Showing 27001 words to 30000 words out of 88044 words

Chapter 10 - MIJIN BARRISTER Complete Hausa Novels By Sadiya Barrister.txt

15 Nov 2025

2020

xaa koma gidan jiya, momy ta share kwalla sannan "tace Ridwan "yace ingayamaki motar da yabari kofar gidanku da handset din shi duk ki dauka yabaki, amma kibada "sim card" din shi in kaimai sannan "yace kibi iyayenki kuma Kiyi biyayya ga umurnin su ki xauna da mijinki lafiya Mai-dubu ta rushe da kuka mai tsumi tana fadin baxan iya ba wallahi momy baxan iya ba.

"Momy ki gayama Ridwan shine xabina, da shi xan xauna, banason Ahmad sae kuma ta rushe da kuka. momy ya fito ta kama hannun Mai-dubu ta sakata mota ta xaunar da ita tana bata haquri har tasamu maidubu tayi shuru amma har yanxu idanunta da basa budewa sosae akan kukan da tasha basa budewa sosae kuma har yanxu basu daina fitar da kwalla ba. "momy tayi kuka itama sosae a wajen dom ta yiwa Ridwan shaawar samun Maidubu a matsayin Matar aurensa" momy ta bata kyawawan shawarwari na xaman aure ta bata kuddi amma Maidubu taki ansa sai da tayi tayi sannan maidubu ta ansa, dubu Dari ne momy ta bata.

Maidubu ta share kwalla sannan "tace Dom Allh momy idan kinje inason magana da Ridwan momy ta girgixa mata kai tana "fadin nop my daughter, "it is not legalized by d law of Allh" kiyi waya da wani kuma Kinada auren wani akanki. "kuyi hakuri kawae ku rungumi wannan abun Dom yana cikin qaddararku ta rayuwa" Mai-dubu ta dago kai tana "fadin shikenan nida Ridwan mun rabu Momy? Momy ta kauda kai gefe dom idanunta sun ciko da kwalla sae da ta share kwalla sannan "tace Mai-dubu kuyi hakuri da rashin junan ku.

"Maidubu ta rushe da wani irin kuka. "tana fadin nop! nop!! ta shige gida da gudu ta fada gado qawayenta sukayo kanta suna aikin rarrashi.

Motocin su momy na tashi tace sukoma hospital haka kuwa akayi.

"Momy taje officer din doctor ta nemi yabawa Ridwan sallama, doctor "yace Kiyi hakuri hajiya danki yana neman kulawa daga garemu. "momy tace nasani doctor idan muka je gida xan yiwa family doctor dimu waya sae ya rika xuwa yana duba shi, "doctor yace OK badamuwa.

"Doctor ya sallemi Ridwan ya bawa momy takardar sallamar, duk suka yo room dinda Ridwan yake ciki, suna shigowa Momy "tace Ridwan ya! ya! jikin naka? Ridwan yace momy kinje gidansu Maidubu, momy ta kalli Dan ta sannan "tace wae Ridwan miye haka? baxaka daina kukan nan ba! Ridwan "yace Kiyi hakuri momy ki gayamin a wanne halin kika sami maidubu? dan na tabbatar itama tana cikin damuwa? momy dom Allah ki gayamin, "momy tayi shuru Ridwan "yace momy maidubu tayi aure ko? tayi aure ko momy shikenan nasan yau xan mutu momy!, sae da momy ta share kwalla a idonta sannan "tace Ridwan katashi muje gida ansallameka idan mukaje gidan xan yima bayani Ridwan ya fashe da kuka ya fada kan gado yana kuka momy ta rike shi tana "fadin Haba my son kuka ba girman ka bane, Mai-dubu batayi aure ba fa muje gida xan gayama wani Labari ne,

Ridwan ya dago kai da sauri yana "fadin momy da gaske Mai-dubu batayi aure ba? momy tace mai eh! sannan fa Ridwan ya tashi ya sako shoe dinshi suka wuce gida.

Suna fitowa gate din hospital suka dau hanyar su ta xuwa gida suna tafe kawae wata motar taci gabansu ta tsaya, sae da driver dinsu Ridwan yayi sauri tsayawa Dom da motocin su sun kauri juna anyi accident.

Ridwan da yake kwance jikin momyn shi a site din baya yayi saurin tashi xaune itako momy sae salati take xabgawa. bodyguards din momy ne suka fara firfitowa a mota da gudu suna gyara bindigar su Dom yin harbi Ridwan yayi saurin fitowa a tasu motar yana fadin nop! karkuyi Harbin ae Yakama ta musan kosu waye ko? Duk suka sauke bindigar su momy ta fito itama.

Daga bayan su suka ji ana taba hannaye juyawar Ridwan keda wuya sukayi ido 4 shida Ahmad. Ahmad yayi murmushi sannan yace kai banxa kaga ko yanxu na nunama nafi qarfin ka, Na auri maidubu a yau miye mafitarka akan aurena da Mai-dubu? kuma wanne hutunci kake shirin xartarwa akaina? dom nunamin kaima cikkakken namiji ne. Dom nasan yanxu kanajin haushina, yayi maganar yana dafa gaban Ridwan yana dariya.

Idonun Ridwan sun kada sunyi jah, tunda Ahmad ya furta Kalmar sunyi aure shida Mai-dubu Ridwan yaji kamar andasa mai wuka a xuciya.

"Momy ce da batajin tattaunawar da suke yi shida Ahmad, ta iso kusa dasu tana fadin Ridwan mi kukeyi haka? Kuma waye wannan? Ridwan "yace momy wannan shine Wanda ya rabani da Mai-dubu, wannan shine Ahmad Ridwan yayi maganar yana kokarin share kwalla, momy tace what? Ridwan ko kusa karka bari inga hawayen ka anan agaban matsiyataci, kuma maqiyinka xaka xudda hawaye ko da alama kar kayi wannan kuskuren.

Momy ta maido kallon ta ga Ahmad Wanda yayi tsaye yana mamaki kamar shi mai dinbin dukiya xaa kira matsiyaci, momy ta fara da "fadin kai! Tana nunashi da dan yatsa wallahi tun bansan ko waye kai ba har naji na tsaneka balle kuma yanxu da naganka kuma sai kayi da kasanin xuwanka nan wajen.

Momy "tace Sannan miya tsayar da motar ka a hanyar mu? Ahmad ya sheqe da dariya sannan "yace nazo nan ne dan yiwa danki albishir da mutuwar sa. Momy ta kalleshi tana fiddo ido waje tana fadin mutuwar sa? yace sosae kuwa.

Momy ta juya ga bodyguard's dinta tana fadin kai !kuyimin shouting din wannan Dan iskan, ku kashe min shi ko kun kasheshi kun kashe banxa inada kuddin biyan diyarsa ko nawa ne.

Bodyguards duk suka saita bindigar su Ridwan ne
"yace nop! momy nop! Momy tah, duk suka tsaya Ridwan yace Kiyi hakuri yake mahaifiyata, karkiyi umurnin a kashe Ahmad banaso akashe shi yanxu, momy tace why? Why my son? Ridwan "yace momy "I want 2 teach dis studip a lesson in life" momy tace dats gud my son.

Ahmad na tsaye yana kallonsu. momy "tace amma duk da hakan baxaa barshi yaje a haka ba Dom a tahiri na baayi wani Wanda ya kawomin takakkaba kuma ya koma lafiya, ta kalli bodyguards dinta tace kai kuyimai tsinan nen duka, taja hannun danta ta ta rikeshi kam suka koma gefen mota suna kallon yarda ake jibgar Ahmad.

Suka fara dukan ahmad wadanda suka xo tare da Ahmad din suka fara firfitowa a mota da wukake a hannun su suna isowa sukaga bodyguards din momy da bindigogi dole suka ja baya Ahmad yasha tsinan nen duka har jamaar area din an taru wajen sosae ana kallon yarda Ahmad keshan duka ba halin isa wajen Dom sauran bodyguards din sun gyaran bindigar su sunyi shirin kashe duk wanda ya isa wajen wannan Command din momy ne ga duk Wanda ya iso wajen ya farka lafiya.

Daga nesa mutane sae hakuri suke bawa momy amma ina "tace sae jikinshi yagayamai yau, taja hannun danta ta sakashi a mota ta kulle sannan tace su shiga mota su wuce ayiwa Ahmad leqis suka barshi kwance cikin jini.

Suna tada motar su suka barwa su Ahmad kura suka wuce! suna wuce wa Ridwan "yace momy ki kira min doctor ji nake kamar ana fixgar min xuciya nasan kawae mutuwa xan yi ya fashe da kuka, momy tayi sauri ta kira family doctor dinsu "tace su hadu gida yanxu, Ridwan bayada lafiya momy "tace yi hakuri my son doctor yana hanya ta ci gaba da shafar sumar kanshi har suka iso gate din gida.

Nidae da naga yarda Ahmad ya jibgu "nace Ahmad hakkin tsohon nan ne yake binka. Abokan Ahmad suka daukeshi sukayi asibiti dashi, aka bashi taimakon gaggawa Ahmad ya samu sauqi da magarib aka bashi sallama yayi alkhawarin shima sae yayiwa maidubu irin dukan da akayi mai a yau din nan.

Barrister for lifeπŸ’‹

Muje xuwa wasa farin girkiπŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„

Mijin barristerβš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–
[22:03, 1/5/2018] Barista: βš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–
MIJIN BARRISTERπŸ’‹

By Barrister S@dy😘

Dedicated 2 my daughters Hafsat Nasir Gwansu nd Seeyamah NuraπŸ’˜πŸ’˜

Jinjinar ban girma ga reader's da baxar ku nake rawa kuna raina aduk inda kuka ina qaunar ku πŸ’˜πŸ’‹πŸ˜˜

Mijin barrister
61-62

βš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–Su Ridwan na sauka gida doctor na isowa suka shiga gida tare, doctor ya shiga bawa Ridwan taimakon gaggawa dom tunda Ridwan yaji labarin auren Mai-dubu yafita hayyacinsa, koda suka iso gida Ridwan baisan waye a kanshi ba, baya gane kowa momy sae kuka takeyi, aka yiwa Ridwan allurai amma har yanxu baya gane kowa.

Mama ce ta fito daki tana waya da malamar da xata yiwa amarya wa'axxi, tana "fadin jamaa sun taru fa ita kadae ake jira"
Baba ne ya shigo gidan da yaji wayar da mama keyi yayi tsaye har ta qare,

Baba ya fara da "fadin banyarda ayiwa Mai-dubu ko wanne "event ba mama tayi tsaye kawae tana kallon baba.

Da misalin qarfe 8 na dare, dangin Mai-dubu sun cika gidan maqil dom xuwa kai amarya, Baba ya kira wayar mama yace taxo ita da Mai-dubu kuma Mai-dubu ta fito da kayanta. Mama ta ja hannun maidubu wacce yanxu ta daina kuka a fili na xuciya take yi,

Kasancewar mama da danginta sunce ta fito cikin jamaa xata daina jin damuwa sosae aranta hakan yasa ta dawo bedroom din mama itada qawayenta aka kulle nata dakin, ana magarib akasa Mai-dubu tayi wanka tayi shiri cikin wata jar atamfa da yellow tayi kyau sosae amma baa saka mata turare ba ance sae xaa wuce da ita.

Mama ta fito dakinta rike da hannun Mai-dubu sae Falon baba. Suna shiga Mama ta xauna akan kujera Mai-dubu ta xauna akan kafet, Baba yayi gyaran murya sannan "yace, Mai-dubu mun haifeki, kuma mun reneki, har kika girma yau Allah ya nuna mana mun aurar dake, kibi mijin ki kuma Kiyi biyayya ga umurnin sa, ya maido kallon shi ga mama "yace Kiyi mata taki hudubar xan wuce da ita gidan mijinta. Mama "tace baban yara ga danginta nan sun taru Dom kaita gidan ta sannan kace da kanka xakaje kaita Baba ya ansa da eh ni xanje da kaina inkaita gidan miji, mama tayi taslima ta fashe da kuka, Baba ya maido kallon shi ga Mai-dubu yace ke tashi muje idan baxata yi miki hudubar ba.

Baba ya tashi tsaye yana fadin tashi muje Mai-dubu ta rushe da kuka mai sauti tana fadin wayyo mamana itama mamar kuka takeyi sosae

Mai-dubu "tace baba Dom Allh bari in dauko kayana "yace maxa ki dauko ki fito, maidubu ta fito tana kuka taje dakin mama ta dauko akwatinta, Xarah ce "tace ya kina Jan akwatayyenki ko munyi dare shiyasa kike shirin kai kanki, Dom nasan kin tsima ko? Suka sa dariya, itadae Mai-dubu sae kuka takeyi mai sauti basu damu da ku kanta ba dom sun dauka hudubar da baba yayi mata ne tasata kuka.

βš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–Maidubu ta kalli qawarta balkisu "tace balkisu dom Allah inason ki taimakeni, balkisu "tace mi kikeso ne qawata Mai-dubu ta bata key din motar da Ridwan yabata "tace dom Allah ki mayarmin da motar nan gidanku,

Dom iyayena basu San anyimin wannan kyautar ba, ta bata dubu darin da momyn Ridwan ta bata, "tace ki ajemin su sae na nemasu, Maidubu "tace sannan ku tashi kowa tayi gidansu Dom yanxu baba xai wuce dani gidan Ahmad sae kuma ta fashe da kuka taja akwatinta ta shigo falon Baba, " Baba "yace muje Mai-dubu ta sake fashewa da wani irin kuka tana dagawa mamanta hannu itama mama kukan takeyi sosae suka wuce suka shiga motar Baba bai tsaya ko ina ba sae gate din gidan Ahmad, maigadi ya bude musu gida baba yashiga da mota suka fito yana gaba Mai-dubu na bayanshi har bedroom din ta,

Suka shiga Baba yayiwa Mai-dubu umurni da ta xauna akan gado ta xauna tana kuka sosae, baba yayi tsaye "yace Maidubu wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Summa tallahi! Idan kika yi kuskuren kashe wannan auren, Nida ke har abada kuma ko lahira bana fatar Allah ya nunamin fuskar ki Mai-dubu sae kuka takeyi, Baba "yace nixan tafi sai da safe, Maidubu tasake rushewa da kuka.

Maidubu na nan xaune tana aikin kuka kuma tana tunanin ko da wacce irin tsiya Ahmad xaixo mata, har ta fara jin tsoro Kasancewar gidan yayi tsaf ba mutsin komi sae kukan tsuntsaye daban daban.

Da misalin qarfe 12 na dare ne Mai-dubu taji tsayuwar motoci a packing space din gidan, Ahmad ne yashigo shida friends din shi suka shigo sukayi adduar da ake yiwa amarya da angonta sukayi musu sae da safe sannan suka wuce akabar ango da amarya.

Sae da Ahmad ya karewa Mai- dubu kallon wulaqanci sannan ya sheqe da Wata irin dariyar qeta, sannan "yace ke miye shirinki na kwana a gidan maqiyinki? me kuke shirin aiwatarwa kaina keda kortonki Ridwan? duk abunda Ahmad yake Fadi Mai-dubu bata tanka shi ba, har saeda ya kira sunan masoyinta Ridwan nan fa.

Maidubu ta "tashi tsaye tana fadin karka sake xaginshi, kayi dani dom nice daidai kai, shi yafi qarfinka kuma yafika ta ko wacce hanyar Mai-dubu bata rufe bakinta ba.

Ahmad ya wanke ta da mari maidubu ta duqe tana kuka, Ahmad yayi dariya sannan "yace yau baxaki rama ba, ya sake sheqewa da dariya ya xauna ya bude ledar da yashigo da ita, ya nemo flat yasaka gyararren xabo daya yaci abun shi shikadae yayi miqa ya tashi tsaye yana fadin Alhmdllh.

"Yaje gefen gado ya dauko Wata bulalar fata tasha mai sosae, ya riqeta kam "yacewa Mai-dubu ke tashi, tayi banxa dashi ya kara da fadin ki tashi nace dom ubanki, maidubu ta tashi tsaye jikinta na rawa tana fadin Allah kayi hakuri, Ahmad ya hade rai sosae, sannan "yace Ashe ke baki ko kai cikakkiyar yar iska ba, tunda har kike da tsoro ya fere iya qarfinshi ya watsawa Mai-dubu bulalar tun tana iya kuka har ta kasa kuka yayimata liqes.

Yana kare dukanta ya fara qoqarin rabata da kayan jikinta maidubu batada qarfin kwatar kanta a hannun Ahmad amma tana bisa bakinta ga adduar.

Ahmad yana qoqarin cire rigar jikin Mai-dubu yaji anbango kofa an shigo ya juyo da sauri Dom ganin ko waye, wasu mutane ne suka shigo dakin kowa da bindiga a hannun shi, Ahmad na ganinsu jikinshi yadau rawa wani daga cikin su yasheqe da dariya yana "fadin kai karamin dan iska. idan kere na yawu xabo na yawu Wata rana dole ne su hadu.

Wani ya kara matsuwa yana fadin kai ka dauka xaka iya guduwa bamu ganeka bane dayan "yace Muna sa ne da duk wani mutsinka, shine muka kwaleka sae yau damu aka kawo ka gidan nan motar mu tana bayan taku Ahmad dae yayi mutuwar tsaye.

Yafara da fadin dom Allah kuyi hakuri nasan nayi kuskure idan kuddin ne gasu can, ya nuna wajen da yatsar sa, "yace amma dom Allah ku barni da raina sae lokacin maidubu ta kallesu da kyau taga irin kayan da tagani ne jikin mutanen nan na video din ta da ya bata, da kuma irin bindigar da tagani a motar Ahmad har ta dauka irinta ce a hannun su hakan ya tabbatar wa maidubu Ahmad Dan fashi ne, tana wannan tunanin taji suna fadin kuddi ba matsalar mu bace. amma tunda mukayo fashi tare kaiko kayimuna sata wallahi yau din nan sae mun kashe ka wae kae ango ko? Sae kuma mutumin tasake sheqewa da dariya.

Mai-dubu ta tashi tsaye tana "fadin Dom Allh kuyi hakuri karku kashe shi, sae kawae dayan su, ya gyara bindigar sa yayi saitin kan Ahmad. Mai-dubu ta riqe bindigar tana kuka, dayansu ya juya bayan bindigar ya kwadawa Mai-dubu a qeya ta Fadi qasa sumammiya. sannan suka harbe Ahmad a kwanya Ahmad ya Fadi qasa dim kuma rai yayi halinshi......

Barrister for life πŸ’‹

Muje xuwa wasa farin girkiπŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„

Mijin barrister βš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–
[10:25, 1/7/2018] Barista: βš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–
MIJIN BARRISTER

By Barrister S@dy

Na sadaukar da wannan shafin ga masoyiyata Zahra Muhammad Mahmud surbajo🀝 marubuciyar zakisan koni waye, wannan littafin yana ban shauqi Allah ya kara mana basira yasa muyi abunda xai anfani jamaa love u dieπŸ’˜ Barrister ta gaisheki.😘😘 πŸ‘πŸ‘

Mijin barrister
63-64

βš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–Suna fita Maigadi ya shigo da gudu ae ko yaga Ahmad har Maidubu ba mai nunfashi, Maigadi ya dauki wayar Ahmad ya kira malam shehu "yace suxo gidan Ahmad yanxu ba lafiya! Malam ya tashi da sauri ya kira qanin Ahmad sukaje tare suna shiga abunda suka ganine yafi qarfin tunanin su. Ahmad kwance cikin jini baya nunfashi, qaninshi ya fada jikin shi yana Kiran sunan sa yana kuka, yana "fadin yaya ka tashi dom Allh, tun nan malam yagane Ahmad bayada rai hakan yasa suka dauke su akayi hospital da su.

Suna shiga aka shiga bawa Mai-dubu taimako gaggawa, Dom har yanxu bata nunfashi amma doctor sunce tana da rai, sannan suka tabbatar wa mahaifin Ahmad da rasuwar danshi Ahmad.

Nan fa suka dau kuka malam shehu ya juri har yanxu baiyi kuka ba, masu kukan ma hakuri yake basu, ya kira Alhj Muhammad "yace suxo hospital yanxu ba lafiya!

Baba ya "tashi gigice yana "fadin ke maman yara tashi muje hospital wae su Mai-dubu na hospital mama ta tashi gigice tana taslima. Baban yara miya kaisu hospital yanxu? baba yace yana wuce shegiyar yarinyar nan ce ta janyo mana magana ki tashi muje.

Baba ya sako riga gaba baya, suka fito sae gate din hospital suna shiga sukaci karo da ana fitowa da gawar Ahmad, baba ya riqe malam shehu yana taslima yana fadin malam miyasami Ahmad ? Waya kashe shi? Maidubu ce ta kashe Ahmad ko malam ?

Maidubu Allah ya isa haihuwar da nayi miki, mai-dubu nayi dana sanin haihuwar ki, Ya Fadi maganar yana kuka, malam shehu ne "yace Haba Alhj Muhammad ka daina furta mummunan kalami akan Mai-dubu, Dan fashine suka shiga gidan kamar yarda maigadi yake yimana bayani itama maidubu har yanxu bata nunfashi, bata San ko waye akanta ba, Dom tayi doguwar suma mama tace na shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login