Showing 39001 words to 42000 words out of 88044 words

Chapter 14 - MIJIN BARRISTER Complete Hausa Novels By Sadiya Barrister.txt

15 Nov 2025

2016

batada hankali ne?. ya kalli shigarta yaga babu alamun hauka a tare da ita.

Barr. Maidubu "tace tabbas banada hankali indae akan Ridwan ne! kuma ba book ba, wallahi ko kai xan iya taunewa idan kayi qusquren taba Ridwan, sae lokacin Ridwan ya dago kanshi Dom tunda yafadi sunan sa ya rufe idonshi kwalla na kwaranya. yana bude idonshi sukayi 4 'eyes da Maidubu ya rugo da gudu Dom rungumarta, amma ina badama, "prison officers" suka hanashi isa wajenta.

Barrister maidubu da kanta ta karaso wajen Ridwan, "tace kayi hakuri Ridwan ko sun hanaka isa wajena karka damu kaji, insha Allah akwae ranar da xamu kwana a daki daya sae inga uban da xai fiddaka a dakinka na aure.

Maidubu ta maido kallon ta ga mai rubuta sunayen "tace kai "case" din Ridwan xai koma court yau kasani! Dom haka karkayi gangancin sako sunan Ridwan cikin book nan. Ta juya xata wuce mutumin ya kalli wani police "yace kai ku kama min wannan karamar yar iskar ayimata "discipline" police din na isowa Maidubu ta fiddo I.D card dinta ta nunamai, batare da kowa yasan mi ta nunamai ba. Police din Yayi saurin tsayawa chak. ta watsa mai harara ta wuce tashiga mota tajata da irin gudun da tashigo sae da ta barmusu kura a wajen tafito

Motar da suka shiga tare da ta Maidubu Ashe JUSTICE ALIYU ne yashigo yana isowa ana rubuta sunan Ridwan JUSTICE yaja ya tsaya yana hawaye. Tunda maidubu ta isowa wajen Justice Aliyu yabita da ido yana kwalla. Har ta taune book din sae da JUSTICE yayi murmushin jindadi dom yasan matsalar ta ragu Dom yanada damar sake saka kara ko a yanxu duk da bayada tabbacin nasara Dom wannan shine karo na 4 da yake sake mayarda case din Ridwan court amma sae justice tayi watsi da qarar. Maidubu tace yanxu babu xancen Executing din Ridwan gobe tayi maganar da ixxa. JUSTICE sae binta kawae yake da ido yana yimata kallon mamaki Dom shi yama kasa magana.

Tana fito yaje ta mayarda maganar Ridwan court kuma ranar Monday xaa fara shariar sa kasancewar yau Friday ne.

Maidubu ta fito daga court ta dau hanyarta ta xuwa gidansu Balkisu, tana tafiya Wata motar na binta a baya har ta iso tana fitowa mota mutum ya fito a tashi motar yana "fadin Maidubu! Maidubu!! Maidubu!!!. Barrister tayi banxa dashi xata shige gidansu Balkisu kenan mutumin "yace Maidubu nine fa ubanki! ae da sauri Maidubu ta tsaye chak! ta juyo tana kallon shi sae da ta karemai kallon mamaki sannan "tace Baba! Baba ya fashe da kuka yana "fadin maidubu ina kikaje? Maidubu munyi neman ki har mun gaji. Maidubu Dom Allh ki yafemin kuma ina kika sami mota? Allah yasa ba duniya kikabi ba Maidubu.

Maidubu ta kalleshi "tace Ubana fa kace? Ae banada uba inadai da uwa! kuma miye na kuka? idan ma nabi duniya ae addua kayimin, dom haka bakomi bata kara kallon shi ba, ta shige warta gidan .

Baba yayi kukan dayasani sosae yana "fadin Maidubu kece yau da Bakin ki kike gayamin magana a yau. keda ko kallona bakyayi a lokacin da nake magana, tabbas duk abunda ya faru ni najawa kaina nayi nadamar abunda nayiwa ya'ta.

Maidubu na shiga gidan tagayama su inna abunda ya faru da taje prison sannan ta gayamata yarda sukayi da baba a kofar gida, inna taji dadin jin baba ya gane qusqurenshi da kuma nadamar sa.

"Baba yaja motarshi . ya shiga da sauri yayi gida yana shiga ya fashe da kuka ya gayama mama yaga Maidubu har yayimata magana tayi kamar bata gane shi ba.

"Mama dake kwance tana jinya! ta tashi da sauri tana fadin da gaske baban yara kaga Maidubu? Baba "yace yanxu haka tana gidansu Balkisu mama ta tashi da sauri ta dauko gyalenta suka fito xuwa gidansu Balkisu. mama na fadin Alhmdllh, Allah Sarki Ashe inada rabon sake ganawa dake Maidubu! suna shigowa sukaji tattaunawar da inna keyi itada Maidubu.

"Inna "tace Alhamdulillah, tunda Babanki ya gane qurenshi Maidubu sae ki shirya in maidaki gida kinji. Barr Maidubu "tace inna baxan koma gidanmu ba, banason xama achan, Baba ne yashigo yana fadin ae dole ki koma tunda mune iyayenki .

"Inna ta tashi tsaye tana "fadin ba dole ba kam, idan dae taga dama idan ko tace baxata koma ba, ba ko inda xataje, Baba "yace Ashe ko xan kaiki court wallahi kinyi Kadan ki mallakemin yarinya.

Maidubu da tun shigowar su ta rungumi mamanta suna murnar ganin juna, mama "tace Maidubu ina kikaje yau tsawon shekara 7 ? maidubu dae tayi murmushi lokaci daya kuma ta share kwalla, jin baba na maganar kai inna court ne yadawo da ita garesu ta saki mama tace me kace baba? Baba "yace idan taki bamu yar mu "nace sae inkaita court.

" Barr Maidubu "tace wallahi Baba idan kayi qarar inna da kaina xan tsaya mata a court. Baba yace Eyyeh to wallahi ko xaki mutum sae kin dawo garemu Dom munfi kowa qaunar ki a duniya.

Duk basu gane inda maganar maidubu ta dosa ba, Dom sun dauka tana nufin xata biya kuddi ne a tsayawa inna Kasancewar daga mama har baba duk basusan shekarrun da tayi bata gari tana wajen karatu ba .

"Mama "tace kul, Maidubu uba ubane duk yarda ya xama Kiyi hakuri da naki uban kinji! nan fa aka sasanta amma Maidubu taqi yarda ta koma gida tayi xamanta a gidansu Balkisu.

Magarib nayi balkisu ta fara shirin xuwan farouq, yaxo ya ga guardians din Balkisu an tsayarda ranar baki nan da Wata daya mai xuwa .

"Yau takama "Monday" ranar xa'a fara sauraren shariar Ridwan.

Maidubu tayi complete dress na lawyoyi tasako "black GownπŸ‘¨πŸ»β€πŸŽ“ da fatar shirt a ciki da hular layoyi Golding color ,ta sako farin glass dom baa saka ko wace kalar glass a court idan ba fari ba, tafito da cover shoe dinta plate. Dom baa sako hellshoe a court doka ceβš–

"Kyawon da Barr. Maidubu tayi bansan ta inda xan fara misaltashi shi ba, tayi kyawo masha Allah. Ta fito a "Barrister dinta sak. Innah tayimata fatar nasara sannan tafito,

Taja motarta bata tsaya ko ina ba sae gate din court.

" Kuma Justice Usman ne xai sake xaman shariar ko yanxu. Dom anso ayi Appeal din shariar amma San maidubu taqi yarda "tace shidin nan takeson tayi hakuri yasake shariar Ridwan ko yanxu.

Hakan yasa JUSTICE USMAN yake yiwa Ridwan kallon gawa, Dom yanada tabbaci shine da nasara akan Ridwan.

"Court ta cika da mutane masu xuwa kallon sharia, Barrister maidubu na shigowa, JUSTICE "yace Alhmdllh Barrister da ake jira ta karaso, barrister wace take kare wanda ake kara RIDWAN! ya dago kai da sauri Dom ganin wace xata bashi kariy, ae ko sukayi ido 4 da Maidubu .

"Ridwan ya fiddo ido waje yana fadin baby miya kawoki nan? Barrister Maidubu ta daga mai hannu tayi shhhhhhhhhhhhhh fuskarta ba alamar wasa ko dariya.

"Tana fadin "don't call me ur baby, I am not ! my name is Barrister Maidubu Muhammad I stand here becouse of u, nd I will Fight for ur right, ta juya ga JUSTICE tace.........

Barrister for lifeπŸ’‹

Muje xuwa wasa farin girkiπŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„

Mijin barristerβš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–
[16:03, 1/12/2018] Barista: βš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–
MIJIN BARRISTERπŸ’‹

By Barrister S@dy😘

Dedicated 2 my daughter's Hafsat nd Seeyamah😘

Kina raina babbar qawata soyayya ta dake bata qarewa baayi kamar ki ba kuma baxaayi kamar ki ba a birnin xuciyar Barrister kin nunamin qaunar a gabana kuma kinyi hakan a bayana Zarah Abdullahi Sokoto( Mrs Nura) gaisuwar Barrister gareki lodi lodiπŸ’‹πŸ‘

Mijin barrister
79-80

βš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–Barrister Maidubu ta maido kallon ta ga Justice Usman tace My lord Sunana Barrister Maidubu Muhammad lawyer dake kare Wanda ake kara wato accused person.

Ta fadi maganar tana nuna Ridwan da yatsar hannunta
RIDWAN sae bin Barr. Maidubu kawae yakeyi da ido yana kallon yarda take moving before d judge har yanxu Ridwan bai yarda da Maidubu tayi karatun law ba. shi kallon ma tausayi yake yimata kar justice yagane ba Barrister din gaskiya bace ya kaita prison dom shi ya dauka tayi acting din Barristers ne kawae Dom ta fiddashi.

Sae kuma yayi mamakin irin kalaman da take furtawa yarda take fadar chapters na CONSTITUTION daki daki Ridwan dae yabita da ido kamar wani soko .

Friends din Barrister Maidubu sunyi mamakin irin qoqarin da Maidubu keyi a court duk da wannan shine karo na farkon da ta tsaye gaban Real Judge Dom bawa wani kariya.

Barr. Maidubu ta gayama court Ridwan bayada sa hannu a kisa Ahmad tace Ahmad ya Kasance Dan fashi. wato (Armed robber)

Lawyer din Gonnati ya tashi tsaye yana fadin" Objection my lord "baikamata abokiyar aikina "Barrister Maidubu ta rika fadar munanan kalamai ba ga late Ahmad, dom tana alakantashi da laifin Fashi kai tsaye bayan batada shaidar hakan wannan yana nufin bata mai suna ga late Ahmad.

Bayan kowa yasan Alhaji Ahmad mutumin kirki mai kamun kai kuma hanshaqin Dan kasuwa Wanda kowa yasan sanaar sa .
Justice yace Barrister ki saisaita kalamanki Barr. Maidubu ta sunkuyar da kai tace Thank u my lord.

Maidubu ta maido kallon ta ga lawyer din Gonnati tana murmushi tace Barrister ko xaka iya gayawa wannan court din ko miye sanaar late Ahmad.

Lawyer din yayi shuru sannan yace ba dolene sae court tasan sanaarsa ba don ba abunda muka xo yi ba kenan anan.

Barr. Maidubu tayi murmushi tace Point of correction Barrister. Court ko keson sannan ko miye sanaar late Ahmad. Idan har ko baka San sanarsa ya tabbata Dan fashi kenan.

Lawyer din Gonnati yace My lord late Ahmad yana kasuwanci ne a Dubai Barr Maidubu tace ko xaka iya fadar irin kasuwancin da late Ahmad keyi a dubai?

Lawyer din ya juyo ga maidubu yace late Ahmad yana dai kasuwanci a dubai Barr. Maidubu tace ko xaka iya fadar sunan company ko Wata masana-antar da yake aiki dasu ko? Kodaya mallaka amatsayinshi na hanshaqin dan kasuwa kamar yanda kace ?

Lawyer din Gonnati yace Banada Masanniya akan wannan. Amma yana aikine da companyn Sutura wato wa danda ke kirar clothes sunan companyn ne bansani ba.

Barrister Maidubu tayi murmushi tace ae ko akwae bukatar musan wannan.

Barrister Maidubu ta kalli Justice tace ya mai girma mai sharia ina neman wannan court mai alfarma mai adalci data daga wannan shariar nadan wani lokacin Dom gabatar da kwararrun shaidar da xata gansar da wannan court.

Sannan ina neman wannan court mai adalci dataai da Maaikatanta muje Dubai tare Dom gane gaskiyar waye late Ahmad

Sae da Justice yayi murmushin qeta ya karewa Barr. Maidubu kallo sannan yace Barrister anbaki damar yin bincikenki na kwana ukku kacal Kuma wannan adjoint din da xan yi shine na qarshe a shariar RIDWAN.

Maidubu ta sunkuyarda kanta tana fadin nagode ya mai girma mai sharia.

Justice yace the case is adjoint to 11 January 2018.

Mutane sun fito shiko Ridwan ansaka shi a mota ankoma dashi prison. Ridwan duk kanshi ya daure da wannan sabon alamari da yagani.

Barr. Maidubu ta rungumi qawayenta suna murnar ganin juna sun jinjina ma qoqarin Maidubu ba Kadan ba sannan suka ce Barrister wannan kyakkyawan gaye haka ai dole ki rude. Ita dai Barrister maidubu sae murmushi take.

Justice Aliyu ne ya fito a court din ya sami su maidubu tsaye shima ya tsaya yace Barrister duk suka juyo Kasancewar dukkanin su barrister's ne.

Yace Barrister Maidubu sannan ta Dan matso kusa dashi Dom ita bata ma San koshi waye ba .

Justice Aliyu yace nine Mahaifin RIDWAN Wanda kike bawa kariya, Maidubu ta fadi qasa tayi knelling agaban justice ta gaidashi ya ansa yace mata tashi tsaye, ta tashi ta sunkuyar da kanta.

Justice yace Dom Allah waye ke? Barrister ta sunkuyar da kanta. Justice yace kuma waya turuki ki tsayawa Ridwan a sharia? Justice yace Kiyi haquri kinji Barrister wahalar banxa kawae xakiyi Dom wannan shine karo na 5 danake saka kara amma JUSTICE USMAN yayi watsi da ita. bakiji ko yanxu yace xamanda xaayi ranar 11January shine na qarshe ba ko yanxu nasan duk hujjar da xaki bayar a court JUSTICE USMAN watse xaiyi da ita.

βš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–Sae da Barr. Maidubu ta sako idonta cikin na JUSTICE tace wallahi! Wallahi! Wannan karon bayada nasara akan Ridwan kuma shine xaiyi wannan shariar baxanyi appeal dinta xuwa ko ina ba.

Sae da JUSTICE ya karewa Barrister kallo sannan yace idan kika fiddo Ridwan kin gama min komi a duniya kuma ba abunda baxan iya baki ba daga naira daya har Billion dubu. Barr. Maidubu tayi murmushi tace bana bukatar komi a wajenka kayimin fatar nasara kawae.

JUSTICE ya fiddo ido waje yana fadin bakyason komi? Tace eh!. JUSTICE yace Dom Allah waye ke? kuma miye tsakaninki da Dana RIDWAN? Barr tayi murmushi tace lokacin da Ridwan xai fito prison xaka San koni waye I promise u. Abun ya daurewa Justice kai yace tau waye kuma wannan? A ranshi yake rayawa kodai yarinyar nan ce da tayi so wato Matar late Ahmad ta turu wannan barrister din sae kuma ya tuna momy tace babanta ya koreta. JUSTICE yace ina yi miki fatar nasara.

Duk abunda akeyi momyn Ridwan bata sani ba Dom Justice bai gayama ta ba Dom yasan ko yanxu basu nasara Dom Justice watsi kawae xaiyi da shariar.

Barr. Maidubu taja motarta ta koma gidan inna ta gayama inna maganar tafiyarta inna tayimata fatar nasara a ranar bata kwana NIGERIA ba ta shiga jirgi sae Dubai itada maaikatan court guda 2 itace ta 3.

Barr Maidubu tayi anfani da ragowar kuddin da yaya Bello ke tura mata lokacin tana INDIA

Sun je a company dinda aka ce yana aiki dasu suka tanbesu amma mutanen suka ce su basu ma sanshi ba sunyita bincike babu wani company da late Ahmad yake aiki dashi a Dubai kuma company daya ne babba nayin clothes a can. Kwanan su 2 acan. Suka dawo gida NIGERIA kuma gobe ne xama na gaba a court kuma na qarshe.

Barrister for lifeπŸ’‹

Muje xuwa wasa farin girkiπŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„

Mijin barristerβš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–
[19:03, 1/18/2018] β€ͺ+234 704 645 3026‬: βš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–
MIJIN BARRISTERπŸ’‹

By Barrister S@dy😘

Dedicated 2 my daughter's Hafsat nd Seeyamah

Kina raina sister Zarah amaryar February amarya kuma uwargida a gidan Nura makers Allah ya nuna mana February musha bikinku(Mrs Nura makers)😘 idan yayi laifi ki riqa hakuri karki kulle mai daki kuma karki dauko wuka Dom wallahi sae yayi hijira yabar gidan baki daya🀣😜😜

Mijin barrister
81-82

βš–πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€βš–Maidubu na kwance da dare ta kasa bacci tana tunani ko ya shariar gobe xata kaya.
Da misalin qarfe 12:00 na dare ne wayar Barr. Maidubu tahau ruri tayi saurin dauko ta tasaka silent sannan tayi picking call din, da mamakinta na ko waye yake kiranta da wannan daren?

Barr. Maidubu na dauka taji muryar namiji yana fadin Assalamu alaikum! Da fadar ina magana da Barrister Maidubu. tace eh! yace yawwa kina waya ne da Justice Usman Sahabi.

Barrister Maidubu tayi saurin danna wayarta (recording) tace banji ba waye kai yace kina magana da Justice Usman sahabi Barrister tayi murmushi tace Ranka ya Dade ya gida? suka gaisa da girmamawa.

Justice Usman yace nasan bakisan dalilin da yasa na kiraki ba kuma bakisan inda nasamu nonbar wayar ki ba kuma kin matsu kisan duk wannan ko?

Barrister tace sosae kuwa. Justice yayi murmushi mai sauti yace maison Dan tsuntsu Shike biyarsa da jifa.

Justice yace inason Kiyi Stepping back ga wannan shariar ta RIDWAN Dom bakyada nasara.

Bara kiji na riga nayi niyyar kashe Ridwan sae da Barrister ta runtse idonta lokacin da taji an kirawa Ridwan mutuwa Barrister tace me Ridwan yayima ne ? da har kake yimai fatar mutuwa.

Justice yace justice Aliyu mahaifin Ridwan yakai dana prison na tsawon 25years yasamin bakin ciki na dan lokaci. Niko ina shirin samai na har abada xan sashi kukan da bayada magana a ranar da nayi Executing danshi niko xan kwana ina murna a wannan ranar.

Barrister Maidubu tace baxan taba yin stepping back ga wannan shariar ba kuma kasani wallahi Ridwan yafi qarfinka.

Justice yace barrister karkiyimin taurin kai idan kuddi ne matsalar ki ni xan iya wadataki da kuddi daga naira dubu har billion 3.

Maidubu tayi murmushi tace kuddi ba matsala ta bace kuma bana bukatar kuddin ka.

Justice yace tunda nabi dake ta lalama kinqi tau bara kiji wallahi xan iyasa akawar dake daga doron qasa akan wannan maganar kuma nasan kina son Ranki.

Kuma wallahi nadau alwashin kashe duk Wanda yakeson kawo min matsala akan wannan case din ki sani.

Barrister tayi murmushi tace ae tunda nayi karatun law yakama ta kagane rayuwata ba komi bace, kuma ko baka fada ba nasan rayuwa ta tana cikin hadari I want u to bear dis in ur mind. Wannan shariar yanxu na fara ta kuma baxan daina ba har sae ranar da nayi nasara akanka.

Justice yayi murmushi yace tunda kinyimin gardama wallahi nayimiki alkhawarin duk ki kayi qusquren fita gobe Dom xuwa bawa Ridwan kariya a court.
wallahi! wallahi!! Wallahi!!! sae dae akai gawarki a court badae kije a raye ba.

Barrister Maidubu tayi murmushi tace idan har kayi nasara akan Ridwan sae bayan raina insha Allh idan dae bana raye na yarda xaka iya kasheshi niko idan har ina nunfashi na dau damarar yakarka.

Justice yayi dariya sosae sannan yace ki fara yiwa kanki kallo gawa daga yanxu xuwa gobe da safen da xakije court.

Barr. Maidubu ta kashe wayarta ta tashi tsaye tana safa da marwa a dakin hankalin Barrister yatashi ba Kadan ba dajin kalaman Justice Barrister bata yi bacci ba har gari ya waye

A bangaren Justice Usman kuwa Barrister na kashe wayarta yayi mamakin irin taurin kanya yana yimata baraxana da mutuwa amma batako damu ba .

Yayi murmushi yace Barrister ki kira kanki da mai kararren kwana.

Ya daga waya ya kira wani sukayi Wata maganar da bansan me suke cewa ba ya kare ya kashe wayar yana Wata irin dariya qeta.

Barrister Maidubu batayi bacci ba har asuba tayi sallah taci gaba da addua har gari yayi haske.

Ta tashi ta taya Balkisu aikin gida tana yi tana tunanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login