Showing 54001 words to 57000 words out of 88044 words
Chapter 19 - MIJIN BARRISTER Complete Hausa Novels By Sadiya Barrister.txt
take bukata a bangaren kayan sakawa.
Haka Barrister ta kafa jibgar kaya sae da tagaji dady yace ta kara tace ae sun isa dady yace idan ta gaji ne Aunties din Ridwan su tashi su cigaba da xabar mata kayan sawar suka kafa jibgar kaya suma.
Dady yace Idan Kin huta my in-law kije gefen kananan English wears kenan. da kuma under wears ki fiddo masu yimiki kinji.
Barrister ta russuna har qasa tana fadin nagode Dady Allah ya kara girma duk suka amsa da amin.
Har Barrister xata wuce dady yace ta tsaya yacewa Ridwan Son katashi kaje ka taya My in-law fiddo kayan dom naga tagaji sosae ae Ridwan kamar jira yake yi yatashi da sauri yace tau dadyna.
Sae da ya kawo wajen Barrister yace Amarya ta muje ko! itadae duk kunya ta kamata Dom Saura kadan tace wa dady abarshi yayi xamanshi kawae sae kuma ta kasa magana a wajen suka wuce a bangaren unders.
Haka Ridwan ya kalleta bako kunya yace wanne size kike sawa? Na brazia da pants. Tace bansani ba yace kigayamin ko in duba. tace ka duba. kamar wasa taga Ridwan yana kokarin daga mata siket a ranta take rayawa shin shi wannan ko baisan baqar magana ba ne?
Ridwan yana nan yana kokarin bude mata xip tayi saurin bugemai hannu tana fadin me haka? Shima bata ran yayi yace xan dubane kamar yanda kika ce.
Murmushi yayyi itako ta sauke kanta a qasa yace xaki gayami ko sae na duba ne. ae ba shiri tagayamai sae da yayi murmushi yace ashe dae babytah babbace Barrister ta kasa cewa komai akan kunyarda Ridwan yabata.
Haka sukayita jibgar kaya. Ridwan yana yimata tsiya har suka gaji sannan suka fito wajen haka aka hadawa Barrister lefe kayan sawa daga lashi shadda materials atamfa English wears anhada kala dari hudu 4000.
gefen gyaluluwa kuwa kala dari biyu. shoe suma kala Dari biyu. Sarqoqi kuwa kala dari Xinari kala hamsi 50. da sarqoqi na fashion kala hamsi 50 suma.
Gefen kayan kwalliya kuwa saeda aka cika akwati 3 da kayan makeup da turarukka kawae. under wears ko sunfi dari 2 haka aka cika akwatayye har akwati 25 da kayan lefen.
Akaje biyan kuddi Ridwan zai biya kuddin dady ya hanashi yace shi zai biya tunda Allah yasa yana raye kuma yanada zarafin yin hakan.
Dady yace duk Wanda yaga abunda yakeso ya dauko sukayi sayayyarsu dady yabiya kuddi fiye da 7 million ta sayayyar.
Ba maidubu ba. ba Mama ba. Ba Baba ba.ba momy ba. Har Ridwan sae da yayi kukan jin dadin irin gatanda Dadynshi ya nunamai a rayuwa dady yace kuyi hakuri
Kiyi shuru dole inyi duk abunda yadace ta wannan auren My in-law ta can can ci inyimata komi na gata a rayuwarta.
Dom haka kudaina damuwa Ridwan ya russuna har qasa yayiwa dadynshi godiya itama Maidubu ta russuna tayi godiya aka kwashe musu kayan xuwa cikin jet dinsu. suka wuce wajen sayarda Fornitures haka aka kafa fiddo kaya manyan bed har guda goma sha biyu12 aka fiddawa Maidubu aka fiddo kujeru har set 15 da bedshit da TV guda 20 haka sae aka hadu duk wasu kayan bukata harda na kitchen aka xo biyan kuddin dady yaje biyar Baba yace ah ah wannan haqqinshine a matsayinshi na ubanta.
Dady yace bai yarda baba ya biya kuddin duka ba Dom shima ae babanta ne Dom haka sae dae araba biyu ko wannensu yabiya rabi akayi totaling kuddi suntashi naira million 20 haka dady yabiya million 10 baba yabiya million 10 Kasan cewar ko Baban Maidubu yanada kuddi amma dady yabace da saninshi gidan naira.
Nan ma sae da Maidubu tayi kukan murna da jin dadi aka kwashi kayan aka jibgasu a jet suka kwana a Dubai tunda safe suka wuce saudiyya.
Zarah ta kira Barrister sumayi fira zarah ta tanbsya mama bata fara bata komi ba gefen hakin maye Maidubu tace ah ah zarah tace kisan yarda xakiyi ki dawo gida dom muyi abunda ya kamata Maidubu tace tau ya Seeyamata Zarah tace Seeyama tana qalau Barrister tace tau ya Nuranki tace shima yana qalau Maidubu tace xan yi magana inga idan xasu yarda mu dawo a satinnan zarah tace OK ina gaida mama da Ango Ridwan da sauran jamaar gidan sukayi sallama
Maidubu na qare wayar tayo Fallon mama tasamu duk sunhallara a falon ta russuna ta gaishesu suka ansa da fararsu sannan tace......
Barrister for lifeπ
Muje xuwa wasa farin girkiππππ
Mijin Barristerβππππππππππππππβ
[13:58, 2/9/2018] Barista: βππππππππππππππβ
MIJIN BARRISTERπ
By Barrister S@dyπ
Dedicated 2 Friend of Mind Zarah Abdullahi Sokoto maman Seeyamah kina raina qawata Allah yabarmu tare ( Mrs Nura yarotella)Soyayyarki ta soke Xuciyataππ irin sosan nan Barrister na qaunar ki zarah.ππππππ
Wannan shafin nakune qawyena farincikina daku nake alfahari ππMaryam Xauro (Umar Farouq).ππ
Nana Bala( Mrs Mudassir Sadiq).ππ
Saa Alkhali tashi ( Mrs Babangida).ππ
Balkisu Maidamma( Mrs Umar).ππ
Jinjina gareku qawayen albarka Barrister ta gaisheku.πππ€
Mijin Barrister
103-104
βππππππππππππππβMaidubu ta kalli iyayenta ta sunne kai qasa "tace yaku iyayena Dom Allah inason kuyimin ixini inkoma gida Nigeria Idan baku tashi tafiya ba sae in wuce idan na isa gida NIGERIA sae in sauka gidansu Dr Balkisu kafin ku dawo.
"Baba "yace idan kin koma Mixakiyi?. ki bari mu koma tare mana.
"Barrister "tace Baba akwai abubuwanda nakeson nayi kafin.... sae tayi shuru duk sukayimata dariya. Momy "tace Kasan amaren yanxu sae sun tara qawayensu an rubuta invitations, kuma suje yawun raba Iv .
"Baba yace ah ah Nifa banasan yawun nan. mama tace yawun raba Iv kam dolene dom sae ta gayyaci jamaa sannan xasu xo duk suka ce wannan gaskiya ne.
Dady "yace tau xakije kinji my in-law, ki Bari har Monday sae jet ya kaiki ya dawo. muma xamu dawo bikinki Saura sati daya momy tace bikin gata mukeson ayi Dom haka ranarda muka dawo " D following day" , xaayi maki kamu Barrister ta sunne kai qasa.
"Mama ce ta shigo dakin Maidubu ta samu tana bacci, ta fita ta kyaleta sae da ta tashi tafito xuwa kitchen Dom girki kawae suke yi da Kansu, bayan girki komi ma'aikatan gidan keyimusu har share.
"Mama "tace Maidubu xo nan, Maidubu tabi mama sae falon mama. Mama ta bude "Fridge ta dauko wani cup ta miqawa Maidubu tace ki shanye. Maidubu na amsa ta fara sha kawae sae amai ta ruga da gudu sae toilet ta sheqa amai ta fito mama na biye da ita. Mama tace lafiyarki kuwa maidubu? Maidubu ta fara kukan shagwaba tana bubbuga kafarta kasa tana "fadin mama Dom Allah ki barshi bana iya shanshi ba dadi.
Mama ta dafe bakinta tana kallon yar'ta "tace kinsan adadin kuddin da na kashe wajen hada maki wannan hakin?, tau wallahi ki shanyeshi kafin in batamaki.
"""Maidubu ta dau cup din tana kuka ta shanye xata wuce mama ta tsayarda ita ta sake bude "Fridge ta dauko madarar ruwa ta gwango ta dauko wani gari ta kadesu tare ta dan saka sugar Kadan, ta miqawa Maidubu ta amsa tana bakin raina amma tana fara sha taji dadinshi sosae, Dom shi kamar madara da sugar ne kawae akayi mixing dinsu ta shanye tas tun ranar kullum haka mama takeyiwa Maidubu kuma ta sakata kama yin tsarki da tuwan dumi.
"Maidubu na kwance a falon mama tana waya da qawarta Balkisu tana gayamata gobe xata diro Nigeria. Balkisu ta daka uban tsalle tana murna Ridwan yashigo falon da sallamar sa.
Ya xauna kusa da ita Dom su mama suna bangaren momy suko dady da baba suna masallaci.
Ridwan yaga wani cup agefen Amaryar yarsa ya dauko yana fadin Barrister nah miye wannan? Maidubu tace maganin dajine! Ridwan ya dauko ya fara sha maidubu tayi saurin tashi xaune tana fadin karkasha karkasha Ridwan yace why nima jiya naji wuyana na dan ciwo shiyasa nasha tace karka qarasha pls mata kawae yake yiwa anfani bada maxa ba.
Dariya Ridwan yayi sae yace gaske dae naji maganin dajin da dadi tau Allah yasa haka maishan maganin take πmurmushi Maidubu tayi sannan tayi sallama da Balkisu ta kashe tace ran angona ya dade sae da yayi murmushi sannan yace Amarya kuma uwargida a gidan Ridwan sae da tayi murmushin jin dadi kalaman shi dom a wannan bangaren baa barshi a baya ba.
"Yace Barrister nah, nagafa sae kyau kike karawa gayamin miye sirrin? murmushi tayi tace ae Kaine Yakama ayiwa wannan tanbayar Dom sae wani shaiqi kake yi, dariya yayi sannan yace ni nasan sirrin Maidubu "tace gayamin miye sirrin?
Ridwan "yace sirrin kawae kikeson kisani tace eh! "yace kawo kunnenki ta matso kusa dashi "yace murmushin da kike munne saeda tayi dariya shima haka. momy ta kirata a waya ta dauka momy "tace ga mai gyaran jikinan nan taxo kixo kugaisa kuma idan kunje gida Nigeria duk gidanda kika sauka idan ayimaki gyaran jiki ki shiga daki ki kunna Air Conditioner kinji dom baason idan aka gama gyaran ki shiga rana. Maidubu tace OK momy nagode.
Maidubu na kashe wayar ta kalli Ridwan "tace momy tana nemana wae mai gyaran jiki taxo yace OK muje ko ? Suka fito tare sae bangaren momy suka shiga momy ta kalli Ridwan "tace wa Maidubu kina nan tareda wannan bita zai zai su mama duk sukasa dariya Aunty Sarah tace haba momy wae missa kike yiwa Dan qanennan namu haka?
"Momy "tace dom nima ya rainani ya mayarda dani kakarshi sukayi dariya.
Aka gabatarwa da maidubu mai gyaran jiki itama Mai gyaran jikin aka gabatar mata da Maidubu a matsayin amaryarda xata yiwa gyaran jikin. suka gaisa Dom ita mai gyaran jikin bata jin Hausa sae dae larabci ko Indiyanci tana jin turanci ba sosae ba. itako Maidubu batajin larabci Kadan Kadan take gane Kalmar larabci amma taji dadin da Matar najin yaren indiyawa Dom shikam ta iya sosae suka gaida da yaren India.
Haka take magana da Matar da yaren Indian kamar ba indiya. Ridwan ya riqe baki yana kallon yarda Maidubu ke xuba indiyanci su momy sae kallonsu suke.
Maidubu ta fito tare da Ridwan suka je wurin wasu resting chairs Suka xauna Ridwan yace ashe matata ba indiya ce. tayi dariya tace kamar yarda mijina yake balarabe ko?
Sukayi murmushi zarah ta kira wayar Maidubu. Maidubu ta dauka suka gaisa zarah tace Amarya ansha qanshi Zarah sae tsiya take yiwa Maidubu tace ina angon Dom nasan yaji dadin wannan tafiyar da kukayi Dom yanxu kullum kuna tare ko?
Maidubu tayi murmushi tace ko yanxu ko gashinan xaune tamikawa Ridwan wayar suka gaisa shima zarah bata barshi ba sae da tayimai tsiyar shidae sae dariya yake yi yace ina angonki tace yafita Ridwan yace ina gaidashi zarah tace zai ni insha Allah sukayi sallama ya miqawa Maidubu wayar.
Barrister for lifeπ
Muje xuwa wasa farin girkiππππ
Mijin barristerβππππππππππππππβ
[13:59, 2/9/2018] Barista: βππππππππππππππβ
MIJIN BARRISTERπ
By Barrister S@dyπ
Dedicated 2 my daughters Hafsat nd Seeyamahππππππππ
Wannan shafin naki ne Qawata kuma masoyiyar mijin barrister Samira Malami ( Mrs mukhtar) ππ
Nagaida Yaseerah Gwandu najinjina wa qaunar da kike yiwa mijin barrister gaisuwar bangirma ga yar mutanen Gwandu.π€
Mijin barrister
105-106
βππππππππππππππβ
"Maidubu ta dauka tana "fadin eh! goben xan dawo insha Allah! sukayi sallama.
"Ridwan sae kallonta yakeyi "yace ke ina xakije goben?
Maidubu "tace xan koma Nigeria ne! Ridwan "yace da ixinin wa? "Tace iyayenmu! "Yace banyarda ba! mi xakiyi a can? kekadae eh! "Tace haba Ridwan colm down pls. dole in komi in time I have alots 2 do.
"Nop baby kiyi xamanki kawae.
"""Washe gari tunda safe aka shirya "jet Mama ta hadawa maidubu kayan mata wadanda xata yi anfani dasu kafin suma su dawo Nigeria ta bata. Baba ya bata dubu dariya 2, "yace ko akwae abunda xata bukata kafin su dawo, suka rakata tayi sallama dasu momy da dady da yayyun Ridwan, lokacin Ridwan yana part dinshi yana bacci suka rikata har "jet ta shiga itada maiyimata gyaran jikin da bodyguards din Ridwan su 4 da driver din "jet din.
""Jet dinsu ya tashi xuwa gida Nigeria. "jet bai tsaya ko ina ba sae compound din gidan dady. suka fito mota ta dauke su sae gidansu Balkisu aka barwa Barr. Maidubu bodyguards mutum biyu sauran suka dawo Saudiyya a ranar.
Barr. Maidubu da qawarta Dr baliksu har Innah sunyi murnar ganin juna ba Kadan ba. Suka kwana a gidansu balkisu washe garin ranar suka shirya suka shiga motar Balkisu. Bodyguards dinta suka shiga motarsu sae kofar gidan Zarah.
Suka shiga cikin gidan da Maidubu da Balkisu da mai gyaran jiki. Bodyguards dinta suka tsaya gate da bindigoginsu Maidubu da Zarah suka rungumi juna suna murna maidubu ta anshi Seeyamah yanxu tayi wayo
Zarah tace qawata Kinga yarda kikayi kyau kuwa maidubu tayi murmushin tace ae kema haka suka shiga dakinda xasu xauna aka fara gyaran ciki dom gyaran fata sae sungama raba Iv.
A kayimasu hadin tantabara ita da Balkisu komi tare ake musu.
A bangaren Ridwan kuwa yana tashi yayi shiri yaje yagaida iyayenshi ya wuce bangaren su Maidubu yana shiga falon mama yaje suka gaisa zai tashine mama tace kayi waya da ita sun dauka lafiya ko? sae da gabanshi ya fadi amma ya dake yace eh! tace yawwa. Dom yayi mamakin yarda Barrister ta ketare maganarsa bayan yace tayi xamanta.
Ridwan na fitowa ya kira wayar Maidubu bata shiga yayita kira bata shiga yayi tsaki ya wurgar da wayar akan bed dinshi.
yace lallai yarinyar nan kin rainani ba Kadan ba ya tashi yayi sashen dady rai a bace.
Yana shiga ya fada jikin dady yana fadin dady meyasa akabar barrister ta wuce? meyasa baxata jira har kowa ya tashi ba mu wuce mu duka ba? dady yadagoshi sae yaga yana hawaye dady yaji tsoron ganin danshi a haka amma yadake yana fadin Haba Ridwan u have 2 b a gentleman pls.
Momy ce tashigo falon dady tana fadin My husby I miss u. tana shigowa taga dansu kwance jikin dady yana kuka momy tayi tsaye tana fadin Subhanallah!! Ridwan lafiya? Husby what's wrong wit our son?? dady yace wae Dom daughter ta wuce ne.
Momy tayi tsaye Ridwan ya tashi tsaye yana fadin dady nima xan bita xan koma gida dom inga yarda aikin gidana ke tafiya. Dom wallahi baxan iya cigaba da xama a garinnan ba duk ba dadi nakejin shi a yanxu! Dady da momy suka ce ae son sunyi maganar a tare ai ko bakaje ba aikin gidanka yana tafiya dai dai.
Ridwan ya tashi tsaye yace nidai inason inje ingani da kaina .
Ridwan na gama fadin maganar yafito falon. momy ta kalli dady "tace wae wace irin soyayya ce Ridwan yakamu da ita? ba Dom Allah yasa Maidubu yarinyar kirki bace, kuma diyar dattawa. wallahi da Ridwan ya wahala sosae, Dom irin wannan son da yake nunawa da sae ta wulaqanta shi! dady "yace Ridwan bai iya so ba, da! ba ruwanshi da soyayya, yanxu ko daya fara soyayyar ta kamashi kuma tayimai mugun kamu.
"Ridwan yana shiga bangaren shi, ya fada gadonshi yayi kwance jicce yana "fadin why baby? why baby? miyasa bakyajin magana ta, miyasa xaki tafi bayan nace Kiyi xamanki bangaji da ganinki ba, ya kara kiran wayarta bata shiga.
Ya tashi ya kira wani bodyguards dinshi "yace ashirya "jet zai koma gida Nigeria shima,. Bodyguards din "yace ranka ya dade yanxu muka dawo fa daga NIGERIA kuma jet din yayi xafi sosae .
RIDWAN ya kalleshi "yace nace ashirya min jet ko? Yayi maganar da tsawa! "yace ko zai kone a hanya inason in kwana a Nigeria yau. Idan ma na mutu a hanya shikenan kin huta shikenan sae ki nemi wanda bakya jayayyar magana dashi ba kamar ni da kika raina ba.
Ya juyo yaga har yanxu bodyguard din yana tsaye a bayanshi yace kaje kawae a shirya jet dom banajin dadin xama a garinnan ji nake kamar akan qaya nake.
Bodyguard din yaji mamakin ganin Ridwan a haka cikin bacin rai Dom Ridwan har wasa yake dasu kamar abokanshi amma yau gashi harda tsawa yake yimai hakan yasa yagaine Ridwan yana cikin bacin rai kuma yana fadin idan ya mutu ta huta ko dawa yake? oho.
Haka aka shirya jet lokacin su dady suna masjid shida Baba momy tana bangaren ta ba kowa a waje.
Ridwan yafito aka dauko mai kayanshi ya kulle bangaren shi duk bodyguards dinshi suka shiga jet shima yashiga suka dago xuwa gida Nigeria.
"Jet dinsu na sauka yashiga gida aka biyo bayansa da akwatayyensa. da kayansa suka shiga ciki aka aje mai kayan har kofar part dinshi, da kanshi yakarasa da kayan ciki.
Ya fara rage kayan jikin shi, ya kira wayar bodyguard din shi ya gayamai abunda yake raayin ci yace yaje restaurant yasayomai. Ya fada toilet yayi wanka yana fitowa ya shirya cikin kananan kaya black Jean's nd Red T'shirt da shoe dinshi Red color da wrisk watch dinshi(Rolex watch) da black cap bodyguard din ya kawo mai takeaway din ya ansa farfeson yan ciki ne. amma kasa cin shi yayi haka ya kulle takeaway din yatashi sae gidansu Barrister.
Yana kai kofar gidan yaganta a kulle yakira wayarta bata shiga haka ya juya sae gidansu Balkisu yayi hone innah ce tafito suka gaisa dom tagane shi ya tanbeta ko Maidubu na nan gidan?
Innah tace suna gidan qawarta zarah tareda Balkisu Ridwan yayiwa innah sallama ya wuce gidan Zarah kafin ya isa yakira Nura a waya suka gaisa ya tanbeshi yana gida Nura yace ya fita hakan kadawo ne?
Ridwan yace eh! Banfi 1 hrs da sauka Nigeria ba suka dan gaisa Nura yace ina nan xuwa gidan ku anjuma Ridwan yaji dadin hakan sukayi sallama Ridwan ya isa kofar gidan zarah.
Yasame taro ya turashi yayo mai sallama da Maidubu yaron yana shiga yagayama ta.
Barrister tafito sanye da material doguwar riga red da manyan fulawoyi black color perfect match ango da amarya.
Bakaramin mamaki maidubu tayi ba. na ganin Ridwan a wajen. Dom tasan yana saudiyya haka yakaremata kallo ba yabo ba fallasa yace kinkyauta Barrister kin nuna ban isa dake ba Tun da babu igiyar aurena a kanki ko?
Barrister ta daure xuciyarta dom karasowa wajen Ridwan duk da tana ganin tsintsar bacin rai a fuskar shi tana karasowa tace Haba my Soulmate kasan dole indawo inyi abunda yadace na bikinmu.
Ridwan yace dakata banason wani magana ba abunda yakawu ni nan