Showing 18001 words to 21000 words out of 86718 words
nace na hada auren ki ke Nusrah da Saifullahi, za ku amsa ni ko kuwa sai na
tashi na sharara muku mari?”
Cikin kid’imewa Yafendo ta saki tusa, jikaki ‘siiit’ ga shegen d’oyi, da alama batasan tayi ba,
Karimatu dake kusada ita tai hanxarin rufe hancin ta, tana muskutawa gefe, murya na rawa take
cewa,
“Yaya kayi hak’uri, da..Dama Nuradden ka hada da Nusrah ba saifullahi ba” (saboda Nuradden
ba karamin kudi yake dashi ba)
Sakin baki Ya Bala yayi yana duban ta, Dr Khaleel dake gefe ya wurga mata harara, cikin isa
yake cewa,
“Saboda saifullahi ba shida halin da xai iya rike ‘yarki ko? Wato Amina har yanzu zuciyar ki
baxata cire burin ‘yayanki sai sun auri masu mugun kudi ba ko? Shin wai ke kudin ne da ke? Ko
kuwa Allah ki ke nunawa ba hakan ba? saboda ke you are not contented with what you’ve ko?”
Girgiza kai tayi, ganin yanzun ba ‘karamin aikin sa bane ya bata takardar ragowar sauran saki
biyun ta, cikin muryar ban hak’uri tace,
“Ba haka bane Alhaji, ga ni nai, shi saifullahin kilan yanada wadda yake so ya ke kuma burin
auren ta, wai dan kar a shiga hakkin sa.”
Dogon tsaki Dr Khaleel yaja, kafin yace,
“Woman will you shut your idiotic mouth up, zancen banza, zancen wofi.”
Daga masa hannu Ya Bala yayi alamun ya dakata, saifullahi ya kalla dake wasa da ‘kasan
carpet yakoma yaro.
“Kai saifullahi! Kanada wadda kake burin ka aura? bani sunan ta da sunan ubanta cikin minti
uku.”
Kada kai saifullahi yayi, a farko yayi niyyar cewa Islam. Sai dai yasan ba za’a tab’a bashi ba don
tayi ‘kan-kanta, a raunane yace,
“Babu Baba..Na amince.”
“Allah ya muku albarka..” cewar Ya Bala.
Sandarewa a zaune kawai Nusrah tayi, ba yadda ta iya, kowa yasan babu wani kuma da xata
kawo tace gashi a matsayin wanda zata aura. Nan dai Inna Bilkisu tashiga yi musu nasiha mai
ratsa jiki, kowa ya yi shiru yana ji, ta qarqare da muhimmancin zumunci, bangaren Haj
Nabeelah itama bataso saifullahi zai auri Nusrah ba. Tafi masa sha’awar y’ar kanwar ta mai
suna Nazneen.
Kamar yara haka Ya Bala ya tasa su Kamaluddeen, kan lalle a yau ba sai gobe ba zasu fara
fuskantar junan su, yabawa kowanne inda zasu keb’e suyi hira, takaici kamar su had’iyi zucia.
Nan parlorn akabar Nusrah da Saifullahi dake faman kukkumbure fuska, gaba d’aya idan ya
kalli surar jikin ta wani tu’ku’kun bakin ciki yake ji, tana daga kan kujera tana latse latsen wayar
hannun ta, shi kuma yana kujerar dinning ya zuba mata idanu.
Taqamaimai yarasa mai yasa aka zab’a masa Nusrah, shi wallahi dama su Shema’u aka bashi,
dan ba laifi sunada kira mai kyau, tsaki yasake ja akaro na ba adadi yana naushin kujerar kusa
dashi tamkar ita tai mai lefi. Dagowa tayi ta dubeshi ba laifi,
“He’s handsome” tafada ahankali,
“Ke me kikace?”
Shiru tayi masa, dan bazata lamunci raini ba, sake kiranta yai da sunan ta,
“Suna na ne, ya akai?”
Zabga mata harara yayi, kafin yatashi ya koma kusa da ita, yana sake kare mata kallo, ya lura
tanada yalwataccen gashin kai dana gira, tanada kyau sosai, amma batada siffar da yake so.
Cikin isa yace,
“Naga alama kece kikai yadda kikai, ki ka cewa su baba kina sona, Toh ki sani ni wallahi bana
sonki,”
Nuna kanta tayi tana wani fari da ido,
“Ni, Barr Nusrah Khaleel, na zubda class dina nace Ina sonka, for what,? How and why?, kaga
baka cikin jerin mazan da na keso wallahi, kuma bazan taba son kaba ko maza zasu ‘kare”
Tana ‘karasa maganar da take, ta mike tai ficewarta tana sakin tsaki, bin bayan ta yai da kallo,
“Sam ba shape..” ya furta yana dafe kansa, tuni siffar Islam tashiga yi masa yawo akai, a
kasalance ya furta,
“Ya Allah..”
_jama’a atayani da addua pls, wallahi banda lapia, gashi banason tsayar da typing dinnan, mun
rigada mun fara shi, pls Include me in ur prayers, love u all fisabilillahi_
_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_
*_NA*_
_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_
® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_
*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_
*TUKWICI NE GARE KU:*
*YA HAJJAH CE*
*BILLYN ABDUL*
*_SHAFI NA 17-18_*
_Wannan shafin na kine *AUNTY MAIJIDDAH MUSA* hak'ika kina baiwa duniyar marubuta
shawarwari ta fannoni daban-daban, babu abunda zamu ce sai fatan Allah ya saka miki da
alkhairi, ya biya miki buk'atunki, Allah ya raya ‘*yan biyu*, ya kare ki daga sharrin mugun mutum
dana aljan_
_nanahafsat.wordpress.com_
*’Ya’yan* Hansa’u, su Kabeer (Kb), Ibrahim kuwa dad’i kashe su ganin su ba’a bada su sadakar
auren dolen ba, duk da sud’in ba sukai shekarun su Saifullahi ba, dan ko Kabeer babban cikin
su bai wuce talatin ba dan dakyar idan ma yakai.
Fita Nusrah tayi fuuuu daga cikin parlourn kamar zata tashi sama, bata tsaya ko’ina ba sai
sashen su, d'akin ta tashiga tana banko k'ofa da k'arfi tamkar itace tayi mata laifin, Yafendo
dake kan kujera tana waya ta juya tana kallon ta kafin tace,
“Ke kuma keda wa?” K'unk'uni tafara yi tana yatsina fuska tace.
“Da kaina nake Umma”
“To fito nan dan uban ki.”
Fitowa tai tana zumburo baki ta zauna a gefan kujera tana hararar tv, tab'e baki Yafendo tayi
cikin fusata tace,
“To badai ni nakar zomon ba sakarya kawai”
Juya kai gefe Nusrah tayi tana ci gaba da k'unk'uni, Yafendo ta d'ad’a mata duka a baya, saurin
matsawa Nusrah tayi tana soshe-soshe kafin ta fara shasshekar kuka,
“Ummah duka na fa ki kai, Me nayi miki ne Umma?”
“Ubanki ki kai min, fitsarar banza da sai ni da kika raina, Kina ganin an cuci rayuwar ki
maimakwan ki fetsare ki ce ke baki yadda da auren saifullahi ba a'a sai kika yi shiru banza
makwad'aiciyar wofi.”
Tab'e baki Nusrah tayi tana k'ara cuno shi cikin fushi tace,
“Ummah ya xanyi wai? Kina ganin kowa bai turje ba sai ni? Ummah idan na nuna bana so ke
xa’a kara tsana a gidan nan, haka d'azun naji kunya da kikai....”
Sai kuma tayi shiru, nan Yafendo ta gano akan tusar datai d’axu ne domin Karimatu ma har text
tayo mata wai girma ya fad’i. Cike da rashin damuwa Yafendo tace,
“Dallah rufemin baki zaki fara yi min wani kame-kame, dan ubanki tusa ce kowa yana yi, kuma
wadda nai d’axu ta bak'in ciki ce domin a kid'ime nake..”
Shiru Nusrah tayi bata sake cewa komai ba sai Yafendo ce keta mitar ta, tana shirga k'aryar
hawan jinin da take dashi idan xai tashi ta tusa yake farawa. Ta karkare da cewa,
“Kuma ni bazan yadda da wannan auren naki da wani Saifullahi ba ehe, Zaki zama barrister xan
wani d'auke ki na bashi yana k'aramin lecturer? ke nifa nak'i jinin masu aiki a makarantu, indai
ba head of department da professors ko doctors and chief of staffs ba, Toh duk sauran
marowata ne, basu da aiki sai lissafin banxa da wofi, suna fama da turancin banza..” Ta karasa
fad'a tana sakin wani dogon tsaki.
Dai-dai lokacin Dr Khaleel ya shiga parlorn, gaba d’aya Yafendo sai ta rud'e tana faman
gyare-gyaren center table, murmushi yayi duk da bai ji farkon zancen ba yasan baxai wuce
mitar had’a auren 'yarta da saifullahi ba, ganin haka ya sanya Nusrah fecewa tabar su,
Kallon-kallo suka shiga yiwa juna, rantsuwa ta fara jerawa tana fad’in,
“Alhaji kar ka d'auka da saifullahi nake, a'a wallahi wani film muke gani na lecturers shine nake
bata labari..”
Kad’a kai yayi yana d'aga kafada. Takardar hannun sa ya ajiye akan takarda yafara rubutu,
ganin haka yasanya Yafendo durqusawa a gabansa tana rokansa,
“Wallahi tallahi bazan sake ba, a yau ma a d'aura musu auran ba sai nan gaba ba, dan Allah ka
gafarceni Alhaji, wabillahil lazi baxan iya rayuwar rugar mu ba na...”
Bata k’arasa ba sakamakon mika mata takardar da yayi yasa kai yai ficewar sa, zunduma ihu ta
farayi, a haka Hidaya da Nusrah suka sameta, ba’asi suka nema ta gaya musu tana dukunkune
takardar, taya ta kukan suka shiga yi a haka Karimatu ta shigo ta same su,
Hannunta rike da wayarta tana taunar chingum, Yafendo ta rarrafo tana sanar mata sakin da yai
mata, tsaki ta saki tana gyara xaman ta a kujera,
“Yaya wallahi ya sake ni” cewar Yafendo tana matsar hawaye.
“Mugani saki na wa ne?”
Mik'amata takardar tai tana sake k'ara sautin kukan ta, dogon tsaki Karimatu taja tana wullawa
Nusrah takardar, mikewa tayi kafin tace dasu,
“Yafendo ki girma wallahi, haka d’axu kika hau tusa agaban ahalin gidan nan, baki daddara ba
yanxu kin saki baki kina kuka kega wacca aka sanarwa ranar mutuwar ta, kidena yanke
hukuncin da baki da tabbas a kai kunata faman kuka bankad'add'u kawai, Idan kingama kukan
sai kizo Inna na neman mu, banda ke da abin ki d’axu ma sai dana miki message, Nace ki
kwantar da hankalin ki aure dole muyi me yiwuwa a fasa shi, ta karkashin kasa, amma wani
lokacin kamar mai toshewar basira wallahi, ku cigaba da kukan idan ya dawo ya miki na gasken
ke kika sani” ficewa tayi tana tana jan dogon tsaki.
Karanta takardar Nusrah tayi inda ya rubuta,
“Ki duba d'akin ki ko nabar littafin ‘sociological physiology of human Milieu d'ina”
Girgiza kai Nusrah tayi tana mikawa Hidaya takardar, duban Yafendo tayi wadda tai tsuru-tsuru,
“Ummah ni gaskia I cant stand these Haba! Ace wai kishiya ta zauna tana gaya maki
maganganu kamar wadda ta haifeki, nifa shi yasa ki kaga baxan tab'a shiri da ita ba wallahi, I’m
a lawyer by profession nasan duk wani tactics wallahi na mutum. Umma learn to stand on ur
own, dan Allah ki..”
Shiru tai sakamakon jefa mata throw pillow da Yafendo tayi, da yatsa ta shiga nuna ta,
“Uhm...uhm Nusrah yanzun sai na tashi na lallasa ki wallahi, bar ganin ina kyaleki kwana biyu,
saboda haka kibi a hankali sarai kinsan hali na dai,”
Fuu Nusrah ta haye sama Hidaya ta mik'awa Yafendo takardar tana daria, karantawa tayi tana
sauke ajiyar zucia. Bin k'afar benen da Nusrah tabi tayi da harara, Shi yasa sam tafi son
Hidaya, saboda itace ta d'akko halinta amma Nusrah kafiya ce da ita gashi basa jituwa da
Karimatu.
Shirye shryen biki a keyi gaba d’aya Ya Bala da matan sa sati d’aya suka koma sukai a lagos
suka dawo da uban kayan lefe na kece rai ni, kaya sunyi tubarkAllah, babu abinda babu komai
yaji acan-acan.
Sati uku aka saka tsakiyar farkon wata mai kamawa, wani uban sun lace safa ta fito dashi na
anko daga lagos, kowa fa shirin biki yake yi musanman Islam da take jin mugun dad’in
sanadiyyar barin gidan da Saifullahi xai yi, yana lura da ita sai dai sam baya ta tata. Cikin
kwanakin duk ya xagwanye yasa damuwa a cikin ransa.
***
Watan biki na kamawa farkon sa, Dr Khaleel yaje ‘BNA’ karbo sakamakon su Islam.. Hidaya
tana nan a Art d'inta ba’a canza ba, sai dai grade dinta yayi k'asa sosai, Islam ma successfully
tayi passing exams d'inta ciki harda tarin prizes da aka bata, Hafsat kuma an mayar da ita Art
class, ciki harda canzen hostel zuwa na ‘yan art students.
Wannan labari bai yiwa Hidaya dadci ba, musanman da taci alwashin snatching d'in Hilal, sai
gashi ma anyi mai gaba d’aya an komar da ita class d'insu harda hostel ma,
Islam kuwa taji dad'in barin Hafsat hostel d'insu dan zata sarara abinta yanzu, Hafsat tasha
kuka dan taci burin zama medical student itama, ta samu Daddy tana masa magiyar ya canxa
mata school, tashin farko ya rufe ta da fad'a, dan da kyar yasha kan malaman ma da repeating
xasu yi mata, so far result d'inta shine worst kaf class din.
Yafendo da Karimatu sun ci alwashin kashe auran Nusrah da saifullahi nan bada jimawa ba, Ita
dai Nusrah ta hakura ne kawai Musanman ranar da aka rantsar dasu suka xama cikakkun
baristoci, a ranar Dr Khaleel ya siya mata galleliyar mota had'e da nemar mata gurbi a chamber
d'in abokin sa, ‘chief judge Aminu Aminu’.
Da wannan ta kuma kwantar da hankalin ta, amma ta d'auki wani babban alwashi a cikin ranta,
wanda saifullahi sai yayi dana sanin bak'ak'en maganganun da kullum yake yarfa mata.
Rankatakaf dangi sun had'u na 'yar gaya, a halin su Haj Nabeelah da Yafendo, kai kowa
danginsa yazo daga ko’ina na jiki-jiki, dan rock-view hotel dake kusa da gidan Dr Khaleel shi
aka kamawa baki suka sauka a ciki. Rantsattsiyar rana d’aya dal aka sanya domin yin ‘mothers
eve’ kawai, kafin nan ne Nusrah da k'awayenta suka shirya d'an k'aramin event d'insu na ‘bridal
tea party da barbecue night’ kuma Dr Khaleel ya nemi alfarmar had'a d'aurin auren rana d’aya a
kuma wuri d’aya, sakamakon idan ance ko’ina sai an kakkai su an d'aura mutane xasu wahala.
Ranar Asabar 15 ga watan junairu, dai-dai misaliin karfe goma sha biyu da rabi na rana aka
d'aura aure angwayen da amaren a masallacin ‘central mosque’ dake Abuja akan sadaki mafi
k'aranci mai kuma albarka.
Mudasser da amaryar sa ‘Rama’, sai Mu’utaseer da sahibar tasa, ‘Miss Hafsy’, kamaludden da
‘Aysha sholey’, sai Shamsudden da ‘Shamie baby’ daga k’arshe aka d'aura auren Saifullahi da
‘Barr Nusrah’, Abun ba’a cewa komai sai sam barka kawai.
Anyi wasa da nairori bugun abuja sun sha dandala, fad'a muku yanayin yadda akai shagalin
bikin b'ata lokaci ne, babu hayaniya masha Allahu anyi komai an k'ar lafiya gaskia saboda anyi
addu’oi an sauke qur’ani yafi a kirga, duk dan ayi lapia. Estate guda mai gidaje goma aciki
mallakin Dr Khaleel, shi ya baiwa kowan ne ango d’aya a ciki kuma kyauta a cewarsa tasa
gudanmawar kenan. Anan unguwar maitama dake ‘Ganges street’.
A daren ranar angwaye masu kukan bakin cikin an ba dasu sadaka babu wanda bai raya
sunnar manzo (SAW) ba, sun gwangwaje kwarai matuka sun dandali sadakin su, banda
Saifullahi da Nusrah tace sam bata san zance ba wallahi sabida yace ita ba kalarsa bace.
Yayi nacin yayi magiyar ta barshi shima ya samu nutsuwa sabida sunsha magunguna amman
sam taki, daya isheta ma mik'ewa tayi tana murmushin takaici,
“Lalle Ya Saifu, kamanta yadda kake siffanta ni? Karka manta babu irin bakaken maganganun
da baka fad'a min kana kushe min halittar da Allah ya yoni da ita, ba kuma wai dan baya so na
bane yayi ni a haka, wallahi kaji rantsuwar 'yar musulmai baxan baka kai na ba, na baka dama
ka auro duk wadda kaga dama ka fanshe takaicina akanta amman ba dai ni ba”
Ta karasa fad'a tana sakin tsaki, bayan ta d'auki pillow tai wucewarta d'akin sama abun ta ta
barshi a tsaye yaxama mutum mutumi cike da mamaki.
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un”
Shine kalmar da saifullahi yake ta ambata yana dafe da kansa, Idanuwan sa sunyi micin-micin
dasu sunyi jawur, mutumin ku dai kamar xai kashe kansa dan tsabar yadda sha’awa take motsa
mishi, hannu a dafe kan marar sa ya shiga band'aki da kyar ya iya d'aura alwala ya fito ya tada
sallah, yi kawai yake sam ba nutsuwa a tare dashi.
_Dankari wannan shine ga k'oshi ga kwanan yunwa... Asubah ta gari saiful_Nusrah._
****
Bayan wata biyu lokacin komawar su Islam yayi shirye-shrye suke tayi, amare da angwaye
kowan ne yana gidan sa cikin kwanciyar hankali amman banda b'anqaren su Saifullahi, kullum
dai Nusrah xata dafa abinci ta gyare ko’ina har ta fara aiki, sam auratayya bata tab'a shiga
tsakanin su ba, Idan ka ganshi sai kace wanda ya shekara yana ciwo, sam bai da kwanciyar
hankali.
Da haka su Islam suka koma school zucjyarta duk ba dad'i musanman da 'yan biyu suka fara
girma suna cikin watan su na uku, gasa 'yan duma-dumai dasu abin gwanin ban sha’awa.
Yakolo kuwa ta kasa ta tsare babu mai d'aukar su face ta yarda da kai domin karfi da yaji ta
koma commander 'yar tsaro. Ko bacci ishasshe batayi sabida tasan tuggun su Yafendo da
karimatu.
*B N A*
‘SS2 Atomic’, shine class dinsu Islam. While ‘SS2 eagles’ nasu Hafsat da Hidaya ita Hafsat sai
taga har gwara data dawo Art d'inma, duba da yanzun hostle d'insu dana su Hilal babu nisa
tsakanin su, a class kuwa suna can karshen seat shi da ita suna abinda suka saba. Hidaya duk
tabi ta ramar da kanta, a yau kuma taci alwashin tarar Hilal tagaya masa yadda sonsa yake
kwarara a magudanar jinin ta.
Zaune ta hango shi yana rike da littafi a hannusa, lokaci zuwa lokaci yana lashi lips d’insa na
k'asa, gangar jikinta sai tursasata take taje garesa, ai kuwa tafara cat-walking har ta isa gaban
sa, d'agowa yai yana duban ta tun daga kan covered shoe d'inta zuwa kan k'irjin ta, sake lasar
lips d’insa yai, murmushi tayi kafin tace dashi
“Hello Handsome.....!”
_Nagode da addu’oin ku gare ni,jiki da sauki Alhamdulillahi! Ga masu nema daga farko ga
grp nan via link zaku samu daga shafi na farko zuwa inda muka tsaya. Love you all
fisabilillahi_
Ga grp link din; https://chat.whatsapp.com/FCICopl029LGkPU2TmA5ov
_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *SAIFUL_ISLAM...*