Don sosai
take jin haushin abubuwan da yake yiwa Islam, bai kawo komai ba ya amsa da,
“Lapia lou Humaira, ya studies?”
“Kalau..” kawai tace a takai ce, ta haura sama abinta.
Har ‘kasa ya tsugunna yana gayda Haj Latifa, fuska a sake ta amsa, sosa ‘keya ya shiga yi,
hakan ya sanyata tambayar sa ko lapia? Ya amsa da,
“Lapia lou Aunty.. Porridge(abinci me ruwa-ruwa) nake so..”
“Toh bari na sa ayi maka kunu.. Ina ita Islam ‘din take, ko tana school?”
Sai duk kunya ta kama shi, ya zama guilty conscious, ya ma kasa magana, Hakan yasanya Haj
Latifa kyautata zaton dagaske ne de maganar da Humaira ta fad’a mata. Murmushi kawai tayi.
Bayan ta mike ne tace dashi,
“Bari a damo maka, a hada maka da cup cake?”
Daga kai yayi kawai alamun Eh, yana jin sa duk a takure. Fita Haj Latifa tayi, ta shiga kitchen da
kanta ta hado masa kunun tsamiya da chocolate cup cake.
Islam kuwa bayan fitar sa, ta shiga study room, dake sama, cikin sauri ta debi books din da
takeson dubawa ta koma kasa, Don tunda akai auren ita a dakin ‘kasa take, shi kuma yana
sama. Dama sama ‘daki uku ne da parlor sai kitchen, ‘kasa kuma daki ‘daya ne da parlor biyu,
sai dinning area da kitchen/ store, sai daki d’aya a waje da balcony.
A ranar ne da rana ahalin Prof. Khaleel suka yiwa Islam zuwan ba zata, Ai kuwa taji dad’in
zuwan su, ta sake wata kwalliyar tana bude musu kofa, Ammi ce kawai bata zo ba, amman
Yakolo ta wakilce ta, da abincin su suka zo, nan aka shiga ci ana shafta, Saifullah kuwa bayan
ya bar gidan su Khaled majalisaar su ya tafi, har yaje zai yi parking yaji gangar jikin sa na ingiza
shi da ya koma gidan sa, zuciar sa na kwad’aita shi da son ganin Islam, idanuwan sa na nuna
masa kyakkyawan murmushin ta, da tastiest lips dinta masu rugurguza mai tunanin sa.
“So suffocating...”
Ya fada yana mai dukan sitiyarin motar sa, kan motar ya juya ya koma gida, tun a kwanar gidan
sa ya hango motoci, lambar kano da na Abuja, mai gadi ya bude masa gate ya shiga ciki, tun
daga gate yake jiyo hayaniyar su, anata zuba hira. Lado mai gadi ya kalla dake zuba masa
kirari, cikin melodious muryar sa yace,
“Baki mukai ne Lado?”
“Eh oga.. ‘yan uwan hajia ne suka zo d’axu.”
Kad’a kai yayi, ya shiga cikin gidah da takunsa na ‘kasaita, bakin sa ‘dauke da sallama,
idanuwan sa suka zumo masa Islam dake zaune a tsakiyar wasu mata sai hira take zubawa,
mamaki yake na ganin dama tana hira haka? Kansa ya ‘kara daurewa ganin Saifullahi da yayi,
hankali kwance yana kurbar lemon robar hannun sa, Sai a lokacin suka lura da shi, aka shiga
gaggaisa wa, shima cike da kunya yake amsa musu, ya bawa Saifullahi hannu suka gaysa, duk
abunnan idanuwan sa na kan Islam dake dankaramai harara idan sun had’a ido, Sama ya hau ,
yana yi yana kallon Islam. Ganin haka yasanya Yakolo murmushi ta dubi Islam dake basu
labarin makarantar su tace da ita,
“Islam je ki kai masa abincin ko? Ya dawo ko sannu da zuwa baki masa ba, shashasha na
‘dauka da kikai auren kinyi hankali..”
Cikin zumburo baki gaba Islam ta mike, duk yan parlorn suka sa daria, a nata ‘bangaren kuwa
damuwa ce fal, na ganin su basusan halin da take ciki ba, ba susan irin zaman cakwakiyar da
suke da Saifullah ba, harda bubbuga ‘kafa tai a ‘kasa irin na shagwabar nan, Yakolo ta kai mata
dukan wasa, Ita dai Islam ‘murmushin da yafi kuka ciwo kawai take musu tana yak’e, Don kar su
gano kan abun. Tana hawa bene tana addua, gaba d’aya a tsora ce take batasan irin bakaken
maganganun da zai sake gasa mata ba. Duk abun nan Saifullah na kwance akan gado, yana
kallon su ta madedeciyar tv da aka hada domin dakko rahotan cctv dake parlorn da suke, da
kuma sauran ko’ina na gidan, bai tab’a kunna taba sai yau, Don sosai zuciar sa take sake
kwadai ta masa son ganin Islam. Yana ganin ta kusa ‘karasowa dakin da yake yai maza ya
kashe tibin (TV/television). Islam kuwa cikin sand’a ta shiga parlorn sama, daki d’aya ta bude
tana adduar Allah yasa baya ciki. Ai kuwa ba kowa ciki, ta shiga tana sauke nannauyar ajiyar
zucia.
Saifullah dake maitar son ganin ta yaji ‘dif , ba Islam ba alamar ta, cikin rawar jiki ya mike yana
gyara collar rigar sa, ya kara banka turaren alharamein yana kallon kan sa a mudubi. Cikin
hanzari ya fita daga dakin, ta kamshin turaren ta ya gano tana dakin tsakiya. Ai kuwa yana
murda handle din kofa ya hangota a zaune akan gado tana raba idanu, daria taso tabashi ya
danne, yana wani hade rai tamkar yaga kashi, kamar bashi ne mai ‘kulaficin son ganin ta ba.
Tana ganin sa ta ‘kara sunkuyar da kanta. ‘Kasa ‘kasa ya shiga kallon ta, ba kadan ba tayi mai
kyau cikin wani material lallausa ja, dinkin bubu, tasha jan jambaki, dauri kawai tayi bata yafa
mayafi ba, jelar kalba biyun da tai ta matukar karawa daurin kyau.
Kusa da ita ya matsa, ta ja baya da sauri, sai da suka kai ‘k’arshen gado a haka, ya samu
kansa da rike hannun ta, Cikin murya ‘kasa kasa kamar rad’a yace da ita,
“Who’s that guy?!”
“Wa kenan?” Ta bashi amsa tana cuno baki gaba, amma fa a tsorace take.
Hade rai yayi kafin yace,
“Na downstairs mana.. Wanene shi?”
“Oh ya Saifu... Cousin dina ne”
Kamar almara yaji abunda ya tsaya masa kwana da kwana ki a wuya yau ya sauka ‘kasa ya
fad’a.
“Cousin?” Ya maimata yana feeling guilty.
Daga kai tayi tana kallon gefe, samun kansa yayi da ‘kara tambayar ta da,
“Malamin ku ne a school ko kuma student ne shima?”
Wani kallo ta watsa mai kafin tace,
“Malamin mu ne, shine lecturer dinmu na community medicine.”
Idanuwan sa ne suka sauka a kan labbanta, wani feelings yake ji a game da su na daban, So
yake ya samu ya rage xafi akan su miskilancin sa ya hana, dakyar ya ‘ka’karo maganar,
“Wane warning na miki akan jambaki?”
Ta gano shi, hakan yasanya ta saurin kwace kanta ta mike a dari zata buda kofa ya rigata, ita
da kofar ya had’a ya rufe da mukulli, ya jinginata a jikin kofar, yana kallon idanuwanta dake
sanye cikin kwalli baki me kyau. Cikin takaici tace,
“Dan Allah ka sake ni na koma wajen su Aunty.,, Dan Allah ka..”
Bata ‘karasa ba taji bakin Saifullah Faruk Muhammad a nata, yana kissing dinta da wani irin
salo na soyayya, wani irin French and passionate kiss yake bata, gaba d’aya jikinta ya zama
weak, sun ‘dau lokaci a haka kafin ya turata gefe, idanuwan sa sun kada sunyi jajir, nunata yayi
da yatsa yana fadin,
“Kar ki ‘kara saka jambaki daga yau idan wani ‘da namiji Yana wajen, ni kadai na yadda ki sa
jambaki a gabana, Banda sauran maza. Wallahi kinji Allah Idan na sake ganin kinsa jambaki da
maza awajen kuma sai na mugun sab’a miki, ko school zaki je ban yadda ki saba, idan kuma
kika shafa without my consent ban yafe ba.”
Baki sararo Islam ta saki tana duban Saifullah, na ganin duk akan jambaki yake wannan bala’in,
cikin tunani ta jiyo muryar sa yana,
“Get lost.. don’t let me repeat my self”
Fecewa Islam tayi ta gudu, shi kuma ya zauna a bakin gadon dafe da kansa, hannun sa d’aya
yasa a saitin zuciar sa yana dafe ta, jin yadda take bugawa da ‘karfi, ahankali yake furta.
“Ya Salam! Me ke faruwa dani? I’m feeling so uncomfortable”
Ya jima a zaune, nan Islam ta shiga, daga bakin kofa ta ce masa bakin zasu tafi, bandir din ‘yan
200 ya dauka ya sauka kasa, su Areef da sauran yaran ya daddan ‘kawa kudin a hannu, sunata
tsalle suna murnar zasu sai alawa. Shi de cikeda kunya ya ‘karasa ya raka su har parking lot,
sukai sallama da su, Sai bayan sunja motocin su sun tafi, Islam da Saifullah suka koma ciki,
dakinta ta shiga ta datse da mukullii, shi kuma ya haura sama yana jin wani bak’on lamari yana
ziyar tarsa. Dakyar bacci ‘barawo ya sace shi, ita kuwa Islam tuni ta bawa gado ‘hakkin sa don
dama a gajiye take.
Gaba d’aya Islam ta fita harkar Saifullah, duk wasu abubuwa da zai hadasu tadena yi, tadena
bari ko haduwa suyi bare ya karta mata rashin mutunci. A satin ne taje ganin gidah, Don tinda
aka kai ta ba taje ba, Ammi batasan dawar garin ba, da Islam tatashi tafiya ta harhada mata
kayan gyaran jiki dana mata, da sauran spices na girki, Ita dai Islam kawai ta amsa ne don karta
‘ki amsa, Ammi ta tambayi jin ba’asi. Sai bayan magrib takoma gidah don dama ta masa
message zata gida, yace ok.
Tana shiga ta ganshi hakimce a parlor, ya kwantar da kansa akan pillow, idanuwan sa kamar
mai bacci, ya rufesu. Sallama kawai tayi, ya amsa a ciki, tai shigewar ta daki tasa key, ajiyar
zucia Saifullah ya sauke yana mikewa tsaye. Kashe komai na wuta yai a ‘kasan, sannan ya
haura sama yana dafe kansa dake barazanar fad’o masa,...
*WASHE-GARI*
Wajajen 6 na yamma Haj Zuwairah mahaifiyar Saifullah ta dira a gidan su Saifullah, lokacin
dawowar Islam kenan daga school, Sosai islam cikin rawar jiki ta cika gaban Haj Zuwairah da
kayan ‘kwalam da makulashe, Ita dai Haj Zuwairah sai bin Islam take da kallo, yarinyar nada
hankali ga nutsuwa, batasan meyasa Saifullah ya bad’awa idanuwan sa ‘kasa a ido ba yai fatali
da wa’azin da tai masa na yasanya soyayyar Islam a ransa, aganinta yarinyar batada wata
makusa da za’a ‘kita..
Jefi-jefi suke ‘dan taba hira, Sai bayan isha’i abadan Saifullah ya shigo gidan, hakan da yai ba
karamin ‘kara ‘kona ran Haj Zuwairah yayi ba, wato sai dare yaja ma yake dawowa gidah
kenan? Yabar y’ar mutane ita kadai sai mai gadi, yana shiga parlorn bakinsa dauke da sallama
ya hangi mahaifiyar sa, cikin rawar jiki ya karasa gare ta yana wani shagwabancewa, Islam
dake gefe ta zuba musu idanu tana kallon sarautar Allah..
Cike da shagwaba Saifullah yake gayda mahaifiyar sa, amsa masa tayi kamar ko yaushe. Ta
danne abunda ke ranta sai nan gaba zata nuna masa fushinta idan ta yanke hukunci. Sai da
suka dan taba hira ne ta mike tana gyara mayafinta, ta dubi Islam dake zaune a gefanta a ‘kasa
tana wasa da gashin center carpet,
“Auta ta! Had’a kayan ki a akwati da duk abunda zaki buk’ata, zamu tafi gida na...”
****
_Wallahi kunci darajar wa’enda nake kunya, ba zan iya ja da su ba sun nemi alfarmar na
cigaba da yi DAN SU, Saboda haka zan cigaba da rubuta littafina kamar yadda na fara, amma
dan Allah duk sanda aka ga banyi post ba to akwai dalili ne, ko na matsalan idona ko wani abu
dai da yasha mun kai☺ Ashe haka masoyan littafin SAIFUL_ISLAM kuke da yawa lord !
I’m impressed☺ amma fa gaskia yawan comments dinku shi zai bani ‘kwarin gwiwar rubuto shi
da yawa, kuma akai akai, less comments, less posts gaskia_
_GA MAI BUKATAR SIYAN *KAI MIN HALACCI* dama sauran books dinmu na *ZAFAFA
BIYAR*, zaku iya tuntubar details namu kamar haka;_
ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka
litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*
_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_
*_NA*_
_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_
_*®HASKE WRITERS ASSO._*
*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_
*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_
_BILLYN ABDUL_
*_SHAFI NA 50-53_*
_nanahafsat.wordpress.com_
Tun kafin ya kai ‘kofa yajiyo kukan Islam, tuni ta zube a ‘kasa tana zunduma ihu, hannuwan ta
dafe da kanta, yadda ku kasan anyi mata aiken sak’on mutuwa. Rerashi tashiga yi ba
‘kak’kautawa, Saifullah dake bakin kofa ya juya ya koma wajen ta yana lashe ‘kasan lips dinsa,
ta fuskar sa zaka gane he really enjoyed the kiss, hannuwan sa zube cikin wandon kakin sa.
Tamkar bai tab’a daria ba ya tsaya akanta, cikin husky voice dinsa yace,
“Ke...”
Bata ‘dago ta dube shi ba, ta cigaba da kukanta, duba agogo yai minti biyar harta wuce, Lalle
dagaske ne tarihin ta da aka bayar na mayyar kukace, tabe baki yayi kafin yace.
“Zaki ‘dago fuskar ki, ko sai na sharara maki mari tukun?”
Dakyar ta iya mikewa tsaye tana kallon ‘kasa, tana ‘dagowa ya zabga mata harara, cikin yatsina
fuska yace,
“I ruined my first kiss akan ki, my very own first kiss, so precious and tantalizing! Daga dora shi
akan lips naki kika cafke kamar kin samu alawa, gashi ke ba good kisser bace, beside wannan
ba shine kiss dnki na farko ba kinyi da maza ba adadi, you better stop pretending, dama abunda
kike so ne, you are desperately in need