Showing 66001 words to 69000 words out of 86718 words

Chapter 23 - SAIFUL-ISLAM Book Complete by miss xoxo (2).pdf

06 Jul 2025

2079

littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka
litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*







_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


_*®HASKE WRITERS ASSO._*


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_

_BILLYN ABDUL_


*_SHAFI NA 57_59_*

_This page is dedicated with love and appreciation, to *every single fan of mine❤*, deeply
appreciates your heartwarming comments, I truly feel beyond blessed. Thank you so much for
the support, it means a whole lot much. KISSES ND HUGS FOR YOU_

nanahafsat.wordpress.com_

Haj Zuwairah ta mike tana gyara zaman gyalen ta, kafin ta juya ta dubi Islam dake zaune a
gefan ta a ‘kasa, cikin murya mai bada umarni tace da ita,

“Auta ta, had’a kayan ki a akwati da duk abunda zaki buk’ata, zamu tafi gida na ne, idan kuma
zaki bar sauran a zo a kwasa daga baya to, amma dai duk abunda kikasan zai miki amfani ki
‘dakko kinji?”

Cikin sauri Islam ta mike tsaye, tana ‘daga kanta, cike da ladabi ta furta,

“Toh Mami, Barin ‘dakko.”

Tana gama fad’a ta shige ‘dakin ‘kasa, Haj Zuwairah ta ‘kara mamaki ganin dama Islam din har
yanzu tana kwana a ‘kasa kenan ita kad’ai? Jaddada kai tayi, Saifullah dake gefan Mami shima
mikewar yayi ya haura sama. Bayan kamar minti talatin, Islam ta fito daga dakin ta da akwatuna
guda uku da handbag, sai jakar laptop a ‘dayan hannun. Haj Zuwairah ta karbi d’aya tana
murmushi, a lokacin Saifullah ya sakko da na shi akwatin guda biyu da brief case. Haj Zuwairah
ta saki baki tana kallon sa, cikin turo baki gaba yace,

“Muje Mami, tunda duk mun ‘dakko komai, sauran kayan sai zuwa da safe xan ‘dauka.”

Wani kallo Mami ta watsa ma sa, na ‘kama rai na mun hankali’, ta dubi Islam dake janye da
akwatunan ta kafin tace,

“Auta ta! Yi gaba da akwati d’aya, ki sasu a motar ki, daga nan ki turo me gadin ku ya ‘dauki
sauran..”

“Tohm Mami..”

Cewar Islam, da kallo ‘daya za kai mata, kasan tana matuk’ar farin ciki da barin gidan da zata
yi, hade da adduar Allah yasa ba ‘daki d’aya xa su zauna da Saifullah ba., Hannu Saifullah ya
sa zai karbi hand luggage din hannun Mami, murmushi fad’ade a fuskar sa yana cewa,

“Mami kawo na taya ki da wannan, sauran sai Lado ya kwashe su.”

Wani kallon ka ma renamin hankali Mami tabi saifullah dashi, cikin fushi ta cire hannun sa daga
kan jakar, cike da fad’a tafara magana,

“Kar ka ‘kara ‘dora hannun ka akai kaji na gaya maka, tunda ka bad’a ‘kasa a idanunka ka
nuna bamu da ‘kima ai magana ta ‘kare, kuma zuwan da nai dama dan na tafi da Islam ne
kawai, kamar yadda muka yanke shawara ni da mahaifin ka, kuma ko da wasa kar ka zo mana
da maganar dawowar Islam gidan nan, ta gama zama anan gidan, daga can sai gidan su..”
Baki,hanci, idanu,haka Saifullah ya zubawa Mami sarautar Allah,har ta gama, sai a sannan ya
dawo hayyacin sa, yana duban mamaki da kyau amma a zahiri jinjina kalmomin data fada yake,
cikin rawar murya yace,

“Mami wallahi ‘karya take min, ki kira ta kiji idan gaskiar al’amarin ta gaya miki, wall...”

Be ‘karasa ba Haj Zuwairah ta haushi da fad’a, ta inda take shiga batanan take fita ba, ta
‘kar’kare da,

“Kuma Islam ta gama zama a gidan nan kenan, Saboda haka kaje ka auro SON RAN KA, tunda
ZAB’IN IYAYEn (Son Rai ko Zab’in iyaye?!, (littafi na)) da mu kai maka bai maka ba, kaga tafiya
ta..”

“Mami please..”

“Please ‘din gidan ku, ku ma ka maida akwatunan da ka ‘dakko, mu ba ‘kananan yara bane,
kunyar daka bamu ta isa haka, ka je ka auro wadda tai maka..”

Saifullah yai kasa’ke yana kallon Mami, Tana gama magana yashjga bata hak’uri, sam idanunta
ya rufe masifa kawai take surfa masa, ya dafe kansa yana salati, bakin sa ‘dauke da duk
addu’oin da suka zo masa, gefen bango ya kalla yana nanata kalmar,

“So suffocating..”

Mami dake ‘kule dashi, jin abunda ya fad’a yasata zabga masa harara, zatai magana Lado ya
shiga parlorn ya ‘debi sauran akwatunan, zai had’a dana gefan Saifullah Mami ta dakatar dashi,

Saifullah da ke kallon ikon Allah ya rike haba yana maimaita,

“I’m feeling so suffocated Mami..”

Wani dogon tsaki Mami taja, kafin ta dube shi tana zabga mai harara a karo na ba’a dadi. Cikin
fada tace,

“Kai da suffocated din na had’a ku na zazzabga muku mari, ka fita idona Saifullah, wallahi akan
maganar yarinyar nan zan iya sab’a maka, sarai kasan hali na idan raina ya kai ‘kololuwar ‘baci.
Saboda haka ni zan wuce da Islam, Daddynku zai kira ka, duk hukuncin daya yanke akai kai ka
jiyo, sakarai da kai da ‘katon kanka tun na haihuwa..”
Tana gama fada tai gaba abunta, cikin fushi harda bige akwatin Saifullah dake gefe, tasa ‘kafa
tai fatali dashi, tana ci gaba da sakin tsakin ta, tana fita tace driver dinta ya ja motar ta da kayan
Islam, motar Islam kuma aciki suka tafi, Islam taja su. Saifullah dake leken su ta window ya saki
labulen bayan fitar su, Sosai ya kara jin ba dadi, ganin Islam na murmushin dad’in zasu rabu.
Samun kansa yai da shiga cikin shekararriyar damuwa. Lokaci d’aya kansa ya hau ciwo,
idanuwan sa suka fara tara ruwan bakin ciki, zuciyar sa kuwa ta canza takun bugunta, gaba
d’aya duk wasu sassa da gab’ob’in dake jikin sa sun fara shiga wani yanayi na azaba. Mikewa
yayi ya haura sama, ko takan akwatunan sa dake ‘kasan bai bi ba. Jiri ne sosai yake ‘dibar sa,
amma sam hakan yaki hanashi wayar da yai niyyar bugawa, mahaifin sa ya kira yasa a
speaker, sai daya kira sau uku kafin mahaifin nasa ya ‘dauka, sallama yai masa, bayan sun
gaisa da daddyn nasu ne yace,

“Daddy...akan.”

Sai kuma yai shiru yana a jiyar zucia, Tuni Alhaji Faruk (mahaifin Saifullah) ya gano akan
abunda yasa Saifullah ya kira shi, cike da dattako yace,

“Ina sauraren ka auta.”

Wata bahaguwar ajiyar zucia Saifullah ya kara yi, hannun sa dafe da saitin zuciar sa, ji yake
tamkar zata faso ta fadi don azaba. Bai tab’a shiga tashin hankali irin haka ba, sai yanzu. Yayi
mamaki kwarai matuka yadda yake jin Islam a ransa yanzu, amma ya ‘dau hakan a matsayin
shakuwa ce kawai( littafi na SO KO SHAKUWA?), sai da mahaifin na sa ya ‘kara kiran sunan sa
a na ukun Saifullah ya amsa yana cewa,

“Na’am Daddy! Akan maganar Is.. Islam ne Daddy, Mami tazo tatafi da ita ynxu, na ‘dauka ma
harda ni a tafiyar, tace a’a, wai zaka nemi dai tukun.”

Murmushi kawai Alhaji Faruk yayi a nasa ‘bangaren, ya gano Saifullah ya fara sa Islam a ransa,
ba zai yi garajen mai da ‘y’ar mutane hannun Saifullah ba, sai yayi hankali, kuma sai an tambayi
Islam din itan ta amince, idan kuma tace a’a to fa reverse is the case.

“Daddy..” Saifullah ya ‘kara kiran mahaifin nasa a karo na biyu.

“Na’am Saifullah, duk naji na kuma gane, amma sai dai kayi hak’uri, ka jira kuma hukuncin da
zai biyo baya, for now I have no idea akan komai..”

“Daddy please..”

Saurin katse shi Alhaji Faruk yayi, ta hanyar cewa,

“Kasan mundawo Abuja yau gaba d’aya, So Ina sabon clinic ‘dina, and I have lots to cover,
zuwa anjima zamuyi magana. Bye!”

Yana gama fad’a ya katse, Saifullah ya ‘kara kiran sa ya katse, ya dubi screen din wayar sa da
kallo, tunda yake a rayuwar sa, baban sa bai tab’a rejecting calls dinsa ba sai yau, hakama
mahaifiyar sa kullum cikin kiran sa da Auta take,amma yau ta kira shi da saifullah, wani irin
‘kululin bakin ciki ne ya tsaya masa a mak’ogaro, haka kawai yaji wasu zafafan hawaye suna
zuba daga idanun sa...

******

*Johannesburg*
(Darrenwood, Cresta and Northcliff.Ave)

Zaune Hilaal yake a gefan kujerar da mahaifiyar sa take, da alama magana muhimmiya suke yi,
mahaifin sa Amb Umar Gumi yana hakim ce a kujera mai cikin mutum 3 (3 sitter),
danne-dannen wayar sa yake yi shi, Hilaal da mahaifiyar sa Haj Ayna’u ne kawai ke magana,
Hilal ya ‘kara fad’in,
“Allah Mama aure nake so, mun gama shirya komai da yarinyar, a cikin month dinnan muke so”

Haj Ayna’u ta dubi Amb Umar Gumi tana fadin,

“Alhaji! Kaji abunda yaron nan ya ke fad’a?”

Ajiye wayar yai a gefe yana kallon su duka, can kuma ya dubi Hilaal yana cewa,

“Kai din yanzu a haka aure za kai? Yanzu fa kake University Son, fad’amin meyasa kakeson ayi
maka aure yanzu?”

Shafa ‘keya Hilaal yai, yana sunkuyar da kai ‘kasa,

“Baba, Kawai inaso ayi mun dai, Saboda dad dinta yace, zai bawa wani ita”

Murmushi Amb Umar yayi, yana shafa gemun sa kafin yace,

“Okay son, Anything for you. A’ina take? Abuja ko wani garin?”

Dadi kashe Hilaal, cike da jin dadi yace,

“Anan Johannesburg ta ke da parents dinta, amma ‘yan asalin garin kaduna ne.”

“Okay son, it shall be well, za muje ayi koma, worry not.. Ya sunan ita yarinyar?”

“Sunan ta Hibbah Bala Sa’eed, mahaifin ta Professor ne a school dnmu, shi yasa suka zamo
residents din nan ‘kasar.”

“Okay son, kamar an gama nema, kakka wani damu.”

Cike da jin dadi Hilaal ya rungume mahaifin sa, daga nan ya rungume mahaifiyar sa, Wadda
kallo ‘daya za kai mata, kasan bataji dad’in hukuncin da mijin nata ya yanke ba, Haka dai suka
ci gaba da harkokin su, a satin kuma aka tambayo auren Hilaal agidan su Hibbah. Take akace
an bashi, Sati biyu kawai a ka saka na bikin, satin biki na zagayo wa aka fara shrye shryen
events. Events uku akayi, sannan amarya da ango suka tare a gidan su dake unguwar St
Mathens anan Johannesburg din. Da dare kuwa Hilaal yaje da soyayyar kazaar sa da sauran
kayan ‘kwalam da makulashe, sai murna yakeyi tayi, shi ma fa yanzun ba sauki tunda yayi aure.

Cikeda jin dadi ya shiga gidan sa, yana shiga parlor ya hango amaryar sa Hibbah kame akan
kujera tana kallo, yayi mamaki, don baiyi zaton haka ba, kasancewar yasan ba haka amare
suke yi ba ko a littafi, amma ya ‘dau hakan a matsayin kila don su abokai ne tun farko, shakuwa
tasa ta yin haka, yana sallama ta tashi da sauri ta rungume shi tana sunsunar wuyan sa, ware
idanuwa yayi yana gasgata hakan a matsayin mafarki, bai gama zancen zucin daya ke ba yaji
tahade bakin ta da nasa, tana k’ok’arin cire masa wandon rigar sa, yai ta maza ya kwace kansa
yana furta,

“Calm down love, easy mana”

Hibbah fa ido ya rufe, kasancewar su tare kawai take jira ita, dakyar tabari su kai sallah, Hilaal
yai googling adduar da ake idan za’ai auratayya. Bai gama karantawa ba Hibba ta jashi suka
fad’a akan gado, hakura kawai yayi yana sakin tsaki, sam bai san Hibbah haka take ba, ya ‘dau
hakan ya ajiye akan kila desire tablet tasha, Sosai suka shiga romancing juna, ta yaga rigar
dake jikin Hilaal tana k’ok’arin cusa kanta ciki,, ahankali yake lalubar hanyar sa, sai dai yana
k’ok’arin shiga yaji ta a wangale, wangal-gal abude kamar kofar rijiya, bai taba’a zaton haka ba,
ya ‘dauka Hibbah descent ce, nutsattsiya, shiysa yai avoiding sauran yan mata, aganin sa ita
virgin ce mai kyan hali, dagowa yayi da jajayen idanun sa yana duban Hibbah, Cikin murya cike
da bacin rai yake ce mata,

“Hib..Ina pride dnki?! Ina kika kai virginity dnki? Kin zubar da mutuncin ki a titi? Shine aka
jajubamun ke, ki kasa na aure ki? To wal..”

Be ‘karasa ba Hibbah ta katse shi, ta hanyar toshe mai baki da hannun ta na dama, hawaye na
reto a fuskar ta, tace dashi,

“Kada ka tsaneni hubby, wallahi wallahi, Ni rape victim ce , Wani mugu ne ya raba ni da
*MARTABA TA*, kuma ya gudu. Pls kakka guje ni, dan Allah I deserves any sort of punishment
amma banda saki pls, kayi tunani hubby, wallahi raping dina akai”

Gaba d’aya Hilaal kwakwalwar sa sai ta chake, tuni memory card din kansa ya yi installing
rayuwar sa ta BNA, irin dabbancin da sukai da Hafsat da Hidaya, wasu hawayen da na sani ne
suka shiga reto a idanun sa....

******

‘_DAN’DANO DAGA;_
_KAI MIN HALACCI_

KAI MIN HALACCI shamsu, wallahi tallahi I love you with all my heart, ba zan iya rasa ka ba, kai
ne mamallakin zucia ta, kayi fatali da rayuwar mu ta da wallahi Allah sharrin shedan ne, domin
shi din la’a..”

Bata ‘karasa ba shamsu ya katse ta, tunda tafara magana yake buga biron hannun sa akan
desk din ofishin sa, an rubuta CEO., kwantaccen sajen sa da turawa ke kira da sideburns ya
shafa, wani shegen murmushi yai iri na gefan bakin nan kafin yace,

“Pls leave my office.. Get lost”

Zatai magana ya daka mata tsawa, yana fadin,

“Walk out... shameless being kawai.”
_______

XAFAFA BIYAR;

DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOX

ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka
litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar

0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.


*Karki bari ayi babu ke*


DAURIN BOYE; NA HUGUMA
BURI DAYA; NA MAMU GEE
SAUYIN KADDARA NA;HAFSAT RANO
WUTSIYAR RAKUMI; BILLYN ABDUL
KAI MIN HALACCI NA MISS XOXO




_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


_*®HASKE WRITERS ASSO._*


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_

*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_
_BILLYN ABDUL_


*_SHAFI NA 60_*

_nanahafsat.wordpress.com_

_*WASHE-GARI_*

Islam na zaune, ta gama shirya wa zata tafi lectures a ‘dakin da aka bata ta kwana Haj
Zuwairah ta shiga, dauke da tray shak’e da abinci. Da sauri ta ‘karasa ta karb’i tray ‘din hannun
Haj Zuwairah. Cike da ladabi ta durk’usa tana gaida Mamin.

“Mami Barka da safiya, an tashi lapia?!”

Murmushi fad’ade a fuskar Haj Zuwairah tace,

“Lapia lou auta ta, har kin shirya zaki tafi kenan?”

Kanta a ‘kasa tace,

“Eh Mami.”

“Yayi kyau, Amma ki ‘dan ci wani abun ko? Ba dadi tafiya da yunwa school. Bari na miki
packaging snacks sai kici da break.”

“Toh Mami, Nagode Allah ya ‘kara budi”

“Amin auta ta, Bari naje.”

“Toh Mami..”

Bubbude warmers din Islam tayi, chips and egg ne da slice bread, sai plantain da sauce din
hanta sai tafarnuwa ce ke tashi, gefe d’aya kuma karamin flask ne, cike da ruwan green tea sai
tashin kayan kamshi yake. Ta ‘danci kadan ta mike tana gyara jikinta, sanye take cikin bak’ar
abaya mai kauri, ta yane kanta da mayafin abayar, har ta goga purple nude lips ta goge, tunowa
da kashedin Saifullah. Mild(marar ‘karfi) turare ta shafa, ta rataya side bag dinta na Dkny.
Kitchen tabi Mami, don Alhaji Faruk sassafe yafita suna da board meeting na clinic dinsu.

“Har zaki tafi Auta?”

“Eh Mami nagama”

Mika mata lunch-bag ‘din Mami tayi, Islam ta sun kunya har ‘kasa ta karba, Mami ta fad’ad’a
murmushin ta, Sosai take jin son Islam har cikin magudanar jininta, yarinyar na da hankali da
biyayya ga tsafta, cikin sakin fuska tace,

“Toh Auta ko na zo na kai ki, ko kuma driver yayi dropping d’inki?”

Kai a ‘kasa Islam tace,

“A’a Mami, na hutasshe ku, ai hannuna ya fad’a sosai, Ina driving ko’ina.”

“Masha Allah.. That’s nice, Toh sai kin dawo, Allah ya bada sa’ar karatu, should in case idan
yan gidan ku sun kira, kice kina nan gidan, zan ma dai fadawa Hajian taku.”

“Okay Insha Allah Mami, na tafi.”

Islam na gama fad’a ta fi ce daga kitchen din tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login