Showing 57001 words to 60000 words out of 86718 words

Chapter 20 - SAIFUL-ISLAM Book Complete by miss xoxo (2).pdf

06 Jul 2025

2083


ganin dagske dai tabar gidah har abada, kiran sallar ma ba ‘daya bane, Ta furta aranta.
Bandaki ta fad’a, tayo wanka had’e da alwala, sallah tayi da azkhar. Kafin ta dakko littafin
anatomy tashiga karantawa, haka wani baccin gajiyar ya sake awun gaba da ita akan sallayar
sallan. Saifullah kuwa da kyar ya tashi yana murza idanu, bandaki ya shiga yana had’a hanya
don bacci ne fal idanun sa, ya sakarwa kansa shower. Sai da ya fitar da baccin daga idanun sa,
sannan ya ‘dauro alwala ya fito ya zira jallabiya ya fita masallaci, ana idarwa kuwa ya shiga
bakinsa dauke da adduar shiga gidah,Kamar ya shiga ‘dakin da Islam take sai kuma ya fasa
yana haurawa sama abunsa, wayar sa ya janyo yana duba time table d’insa, ‘jogging time’
shine abunda yakamata yayi a lokacin. Kayan exercise dinsa ya ‘dakko yana feshesu da turare,
sannan ya zura su ya fice motsa jikin daya saba. Haka yai ta jogging har takwas saura kafin ya
koma a matukar gajiye, ya bude gidan don ba’a kawo musu mai gadi ba tukun.

Lokacin kuma Islam ta gama turara kayanta akan kabbasa, dinkin riga da skirt, cikin dakakkiyar
atamfa Holland, pusher pink and black color, mai zanen agogo. Ta gyara ‘dakin duk da ba wani
datti yai ba, haka ta karkad’e ko’ina tana yaba tsarin gidan. Ba kadan ba yayi mata kyau, sosai
kayan da aka zuba sun ‘kara ‘kayatar dashi. Simple ‘dauri tayi ta fito hannunta rike da burners
guda biyu da ledar magic coal, ta jona burner ‘d’aya a corridor ta zuba turaren halut, a parlorn
‘kasa kuma ta jona ‘d’aya ta zuba ‘sandal bange’. Kitchen ta nufa da ledar magic coal a
hannunta tana yaba tsaruwar kalar kitchen cabinets din, domin orange and black ne, sai kitchen
utensils kuma duk silver color aka zuba mata, santin komai take yi tana shi wa iyayenta albarka.
Nan da nan ta kunna gas ta dora coal igniter ta kunna coal biyar aciki, suna kamawa ta zuba a
kasko, tuni ta barbad’e shi da turaren wutar Hawi. Jama’a gidah dai ya tashi da ‘kamshi kala
kala, ba a magana kawai, Ga na jikin ta dake tashin turaren kaya dana khumrah’s.

Heater ta jona, ta ‘dora ruwan zafi na tea. Don taga komai akwai shi wadatacce a kitchen din,
domin store dinma shak’e yake da kayan gara, tea yana tafasa ta juye a royal flask dinta ta kai
kan dinning ta’ajiye. Ajiyewar ta yayi dai-dai da shigar Saifullah parlorn, bakin sa ‘dauke da
sallama. Amsa masa Islam tayi duk a rud’e take. Tunowa da jawabin Inna Bilkisu datai hakan
yasanya ta hanzarin tsugunnawa, cikin siririyar muryar ta tace,

“Ina kwana?!”

Tabe baki Saifullah yayi, bayan yagama kalleta sama da ‘kasa, ga ‘kamshi na dukan hancin sa
na jikin ta da turarukhan wutan, cikin turo baki gaba yace,

“Yana kwano.”

“Me za’a dafa maka?” Cewar Islam, kanta a ‘kasa..

Ware idanuwa Saifullah yayi, yana mata kallon renin hankali kafin yace,

“Ni zaki dafawa abinci?! Lalle ma yarinyar nan.”

Yana gama fad’a ya haura sama abunsa, tab’e baki Islam tayi, ta koma kitchen, cikin minti biyar
ta kammala dafa indomie d’aya had’e da soyayyen kwai guda biyu. Daki ta koma abin ta, tana
ci, sannan ta koma kitchen ta wanke duk abunda ta ‘bata. Ta zauna a palor tana tunanin
cakwakiyar zaman da xasuyi da Saifullah. Tana jiyo ‘burin ‘burin ‘dinsa a kitchen din sama. Ashe
coffee ya had’a a coffee machine. Sai tara dai-dai aka kawo musu abinci daga gidan su
Saifullah, Fatma da Humaira ne suka kawo, sai tsokanar ta sukeyi itadai murmushi kawai take.
Cikin haka kuwa Saifullah ya sakko, sanye cikin dakakkiyar shadda galila golden datasha aikin
hannu milk color, hular sa a hannu milk color yana gyara karin ta, Kallo ‘daya yai musu dukkan
su ya maida kansa kan hular sa, Fatima yayar sa ta mike tsaye tana nufar inda yake,

“Autan mu..”

“Ya fati..”

“Na’am Auta, yauwa ga abinci can aunty tace akawo muku, naga amaryar mu ma har da
wahala, tayi tea gashi can a dining.”

“Tohm angode”

Cewar Saifullah, Humaira dake gefe tace,

“Ya Saif ina kwana?”

“Humaira..” abunda yace kenan kawai ya sa kai zai fice, Fatima ta riko rigar sa,

“Ina zaka ango da sanyin safiyar nan? Indan mune dawo ka zauna, yanzu zamu tafi. Dama
sallama nazo muku yau zamu koma mu.”

Ware idanuwa Saifullah yayi, cikin sauri yace,

“Komawa kuma?! So soon haka? Amma banda Mami ko?”

“Duk ‘yan lagos yau kowa zai tafi bare ni da ke port-harcourt,k..”

Ai be jira ta gama ba ya fice cikin sauri, Islam dai duk tana jinsu bata tanka ba, nata dai
murmushi ne kawai, Fatima da Humaira suka shiga hirar su, lokaci zuwa lokaci islam ke samu
su baki, sam kunya take ji, haka kawai taji har Humairan take kunya, uwa uba kuma Fatima
yayar Saifullah.
A ‘dari Saifullah ya figi motar sa, sai gidan su, yana zuwa ya tarar kuwa yan uwa nata shirin
tafiya, duk sai yake jin ba dadi, haka dai ya amsa gaisuwar kowa awajen a kunyace musanman
yadda suke tsokanar sa, ‘dakin Haj Zuwairah ya nufa, lokacin ta fito kenan daga kitchen
hannunta rike da kofi da kunun tsamiya aciki. Fad’ada murmushin ta tayi, tana karasawa cikin
dakin.

“First love..” cewar Saifullah,cikin shagwababbiyar murya.

“Auta na.. kadde kace su Fatima ba su kai muku abincin ba, yau naji shirme a wajen yaran
nan.”

“No sun kai.. Ni first love zuwa nai wajen ki, I love and miss you, dakyar nai bacci jia” ya karasa
fada yana dora kansa a cinyar ta.

“Shine ka baro yarinyar mutane acan? Ni auta yaushe zaka san ka girma ne? Tashi ka tafi”

Make kafad’a ya shiga yi, yana jijjiga kansa alamun a’a. Cikin cuno baki yace,

“Ni fa first love kinsan inde ba siblings dina ba da ku, da sauran family i barely eat with
strangers.”

Salati Haj Zuwairah ta rafka tana ‘daga kansa daga cinyar ta,

“Wacace stranger auta? Islam matar taka ce ta koma bare kuma? To tashi tun muna shaida
juna ni da kai ka tafi gidan ka, ko na mugun sab’a maka. Akan yarinyar nan Allah auta zamu
‘bata dakai, ka kasa sakin jikin ka da ita, kar dai kacemin kana mata wannan halin naka itama.”

Cikin cuno baki gaba yace,

“First love, Ya Fati ce fa tace yau zaku tafi..”

“Sai akai yaya da tafiyar mu? kai fa nace ka kwantar da hankalin ka, Baban ku yace zamu
dawo muma nan ‘din cikin shekaran nan, to menene abun damuwa kuma uhm?”

Shiru Saifullah yayi, gaba d’aya tamkar zaiyi kuka haka fuskar sa ta koma, ganin hakan

yasanya Haj Zuwairah, tausar sa, don tasan halin autan nata baya cin abinci sai ta tasa shi
agaba, kamar yaro, bayason abinci, yawanci sai abu mai ruwa-ruwa, kuma bana ko’ina yake ci
ba, sai na gida, Sam bayason na roadside ko na wasu restaurants din. Abincin ta zubo masa,
da kunu sai da yaci sosai, sannan ta tasa ‘keyar sa suka tafi, dama tayi niyar zuwa ta gano
gidan daganan ta musu sallama, fal suka cika motoci uku, sukaje gidan . Lokacin itama Islam
yan uwan Ammi sunzo fal na bornu suma duk yau zasu juya hakama na ‘yan ‘kauyen y’ar gaya.
Tuni gidan ya kacame, Ita dai Islam na dakinta tana canza wani kayan, domin tayo wanka na
biyu. Ta shirya cikin wani lace ja, doguwar rigar A shape, hannun kuma peplums akai masa. Ba
kadan ba tayi kyau. Light makeup Lee keyi mata,

“Lam Lam ba ki labarta mun first night ba..”

Dariarta Islam ta danne, ko da hakan ta kasance ai ba zata tab’a fada ba domin Yayya Safa
tace karta soma bawa kowa labarin yadda sukai auratayya da mijin ta, dama duk wani sirri dake
tsakanin su, don babu kyau. Murmushi tayi kafin tace,

“Bari kawai, ba’a magana it’s beyond your imagination, ki shirya hajjaju..”

Lee ta bude baki, ganin da gaske labarin da take ji akan hakan ashe gaskia ne, Yatsina fuska
Lee tayi kafin tace.

“Tab zan iya yadda kuwa?”

“Da me fa” cewar Islam, cikin zakuwar abunda Lee zata fada.

“Wallahi ina gaya miki, Fahad ya matsa shi aure kwanannan, Naga abun nasa na neman
zautar dashi nace yafadawa Baba sunfi kusa, shine jiya yake cemin cikin satin nan za’a kawo
komai, kuma biki bayaso ya wuce nan da wata ‘daya.”

Cikin murna Islam tace,

“And so?! Kakki wani damu wallahi, Allah yasa hakanne yafi alkhairi, mu gwangwaje mu
rak’ashe.”

“Waye zai barki ki rak’ashe ki gwangwaje? Lokacin ma akwai little unborn, beside Ya Saif baze
yarda ba”

Tab’e baki Islam tayi, cikin cuno baki tace,

“To y’ar ciki baki, sai ki hana ai..”

“That aside.. Ni kuwa kinji labarin cousin d’inki Saifullahi, zai fara lecturing a school namu ko,
as visiting lecturer amma, shi zai ‘dauki course ‘din: Introduction to Humanities and community

medicine”

Tabe baki Islam tayi, kafin tace,
“Lalle, Za’a sha ruwan carryovers”

Lee ta kyalkyale da daria kafin tace,
“Kiji tsoron Allah Lam-Lam, dan jinin ku bai hadu ba sai ki laqaba masa sharri, in sha Allah
zamuyi passing kowanne course with flying colors..”

Islam ta mike tana kallon kanta a wani mudubi, dogo fari kal, kana kallon kanka full dnka ta ciki.
Ba kadan ba ta yaba kwalliyar da Lee ta mata, ta faffesa perfumes kafin tace,

“Can ta matse muku ke da shi, yanzu dai tayani kwaso ledojin nan, Ammi tace na babbawa duk
wanda sukazo zasu tafi..”

Kad’a kai Lee tayi, tana duban ledojin, atamfa ce guda d’aya, da kwalba cike da turaren wuta,
sai kasko da hair dryer set a kowacce leda, kin kima sukai, suka kai parlor, Islam duk ta takure
da irin shegen kallon da Saifullah ke jefanta dashi, in sun had’a ido kuma ya sakar mata harara,
ita abunma daria yake bata.
‘Y’ar walima dai akai na yan uwa da suka zazzo, yan bornu ne suka fara yi mata sallama suka
tafi, ta bisu da ledojin su, daga nan yan Y’ar gaya suka ‘daga suma, bayan sun tafi da awa
d’aya su Haj Zuwairah suka fara mikewa don tafiya, Saifullah yayi rau-rau da idanuwa kamar zai
yi kuka, sosai ‘yan autancin suka motsa masa, sai da Haj Zuwairah ta tasa ‘keyar sa ‘daki, daga
shi har Islam din ta sasu agaba, ta dubi Saifullah tana murmushi kafin tace,

“Haba auta, ai sai matar taka ta rena ka, ‘katoto dakai zakai kuka”

Ai kuwa daria ta tahowa Islam ta gimtse ta dakyar, Nan de Haj Zuwairah ta shiga yi musu
nasiha da jan hankali na yadda zasu gina rayuwar auren su, ta ‘kark’are da,

“Wannan sabuwar rayuwa ce kuka shige ta, wadda ba irin ta baya bace, sai kunyi hak’uri da
juriya akan komai, ga ku duk ‘yan auta, ni dai auta ga amanar Islam nan, kaga itace karama dan
Allah ko menene zatai maka kayi hak’uri, komai ‘dan hak’uri ne, ke kuma Islam ki bishi sau da
‘kafa, karki bi zugar ‘kawaye ko shawarar su wurin munanta masa, yi nayi bari na bari, nasan
Auta na jan ido ne sai da magani, sai kina hak’uri dashi, amma idan ki kai hak’uri zaki ga ribar
sa, domin shi mutum ne mai saukin kai, Allah ya muku albarka..Duk abunda kike bukata ki
gayamin kinji auta ta?”

Murmushi Islam tayi tana rufe fuska jin itama ana kiranta da auta, Mami tai daria kawai kafin
tace,

“Sai maganar abinci, sai kin matsa masa bayason abinci, tun yana ‘karami muke fama, ungo

nan, lists ne na duk abunda yake ci.” Ta karashe maganar tana mika mata wata takarda, kafin ta
sake cewa,

“Kema ki dinga cin abinci kinji auta ta, duk abunda kike so kici ki girka kinji, idan an kawo miki
y’ar aiki ma sai ta dinga tayaki da wasu abubuwan, Allah ya muku albarka..”

“Ameen..” suka amsa gaba ki d’aya.

Dakyar dai Saifullah ya bari su Haj Zuwairah suka tafi, har ‘dan zazzabi yai, domin duk dunia
yafison mahaifiyar sa, ya shaku da ita fiye da komai, bai tab’a soyayya ba, bai san ya ake yi ba,
domin duk ‘yammatan dake nuna suna sonsa ba ya taba basu fuska, ya ‘dauki mata marassa
kamin kai, aganinsa duk haka mata suke, domin yadda suke farautar zuciar sa abun har
mamaki yake bashi, shiysa ya jingine kalmar So gaba d’ayanta ballantana soyayyar kanta. Shi
kadai yake rayuwar sa, ko kadan bai taba sawa a zuciar sa, zai yi soyayya ba bare aure nan
kusa ba ma, sai gashi rana tsaka anyi mai auren dole. Auren dolen ma da yarinyar dake rokar
maza su aure ta, take kuma zubar da mutuncin ta a titi....

Haka dai rayuwar gidan *SAIFUL_ISLAM*, ta cigaba. Kowannen su harkar gaban sa yake,
gwara ma Islam tana k’ok’arin saukar da hakkinta na gaisuwa dana abinci, amma sam bayako
kallon dinning table, kullum sai dai ya hada porridge yasha, gashi scent din abincin ta na shiga
har hanjinsa don tsabar dadi, amma saboda fadin rai da miskilanci irin na Saifullah ko kallo mai
abincin da abincin basu isheshi ba..

Haka dai ta koma makaranta, haduwar su kullum sai magrib, ta gaisheshi ya amsa a dak’ile, har
bikin Lee ya ‘karaso, da ita aka karbi lefe da komai, aka fara shirin biki, su bridal tea party da
duk sauran events da akai Islam taje, domin Ya Bala ya aiko mata da kyautar mota, tuni harta
koya cikin sati biyu ta kware. Ita ta tuk’a kanta ko’ina, ita har addua take yi Allah ya kawo
k’arshen wannan ‘kaddararren auren nata da Saifullah, tunda ta gano baya sonta ba kuma zai
tab’a son taba a cewar ta, domin shekaran jia abunda yace mata kenan, ‘baya son ta ba kuma
zai tab’a son ta ba’. Ta ajiye kalmomin sa a kundin zuciyar ta, sosai tai musu kyakkyawan
mazauni.

Ranar lahadi aka kai Lee gidan ta dake nan garin Abujan, domin basu da nisa sosai ma da
gidan Islam din, shiysa ma Islam ta ‘kara jin dadi, ganin ta samu y’ar uwa kusa da gidah.
Monday da sassafe Islam ta gama gyaran ko’ina na gidan lungu da sak’o, ta sassaka turarukan
wuta, riga da skirt tasa na English wears ta ‘dakko after dress shara-shara a hannu zata yafa,
da babban mayafi wadatacce saboda yanayin zafin garin. A lokacin Saifullah ya sakko shima,
sanye cikin Kaki na NYSC zai je monthly clearance, yana tafe yana taje sumar gashin sa, kallon
kallo sukai ya dauke kansa, Islam ta daure ta dan rissina tana,

“Ina kwana?!”

“Lapia.” Ya fada a takaice yana wani shan kunu.

Ita dai Islam kitchen tayi abinta, ta had’a kayan breakfast dinta a wata y’ar jaka, ta zuge ruf
abunta, a kitchen ta zura rigar ta yafa mayafin,bakin nan ya sha jambaki ja,Ta koma parlor inda
yake, daga tsayen tace masa,

“Toh ni na tafi school, and I might be late today, Saboda yanayin lectures din namu na yau.”

Tana gama fada ta juya zata tafi, Don kullum idan tayi masa sallama zata tafi baya tankawa, Ita
dai tana k’ok’arin binsa ne kawai,

“Ke..” ya fada yana wani yatsina fuska,
Juyawa tayi tana kallon sa.Batare daya kalleta ba yace,

“Koma ki saka hijab, ki rage wannan lip stick din yan ‘kauyen da kika sa, you luk so
suffocating..”

Tabe baki tayi,cikin kasa da murya ta furta,

“Latsi..”

“Kika ce mene?”

“Da kai na nake..”

Ta bashi amsa da sauri tana komawa daki,gudun karta makara, kayan gaba d’aya ta canza,
zuwa wani material blue and pink, ta zura jilbab tafito, Sam ta manta da maganar janbaki, zata
wuce yai taku d’aya biyu ya riko ta,tuni jikin ta ya fara rawa, siririn tsaki ya saki yana
harararta,cikin isa yace,
“Wato saboda ga sa’an ki ko? Na miki magana ki goge jambaki shine kikai ignoring ko?”

Shiru Islam tayi, tana raba idanuwan wannan bakon al’amari, k’ok’arin kwatar kanta take ya
hana, ta hanyar riko hannayenta ya jasu can k’arshen corridor ya jingina ta,hannun sa sakale da
kugunta, kafin tayi aune sai ji tayi ya had’a bakin sa da nata ya shiga yi mata wata irin sweet
and passionate sumba mai ratsa jiki, mutumin ku daga shanye jambaki ba sai ya rike lips din
yarinya ba, har wani lumshe idanuwa yakeyi, Ai kuwa da karfi Islam ta ture shi, yaita maza ya
hade rai, ya yagi tissue yana goge kan bakin sa, zatai magana ya rigata cikeda borin kunya
yace,

“Tun ba yau ba, nake kama ki kina satar kallon lips dina, sai gashi daga gwadawa kuwa kin rike
mun lips sai kace kin samu alawa, idan nace ban yafe ...”

Katse shi tayi, tana masa kallon yaushe nai haka? ! Cikin bacin rai tace,

“Ni ce na rike maka lips?”

Ko kallon ta beyi ba ya fice daga wajen corridor yana nanata kalmar,

“So suffocating”


(THE START OF SOMETHING NEW; SAIFUL_ISLAM#LOVE STORY BEGINS‍♀)



_Unedited... Pls do ignore all typos_



_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_
[1/3, 10:53 PM] Miss Xoxo: *_SAIFUL_ISLAM...*_


*_NA*_


_*©NANA HAFSAAT*_
*_(MISS XOXO)*_


_*®HASKE WRITERS ASSO._*


*_SADAUKARWA GA:*_
_ASY KHALEEL_


*_TUKWICI NE GARE KU:*_
_YA HAJJAH CE_
_BILLYN ABDUL_


*_SHAFI NA 54-56_*

_nanahafsat.wordpress.com_

Saifullah na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login