Showing 54001 words to 57000 words out of 86718 words

Chapter 19 - SAIFUL-ISLAM Book Complete by miss xoxo (2).pdf

06 Jul 2025

2097


kan abinda ya faru, Riri ma ta k'ara bata, da kyar Ubale ya samo mechanics suka gyara motar,
sannan yaja su suka tafi ciki harda Riri da taji baxata iya zama ba acan. Saifullah daya koma

gidah kuwa sakawa da warewa ya shiga yi, yarinyar nan dama haka take? ya ‘dauka son aure
da nacin sai taxama matar sa shine burin ta, ashe ashe mizanin tunanin sa kad’an ya d’ebo
akanta, harda harkar maza take bi kenan?

“Subhanallah ya Allah..”

Ya furta yana mai dafe da kansa sabida yadda yake sara masa yana barazanar fad'owa. A
daren bai kwanta ba sai da ya yanke babban hukunci da zai aiwatar akan Islam inda sukai aure.
Islam baiwar Allah kuka sosai ta shiga yi a sujjadarta, tana neman yafiyar ubangiji abisa abinda
ya faru d'azu. Nan jikin Riri yayi sanyi lokaci d’aya itama ta mike ta shiga band'aki ta d'auro
alwala ta shiga jera salloli..

Shirye-shiryen biki ake yi ganga-ganga daga duk b'angare biyun, nasu Islam dama na d’aya
amarya wato Dr Teema, ango Khaled kuwa duk ya matsu so yake kawai a d'aura aure a damka
masa matar sa su ware subar k'asar domin visa da yake jira ta fito, kai kace a gidan rik’o yake
gaba d’aya tamkar wanda yake akan k'aya haka ya k’agu su bashi amaryar sa, shi kuwa
miskilin sarkin fad’in rai wato auta saifullah kuwa, sai abinda aka tilasta shi yayi shi yake, domin
abokan sa sun yi shirye-shirye sun shirya lafiyayyar liyafar barbecue yace babu inda xashi,
k’arshe dai sai ‘kawayen Islam ne da abokanan nasa sukaje aka d'an gwangwaje duk da ba
haka aka so ba.

Da misalin k'arfe sha biyu 12:00pm jirgin 'yan tafiya kano daga Abuja ya sauka a filin jirgin
malam Aminu kano dake kano. Kowa kagani sai murna yake da wannan babban budiri da za'ai,
'yan d'aurin aure ne suka fara zuwa inda aka d'aura auren Fatima Muhammad wacce ake kira
da Dr Teemah, da angonta Khaled Mommodu Mele, akan sadaki dubu d'ari biyu cif. Dubban
mutane ne suka shaida hakan inda da rana mahaifiyar amaryar wato hajia Fareedah
Muhammad Abbas ta shirya had'add'iyar liyafa wadda ake kira da mother's Eve. Taro yayi taro,
anci an gyatse 'yan uwa duk sunxo kano,

B'angaren su amarya Islam kuwa k'awayen ta na BNA dama na Nile sune suka had’a mata d'an
event d'insu na k'awaye na ‘bridal tea party’ , Amarya Islam tayi kyau ba k'arya inda Mamza
Beauty ta tsantsare mata kwalliya, kayanta kuwa Hudayya Fadoul ce ta d'inka, gayawa mai
karatu irin had'uwar da Islam tayi b'ata Lokaci ne, domin kunsan yadda prof Khaleel yake san
Islam da ma Ya Bala, uwa uba autar mata ce, gata ta gaban goshin mahaifiyar Saifullah.

Washe garin safiyar Asabar da misalin k'arfe biyu na rana aka d'aura auren Saifullah Faruk
Muhammad da amaryar sa Bilkisu Khaleel Muhammad (Islam) akan sadaki sisin gwal guda d'ari
biyu cif, A masallacin central mosque dake Abujan. Domin mahaifin Saifullah yace tunda dai
Islam ta had’a zuri’a da kanuri babu abunda zai hanashi yi mata irin al’adar su. Daganan aka yi
reception d'an gaske domin anci ansha, ango yayi shiga cikin dakakkiyar getzna kalar sararin
samaniya ya d'ora hula zanna bukar gashi yasha takalmin sa batozzi sau ciki dark blue, agogon
hannun sa na azurfa da zobe da suka amsa sunan su, kallo d’aya xakai masa ka furta kalmar
‘TubarkAllah’. Duk inda yayi masu hoto na binsa, sai murmushi yake yi kai kace auren soyayya

ne.

Cikin takun k'asaita yake tafiya, daga nan suka koma gidah shi da abokan sa yin wanka na biyu
dan zuwa gidan su Islam, kafin anjima suje liyafar gidan su Islam d'in da aka shirya ta
‘wushe-wushe’. Domin hatta kayan da zai saka komai irin na al’adar ne, shi abun har mamaki
Maman ke bashi ganin yadda take komai a tsare sai kace akansa ta fara aurarwa.
Islam kuwa na can tana kuka, tunda akace an d'aura auren take hawaye domin tasan babu
wanda ya isa ya yanke wannan k'addararren auren dole da Allah yayi sai anyi shi. Da kyar
tadaina kuka ta koma ajiyar zucia. Hafsat da Hidaya dake gefe kuwa murna suke mata ganin ita
kam ta tsallake sirad’in auren sa’annin daddy, zata auri sabon jini uwa uba kuma yaro matashi
mai jini a jika. Duk sun wani yamushe duk da yanzu ba laipi suna samun kulawa, amma ba
kamar suna gidah ba, domin sai kace wanda sukai shekara goma a gidan aure. Hidaya duk ta yi
laushi, Hafsat kuwa idan ba dole ba yanzu bata fiye magana ba, domin dunia ta koya mata
hankali. Cikin taushasshiyar murya tace,

“Uhm! Islam ba kuka ya kamata kiyi ba, alwala zaki d'auro kiyi sallah ki godewa Allah ya
azurtaki da wannan babbar kyautar..”

Hidaya dake gefe tai murmushi tana jinjina kai kafin tace.

“Wallahi kuwa Hafsat, yanzu da ace ba muyi wasa da rayuwar mu mun cuci kanmu ba, ai da
muma samarin kila zamu aura, amma dubemu Islam, ko ba kya son mutumin nan karki tab’a
nuna masa da sannu zaki so shi, ki kuma kyauta ta masa sai kiga Allah ya dube ki da idanun
rahama yasa ya mato akan ki.”
Islam dake gefe ta dube su kawai tana d'auke kanta, kafin cikin sark’ewar murya tace.

“Ba zaku gane ba, baya so na shima yana min kallon wata k'ask'antacciya, fisabilillahi meye
nawa aciki? Wallahi bansan anzo an nema masa aure na ba sai da Yayya Yakolo take fad’a
min... ku..” Hafsat ta katseta tana mikewa tsaye, cikin fushi tace,

“Islam ya kamata ace ni da Hidaya mun isheki ishara, kalli yanzu ni wanda aka aura min mai
mata biyu fa, daga shi har matan nasa sun haife ni. Kai ‘ya’yan sama sun mugun girme mini.”
Hidaya dake gefe ta amshe da,

“Ba gwara ke ba Hafsat, ni fa matan sa uku ni ce ta hud'u, ko a mafarki ban tab’a zaton hakan
zata kasance dani ba, sai gashi wanda ya girmewa mahaifi na shine ya zamto mijina, harda
rabon d'ansa ko ‘yar sa gashi a k'unshe a marata. Amma Alhamdulillah kukan kurciya jawabi ne
ga mai hankali, Tabbas abubuwan da mukai na laipi ada shine muke girbesu yanzu. Fatanmu
Allah ya k'ara karb'ar tubanmu yasa hakan shine mafificin alkhairi”

“Ameen..”

Suka fad'a baki d’ayan su, zumbur Hafsat ta mike ta fita daga dakin da alama ta tuno mahaifiyar
ta, maganganun da sukai ya taso mata da zaman mahaifiyarta Karimatu a baya. Nan Hidaya ta
shiga baiwa Islam shawarwari na irin yadda zatai zamantakewar gidan aure da sauran su. Sun
jima kafin Yakolo ta shiga d'akin ta tasa keyar Islam su koma sama.
Wani ruwa mai tashin k'amshi a babban baho Yakolo tasa Islam agaba ta cire kayanta ta shiga
ciki, bayan ta fito daga ciki ta sake turarata da wani turaren wuta na jiki, kafin a d'akko mata
wasu kaya da sukai kwana da kwanaki ana turararasu a kabbasa. Lungu da sak’o na jikin ta sai
da aka shafeta da wasu irin turaruka.. (sirri ne tawan (billyn Abdul) tace karna soma fad'a
muku).

Wani arnen komole lace royal blue ta saka mai kwalliyar golden, tasha adon gold hatta
mayafinta da takalmin duk Golden ne, ba kad'an ba Islam tayi kyau ga wani sihirtacce kuma
ni’imtaccen k'amshi da yake tashi daga jikin ta na shuwa-shuwa-yerwa fato-Chadians, kai duk
ita d’aya dai akai mata wannan combo. Light makeup Lee tayi mata, sannan takama hannunta
suka sauka k'asa wajen angwaye inda Saifullah ya wani hakimce a zaune yana danna waya.

Ta k'asa-k'asan ido yake duban su Islam dake sakkowa, baki da hanci harda idanuwa haka
Saifullah ya baje yana kallon Islam.. ‘Fata barakAllahu ahasanul khaliqeen.’ Shine abinda ya
furta ba tare da yasan yayi ba daman k'asa-k'asa ya fad'a yana neman sai-saita kansa, sai
yanzu ya lura yarinyar bayan jiki mekyau tana da wani irin sihirtaccen kyau sosai. Ya dubi
abokansa yaga yadda suka zuba mata idanu gaba d’aya sai yaji haushi ya kama shi kuma.

Cikin takun sa na isa ya k'arasa ya fincikota zuwa jikin sa, kirjinta ya manna a nasa, take yaji
tsigar jikin sa na tashi yarrrr, itama mutuniyar taku anata b'angaran hakan ne ya faru. Cikin
rad’a-rad’a kamar irin soyewar nan suke yi ya shiga yi mata magana a hankali kamar zai lashe
mata kunnen, gaba d’aya kamshin jikin ta narkar dashi suka yi, k'ok'ari kawai yake yi ganin bai
yi wani abun da zai sa a gane yanayin da ya shiga, gashi abokansa da kawayen ta sai tafa
hannuwa suke a lamun ya burgesu domin yadda suka yi irin na masoyan nan ne,

“Sam baki yi kyau ba malama... Ga wani kaurin turare dake tashi a jikin ki so suffocating.” Shine
abinda Saifullah yake gayawa Islam a cikin kunne gashi ya nanuke ta danma dai ta zama tasa
yanzu. Mutsu-mutsun kwace kanta take yi ya sake rad’a mata cewar,

“Don’t you dare create a shameless scene here, abokai na masu class ne basu zubar da nasu
ba kamar yadda kika zubar da naki a titi. So karki bawa kanki kunya a gabansu fatana Allah ya
shiryeki.”

Yana fad'a ransa na k'ara jagulewa tunowa da yai da ranar da daya gansu da 4gig a joint,
mayafinta a hannun gardi tana sakin murmushi. Saurin tunkud’eta gefe yayi yadda ba kowanne
zai gane ba sai ita, murmushin takaici tayi ta shiga gaishe da abokan ango, sunata tsokanar ta
aka shiga d'aukar hotuna, Saifullah na k'ak'ume da hannun Islam kamar gaske, mintuna kad’an

ya juya ya gasa mata bak’ar magana a kunne. Duk Islam a takure take dan haka suna tafia taji
dad’i a ranta, nan ta koma cikin 'yan uwa aka cigaba da shewa lokaci zuwa lokaci maganganun
saifullah na mata yawo a zuciya suna kuma susar ta idan ta tuna kalamansa.

“Wai na zubar da class d'ina a titi, toh mai yake nufi da ina yi kenan?! Ya Allah”

Haka Islam ke fad'a a hankali idanuwanta sun ciko da hawaye, da wannan su Yayya Yaburra
suka sake d'aukar ragamar shirya Islam don zuwa wushe-wushe, an yarfa mata 'kela yaske’
(kitson gaba), gana lalle baki da ja, kamshi ta ko'ina tashi yake daga jikin ta, ita dai Haj Aysa
nata idanuwa ne kawai domin duk k'annenta sunyi kanai-kanai akan komai, wani dandatsetsen
cotton lace ta sanya aka nad’a mata laffaya wadda taci sunan ta 'yar gaske, komai na al’adar
kanuri tasa, sarkar k'afa data kai ga kuma b'ular hancinta tasha ado da ‘yar barima itama, komai
dai tsab abun ba’a magana sai dai a ce tubarkAllah kawai.

K'arfe bakwai aka fara tafiya wushe-wushe ango Saifullah shima yasha shiga cikin komai na
al’adar barebari, ba kad'an ba yayi kyau, abokan sa sunsha ado suma, k'awayen Islam ma
sunci ado cikin dangashe da mandil peach color, 'yan uwa kuma sun sa blue and black. A
convoy suka tafi inda xa’a gudanar da sha’anin. Motar Saifullah da Amarya Islam itace a
k’arshe, tunda ta shiga cikin motar yake kallonta ta gefen idonsa, ba kad'an ba tayi masa kyau,
amma abunda ya dasawa zuciyar sa akanta ba zai iya furta komai ba. A haka suka k'arasa inda
za’a gudanar da event d'in,

Sai bayan kowa ya shiga mc tai announcing shigowar couples SAIFUL_ISLAM, a tare suka
shiga hannun su sarke dana juna, da abokan su dake binsu a baya mace d'aya namiji d'aya
suna bin taken gangaa kura kowanensu yasha kitson gaba abindai sai sam barka kawai... Can
baya kuma 'yan uwa ne su Yakolo, Yaburra da sauran ahalin prof Khaleel. Tuni aka fara xubawa
makad'an gangaa kura yirne, waje kuwa jin kid'a yana tashi yasa aka fara sakin al’adar durum
kageye, su kaka deeja kuwa sa bada nagaya ka ajiye suke(turaren wuta).

Riri ce ta bada tarihin amarya inda take cewa.

''Amaryar mu dai ta kasance 'yar autar mata a wajan iyayenta, sannan tana da kuka dan duk
abinda aka yi mata ko hararta aka yi, Sai tayi kuka dan haka ango sai ka kiyaye dan karka ce
ba'a sanar da kai ba, sannan amarya tana da hakuri uwa uba kawar da kai akan abinda duk
ba'a sanyota a ciki ba, tana da ilimin ta dai-dai gwargwado na arabi dana zamani, sannan akwai
shagwab'a, ga karatun novel’s da son girki, My bestfren is amazing to the extend that no word
could describe how sweet she's. Ga 'kamshi malam, Angonmu xaka sha 'kamshi. dan haka
ango Saif sai ka shirya dan wasu abubuwan sirri ne sai kunyi aure zaka binciko su.' May your
new home be forever blessed.”

Gabaki d'aya gurin babu wanda bai yi dariya ba, shi kansa Saifullah banda yana jin haushinta
yaso ya dara sai kuma yayi ta maza ya basar. Riri na komawa wajan zamanta Abbas ya taso
wanda shine zai bada tarihin ango, yana sosa saman hancinsa yace.

''Kowa dai daga gani yasan angon nan ba baya ba, shalele ne d'an gata d'an auta kuma d'an
gayu. Ni abu na farko da zan bawa amarya shawara akai shine, kiyi ta hakuri domin kuwa mijin
nan naki akwai 'yan mata gashi sune suke kai masa hari, abinda zance dake shine kisan yadda
zaki wajan kama zuciyarsa ya zamo naki ke kad'ai. Sannan Saifullah yana da hakuri wanda ba
kowa zai shaida hakan ba sai wad'anda suka zauna dashi, Toh Aboki na dai miskili ne gaskia,
mr arrogant ba hehe, amma azahirin gaskia he's fun to be with, Saboda bestie na komai yanada
time awajen sa, yace time dinsa is priceless. Amma amaryar mu kinyi sa'a saboda saif is kind,
attentive and most caring wlh.. sannan lastly Kiyi hak'uri da addicted kalmar sa ta kullum wato
so suffocating. Nima dai a karshe zance amarya ba zata gama sanin waye ta aura ba sai sun
fara rayuwa, Allah bada zaman lafiya ya kawo kazantar d'aki bata sharaba ta....''

Saifullah kuwa cikin makoshi ya furta,
“So suffocating”

Gabaki daya gurin sai ya hargetse da surutu, wasu suce Allah sarki Islam wasu kuma suce ai
itama tana da kyau wasu suce idan ta kama wata na soyayya da mijinta taci kaniyarta, da
alama dai Abbas yabar gutsiri tsoma a wajan yayin da shi kuma yana gefe yana bankar dariya
harda rike ciki.
Amarya Islam na dosar tsakiyar fili wace jikinta ya kuma yin sanyi jin yadda mijinta yake, aka
canxa waka xuwa na shuwas wato can dangin mahaifiyar su baban Saifullah, wakokin khamal
yaqub/mansur ne ke ta tashi dana Amina rawaram.. Islam na xama aka fara gudanar da al’ada,
komai a tsare Saifullah da Islam sai magana suke a hankali, kai kace hira suke yi, amman ina
warning yake korawa Islam kan tacigaba da acting it suits her, idan ta nuna akwai wani abu a
tsakanin su, sai ya dizgata a gutin ita kuwa cewa take ya kyaleta, yana kara damke hannuwanta
har wani lumshe idanu yake.

Anci ansha ankuma gyatse, can na hango 'yan Saiful_Islam fans group da home of novels suna
lafta loma, idanuwa hud'u mukai da rano dake saye kisre tana dannawa a nursing bag d'in affan
girgiza kai kawai nai don tasaba, Can gefen Hall kuwa rano Online novels ne da ya hajja ce
novels keta lomar abinci, excellent writers members ma can na hangosu irin su nafee anker da
didi sai danna snacks suke a jaka..

Cikin basarwa nace wa Ya Hajja dake gefe ''Gaskia k'awayen Billyn nan (billyn Abdul) basu
hadu ba, kallesu suna yarfa mu a idanun mutane.'' dota billy s fari dake gefe taja tagumi tana
cewa, ''wallahi Mom sai a hankali kam, mu tafi kawai so uncomfortable.''

Washe gari akai English party wanda su Ya Safa suka had’a. Daganan akai bud'an kai da safe a
gidan su Saifullah dake Abuja, Saboda rankatakaf k'wansu da kwarkwatar su tun biki na sati
hudu suka dawo Abuja da xama, hadadd'en gidah mai kyau na mace d’aya sama da k'asa
Alhaji Faruk mahaifin Saifullah yabasu kyauta su zauna shida matar sa, anan unguwar Asokoro.
Tunda aka fara maganar kaita gidan ta Islam take kuka mai tsuma zuciyar duk wanda yake

sauraro.


_kunji shiru kwana biyu ko? Wlh rasuwa akayi mun, Banda nutsuwar typing shiyasa. Thanks for
the messages and call. Allah ya bar zumunci_



_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_

[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


_*®HASKE WRITERS ASSO._*


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_
_BILLYN ABDUL_


*_SHAFI NA 46-49_*

_SHAFIN YAU NA KI NE MYRIAMFATAN ALKHAIRI AGARE KI TAWAJE NAALLAH YA
BIYA MAKI BUKATINKI NA ALKHAIRI, KUMAO_

_nanahafsat.wordpress.com_


Nannauyar ajiyar zucia Islam ta sauke bayan fitar Saifullah. Sai raba idanuwa take yi. Dakyar ta
iya jan sayyadar ta, tashiga ‘bandaki, alwala tayo tayi sallah, ta bude drawer dinta da su Yakolo
suka shirya mata kaya, riga da wando kakkaura ta ‘dakko ta saka. Tabi lapiar gado, Don dama

tayi sallah d’axu. Wayar ta, ta ‘dakko ta shiga WhatsApp, messages rututu tagani ana tayata
murna da Allah yasanya alkhairi. WhatsApp family group ‘dinsu ma na ‘Y’ar Gaya Fam Bam’
duk maganar bikin ake yi, sai na secondary school dinsu na BNA 2k14. Shima sai yad’a zancen
akeyi, ita dai dariya kawai takeyi, sannan ta turawa kowanne grp emijo na love ❤. Nan aka
shiga maganar ‘ya amarya da yin reply,ina ango,’

“Yana gaida ku, sai da safe..”

Tacewa kowannen su, kafin ta kashe data dinta ta kwanta, ko takan reply din Lee dake cewa
‘sai tazo gashin amarya da safe’ bata bi ba, nannauyan bacci lokaci d’aya yai awun gaba da ita.
Da asubah ta mike jin kiran sallan masallacin mak’otansu, hawaye ne ya ciko fal idanunta na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login