Showing 21001 words to 24000 words out of 88044 words

Chapter 8 - MIJIN BARRISTER Complete Hausa Novels By Sadiya Barrister.txt

15 Nov 2025

1922

da xan iya yima bayanin halin da nake ciki muyi waya anjuma Ridwan ya ansa da fadin ah ah baby! ah ah baby! kigayamin kawae damuwarki damuwa ta ce.

Maidubu tace kabari sae anjuma pls Ridwan yace baby maganar Waya batayi Kiyi hakuri inganki kinji idan bakyason inxo gidan dom Allah kiyimin alkhawarin ganin ki gidan Nura Maidubu tace OK ba damuwa I will talk 2 my mother Ridwan ya ansa da OK ya saka mata kiss a waya duk da damuwar da take ciki amma sae da tayi murmushi dom taji dadin sautin kiss din da yayi mata

Haka suka kwana kowa da abunda yake tunani har gari ya waye Maidubu ta fito taje ta gaida iyayenta sannan ta fara aikin gida kamar yarda ta saba, tana karewa ta fada toilet tai wanka tafito tayi sallah tayi shiri cikin Wata doguwar Riga ta shadda marrow color wacce tasha kwado da pink din xare anyi kwadon ne daga wuyan rigar har qasan ta duk kwado ne rigar tadan kamata masha Allh tasako sarka da yan kunne pink color masu ratsin marrow ta sako agogon hannu shima pink color ta sako Dan qaramin mayafinta pink da shoe dinta suma pink color amma anyi musu ado da marrow ta yiwa kanta barin turare ta fito tayi wa mama sallamar Dom tunda suka kare waya da Ridwan tagayama mama tanason taje gidan qawarta xarah gobe mama bata hanata ba tace adawo lapia ina gaida amarya yawwa mamana xataji insha Allh

Maidubu na fita ta hau napep sae gidan xarah tana shiga suka rungumi juna itada qawarta suna murya Nura ya fito daga dayan falon suka gaisa sannan yace shine harda ja mana aji ko abarmin aboki tun daxun yana jira Maidubu tayi murmushi xarah tace har fa cewa nayi bara na kiraki amma qememe yace mun wae ah ah bayason adameki inbari kawae har ki fito dom kanki Maidubu ta fiddo ido waje tana fadin ke har yaxo eh wallahi yana babban falo. qawata Ridwan ya kamu fa sosae wallahi cewar xarah kenan duk suka sa dariya xarah ta qara da fadin qawata Kinga yarda kikayi kyau kuwa Mai-dubu dae sae murmushi takeyi Nura ne da yaga idan yakyaleso wannan firar bata qarewa ya kalli xarah yace madam tashi muje ciki ko yaja hannun ta suka shige

A bangaren Ridwan kuwa yana jin sunshige yafito xuwa falon da Mai-dubu take ciki dom yaqagu ya sakata a ido yana shiga qanshin turaren maidubu ne yaduki hancin sa ya isa inda take yana fadin Allah ya taimaki gimbiyata yau har Wata sarauta akeji? Mai-dubu tayi murmushi tace sarauta fa? Ridwan yace eh Nida banajin ta ae gani na kawo kaina ko!

Murmushi tasake yi tana wasa da yatsar hannun ta Ridwan yabi ta da kallo nan Ridwan ya qara yaba kyakkyawar surar Mai-dubu ya axa mata hannun shi akan nata yana murmushi Maidubu tadago Dom sauke hannun shi ya riqe hannun ta yana fadin umm uhmm baby ki bari inshafa koda hannunki ne inshafi wannan lallausar fatar ko! Maidubu na dago kai sukayi ido 4 da Ridwan sae kawae taji yayi mata kwarji kuma taji tsikar jikin ta tayi tsam tayi saurin dauke kanta gefe tana fadin pls Ridwan kadaena kar sufito su ganmu a haka Ridwan bai daina ba har ma yana neman cusa kanshi jikinta yana shinshinar qanshin jikinta ya fara kokarin rungumarta yana shaqen kanshin da jikinta ke fiddawa Maidubu na fadin pls Ridwan ka daena bai kulata ba har sae da ta fara kwalla yana ganin kwalla a idon ta yasake ta yana fadin baby dom Allh kiyi hakuri idan nabata miki rai kinji yasaka hannun shi ya share mata kwalla sannan yace tashi muje dayan falon Maidubu tace nop ku xauna nan kawae

Ridwan yayi murmushi yace minene? Ko tsoro na kikeji? Maidubu tace ba balle inji tsoronka ba naga lokaci daya ka chanxa har wani ja idonka yayi murmushi Ridwan yayi yaja hancin ta yana fadin ae duk kece Maidubu ta fiddo ido waje tana fadin ni kuma? Ridwan yace eh sosae kuwa wannan turare da kikasaka ae dole ne inxautu idan har lafiyata qalau Maidubu tayi murmushi ta rufe idonta da hannayenta shima Ridwan dariya yayi shine kikasa ki batajin kwalliyar tun ban gama saka albarka ba ko tau ki dauke hannun ko kiji ni jikinki ae ba shiri Mai-dubu tasake hannun tana murmushi Ridwan sae kallon so da yake yiwa Mai-dubu

鈿栶煄€馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰鈿朢idwan ne ya fara da fadin baby mi akayi maki jiya? Waya saminke kuka ? Kuma miye sanadin kukanki ? Kigayamin Niko nayi alkhawarin sharemaki hawayenki insha Allh Mai-dubu tayi murmushi sannan tace baxaka iya share min wannan hawayen ba Ridwan yace why? Maidubu ta gayamai komi tsakanin ta da Ahmad tun ranar farko da suka yiwa juna rashin mutunci har xuwanshi gidansu ba abunda ta boye mai har maganar auren ta da Ahmad Ridwan ya jinjina irin biyayyar Mai-dubu da tarbiyarta ga iyaye kuma yaga qarfin halinta na wanke gwabjejen kato da maru Maidubu ta share kwalla a idonta sannan tace kaga ko baka iya share min wannan hawayen ko? Ridwan ya girgixa kanshi yana fadin waya gayamaki?

Kinsan meye Maidubu tace ah ah kibar komi a hannuna kawae xansan abunyi yau din nan insha Allh Mai-dubu ta ansa da OK sukayi firar su ta masoya sannan suka yiwa su Nura sallamah Ridwan yayi juyin duniya akan ya mayarda Mai-dubu gida amma San taqi yarda Dom tana tsoron abunda ya faru tasake faruwa haka ya hakura ta shiga napep shiko ya koma ya dauko motar shi ya wuce gida

Barrister for life馃拫

Muje xuwa wasa farin girki馃憚馃憚馃憚馃憚

Mijin barrister鈿栶煄€馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰馃巰鈿�
⚖🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀⚖
MIJIN BARRISTER💋

By Barrister S@dy😘

Dedicated 2 my daughters Hafsat Nasir Gwandu nd Seeyamah Nura😘😘

Ina alfahari da reader's naga comments dinku da adduar ku gareni ina godiya maras adadi Allah yabar qauna kuna raina dear reader's😘😘😘👍

Mijin barrister
51-52

⚖🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀⚖Maidubu ta koma gida tana kwance jikin mama sae tunanin Ridwan dinta takeyi tana murmushi har lokacin islamiyyah yayi kusa ta tashi ta fara shirin tafiya tayi shiri Kiran uniform dinsu black nd white tafito fes da ita tayi wa mama sallama ta wuce sae gidansu qawarta Balkisu ta gaisa da innar balkisu. Balkisu tafito suka dau hanya suna tafe Maidubu na bata labarin Ridwan da irin soyayya da suke sha Balkisu tajiwa qawarta dadin samun masoyinda ke sonta da gaskiya Maidubu tace qawata matsala daya nake hangowa Balkisu tace gaskiya ne qawata dole Kiyi tunanin akan matsala Baba Maidubu tace naso inyi biyayya ga wannan auren da iyayena xasu min amma wallahi Balkisu haduwa ta da Ridwan banajin xan iya rayuwa da wani idan ba Ridwan ba Balkisu ce tace yaushe xai xo mu gaisa Mai-dubu ta fiddo ido waje tana fadin me? Kinason ayi kusan kasheni idan aka San ina kula wani ko? Balkisu tayi dariya tace Sarkin tsoro kawae ae ba gidanku xai shiga ba ku tsaya ta bayan Layin nan mana idan muka gaisa sae mu dawo tare Maidubu tace eh hakan yayi murmushi Balkisu tayi sannan tace tau yaushe ne yakama yaxo Mai-dubu tace yau dom wallahi koni nayi missing din shi Balkisu ta kalleta tana riqe baki Maidubu tayi murmushi tace lafiyarki kuwa?Balkisu tayi dariya tace ae naga kinfi qarfinane duk suka sa dariya suka taba hannu da wannan firar har suka iso islamiyyah suka dau darasi aka tashi kowa tayi gidan su

Maidubu na shiga ta gaida mamanta ta dauko wayar mama tayi dakinta tana shiga ta rage kayan jikinta ta haye makeken gadonta ta janyo wayar tasaka kiran Ridwan sae da kiran ya tsinke sannan ya kira tayi picking

Suka gaisa Allah ya jima da ran gimbiyata sarauniya a birnin xuciya ta Maidubu sae murmushi takeyi Dom tanajin dadin irin tsintsar qaunar da Ridwan ke nuna mata tace duk wannan ni kadae kedasu? Sosae kuwa ae kin wuce nan ma wallahi baby bantaba son wata yarinya ba kamar yarda nikeson ki Kinada abubuwa da dama wadanda duk namiji yana gurin samun su tare da Matar da zai aura baby ki tayani da addua Allah yasa ke mata tace Mai-dubu tayi shuru tana mai tausayawa Ridwan dama ita kanta Dom tasan xatasha wuya bata wasa ba a gidan Ahmad Ridwan ne yace hello Mai-dubu tace inajinka fa ya kinyi shuru ko bakyasona tayi dariya yace gayamin tasake dariya tana fadin har na isa ince haka Ridwan yace har kin wuce kuwa duk suka sa dariya

Maidubu ta fara da fadin idan kanada time kaxo area dinmu anjuma xaku gaisa da Wata Frnd dita Ridwan yace idan nazo zan ganki dae ko ? Maidubu tayi dariya tace eh yace yawwa baby zan xo da magarib kinji Maidubu ta ansa da Allah ya tsaremin kai Ameen ameen baby ta ki kula min da kanki kinji Mai-dubu ta ansa da OK bye

WAYE RIDWAN
Ridwan Dane ga Alhaji Aliyu Alkhali Alhaji Aliyu yakasance mutum mai dinbin dukiya kuma mai sadaka maiyi Dom Allh Alhaji Aliyu Tsohon alkhali ne kuma har yanxu yana sharia Allah ya bashi da daya tilo Wanda yake ji dashi sosae wato RIDWAN amma yana yayyu mata har guda 3 Ridwan mutum ne mai hakuri mai tarbiyya Wanda baya nuna ko dan gidan waye sae dae ga Wanda yasanshi saboda da mai kuddi da talakka duk nashi ne mafi yawan frnds din shi ma talakkawa ne ya biyo halin babanshi sak yayi karatu mai tsawo yaje har waje yayo karatu inda yakaranto yarda ake xanen gini wato ( Architecture) yadawo gida Nigeria ya sami aiki labarin Ridwan kenan

CIGABAN LABARI
⚖🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀⚖magarib nayi Mai-dubu har tayo wanka tayi shiri cikin Wata atamba baqa mai manyan fulawoyi yellow color Mai-dubu tayi shiri kuma tayi kyau sosae abu ga mutum mai Dan haske tasaka basin abu masha Allah

Baba ne yashigo gidan yashiga dakin Mama suka gaisa yanemi kujera ya xauna yana fadin maman yara wae Ahmad ne yaxo yace yanason Maidubu ta riqashi gidan abokin shi dom koda akayi bikin su baya nan jiya yadawo mama tace ina yaje ne wae yana Dubai wajen business din shi amma kinga yarinyar nan bata yagayama kowa baya nan ba mama tace kuma kullum suna waya Mama tayi shuru sannan tace ta rakashi kuma baban yara miyasa baxaije shikadae ba tace ah ah Baban yara nifa banason fitar nan ta saurayi da budurwa ya jira har ayi bikinsu mana miya ragene iyaka fa Wata biyu yanxu anyi bikin basae suje duk inda yakeso ba Baba yace wannan gaskiya ne amma muyi mai uxuri tunda wannan shine na farkonshi ko Mama tace tau yagayama ita Mai-dubu din Baba yace bansani ba amma kije ki gayamata da kanki

Mama ta fito tayo bangaren Maidubu tana shiga ta hango Maidubu kwance akan gado ta iso wajen Mai-dubu itako maidubu ta tashi xaune tana fadin sannu mamana. yawwa Mai-dubu ko dama kinsan da maganar Mai-dubu tace maganar me mama? Mama tace ta fitarki da Ahmad mana naga kamar ma har kiyin shiri Maidubu tace Ah ah wallahi mama ni bansani ba

Mama tace tau yana mota yana jiran ki wae xaki rakashi gidan abokin shi da yayi aure Maidubu ta turu baki tana fadin ni mama gaskiya ba inda xanje
Mama tace Haba yar mamarta tashi kuje kinji Maidubu sae turu baki gaba takeyi Mama tace banason taurin kai fa ki tashi nace ko Maidubu ta tashi tana turu baki sae kuma ta tuna da Ridwan dinta tasan yanxu yana waje yana jiran su Maidubu ta kalli Mama tace Mama don Allh aramun waya mama tace xaki tashi ko sae naci mutuncinki mi xakiyi da waya Wanda xaki kira yana waje yana jiran ki Maidubu ta tashi badon taso ba tafito

A ranta take rayawa ae duk laifin balkisu ne dom inda taxo tun daxun da yanxu ina tare da Ridwan dina ta tashi ta sako hijab tace natafi mama tace adawo lafiya

Maidubu na fitowa ta bude mota tashiga batare da tayi magana ba shima Ahmad baiyi mata magana ba yaja mota sae bakin wani supermarket yayi packing yafito yace ke kifito Maidubu tayi kamar bata jishi ba yakara da fadin ke ko bakyaji na ne yayi maganar da tsawa itama maidubu ta mayarmai da martani da irin tsawar da yayi mata tace baxanje ba Ahmad bai tanka ta ba ya wuce abun shi cikin supermarket din ya dade bai fito ba har Mai-dubu ta fara jin tsoro don inda Ahmad yayi packing yanada dubu kuma ba mutane da yawa Maidubu na waige waige taji kamar ta axa hannun ta akan wani abun a gefen kujerar da take xaune ta sa hannu ta dauko ae ko taga bindiga gaban Mai-dubu ne yahau dukan ukku ukku sae da ta karewa bindigar kallo tace ni Mai-dubu na shiga ukku bindiga kodae Ahmad yasheni yakeson yayi wayyo Allah ni maidubu na shiga ukku taji motsi tayi saurin saka bindigar cikin rigar ta waya ce tayi kara maidubu tayi saurin kallon inda wayar take taga an saka my son sunan Wanda ke kira

Kiran na katsewa taga wayar ba pattern taga wayar cikin videoting ta dauko tana tabawa taga har yanxu ma video ting din take tayi stopping dinta sannan ta bude video din wasu mutane ne tagani ko wanne su ya rufe fuskar shi da baqin kyalle taji wata mata tana fadin na shiga ukku Dom Allh karku kasheni ga kuddi can ku dauka tana kallon ta hango Ahmad yana fitowa a supermarket din tayi saurin kashe wayar gaba daya ta sakata cikin kirjinta Ahmad yashigo motar jikin Maidubu sae bari yake yi Ahmad ya kalleta yace..........

Barrister for life💋

Muje xuwa wasa farin girki👄👄👄👄

Mijin barrister⚖🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀⚖
[10:19, 1/2/2018] Barista: ⚖🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀⚖
MIJIN BARRISTER💋

By Barrister S@dy😘

Dedicated 2 my daughters Hafsat Nasir Gwandu nd Seeyamah Nura daughter's lyk no others😘😘😘

Mijin barrister
53-54

⚖🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀⚖Ahmad na shigowa motar yaga jikin Mai-dubu sae kaduwa yake duk da ana sanyi sosae amma ta jike shataf da xufa har ruwan xufa nayimata tsiyaya Ahmad yace ke lapia? maganar da Ahmad yayi sae da Mai-dubu ta xabura alamar taji tsoro tana fadin dom Allah kayi hakuri ka maidani gida Ahmad yayi mamakin duk irin rashin kunya na Mai-dubu amma yanxu duk ta susuce Ahmad ya dauka dom yabar ta a mota ne kila taji tsoro sae kawae yaja dogon tsaki sannan yaja motarshi suka dau hanyar gida

Yana tuqi Mai-dubu sae raba ido takeyi ta matsu itadae taga tafita motar nan lapia Maidubu na nan sae tunani takeyi fatar ta kawae idan ta fita motar nan lapia taje taga wannan video din shin yan tashi ne kuma idan yan fashine akwae Ahmad acikin su ko kuwa tabbas idan Ahmad yana ciki yau din nan xata nunawa babanta wannan video din da wannan tunanin har suka iso kofar gidan su Mai-dubu

Ahmad yaga wata motar gefe shiko yayi packing gefe a kofar gidansu Mai-dubu yana tsayar da mota Maidubu ta bude motar ta fito shima Ahmad din yafito yana fadin ke! Maidubu ta tsaya kawae batare da ta juyo ba Maidubu ko tsayin da tayi dom ta hango Baba xaune a kofar gidane amma inda baba bayanan da baxata tsaya ba

Ahmad ya fito mota ya iso wajen da Mai-dubu take tsaye yace ke wannan ledar uban waye xai kaimiki ita gida? sae da maidubu ta karemai kallon wulaqanci sannan tace banason ne Ahmad yace ai dole ne kije da ita ko bakyaso kina nufin inyi hasarar kuddi na ne ko miye? Maidubu tace Oho ka kaiwa iyaye dom sunfini bukata. yayi murmushi sannan yace bada sunan su na sayo ba kuma amatsayina na mai kuddi mai dukiya da bakadan ba iyayena sun fi qarfin wannan ke ko qarshen wulaqanta talakkana kenan masu yimin hidima ina biyansu kuddi don suci abunci tau kosu sunfi qarfin wannan balle iyayena

Nasayo miki wannan ne dom nasan baa taba cikin irinshi a gida ba Dom haka ki ansa kije kuci keda
wancan tsohon birin Maidubu ta juyo da qarfi ta qarewa Ahmad kallo sannan tace idan kasake furta mummunan kalami akan mahaifina wallahi xamuji xafin juna Ahmad yayi dari yace kara dae ki ansa dom nasan baa taba cikin irin shi ba wannan ma na sayo maki maras dadi sosae Dom banason insaba naki da dadi ina na aureki na fara axabtar da ke na fara baki qanxo da kwaki a matsayin abuncin ki ki tuna da irin wannan dadin ki fara bin maxa suna baki indomie da eggs ki basu kanki daga qarshen a haifamin Dan shege

Ran Mai-dubu yayi mummunan baci tace eh tabbas xan haifi Dan shege kamar yarda na auri shegen ko maras xuciya banda baisan baa qaunarshi ba ran maxa ya baci Ahmad ya daga hannu dom dauke Mai-dubu da mari amma sae yaji anrike mai hannu

Ahmad ya juya ga Wanda ya rike shi yana fadin kaiko waye kai? kasake ni kafin inci xarafinka dan gidan matsiyata Dom da ganin wannan kirar taka kaci tuwun dawa ka qoshi kasake ni kafin in dauke mummunan mataki a kanka dom bana ko rabar talakka balle ka rikeni amatsayinka na talakka matsiyaci Ridwwn dae sae murmushi yakeyi dom yayi imanin Ahmad baiyi dukiyar dan ga aikin gidansu ba Ridwan yace eh naji duk wanna abun da ka fada akaina tabbas hakane amma mi tayima da har kake kokarin dukanta?

Ahmad ya fige hannun shi ya shafe inda Ridwan ya tabashi sannan ya dauke maidubu da mari hannun shi na sauka na Ridwan na hawa shima ya wankeshi da mari Maidubu ta dago dom ganin waye wannan sae kawae tayi ido 4 da Ridwan tana fadin Ridwan muryarta na rawa Ridwan yace Baby waye wannan ? Ahmad dae yabisu da kallon mamaki

Babane ya iso wajen yana fadin kai! kai! Lafiya? Maidubu ta kasa yin magana sae kallon Ridwan da takeyi idonta na fiddo kwalla Ahmad ne ya fara da fadin wae Baba har wannan matsiyacin yayi hannun duka na Baba ya maido kallon shi ga Ridwan yana fadin kai lafiyarka qalau kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login