Showing 36001 words to 39000 words out of 86718 words
sa duka biyu dafe da kuncinan sa,
idanuwan sa kuwa, zubar da hawayen bakin ciki suke yi, abun tausayi. Kallo d’aya zakai masa,
ka tabbatar yana cikin babbar damuwa. Rasa yadda xai yi yayi, cikin hanzari ya ‘dakko paper da
biro yana k’ok’arin rubutawa kowaccen su saki. Wata zuciar tace masa,
“Rubuta musu uku-uku kawai, hakan shine dai-dai”
Gyada kai yayi, alamun ya aminta da yadda zuciyar tashi tabashi shawara. Yana cikin rubutawa
dayar zuciyar tace,
“Uhm-uhm Khaleel, kakka soma yanke ‘danyen hukunci irin wannan, kanada magabata fa, shin
xasu ji dadi idan suka ga ka tsallakesu kayi gamon kanka?”
Jefar da takardar yayi yana lumshe idanu, zafafan hawaye masu ‘dumi ne ke faman raito daga
idanun sa, cikin murya gwanin ban tausayi yace,
“Hasbuna-Allahu wa ni’imal wakeel”
Haka ya dinga maimaitawa, kafin ya samu nutsuwa, mikewa yayi ya shiga band’aki, ya dad’e
aciki kafin yafito ya canxa kaya, sallar nafilfili yayi. Ya jima yana zaune yana addua . Kafin ya
mike ya ‘dauki wayar sa dakekan dressing mirror.
Kiran Ya Bala yayi, Kan idan babu damuwa, yanason ganin su gobe, tareda Inna Bilkisu, domin
bayason yanke ‘danye hukunci. Ganin bai sanar masa ko akan me bane, hakan yasanya Ya
Bala jaddada masa, lalle yayi hak’uri, ya samu qur’ani ya karanta ko yasamu nutsuwa. Jirgin
safe zasu biyo da yardar Allah.. Bayan yagama wayar jiki ba dad’i ya koma bakin gado ya
zauna, Qur’ani ya ‘dakko ya karanta, har saida yaji nutsuwa kafin ya tashi, ranar ko takan direba
dake tambayar ina xai kai shi baibi ba. Da ‘kafa ya taka har gidan sa, dasu Haj Aysaa ke ciki.
Domin dama shidin ba gwanin zuwa majalisa bane, kullum yana school yana research, ko yana
gidah cikin iyalinsa. Jefi-Jefi ne yakan zagaya wajen abokansa su d’an tab’a hira. Saboda
bashida wani lokacin kansa, kullum hidimar iyalinsa ce da ta ‘yan uwa, sai ta ‘dalibansa da
ma’aikatan sa, da jama’a masu nemon temako.
Karimatu da Yafendo kuwa duk sun zauce, Yafendo sai sakin Iska takeyi, minti kad’an kaji ‘bot’
‘bobot’ ‘siit ‘ ‘sirrr’ . Yanzu ma ji kake ‘birrr’ takai-kaice ta sauta, cikin hanzari Karimatu ta rufe
hancinta tana hararar Yafendo kafin tace,
“Kede kamar sabuwar tab’i wallahi, Haba Yafendo, kin saki ‘duwawu kina sakin tusa, idan anyi
magana kice kin ‘dimauce ne, ko jinin ki ne ya fara hawa. Gaskia ba zata sab’uba. Haba sai
kace mai ‘duwawun iska, minti kad’an ki saketa kamar wani abun arziki, bazai yiwuba wallahi,
haka kawai ba zaki rud’an ciki ba, gata da shegen wari kamar shekararren mushe, Tashi ki fita
gaskia, ki koma ‘bangaren ki.”
Yafendo tashiga girgiza kai, tana riko ‘kafar Karimatu, cikin tashin hankali tace.
“Yaya wallahi bazan iya komawa rugar mu ba, Allah idan Alhaji ya sake mu bazan iya rayuwar
can ba, na saba da jar miya anan, ga Ac tana gyaramin jiki, inci abunda naga dama, nai yadda
nake so anan, wallahi acan Bappah Ardo bayan ya sani tatso nonon shanu, Allah harda talla zai
sa nayi da su ‘kanwar ‘kanwata joda, a kasuwar birnin-jimeta, ba...”
Bata k’arasa ba Karimatu ta shure hannuwan ta, tana banka mata harara. Kafin tace,
“Bakida aiki sai zancen Baffah kaza, Haba ki kyaleni mana, da wanne zanji uhm? Da sakin
daze mana ko kuwa da rayuwar ‘yata dake hannun sa’an ubanta?! kishiya na yadda taga dama
da ita? Kamar Hafsa ace itace ke ‘dora girki a babbar tukunya, tana wanki, tana aikatuwa kamar
‘yar aiki? Yarinya ta data taso cikin gata? Komi yi mata akeyi, batasan babu ba, amma tsabar
rashin imani Alhaji ya ‘dauke yarinyar nan ya bada ita ga wanda bashida tausayi. Idan har zan
bar gidan nan to sai da Hafsa da takardar sakin ta a hannun ta. Wallahi ba zai yiwu ba. Ai Allah
ya shiwa Furera albarka da ta sanar da ni ‘kuntacciyar rayuwar da Hafsat ke ciki, shiyasa Alhaji
yace kar muje gidajen su, ashe yasan abunda yayi. (Furera! Y’ar leken asirin su ce dake kano,
itake kawo rahotan gidajen su Hafsa da Hidaya)
Yafendo taja majina tana matse hawayen ta,
“Hakane Yaya, amma mu fara kashe wutar gabanmu tukun na.” Cewar Yafendo, Wacce gaba
d’aya jikinta yayi la’sar, tsantsar tashin hankali ta bayyana a tattare da ita.
Tsaki Karimatu taja, tana ‘kara wurgawa Yafendo mugun kallo, kafin tace,
“Ke kam zuciyar ki kamar kare ya cinye, Toh banda ke da abun ki duk wanda yai rik’o da Malam
na dotsa ai aikin sa kamar yankan wuk’a ne, ki kwantar da hankalin ki, domin yanzu zan kirashi
na sanar dashi cewar yayi yadda xaiyi a rufe bakin Alhaji, sannan ya shafe wannan zancen
dayaji a kunnuwan sa yanzu, ya sanya masa fushin wani abun daban, kafin safiya ya manta. Na
miki alqawarin iya damuwar su Hafsat kawai zamu saka aranmu, yadda xamu ‘bullowa lamarin
su yanzu shine agaban mu, ga garin magani nasa Furera ta karb’a, yadda zata barbad’a
shegun su tsallaka shine aiki, don tace kullum gidan arufe yake,”
Ajiyar zuciya Yafendo ta saki, kwarai tafara na’am da zancen Karimatu. Sai data kurbi ruwan
dake gefanta kafin tace,
“Wallahi Yaya maganar yaran nan na damuna, hakika suna cikin *MATSALAR RAYUWA* (littafi
na) . Kamar wa’enda akai *AUREN BASHI* ( littafi na)dasu? Wallahi na ‘dauka Alhaji acikin
‘ya’yan Yaya (Ya Bala) ko Ya Hansa’u, zai samu wani ya dubi *SO KO SHAKUWA?* (littafi na)
dake tsakanin su ya aurar dasu.”
K’wafa Karimatu tayi, tana faman jijjiga ‘kafa, cikin isa tace,
“Yo ai gani yakeyi idan ya bar su sun zabi *SON RAN* su, akwai matsala, shiysa ya basu
sa’annin sa a matsayin *ZAB’IN IYAYE*, (littafi na (SON RAI KO ZAB’IN IYAYE?), kuma Allah
sai yayi mana hisabi dashi, tunda muma munada iko akansu, namiji hankaka gabansa fari
bayan sa bak’i, banda butulci irin na d’a namiji, mu sha wahalar rainon cikin yaran, mu haife su,
mu shayar dasu, kafin wahalar yayen su, amma rana d’aya ka ‘dauki babban mataki, har ka
yanke ‘kazamin hukunci haka, ai wallahi Yafendo tunda ga *RAYUWAR MARYAM* (littafi na)
‘din gidan mu, na tabbatar da maza mugaye ne. Amma humm! Idan yasan wata bai san wata ba
ai.”
Yafendo ce tashiga bata baki, tamkar marok’iya, kai idan ka gansu tashi d’aya, zaka ‘dauka mai
gidan ce da y’ar aikin ta, domin Karimatu na hakimce akan doguwar kujera, Yafendo kuma na
‘kasanta a tsakure. Wai nan kishiya da kishiya ne, kuma ta uku data biyu. Sam ba tsari.
Dr Khaleel kuwa yana gidan su Haj Aysa, wannan karan duk zurfin cikin sa, ya kasa b’oye mata
damuwar sa, tashin farko data tambayeshi menene? Ya xaiyane mata komai, hak’uri tashiga
bashi, kan kada yai saurin yanke hukunci dan Allah, tareda ‘doriyar shai’danne kawai ke
‘dawainiya dasu, ta ‘karkare da,
“Komai nisan dare, gari zai waye, wallahi Allah, xai bayyana mai gaskia Alhaji. Kama dena
damun kanka , Insha Allahu babu abunda zai faru da ni ko zuriyata. Allah yai mana katangar
‘karfe da shed’an domin a har kullum babban burin sa shine, ya sanya bil adama aikin sabon da
Allah zaiyi fushi dasu, shiysa Allah yace mu nemi tsari daga garesa, Saboda sharrin shed’an
la’ananne. Kayi hak’uri Ibrahim-Khalellullah. Iya sani na da kai, kai d’in jarumi ne, baka sanya
damuwa a zuciyar ka, kakka wani damu first love, Ungo ruwan sanyi, sha ko kaji sanyi a
ranka..”
Tunda take magana yake jin wata nutsuwa da kwanciyar hankali acikin ransa, gaba d’aya idan
yana tare da ita baida lokacin kowa da komai, tun suna saurayi da budurwa har kamawa yau ,
bata taba sab’a masa ba, sai dai abunda ba’a rasa ba na yau da kullum, domin tsakanin harshe
da hak’ori ma ana sab’awa ballantana mata da miji.
‘Dagowa yai yana dubanta, cikin tacacciyar ‘kauna marar gauraye, hannun sa yasa ya kamo
nata yana murzawa, ahankali yafara mata magana cikin rad’a-rad’a.
“Nagode uwargida na, hakika kin zamto haske da ke mamaye dukkan duhuna, kece
tauraruwata cikin taurari, Allah ya saka miki da alkhairi. Dan Allah har abada kakki rabu dani,
domin zan iya shiga ‘kuncin rayuwa.”
Kanta akasa take murmushi,
“Amin Alhaji..”
Duban hannuwanta yake, yana ‘kara shafa yatsun hannun. Cikin kasalalliyar murya yace,
“Waya miki lalle? Yayi kyau, ya miki kyau Aysaana”
“Yakolo ce”
“Ah dole nayi mata kyauta, mutumin ta kuwa yace cikin watan nan yakeso ta tare fa.”
“Haba?”
“Wallahi, ai ya mato da yawa, gaskia ta biyani dole na biya tukwicin lallen nan, amma kafin nan
kema taso na baki naki tukwicin”
Tasan me yake nufi, shiysa cikin sauri tayi ‘daki tana murmushi...
*LAGOS*
(IDIROKO,MARYLAND, 12b)
Zaune suke a parlor, Uncle Faruk, Haj Zuwaira, Fatima, da Khaled. Plate ne shak’e da fruits
akan center table. Kowanne da toothpick a hannun sa yana ‘dakkowa yana ci. Hira suke sosai,
suna shewa cike da farin ciki, nan hira tayi hira, aka ‘dakko zancen auta Saifullah.
Uncle Faruk yace,
“Ni kuwa Khaled, kuna waya da mutumin naka kuwa?”
Khaled ya ajiye zucia yana murmusawa, cikin shafa ‘keyar sa yace,
“Uncle muna ‘dan tab’awa, kasan saifullah ‘dinne sai a slow. Sai ya gindaya wasu
sharad’od’i...”
Kafin ya gama fada, Fatima dake gefe ta amshe da,
“Yanada time din bacci, karatu, gym (walkout), da kuma family time.”
“Ah, excellent! Wallahi haka yake fada Uncle, jia dana kirashi, ca yai na dinga duba timezone
din tukunna, Wai time din ball d’insa ne, kaji fa Uncle. Kamar ni banda abun yi.”
Uncle Faruk ya shiga ‘babbaka daria ba ‘kakkautawa, Haj Zuwaira dake gefe ta dan’kawa
Fatima da Khaled dak’uwa tana,
“Ungo nan! Haba. A kyale auta ne dan Allah, Naga kowa yanada tsarin sa a rayuwa, ku
godewa Allah ma da yakeda family time dinku.”
Khaled dake gefe ya kyalkyale da daria, yana cewa.
“Kai Aunty! Shi fa nashi abun yayi yawa, idan ka kira shi fa cikin wannan shagwababbiyar
muryar tashi, xaki ji yana cewa,uhum ina ji, kayi sauri pls akwai abunda zanyi.” Ya fad’i hakan,
yana mai gwada muryar saifullah.
Haka dai su kai ta hirarrakin su, gwanin ban sha’awa, suna ‘kara tsara yadda bikin Fatima zai
kasance. Don dama wanda zata aura take jira ya dawo daga Russia, inda ya zama
anesthesiologists’. To yanzu ya dawo, dama an gama komai, kawai biki za’a gwangwaje dashi.
*IDIROKO 17b*
Riri ce zaune da Islam a parlor suna kallon wani show na ‘Grey’s Anatomy ’. Gaba d’aya Islam
ce ma ta maida hankali tana kallon, saboda sosai show din yake ‘kara mata *WANI HASKE*
dake tattare da ‘bangaren medicine. Ya Bala ne ya kira Islam a waya kan taje suyi sallama, don
su zasu je Abuja, kuma zasu kwana biyu ko uku,
“Babu wata matsala dai ko Islam?” Cewar Ya Bala.
“Babu Uncle B.”
“Toh ba abunda kike buk’ata kafin dawowar mu?”
Nanma ta gyad’a kai alamun babu. Bundle ‘din yan ‘dari biyar guda ya ciro ya mika mata, k’in
karba tayi tana cewa,
“Aa Uncle B. Wallahi bana buk’atan komi, kudin daka bani wancen week dinma sunanan, sun
isheni haka Uncle B.”
Murmushi yayi, kafin yace.
“Toh shikenan, Allah ya miki albarka.”
“Ameen Uncle B.”
Sallama tayiwa Inna Bilkisu, suka rangad’a duka airport harda Riri, sannan suka koma hanyar
gidah. Tun a hanya Riri ke jaddadawa driver, ya sauketa a KFCJ(Kentucky Fried Chicken Joint).
Islam tayi k’ok’arin hanata, Sam Riri ta nuna batasan zance ba. Hakan kuwa akai, suna
sauketa, suka koma gidah. D’aki Islam ta wuce ta zauna. Gaba d’aya ji take ba dadi, ba wajen
zuwa, friends dinta duk a Abuja suke, kad’anne ‘yan Lagos. Kuma bawani shiri suke ba, wayar
ta ta janyo sabuwa dal, wadda Ya Bala ya siya mata. Numbers din siblings dinta ne kawai aciki
sai na friends, Sam bata social media activities ko d’aya, dan babu applications ma. Kiran Lee
tayi suka gaysa, wadda itama ke kaduna taje hutu, sun ‘dan tab’a hira, takira Fatima Bichi. Inda
Zaran take sheda mata ai ankawo kudin auren ta, nan bada wani jimawa ba za’a sha shagali.
Daganan ta katse ta kira Hafsat Rano, ringing biyu ta ‘dauka. A speaker Islam tasaka wayar,
tana gyara kwanciyar da tai akan kujera..
“Hello Lam-Lam!” Cewar Hafsat Rano cikin zak’uwa.
“Na’am future biologist. Ya kike?” Islam tafada tana mai rage volume na TV.
“K’alau fa, ya Lagos. Hope kinyi new catch?! Ki tabbatar kin samo mana Lagosian breed.”
Daria Islam ta kyalkyale da ita, kafin tace.
“Ku kam yaran nan kun shiga uku da harkar maza, ni rabu dani da wasu samarin Lagos, ‘dan
Abuja zan samu.”
“Toh Allah ya kawo Lam-Lam. Ke ‘dince tsoron maza kikeyi, shiysa ma kilan suke shakkar miki
magana.”
“Ko?”
“Kwarai kuwa, That aside, ke na kusa aure fa”
“Dan Allah dagske?” islam tafada, cike da farin ciki .
“Wallahi na kusa..Ba nagaya miki dana dawo na fara sana’ar wainar fulawa (flour) ba?” (Littafi
na, (RANO MAI WAINAR FULAWA)
“Yeah! Haka kika fad’a. What about it?”
“Toh yazo siyan wainar ne, ya ganni, irin love at first sight ‘dinnan, sunan sa Nasser wallahi”
“Ah.. Masha Allahu! Congratulations babe. So karatun fa, yanzu ya xakiyi kenan?”
“Zanyi Insha Allahu a gidan sa, ai Kinsan biology ne, a nan BUK zanyi”
“Oh yeah hakane. That’s nice wallahi, I’m happy for you. Allah yasanya alkhairi babe.”
“Ameen Lam-Lam. Allah ya kaimu naku, idan anfito da ashoebi xan turo miki, ki bude
WhatsApp pls.”
“Ameen ya Rabb. Okay babe. I will soon. Insha Allahu!”
Hira suka ‘danyi kafin Islam ta katse wayar,ajiye ta tayi a gefe, tana tunani gashi har mutum biyu
a a set dinsu xasu yi wani auren. Plus Lee ma anytime soon kila za’ai nata. Dafe kanta tayi,
dake barazanar fad’o mata, cikin murya mai d’auke da damuwa ta furta,
“Subahan’Allah! Ya Azeezu sa’adneey min kullu Amr.”
*ABUJA*
Gaba d’aya sun hallara a babban parlorn Dr. Khaleel, Ya Bala, Inna Bilkisu, Dr Khaleel, Haj
Karimatu da Haj Aysa... Inna Bilkisu na hakimce a doguwar kujera, Ya Bala da Dr Khaleel na
gefan ta a ‘kasa, domin basa iya zama a kan kujera idan har tana kai. Can gefe d’aya kuma
Karimatu ne da Yafendo a rakub’e, sai raba idanuwa suke yi munafukai. Gyaren murya Ya Bala
yayi yana.....
***
_Love is patient love is kind it does not envy it does not boast its not proud it does not dishonor
others,it is not self seeking,it is not easily angered it keeps no record of wrongs,Love does not
delight in evil but rejoice with the truth,it always protects,always trusts,always hopes,always
perseveres_ #SAIFUL_ISLAM 2k19.
_Assalamu Alaykum dearies Thank you so much for the love and care, The calls, messages,
WhatsApp dm, Wordpress site, on and on and on. Wallahi I deeply appreciate itDa sauki
sosai, Nagode for the warming prayers it means a lot to me wallahi. With out you guys I wud be
fish food I knw. Álà bárgà njó love y'll fisabilillahi . Have a blessed weekend
ahead._
_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_
*_NA*_
_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_
® *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
(_Home of experts and perfects writers)_
*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_
*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_
_BILLYN ABDUL_
*_SHAFI NA 30-31_*
_Shafin yau na ki ne FATMA_ZARAH (BICHI)Fatan alkhairi a gare ki, dangin agalawaAllah
ya baki miji nagari, kyakkyawa mai kyawun hali_
_nanahafsat.wordpress.com_
Gidan sa na da dasu Karimatu suka tashi, Dr Khaleel ya k'ara gyara shi ya koma tamkar sabo,
aka rushe wasu sashen aka mai dashi sashe biyar kawai, b'angaren sa, dana Haj Aysa da
Helwa uku kenan. Sai na Inna Bilkisu da b'angaren baki. Tamkar wasu amare haka ya mai dawa
kowacce apartment d'inta, Royal furnitures sababbi fil aka sanyawa kowane sashe, amma na
b'angaren Inna Bilkisu yafi kowan ne tsada tun farko haka suka saba yi komai nata yafi na
matansu tsada, ko atamfa ce tata super ce, su kuma Holland domin iyaye ba abin wasa bane
musamman ita da ta tashi tsaye da addu’oi, dan ganin Allah ya cika musu burikan su tun suna
k'anana.
Sosai su Islam suka fara lectures, gaba d’aya bata da lokacin komai, dan da asubah malam
yake zuwa yayi mata tahfiz da safe kuma take tafia lectures sai yamma ta dawo da daddare
kuma lesson teacher d'inta yake zuwa, sam bata da wani spare time kullum she’s busy, har
time-table tayi na yadda xata dinga gudanar da ayyukan ta na yau da kullum. Cikin lokacin ne
kuma aka sanya bikin Fatma Bichi dake kano, event d’aya Islam da Lee suka samu zuwa
saboda school, gashi class d'insu d’aya kuma. Can Middle-East aka kai Fatima k'asar Qatar ko
d'igon hawaye ba tayi ba domin tana matuk’ar son mijin nata, ko makaranta tace ita baxa cigaba
ba ta yadda zata yi ABU mai labule.
****
Zaune suke a parlor Haj Aysa da Yakolo, wannan karan harda k'arin Yaburra(Zainab) ‘yar gidan
Aunty d'in Haj Aysaa dake Bornu. Shirye-shiryen auren Yakolo suke yi sai kace auren budurwa,
dawowar Islam kenan daga school a matukar gajiye take, gaishe su tayi ta haura sama abunta,
mai aiki ta bita da abinci. Wanka tayi kawai tayi sallah ta kwanta bacci. Can k'asa kuwa suna list
na kayan gidah. Yaburra da tun d’azu zancen ke cinta ta kasa