Showing 12001 words to 15000 words out of 86718 words

Chapter 5 - SAIFUL-ISLAM Book Complete by miss xoxo (2).pdf

06 Jul 2025

2073

wuce shekarun da zatai wani
shagalin suna gotai-gotai da ita, Sam dr Khaleel yace bai san zance ba, suna kamar anyi
angama, ya tsara komai, kayan fitar sunan ma abun kallo ne, ita har tsoro abun ya soma bata.

Tamkar wata budurwa, haka Dr Khaleel yayo mata kayan fitar suna kala kala, designers masu
tsada nagani na fada, haka ma yan biyun sa ya shirgo musu kaya, raguna da shanu, su aka
yanka akai rad’in sunayen yaran.

‘Abubakhar da Muhammad Tasi’u shine sunayen yan biyun Haj Aysa da aka sanya musu,
laqabin su kuma Areef da Abeed xa’a dinga kiran su, kamar yadda Islam ta nemi adinga ce
musu.’

Safa tazo tun daga Lagos, hakama Marwa na nan tafe daga Manchester, tace da ita xa’ayi
shagalin komai, satin da zai zo na suna xata zo. Tuggu da makirci ciki harda qulle-qullen
magani, babu wanda su Karimatu basu tana da ba, jira kawai suke dama tazo, su aiwatar da
mugun nufin su.
*B* *N* *A*

Sosai fa kowa kansa na kayuwa, suna zana jarabawar su, banda Hafsat da gaba d’aya gangar
jikin ta taxama mallakin Hilaal, sha’anin su suke shanawa kawai, sam bata maida hankali wajen

karatun exams din tasu,

A haka suka kammala, hutun wata uku cur aka basu, da jaddadawar kar wanda ya kara hutu,
da zarar ya kare an dawo kowa yadawo, koya fuskanci hukunci mai tsanani.

Wata mai kamawa kuma, satin farko kowa iyayen sa yazo taron malamai da iyaye da akeyi
wato ‘parent and teachers meeting’ a kuma ranar xa’a bawa iyayen yara takaradar sakamakon
da suka samu ‘result sheet’ ko kuwa na maida kai ajin baya ‘repeating’ ko kuwa canxa
bangaren abunda ake karanta ‘Field swap’.
Ranar Friday kowa akazo daukar sa daga gidah, su Lee da sauran kawayen Islam kowa suna
bankwana da saurayin su, Banda Islam da Kamalu class rep kawai sukai sallama ya tafi,

Sai da Hafsat sukai sha’anin su da Hilal sannan tafito tana wani sussun ne kai, ganin Islam ta
gansu lokacin da yake cire hannun sa daga rigar ta, yi tai kamar bata gansu ba, har Hafsat
tashige cikin School Bus din da tazo daukar su, Hidaya sai basar da Hafsat takeyi, hade da cin
alwashin idan sukai resuming babu abunda zai hanata kula Hilal, sai dai Hafsat ta hadiyi zucia.
Islam da Lee ne sukai hugging juna, da yake su duk a Abuja suke basu wani damu ba, Hafsat
Rano da Fatma Bichi ne ‘yan kano. Sallama sukai wa junan su, kowanne ya nufi wajen motar
da akazo daukar sa.

Hilal na daga gefen motar da akazo daukar sa yana bin Islam da kallo, a tsorace take duban sa,
ya sakar mata wani killer smile yana lashe ‘kasan lips d’insa, Tamkar kamar tsohon maye. Da
sauri ta wuce har tana cin tuntub’e.

Cikin luxurious School bus din da akazo daukar su tashiga, can baya takoma ta jingina da pillow
abinta,
Harara Hafsat ta maka mata, tana karkada hannuwa alamun jaddada abu,

“Yawwa ke!..Sauran ki kuskura ki gayawa Daddy abubuwan da yake faruwa, wallahi idan naji
makamancin haka sai kin gayawa aya zak’inta”

“Okay! ga y’ar iska tana magana da wofi ko?” Hafsat ta sake maimaitawa cike da isa,

Ko kallonta Islam batai ba, saboda yadda kanta ke matukar sara mata, yatsina fuska Hidaya
tayi tana hararar Hafsat din a fakai ce, duk dan saboda ganin datai musu da Hilaal. Juyawa
Hafsat tayi tana kwankwasa gaban driver, dake baya akwai dan window daya kare tsakanin
driver da passengers.
“Yes..sifik(speak)”

Cewar driver dinsu wadda suke kira da Delman, sunan yasamo asali ne, bayan yakai wasu

shekaru yana aiki tare da ahalin na Dr Khaleel. Dan kauyen Dal ne dake garin Kano. Suke mai
laqabi da ‘Na Dal’, cu’danya da yare na yau da kullum da yake a habujan, yasa shi fara ‘dan jin
turanci. Nan dai ragaya ta sauya masa ya canza sunan sa da ‘Delman’ del a ganin sa a turance
yana nufin Dal sai kuma kalmar Man ta ingilishi.
Daria Hafsat ta tuntsire dashi, jin yadda yake turanci ka’in dana’in. Sai da tayi mai isarta kafin
tace dashi,

“Dan sa mana wakar joeboy ‘baby’ dinnan”

Kada kai yayi yana sauya wakar daga ‘Mad over you’ zuwa ‘baby’ din da tace.

A haka suka karasa unguwar su, Hafsat ce kawai keda liver din bin wakokin da Delman yake
saka mata, Banda Hidaya datai tagumi ta fada duniyar tunanin yadda xatai snatching Hilaal karfi
da yaji.

Islam kuwa tun da sukayo hanyar exclusive store, wani mall dake unguwar su take jin gaban ta
na tsananta faduwa. Sosai yake bugawa yana mata barazanar fadowa daga k’irjin ta, har suka
shawo kwanar gidan su bai dai na bugawa da ‘karfi ba.

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” shine kalmar da take ta faman maimaita wa.

Zaune suka hango mazan gidan gaba d’aya awaje, har da yan lagos dukkan su, ciki harda
Najibulla mijin Marwa dake Manchester, duk sunzo, saboda babban buri ne Allah ya cikawa Dr
Khaleel, kuma abune da ya zama dole a yi masa barka.

Sosai Islam ta shiga rud’i jin yadda gaban ta ke ta faman ‘fat fat fat’ ba ‘kak’kautawa. Horn
Delman ya danna yana jiran masu gadi su bude, dake motar ba tinted glasses bane, kana iya
hango na waje, suma suna iya gano ka.

Mudasser da Mu’utaseer suna tsaye suna duba wata takarda ajikin bango, shi Mudasser ya
jingina yana nuna ta, shi kuma Mu’utaseer ya watsa hannu baya yana magana yana daria, da
alama dai musu suke.

Kamaludden kuma da Ibrahim ‘dan Hansa’u da Shamsudden wot suke bugawa akan benchi.
Sai Kabeer, Ibrahim da Yusuf su kuma suna kan tabarma dasu da sauran samarin makotan su,
sai zuba hira suke, suna musun siyasa.

Mubassher,da Nuradden kuma suna tsaye, da yarinyar yaya Safa a hannun Nuradden. Baby
Aysha,sunan Haj Aysa taci, suke kiran ta da ‘pinky’. Sai zuba surutu takeyi,suna kyalkyala daria.

Gate mai gadi ya bude,Delman ya zura Kan mota dai-dai lokacin Saifullahi dake zaune a
balcony ya d’aga kansa yana kallon motar, karaf idanuwan sa suka sarqe dana ISLAM...

_sau uku ina typing, yana gogewa wlhpls ignore all typos_



_Ashe haka masoyan littafin _SAIFUL_ISLAM._ _ku ke da yawa? Kai Masha Allah.. _ _Duk Ina
ganin ruwan comments dinku wlh, kuma ana gayamin duk wanda bana gani, Ana sanar min,
knw that I appreciate every single heartwarming feedbacks of urs. _ _Jazakum Allahu khairan.
Lobiyu ol fisabilillahi❤_



_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...*


*NA*


*©NANA HAFSAAT*
*(MISS XOXO)*


*®HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_


*SADAUKARWA GA:*
*ASY KHALEEL*


*TUKWICI NE GARE KU:*
*YA HAJJAH CE*
*BILLYN ABDUL*


*SHAFI NA 12-13*

_This page is dedicated with love and appreciation to my little sissy..STYLISH BCH,#habeebtyn
habeebty.. Mamma Yasmeen❤_

nanahafsat.wordpress.com


Babu kowa a wajan, ya jata tare da rik'eta gam, dai-dai kan bakinta da yasha nude lipstick yasa
hannunsa ya bige mata shi da k'arfi,

“Ouch..” cewar Islam tana rike da labb'anta wad'anda suke yi mata zafi da rad'ad'i.

“Mugu..azzalumi” Ta fad'a cikin zuciyar ta.

Ture ta yayi can gefe yasa hannunsa yana karkad'e jikin sa kamar wanda ya gogi kura a jiki,
yatsansa yasa yana mai nuni da ita yana cewa,

“Bana son na baki kunya ne a gaban friend d’inki wallahi, amma da agaban ta xan sharara miki
mari.”

“Toh da nai maka me Ya Saifu?” Cewar Islam wadda lokaci d’aya hawaye ya soma zirara daga
cikin idanun ta.

“Da zaki had’a kazamin jikin ki da nawa mana, jiki na one in town ne, amman saboda tsabar kin
renani shine kika cacume ni. Ke sai na baki punishment ma wallahi”

Cike da mamaki take kallon sa jin abinda ya fad'a, shifa ya kwakume mata jiki a nasa, sannan
k'iri-K'iri yayi musu amman shine yake cewa hakan. Maganar da ya sake fad'ace ta bata
mamaki jin yace,

“Tun ba yau ba ina lura da ke so kike ki dinga tab’a jiki na, kin dauka ni irin mazan nan ne masu
tab'a mata..”

“Kutu..” Ta furta cikin tsantsar mamaki dajin abinda ya fada kafin tayi shiru tana jinjina kai.

“Ahh! ‘Karasa zagina mana, ga makaryaci ya saki ‘kwan k'aryar daya saba yi miki ko?”

“Haba Ya Saifu. Wallahi ni ba ni ce na tab’a kaba, fad'uwa zanyi kayi saurin ta..”

Bata k’arasa ba sakamakon wani zazzafan rankwashi daya sakar mata a tsakiyar kai,

“Ko da wasa naji kin k'ara bud'a kazamin bakin ki kina musanta abunda nafad'a...Hmm! Zaki
sha mamaki na yarinya.”

“Allah ya baka hak’uri.'' Ta fad’a tana kunkuni,

“Karki sake attempting tab’a ni wallahi, Idan kika kara Allah ya isa..” Dariya abunma ya bata,
murmushi kawai tayi kafin tace,

“Ai nima ba 'yar iska bace, saboda Ammi tace, duk macen da take bari namiji yana tab’a ta, to
zatai ciki ta haihu”

Baki Saifullahi ya bud'e yana binta da kallo, shi ba abunda tace bane ke bashi mamaki, No!
Yanayin yadda take motsa bakin tane d'an k'arami dashi awajen, sai yau ya lura tana da wani
irin idanuwa masu fassara abubuwa.

“Ke! shekarar ki nawa ne?”

“15 years” Ta fad'a tana gatsine baki. Murmushi kawai ya yi. Kafin yabar wajen da sauri.

“Allah ya isa na, d'an iska kawai”

Ta fad'a a hankali, barin wajen tayi da sauri bayan ta gyara fuskarta ta waya datake kalla. Tsaye
tasamu Lee tana vid call dasu Hafsat Rano da Fatima Bichi, su basu samu zuwa ba suna can
kano, ko 'yan uwa basuda su a habujan

Gaisawa sukai dasu Hafsat Ranon, kafin subar wajen su shiga filin rawa, lokacin su Ya Marwa
ne aciki suna taka rawa.

Sabuwar shiga Haj Aysa tayi cikin wata rantsattsiyar Laffaya kalar ‘Amber orange’ , tamkar ba
ita ba, domin kwalliyar da akai mata kwarai matuka ta sake bayyana ainihin kyawunta!.

Tuni photographers sukai kanta suka shiga d'aukar hotunan ta, manyan ‘Kawayenta ne ke take
mata baya, tana shiga filin DJ ya canxa waka zuwa ta shaba wacce akewa laqabi da, ‘uwar
gidah ran gidah’

Wayyo zo kuga bak'in ciki awajen mahassada, komawa gefe sukai, suka yi cirko-cirko, kallo
d’aya xakaiwa Haj Karimatu kasan kukan zuci take yi, Yafendo kuwa na fili takeyi a hankali tana
sharewa tsabar hassada da tsantsar kiyayya ko ‘yay’an su dake gidajen aure basu bari sunzo
sunan ba. Sosai Haj Aysa ta shammace su domim basu san haka xatai kyau ba, duk kuwa da
tarin dukiyar da suma suka kashe wajen ganin sun fita kyau amma hakan ya citura.

Hankulan su bai qara tashi ba saida Dr Khaleel ya shiga cikin filin rawar shida abokansa,
kowannen su ya balle hancin naira, sai zubasu suke yi. Nan dai DJ ya sake canza aqalar waka
zuwa ‘perfect ta Ed sheeran’ Wayyo, nan Dr Khaleel ya yage kunya daga zuciyar sa ya bawa
matar sa da ‘yan biyun sa kyakkyawar rungumaa,
MC ya cigaba da zuba kirari, mutane sai ihu suke yi, nan dai aka canza waqa zuwa ganga kura,
mutan bornu 'yan uwan Haj Aysa suka mimmike, kowannen su ya shiga taka rawa yana hura

hanci.

Sum-sum Haj Karimatu ta mike ta baya ta sulale ta arce zuwa sashenta, bata jima ba Yafendo
ta bi bayanta bayan ta zuzzundumawa su Haj Aysa kwandon d'auke albarka a zuciyar ta.

Ganin bata sashen ta, ya sanya yafendon juyawa zuwa b'angaren Inna Bilkisu. Tana tsugun ne
a qasa tana matsar hawaye Inna Bilkisun na bata hak’uri, da alamu dai mutuniyar ku ta kasa
riqe tsantsar hassadar da takewa Haj Aysa na yau, sosai ta shirgawa Inna Bilkisu k'arya.

Inna Bilkisun tana hakimce a doguwar kujera, hannun ta rike da casbaha tana ja, a hankali take
mata magana, kan Karimatun yana qasa,

“Kiyi hak’uri Karimatu, karku sawa kanku damuwa kan hakan, ita ai Allah ke bada ita ko?”

“Kwarai kuwa Inna”

Cewar Yafendo wadda ta zauna daga k'asa, ta shiga yiwa Innan tausar munafunci.

“To kuyi hak’uri kun san dama xa’ai haka, tunda kunga ya jima yana burin samun hakan Allah
bai yadda ba sai yanzu, kuyi hak’uri ku cigaba da addua, Idan kuna da naku rabon sai kuga ya
baku kuma”

Kad’a kai suka yi suna had’a baki wajen fad'ar,

“Hakane Inna, Allah ya yarda.”

Amma fa ba hakan suka so ba, sun so ta ci mutuncin Haj Aysa, ta fadi maganganu marassa
dad’i. Sai dai kash! sam ba haka Inna Bilkisu take ba, domin mutuniyar kwarai ce, wadda tasan
dattaku!

Can wajen 'yan rak'ashewar suna kuwa sai tular rawa suke yi, su Lee sai rawa suke amma cikin
nutsuwa, haka aka watse bayan kowa yayi hoto da mai jego, sannan kowa yaci ya sha sannan
akabi kowannen su da k'atuwar jaka ta rabo, mai d'auke da sunayen 'yan biyun ajiki, tarkace ne
na rabo fal aciki domin harda turmin atamfa, akwai kuma extra leda ta snacks.
Daga nan Haj Aysa ta sake canza shiga zuwa atamfar super wax inda sukai anko da Helwa, red
color ce tasha stone work, sashen Inna Bilkisu suka nufa da masu hoto, suna shiga suka tarar
da su Haj Karimatu da alama suma basu yi tsammanin ganin su ba, domin turus sukai suna
raba idanuwa.
Hakan yai nuni da sun qulla qullalliya kenan a wajan, murmushi kawai Haj Aysa tayi, ta karasa
wajen Inna Bilkisu, Inna Bilkisu dake kishingid'e ta mike tana tafa hannuwa,

“Maraba da masu gidana,..Bismillahin ku” Ta fad'a tana karb'ar Abeed dake faman kallon ta
kamar yasan mai take cewa,

Har dasu Haj Karimatu akai hotuna ransu bai so ba, ganin Inna Bilkisu yasa suka daure suka yi,
amma kallo d’aya xakaiwa hotan kasan ransu bai so ba, domin mai d'aukar hotonma sai
jaddadawa yake yi,

“Hajia ku biyu d'innan ku d'an yi murmushi mana, Yawwa hajiya” Aikuwa ya karbi nashi rabon
hararar, domin Yafendo da xata fita sai data bangaje shi.

“Ikon Allah..” Ya fad'a yana karkad'e rigar sa, domin shi bai masan su din su waye ba.

Haka dai akaita shagali har sati d’aya, kullum sai anyi d'an k'aramin party, a satin ne kuma Safa
ta koma lagos, Hakama 'yan bornu duk sun koma amman banda Yakolo da tace ita kam taga
gidan zama, tunda sun rabu da mijin ta.

Sam su Haj Karimatu basuji dad'in xaman da zatai ba domin duk tayi kanai-kanai akan komai,
ta hana su ai watar da mugun nufin su akan jariran. Idanun ta nakan komai, amma idan tasan
wata ba tasan wata ba. Matan Ya Bala ne basu koma ba sai wani satin saboda ana musu
gyaren gidah. Kuma Inna Bilkisu zata tsaya ayi sa ranar Nusrah ‘yar Yafendo.
***

Satin nayi ya zo da magana marar dad’i, domin gidan su ‘Aliyu’ wanda yake neman auren
Nusrah, sune suka aiko cewar sun janye batun sa rana da aure baki d’aya, domin d'ansu baxai
auri marar mutunci ba, acewar su.

Zo kuga kuka a wajen Yafendo, taita d'ura ashariya tana asiri Haj Aysa da Helwa sukaiwa ‘yarta,
don sunga zata shiga gidan jin dad'i ta dandali arziki shine sukai asiri suka hana. Tai ta hauka
tana birgima.

Aliyu Anas Askira d'an gidan senator Anas Askira ne, shine babban d'a namiji awajen iyayen sa,
domin mahaifiyar sa ce kawai matar Anas Askira, su uku ne sauran biyun duk mata ne. Aliyu ya
had’u da Nusrah ne ta sanadiyyar kanwar sa Hibbah, da sukai school d’aya suka qulla zumunci
mai tsanani, har Aliyu yai sabo da Nusrah, soyayya ta shiga tsakani, suka qulla alqawarin aure.
Amma kash Aliyu matashi ne mai son ace ya tara 'yan mata da yawa, yayin su yake kamar
hular sawa, yasa ya cire, haka yake tayi.

Ta haka ne kuma ya had’u da d'iyar gwamnan bornu, ta fad'a masa baxata iya hak’uri ba, kuma
da aure take son sa dan tuni ta fad'awa mahaifin ta, shi kuwa ganin tilon ‘yar sa na neman
sadaukar da rayuwar ta akan d'an sanatan da ya d'orashi akan kujerar mulki yayi hanxarin kiran
uban Aliyun ya sanar masa komai, jiki na b'ari jin ya masa alqawarin tsayar dashi a d'an takarar
gwamna idan ya sauka.

Hakan kuwa aka yi, ya kira Aliyu ya sanar masa, ko ajikin sa shima ya ji kudi ya amsa da ba
matsala. A take suka kira Dr Khaleel suka sanar dashi su fa sun janye.

Ransa duk ba dad’i ya bawa Yafendo hak’uri, don kowacce uwa baxata tab'a so akawo kud'in
auren ‘yarta ace anfasa ba kuma. Nan dai yabar Karimatu harda kukan munafunci tana ta k'ara
mata famfo kan ai wlh su Haj Aysa da Helwa ne xasu shiga su fita, tunda ai Alhaji Anas Askira
d'an kauyen Askira ne dake Bornu.
Sashen Inna Bilkisu Dr Khaleel ya wuce, zaune ya sameta akan sallaya tana addu’a, a tare
suka shafa yana cewa,

“Ameen Inna”

Sai data babbashi baki akan dangana da rashin mutuncin da su Alhaji Askira sukai masa, ya
kuma bata labarin yaji duk yadda akai har hakan ta faru, gyara xama tayi kafin tace dashi,

“Toh.. Ni kuwa a gani na, mai zai hana a had’a auren Nusrah da SAIFULLAHI...?”








_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER; MISS XOXO_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...*


*NA*


*©NANA HAFSAAT*
*(MISS XOXO)*


*®HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login